Showing 222001 words to 225000 words out of 304445 words

Chapter 75 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

110

mafuta" Kallonshi nake kafin na ce mishi. "Na gode sosai!" Na faɗa ina bude jakata na ciro kudi na bashi. Kallon Mamaki ya min. "Hala kin yi magana da Baba Isma'il ko?" "Ban gane ba?" Na ce mishi girgiza kai yayi ya ce min.."Ba ni kika samu ba, wani abokina ne ya wuce ma wallahi! Me kika ce zan miki ma?" Nan na sake mishi bayani, sannan na mike ina godiya. "Y'ata!" Kallonshi nayi na koma na rage tsawona. "Wannan zoben a wurin kakata na same shi ko zaki amsa in.sha Allah akwai alkhairi a tare da shi." Amsa nayi ina ta godiya, sannan na bar wurin kallon zoben nayi na nufi cikin gidan, na gaya musu yadda muka yi, bamu bar gidan ba aka fara mata rubutun, ana wankewa da ruwan zam-zam, sai a zuba dabino a ciki kwaya goma, zata na ci kullum biyu idan tayi sallah tasha ruwan rubutun yadda na musu bayani, shima Baba buzu zo ya kara musu nashi bayanin ya gaya musu sai an tsaya sosai akan cikin da ita kanta domin masarautar akwai abubuwa masu ban mamaki. Shima kanshi Sarki ban da Allah yana tare da shi Uwarsa da ni muna tare da shi da ba abinda zai hana jifar da ake mishi bai same shi ba, ya kalle shi da kyau ya ce mishi. "Ka tsaya da kyau a duk lokacin da hukunci yazo akan wannan yarinyar kayiwa Allah ka yi shiru kada ka daka ta mutane, kaf duniya su uku ake bukata su fita daga duniyar ka, daga ita, Mahaifiyarka jekariyanka, wanda yake zaune a cikin mota. Wadannan sune asalin sarki Shago idan ka rasa su kamar yaki ne aka cika. Kada ka rasa ukun nan idan ka rasa daya ya zama biyu na tare da kai, wallahi masarautarku cike yake da miyagun shaidanu tsakiyar birnin!" Wannan shine karo na biyu da naji sunan shaidanun tsakiyar birnin!.......
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 73
Tsikar jikina ne ya mike tare da Kallonshi na ce mishi. "Mu tafi ko!" Na faɗa ina kallonshi, maganar da mutumin yake ne ya hana shi tafiya haka muka yi musu sallama, Nady kamar ya bi mu, na tuna mata muhimmancin addu'a da azkar, yayi alƙawarin mikewa, karfe hudu na yamma muka iso Zanzabira kamar kada mu dawo nake ji, a gefen Mai Babbar daki na zube ina nishi. "Me ya faru? Duk gajiyar ce?" Gyada mata kai nayi ta ce min. "Kin yi kiba kuwa hankalinki kwance babu tashin hankali!" murmushi nayi na ce mata. "Kin san Nady ba gwanar magana ba ce." "Kema kuma haka ce ai idan magana bata miki ba, kinyi ta lumshe idanun kenan kamar macijiya!" Washe hakori nayi ina faɗin. "Ummina wai macijiya!" "Allah ya baki lada, kema Ubangiji ya baki zuri'a na gari. Ina cikin farin ciki sosai ko ba kome ina jin so da kaunar abinda Nadiyyah zata haifa. Wannan jinjiri ban san sunan da zaa kira shi da shi ba." "Muddansir, Muzabil, Abdullahi! Aminullah, Habibullah, Saifullah, Saiful islam, Saifuyuddeen, Abdulkarim, ABDULKADIR, Abdulhafiz, Abdulaziz. Abdul Malik!" Tsayawa tayi tana kallona ina ta lisaafo sunan da naga sun dace da Babyn Nady. "Idan kuma mace ce fa?" " Amatullah, Amatulrahman, Amatulmalik, Sayyadah Fatimah, Nana Khadijah, Nana Ummuna Maryam, Ummuna Aisha, Ummuna Ramlah, (wato Ummu Habibah) Ummuna Mariyah, Ummuna Hafsat Sawwama kawwama, Ummuna Zainab, Ummuna Saudat, Ummuna Rukayya, Ummuna Kulsum, Ummuna Hadiyya, Ummuna Asiyah!"
"Duk Waɗannan sunayen wa mutum daya za a sakawa?" Dariya nayi na ce mata. "A'a, idan aka yi dace yazo yadda ake bukata ne Umminmu!" Shigowa yayi da Sallama na mike ina mai faɗin.."Barka da shigowa." "Yawwa Maisha!" Zama yayi yana faɗin. "Na gaji wallahi!" Tiren abincin da aka kawo mana na ja gabanshi, na shiga zuba mishi ina kallon yadda suke magana mai muhimmanci da Umminsa. Sai da na zuba mishi sannan na dauki cokalin na saka mishi akan abincin, a hankali ya fara ci yana faɗin. "Barnan da suke yi ya dame su, ni na gama abinda ya kai ni Scotland dama sun san zaa bibiye badakalar da suka yi shine suka yi ta niman hanyar da zasu rufe zancen zuwan Baffa Rulwanu ya manta da zancen saboda." Shiru yayi ganin yadda Jakadiya Iyaami ta zube a gabanshi. "Ranka shi dade, akwai bakin da suke son ganawa da kai." Kallonta nayi na ce mata. "Ki je idan ya gama zan miki magana!" "Allah ya huci zuciyarki!" Ta fada tana mai barin parlourn. "Zaku koma bangarenku da Iyaami." "Ummi bata min ba kawai a barta anan." Zama mai babbar daki tayi da kyau ta ce min.."Fulani Babba, dole ki zauna da Iyaami saboda ta haka zaki san al'adar cikin gidan nan,." Gyada mata kai nayi shima a tunaninshi zan ce a'a ne sai yaji na ce mishi tow, murmushi yayi ya cigaba da cin abincin. Kara mishi nayi na cigaba da jan shi da hira, duk da hankalinsa yana tare da ni, amma nutsuwarshi tana ga mai babbar daki da take ƙara mishi nasiha, dole nayi shiru na zuba musu idanu, har suka gama Sailuba ta fito ta kwashe abincin.
Mun jima kafin muka mata sallama, bayan na ware mata tsarabatar, muka wuce zuwa gidanmu. Baa ga Nady ba sannan babu wanda ya tambayeta, haka yasa hankalin kowa bai zo akan ko wani abu aka mata ba ko ya same ta,haka kuwa da muka dawo, kowacce da part dinta ni da Nady gidanmu muna iya haduwa a haraba, sai Matarshi da ya ware mata bangarenta daban, shi yana gefenmu sai ya kasance zamu iya shiga bangarenshi ta babban gate dinmu ita ce dai bai hada mu da ita ba. Amma bakiɗaya muna compound daya ne.

Bangarena ya rako ni muka shigar da kayan kusan shi da faruq suka shigar min da kaya, can you imagine kome na gidan sabo ne fil,hatta kayan sawa kai kayan kitchen ne kawai zan ce nawa ne, amma kome ma gidan is look unique, bangaren Nady itama na laifi kome nata na can aka dawo mata da su, amma kayan kitchen da labulaye sabi ne, ya ce min bangaren Uwar magaji itama kome nata aka kawo mata wai Hajiya Mardiya ta kara mata wasu abubuwan jin labarin kome nawa sabo ne, work get then.
Abinci kuwa an zuba min ga wani store a bangarenshi na kayan abinci ne. Ya mika min key. Haka na karba ya zuba min abubuwan da zan bukata na yan kwanaki ne, saboda kada ya lalace. Ina fitowa wanka na same shi a dakin. Jan hancina yayi yana faɗin. "Shine kika yi ke daya?" "Na gaji ne kuma nasan zaku bukaci abincin dare!" "Gaskiya kam!" Ya fada yana jan towel ɗin. "Please kada ka kara gajiyar da ni zuba zan moru ba!" Shafa fuskana yayi ya ce min.."zaki moru kai kawai lalaci kike ji, gaya min me zan yi miki idan na gama?" "Na ga doya sakwara da miyar egusi zan yi." Murmushi yayi ya ce min. "Ni xan yi dakar?" "A'a ina da Bunchy mix!" Dariya yayi bayan ya kwance towel din ya ce min."bari nayi wani daka sakwaran anan duk lokacin da ya dace mu yi wanka kika yi sai kin yi wanka biyu in sha Allah!" Ya fada yana mai cillani gado anan aka fara wasan kafin wani lokaci wasan yayi nisan da ni kaina ban san yadda aka yi na ja ragamar daka sakwaran ba, tabbas yau na yarda namiji na iya lalata mace kuma ta fishi lalacewa. Eh tow ya lalata ni cikin ruwan sanyi amma ni ma na dauki fansa ta, ta hanyar kibarshi kamar na samu sakwara da ya b'ata. Juyar da ni yayi cikin sanyi da jarumta, daga nan ya shiga baza Capacity yadda ranshi yake so. Yana yi yana haɗawa da identity, bai rage min Quantity ko daya ba, amma shi kansa yasan ina da Quality. Duk da ni ce uwar gidan ba, amma yadda nake baza Capacity yasa shi jin kamar ya cinye ni danye tsaf ya tashi tsaf, kiran sallah Magariba ne ya saka
shi ya mirgina gefe yana sauke ajiyar zuciya.

A tare muka yi wanka ya shirya cikin farin jallabiya tas, ya nufi massalaci ni kuma nayi nawa kitchen na fere doya, na daura akan wuta sannan na koma daki nayi sallah, sai da na yi addu'a sosai sannan na dawo kitchen ina tasbihi, ina zuwa na cire nama da kayan ciki na wanke namar na daura a tukunya daban, kayan cikin kuwa da na wanke na zuba a pressure pot, na koma na dauko kayan miya na gyara na wanke sannan na zuba mishi a blender, na markade shi tsaf, sannan na cigaba da aiki akan man, smoke fish da stock fishi na hada na wake su bakidaya na zuba a cikin kayan cikin nan, suka cigaba da nuna. Sannan na koma kan namar miyar shima ya juye shi na soya egusi na da ridd'in, kafin na dauko ruwan naman na zuba na cigaba da soyawa suka hadu sai na juye kayan miyar nan, suka cigaba nuna sosai. Sannan na kawo nama da kayan ciki na zuba, ganda na dauki na wanke na zuba a pressure pot na rufe shima bai wuce minti Ashirin ba na kwashe saboda bana son ruwan namar, ina cikin aikin na ji motsin Jakadiya Iyaami da wasu a waje. Fita nayi na bude musu kofa, suka zube a kasa suna gaishe ni. "Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana, ga bayi muka kawo miki ko zasu taya ki da aiki!" Murmushi nayi na ce mata. "Mama iyaami sai dai ko gobe su yi sammako, amma yanzu na ma aikina! Yawwa Wildat zo nan ke zamu yi aikin da ke!" "Allah ya kara lafiya da nisan kwana.." murmushi nayi na ce mata. "Amin mu shiga!" Haka suka koma, tana son ta gaya min magana amma ganin hankalina baya kanta, ta kara buga kofar. Budewa nayi kanta a sunkuye ta ce min. "Akwai sako a wurin Wildat zata gaya miki!" "Shi kenan!" Na faɗa ina mai wucewa ciki, muka koma muka cigaba da aiki. A cikin kuwa Wildat take gaya min abinda ya faru. "Allah ya baki nasara, a wancan tsohon gidan an samu abubuwa a cikin dakinki da bayan dakinki an binne, wallahi tashin hankalin da mai babbar daki ta shiga ba na wasa ba ne, shi yasa tazo ta ganki ko kina lafiya, koda tazo aka ce lafiyarki lau. Fulani Babba kina addu'a sosai domin akwai mugaye da basu kaunarki kamar su ga bayanki amma naji Sailuba ta ce min an gayawa Abbanki ya saka anyi saukar Kur'ani sannan ya ce kada a bar kowa ya shiga bangarenki kafin ki dawo, kusan aikin da aka yi Abbanki da yan uwanki ne akan aikin har aka gama domin kada a cutar da lafiyarki?" Dakewa nayi amma tsoro yasa naji kamar na zura da gudu, haka muka gama sakwara. Na zuba mata da muka gama tayi wanke -wanke sannan ta min sallama na zuba mata ta ci a wurin,na kara zuba mata na jakadiya na ce mata. "Ina fatan kuna girki?" "Ana amsowa daga cikin gida!" "Tow tsaya ki dafa muku taliya mana!" Shiru tayi sai kuma ta ce min ."Jakadiya zata ce na roke ki ne!" "A'a ni zan dafa na!" Haka na musu jollop lokacin ana sallah isha, don ba ayi da wuri sai takwas saura, na tafi nayi sallah na barta sai da na dawo na ga bata juye ba, nuna mata kula nayi ta juye musu sannan tayi godiya ta tafi. Ni kuma na wuce nayi wanka na saka turaren wuta a gidan, ya cika da kamshi. Sannan na zauna na tsara makeup Mai sanyi mara hayaniya da tashin hankali. Kafin na dawo parlourn na kara gyarawa, ina sanye da wata doguwar riga da mayafinta irin Somalias abaya nan kampala ne, ina gyara kujerun ya shigo da sallama. Da sauri na isa gare shi ina mai rungume shi.."kin yi kyau!" "Na gode!" Na faɗa ina jan hannunsa zuwa dakinsa ya sauya kaya zuwa kanana, sannan ya fito na zubawa Faruq na shi, ashe gidan Faruq yana bayan nashi, da wasu kartin jami'an tsaro bakiɗaya unguwar aka zuba jami'an tsaro, sannan idan zaka shiga sai an bincike me yake tare da kai. Murmushi nayi kawai domin masu shiri ba zasu daina shiri ba.

"Faruq ba shi daya bane,zaki iya kara musu da nawa nan!" "Ai nayi abincin dayawa!" Faɗa ina komawa kitchen na zuba musu, sannan na kawo nuna min wuri yayi na ajiye ya kira Faruq din a waya yazo ya dauka, ni kuma na tattara hankalina akan shi muka ci abincin tare. Muna ganawa na kwashe na gyaara parlourn. "Zainab ko zaki dauko min laptop a dakina da wyata!" Wucewa dakin nayi kasancewar akwai dakin shi a kowacce bangaren, ina shiga na ga wayarshi a saman wayar an rubuta. "User" na furta sannan na dauki wayar da laptop din na kawo mishi, na ce mishi."user yana ta kiranka!" Naga ko budurwa yake nima ya boye sunanta. D'ago kai yayi ya kalle ni, ganin irin kallon da nake mishi. "Ba budurwa ba ce Yarinyar nan Ijlal ce!" Washe baki nayi ina faɗin.."Na zata kanwa ka hango mana!" Janyo ni yayi jikinshi yana faɗin. "Gaya min gaskiya irin wannan kallon fa?" "Kawai sunan!" Shiru nayi saboda kiran da ta kara yi dauka yayi ya saka a kunnensa."Lafiya?" "Dama akan maganar cikin ne ko zaka saka hannu ayi mata tiyata ne, muna asibiti tun jiya!"

"Likitan ce ta ce ayi aikin?" "A'a mune dai muka ga ya kamata a rabu haka tunda haihuwar taki zuwa!" "Ni ban amince ba;" ya kashe wayar, bai gaya min kome ba, amma na fahimci kome a tare da shi, haka iyayen Ijlal suka matsa mishi, akan lallai sai an yi aikin. Kwana biyu da dawowa kenan Aunty Sajida ta haihu, haba jama'a bakiɗaya jikina wani irin rawa yake, sanin yanzu na nuna zan shiga lamarin zai iya min tsaya sai naki nuna rawan jikina, Mai Babbar daki da kanta ta saka na shirya muka je ganin baby da namiji ne. Haka muka gaishe su muka dawo gida, ana jibi suna aka kira shi Ijlal tana asibiti, dangi da kowa na taru asibitin, kusan tare muka iso da shi, yan uwansa da iyayenta suka yi ta ƙananan magana wai kasa a danne musu haihuwar. Da yake wawuya ce ashe tabi kowa ta gaya musu namiji zata haifa, haka muka yi ta zama ga ihu ga surutu. Rike hannunsa nayi cikin nawa ina dan rarrashinsa. Can kuwa ta sake wata irin ihu tana zagin wata Nurse. Kukan baby muka ji na rungume shi a gabansu ina ruwana. Wani uwar kuka ta fasa tana faɗin.."a'a nu namiji xan haifa ba mace ba, wannan ba babyna ba ne!" Ihu da hauka da take musu yasa Nurse din suka fito waje, suna faɗin. "Waye Mijinta?" Mikewa yayi suka fara faɗin ."Doctor kai ne?" "Ina Nabila?" Ya fada yana nufar sakin, juyawa yayi ya kalle ni ya kira ni da hannu, Hajiya Mardiya ta sha gabana tana faɗin. "Ba wani ta bika salon ta yi wani abu!" Kallona yayi kafin ya ce min. "Tow muje gida!" Ganin da gaske juyawa zamu yi ta ce mishi. "Idan wani abu ya same su wallahi kotu zata raba mu da ita!" Wani irin tsawa Faruq ya daka mata, Sarkin mota ya ce mata. "Hattara dai matsiyaciya, al'ummar Zanzabira mun yi alwadai da kalamanki, ki bawa Mai Martaba hakuri ko kuma kowa ya ga tijarar da zan miki!" Ya nufota da bulala zabgagge kuwa. Zubewa kasa Yaranta suka yi har da ita suna bashi hakuri."A uwa na dauke ki,shi yasa nake shanye abinda muke yi, idan na cire wancan darajar yarinyar da take cikin dakin nan bata isa ta tsaya a inda nake ba." Ya riko hannuna muka shiga cikin dakin, wayyo Allah na. Yarinayr kyakkyawar gaske ce, wacce ta dauko Ubanta sai dai hasken fatar Uwarta. Gwanin ban sha'awa, kallonshi nayi na kalli dimple din da yake kasar habbarshi, na ga shine a kasar nata, yatsunsa da nata iri daya ne har gashin da yake kwance a bayanshi irin nata ne, juyawa nayi ina kallonshi hawaye na zuba min. "Kaga ikon Allah ko;" shafa bayana yayi ya ce min. "Dauketa ki mata huduba da duk sunan da ya miki!" "A bawa mahaifiyar dama!" "Babu wata Alfarma da xan mata, wanda ya wuce wnada na mata baki ji tace bata son Yar ba!" Sai na rasa abin ba faɗa, domin ko ina take bai kalla ba, juyowa tayi ta ga an mika min Babyn ta fasa ihu na ajiye mata Yarta. Bai kalli inda take ba na gama mata addu'a da huduba, sannan na ce mishi. "Na saka mata sunan Mahaifiyarta Hajiya Zaitunah!" "Na gode!" Mika mishi yar yayi ta rungume ta, "Allah ya rayaki, yasa sunan da kika ci ki yi gadon mai halin!" "Amin Ya Allah."
Kallona yayi kafin ya ce min. "Ina sonta sosai, amma bana jin yadda nake ji akan cikin Nady!" "Wancan saboda da dukkan zuciyarmu muka nima wurin Allah, shi yasa Soyayyar shi daban yake, wannan kuma kyuata ce lokaci guda muka wayi gari da shi, akwai banbanci a tsakanin kyauta da kuma roko, muka yi wannan kyauta ce, wancan tsantsar nima muka yi ya bamu ko ya hanamu, muna rokon shi ya bamu me albarka, sannan kowanni Yaro da girman soyayyar mahaifiyarsa yake samun karɓuwa a wurin mahaifinsa. Allah ya baka ikon kamanta adalci akanmu da Yaran bakiɗaya." Ba zan boye muka ba har ga Allah na ga rashin mutuncin iyayen Ijlal, domin kiri -kiri suka nuna yarsu tafi kome, ban damu ba, haka muka bar asibitin akan an jima zan dawo, yadda ta dake ni sai na rama wallahi, haka muka tafi gida na hada girki mai lafiya, da la'asar ina zaune Nady ta kira ni, tana faɗin. "Ashe Uwar Magaji kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login