Showing 189001 words to 192000 words out of 304445 words
bata parlourn tana can uwar dakin, ya hango ya zaune da wayar a kunnenta, tana ganinsa ta ce mata. "Tow Mama!" Ta kashe wayar saukowa tayi a gadon cikinta da ya fara girma ko nace ya girma, "Yallabai!" Kallonta yayi for while kafin ya juya ya fita yana jin kamar ya mata magana sai ya ga no way yayi fight akan Zainaba ita ce zata yiwa kanta yaki yadda take da tsiwa dole sai ita.
Study room dinsa ya wuce, ya zauna yana nazarin abubuwa dayawa kafin ya ɗan kishimgid'a, ihsinul Muslim ya dauka yana karantawa,a hankali barci ya fara fisgarshi. Barci ne yayi gaba da shi,.a wani babban farfajiya ya buɗe idanunsa, al'umma ce wanda zai san iya yawansu ba, sannan sarakunan da suka gabaci daular ce a zaune ga wani kujeran zinari da aka ajiye mishi, rike hannunsa aka yi zuwa kujeran wanda yayi dai-dai da bayyanar shi a wani daki yana kwance da kaya a jikinsa Ikhlas ta shigo, a hankali ya janyo ta. Juyar da ita yayi mata rumfar, kyakkyawar mu'amala ce ta shiga tsakaninsu wanda yana gamawa ya ga wani bakin hayaki yana fita a kanta. Bude idanu yayi daga barcin. Sakamakon kiranshi da aka yi a wayarshi, dauka yayi ya saka a kunne. "Prince we need you please!" Inji Doctor Jacob ya kira shi, tashi yayi ya nufi waje kofar Ikhlas ya rufe don Nady tana asibiti tunda Zainaba ta suma take can sai yamma take dawowa gida, lokacin da ya isa asibitin jami'an tsaro ya samu suna bincike, yana isa wurin Doctor Jacob ya mika mishi hannu yana tambayar. "Lafiya?" "Wai daga ministry of health suke an turo su bincike!" "Ina warrantee din da suka kawo?" Ya tambaya. Shugaban team din ya juya yana kallon Salamanu Farisa ai an gaya musu kada su d'aga mishi kada, idan suka isa shima su kama shi, sannan su kulla mishi sharrin da sai ya gwammace bai dawo Zanzabira ba. Kudin da aka biya aka dauko wannnan jami'an ba karami ba ne wai saboda karfin zaluncinsa ko kai ne da gaskiya ya saka ka a gaba sai ya ga bayanka, cikin wani irin isa ya nufi Salamanun Farisa an gaya mishi shi ɗan sarki ne da bai da izza. Lokacin da ya isa gaban shi, a daidai isowar su mai babbar daki da Faruq da Nady.
"Ka ce ina takardan shaidar?!" Ya fada yana dariya, "Anya kai jinin Attahiru ne kuwa? Ka binciko da kyau ko Mai Babbar daki ta ajiye wani sad'aka a waje ne...." "Tass" karar marin ya zaga ko ina na wurin, "kai waye zaka mari jami'in tsaro?" Ya tambayi Faruq da ya kafta mishi mari. Juyawa Doctor Mu'azzam yayi zuwa office can sai ga shi dauke da kujera ya ajiyewa Salmanu Faris, Doctor Bashir ya karkad'e ya ce mishi. "Mai martaba ga wuri zauna!" Zama yayi ya daura daya akan ɗaya. Yana kallon Jami'in tsaron, lema Doctor Mubarak da baya shiri da Salamanun Faris yayi Nurse da sauran Staff suka kewaye jami'an. Shiru yayi yana wani matse hannun yana bada wani sauti kas-kas. "Kai waye zaka mari jami'in tsaro?" "Shiii!" "Akai majinyata kimanin mutane dari biyu da goma, sittin a cikinsu mahaukata ne, da suka gamu da laluran tab'in hankali ta sanadin kwayoyin da kuke basu, ai dama na jima da sanin zaka zo an dauko hayarka."
Murmushi yayi kafin ya juya ga Mai babbar daki. "Ummi koma wurin Fulanin zanzabira, ki gaya mata Mijinta yana nan zuwa gare ta cikin amincin Allah." Riko hannun Nadiyyah tayi tana faɗin. "Muje Sadauki ya samu ikon sarrafa kanshi, ba iya su ba hatta mace idan ta sake tayi mishi wani hauka zai iya sakawa a rufeta har abada wannan Sadaukin da yake zaune shine jinin da na haifa shekaru arba'in baya, wanda yake da kimanin shekaru arba'in da uku a duniya. Ya bata yana da shekaru sha biyar ya rayu a gwagwarmayar rayuwa a shekaru ashirin da wani abu. Idan ina da abinda zai yi alfahari zai yi da haifar jarumi me fuskartan kowacce matsala, Madalla da kasancewar shi ahalin masarautar Zanzabira jinin da yake yawo a jikinsa tafashe take da izza yau kowa zai san ya tab'a shi." Tabbas ta yarda da kalaman Mai Babbar daki, domin Salmanu Faris da yake gabanta ba shi ne wannan mutumin mai sanyin da sanyin jiki ba. Ba shi ne na yanzu wannan da ko dazun da tayi mishi magana kamar bai ji ta ba, wannan da yanzun maganar kamar dole ake saka shi yinta. Ita ba wannan na gabanta take so ba wancan take so, wancan shine mutumin da zata iya rayuwa da shi, wannan kome na shi akan ikonsa da mulki yake, wancan ba ruwansa da mulki wancan baya son abinda zai cilla shi mulkin zanzabira. "Umminsa ki taimaka ya dawo wallahi wancan nake son gani wancan ne nawa wannan ba nawa ba ne." Sake hannunta Mai Babbar daki tayi tana me juyawa ta kalleta. "Kwantar da shi aka yi yanzu ya farka zaki ce na dawo miki da wancan? Ni uwa ce ya rayu ko ya mutu dole yayi duting dinsa, dole ya kasance yadda yake koda ba zai zama sarki ba, ina son idan yayi tsawa kowa ya ji haka! Idan ba zaki iya zama da shi a haka ba zaki iya tafiya ba matsala we are already chosen that path!" Daga haka Mai Babbar daki ta bata, a yadda take ganinsa namiji ai ko Ikhlas ce bazata zauna da shi ba, zata iya cewa ya rabu da ita kowacece kuwa.
Haka suka shiga ina zaune na kalle su. "Ummi Lafiya?" "An turo wasu marasa kunya ne su tab'a asibitin da iya shi yake ganin Abbanku!" Shiru nayi ina kallon Nady da take cikin damuwa, na ce mata. "Lafiya dai!"Girgiza kai tayi tana me sunkuyar da kai kasa. Ina zaune har bayan wani lokaci sai gashi tare da Abokan aikinsa da wanda suke sonshi da wanda basu sonshi, sun shigo duba ni. "Sannu!" Kallonshi nayi ina son ya matso, kamar yasan abinda nake so kenan ya matso gabana. "Akwai wata matsala ne?" A hankali ya rungume ni. "Lu'lu'a!" Da sauri na d'ago kai ina kallonshi. Hawaye ne ya zubo min daga idanuna, a hankali aka fara barin dakin, hatta mai Babbar daki, Nady ce na ƙarshe riko hannunta yayi a hankali ta juya tare da rungume shi. "Please ka daina abinda kake tsoro kake bani tsoro nake ji Prince na bar kome saboda kai Please kada ka kara razanani." Ta faɗa tana kuka, bai ce mata kome ba ya ce min. "Kin gamsu da abinda nake?" Gyada mishi kai nayi ina jin tausayinsa a raina.. "Yaya!" Juyawa yayi ya nunawa Nady wuri ta zauna, sannan ya zauna a gefena, rike hannuna yayi yana faɗin. "Gaya min me kike so kanwata?" "Yaya zan warke? Idan zan warke ina tsoron komawa gida kada na sake dawowa asibitin?" "Zaki warke kai! Amma wurin Mai Babbar daki zaki koma, domin ki ji sauki sai a gyara miki dakinki!" "Shi kenan yaya!" Haka kuwa aka yi bai bani labarin abinda ya faru ba, amma tabbas na ga kamar rashin a b'ace yake.
Washi gari aka sallame ni, sai dai kamar an samu matsala a wurin da zan zauna Mai Babbar daki ta ce a wuce da ni gidanmu wurin Iyayena su kara min da nasu taimakon, haka sai yasa ni jin wani irin domin kamar sun nuna gazawa ce, sai dai da zamu tafi Mai Babbar daki da ta kira a wayarta ta ce min. "Kiyi hakuri kina bukatar zama a jikin iyayenki sannan akwai maganin da na musu magana zasu nima miki ina son ki dawo Ikhlas din da na a sani ba wacce ciwo tayi bugu daya ba."
Haka yasa na ji dadi da sanyi, ta ni ake sannan naji labarin zai tafi da Nady a duba dashen kusan da ita muka zo ta ga Abba, yadda take ta kuka a gaban Abba sai ya karya min zuciya. "Abba Ikhlas bata tab'a min kome ba, asalima ni ce kishi yasa na mata ba daidai ba, Abba idan haihuwar babu alkhairi na hakura da shi fatana Prince ya dawo yadda yake. Girgiza kai yayi ya ce mata. "Shi jinin sarauta ne, kuma mun jima muna fatan jinin ya motsa, Alhamdulillahi ya motsa dole mu gani muki gani, sannan ki yi hakuri fata domin sai ya bayyana kansa." "Abba ina tsoro kada wani abu ya same shi ne!" "In sha Allah ba zasu tab'a cimma shi ba yayi nisa fa." Da wannan yanayin tayi ta kuka tana jin wani irin abu a ranta.
Bayan ta tafi Abba ya kalle ni, "Mamana ke baki damu da halin da yake ciki bane?" Murmushi nayi nace mishi. "Sadauki ai bai yi kome ba, idan aka ce za a bincika abinda suka saka ya koma haka shi ne da gaskiya ka ga kenan dole mu amshe shi a yadda yake." "Me yasa baki jin tsoron yadda yake?" "Abba kenan, shi ban tab'a ganin tsoro a idanunsa ba, duk abinda yake kai tsaye yake baya shakkar kome sau daya na ga tsoro a kan idanunsa." Kallona yayi yana jiran karin bayani murmushi nayi na ce mishi. "Ranar da aka gaya mishi abinda Khalifa shaina da Ahmad Yayari suka so yi min a ranar na ga tsoro a idanunsa, tsoro da kishi suka yi ta yawo a idanunsa. Wanda ta kai ya kusan zane ni. Amma bai zane ni ba domin shi mutum ne mai kiyayewa kuma mutum ne mai sanyi yanayinsa yanayi ne da baya son damuwa, sannan yana damuwa da duk wanda yake tare da shi matukar kana tare da shi ne domin Allah, Abba Salmanun Faris idan aka ce min ya zama sarki tabbas zan so amma zaman Sarki janyo hankalin wasu abubuwan da bana fata, zai yi mulki ne da wani irin karfi da iko. Kawai abu daya ne nake tsoro kada ya ce zai yi amfani da mulkin wurin hukunta masu laifi a mutuwar Abba mai martaba da Abba Saddam!" Ya manta da cewa yarshi yar jarida ce, ya manta da cewa yarshi ta san iya aikin sirri. "Yaushe kika fara aiki akanshi?" Girgiza kai nayi na ce mishi. "Mai Babbar daki ta bukaci haka, sannan ba iya ni daya nake wannan aikin ba, ina da masu taya ni, ai ko abinda yake faruwa yanzu idan na gaya maka waɗanda suke da hannu a cikinsa zaka sha mamaki. Abba a da nake gudunsa a yanzu ina son zama da shi domin shi ne kaɗai mutumin da zuciyata ta amince da shi."
"Zan yi duk abinda xan yi domin ki koma gare shi ki bashi duk wani irin taimakon da ya dace wannan shine karfin hada aurenku!" Murmushi nayi sosai.
FADA
Alhaji Nafi'u da Rilwanu guduwa suka yi suka bar Zanzabira aka ce sun yi tafiya, domin shi Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari bincike aka fara akanshi wanda haka ya tab'a masarautar.
Sannan Salmanu Faris ya tsaya kai da fata, ayi binciken haka yasa kafin ayi nisa Emirate council board suka ce a sauke shi, haka yasa wasu manya daga Fada suka kira shi akan lallai ya saka hannu akan yayi murabus Daga cikin waɗanda suka bada shawarar har da Alhaji Mamman Abba yayari, babu yadda ya iya abinda yasa Salamanu Faris ya dauki wannan gagarumin al'amarin saboda ya je Office din Mai girma Gwamna Musharraf har sau uku yaki yarda ya gana da shi, sai ya bada sako a bawa Musharraf din tare da mishi gargadi ya cire idanunsa a cikin fada idan ya sake ya shiga wallahi yayi kuka da abinda zai faru. Yasan karfinsa Nafi'u ne tow ya bincika ya saka su, sun gudu da kafarsu.
A lokacin da yaji wannan batun da kanshi ya kira Alhaji Nafi'u ya gaya masa, mutanen da suka turawa Salmanu Faris fa ga abinda suke yi har yazo da nufinsu. Ai wannan al'amarin ya dame su, don haka suka bashi Umarnin ya saka a fitar da Dakare, tabbas an fitar da dakare wani dogon tsoho mai yawan sumar gashi, bayan fitarsa su Nafi'u suka dawo Zanzabira, domin wani gagarumin shirin da suka yi. Tare da sakawa aka fara cin mutuncin Salmanu Faris da cewa ya cutar dasu take suka mai da kansu kamar sune masu gaskiya shine mara gaskiya. Haka aka yi ta rigima.
Ranar wata Juma'a, Abdullahi da iyalinsa suka tawo gida, abun gwanin dadi duk aka hadu aka yi ta hira da farin ciki ana murna, a fada ya zauna bai tafi ko ina ba, haka duk kwanakin da yayi shi nan da Salmanu Faris suka yi. Kamar su hadiye juna har Salamanu yana gaya mishi halin da ake ciki. "Kasan meye target dina? Dole ka ajiye aikin banki kazo ka rike Zanzabira kai zaka iya zama da al'ummar Zanzabira Nady bata son zama sarki ina son na mata wannan alfarman na wacce ta zab'e ni akan kome." Murmushi yayi ya ce mishi. "Ni kuwa kai kafi dacewa da zama sarki domin zaka iya handle duk wani case, kasan yadda rayuwar mutane suke kai fa baka yi kome ba suka gudu ina kuma da ka fara mulki, Nadiyyah tana tsoro ne kuma ban ga laifinta ba, Yaya duk abinda zaka yi ka tabbatar ka tsaya a gefen Mai Babbar daki haka zai sakata jin kamar Mai Martaba ne a gefenta. Yaya Mai Babbar daki tana cike da kunci da damuwa amma a kowa ya sani ba sai ni, tana iya ji da duk wata damuwa amma akanka bata iya ji da case dinka." Murmushi yayi ya ce mishi. "Idan aka ce yau bana nan, zata yi kuka amma idan aka ce kana nan Mai Bauchi na nan ga Aneesah da Daulah kukanta kaɗan ne shi yasa na kawo mata Khairat ta zauna da ita ina son ta yi mata irin tarbiyyar da ta mana."
A wannan ranar sun jima har bayan isha hira suke, a tare suka shiga wurin Mai Babbar daki ta ce. "Mai Kano ya na ga kafin yayanka girma ne Allah ka cika idanu kamar ba shi bane yayanka!" Dariya suka yi aka bazaje ana ta hira kamar ba gobe, a daren ya ce musu.."an gama gyara mana gidanmu zamu tafi,a can zamu kwana ga yarki nan;" ta kalli Khairat da take barci ta shafa kanta, ta cewa Uwar Yar. "Jasrah ba dole ya miki ba ko aka kawo min takwara ba ko?" Dariya tayi ta ce mata. "Ummi ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, wannan naki ne muma naki ne!" Haka suka sha hira sannan ya fita ya gaida matan Babanshi ya gaya musu zai yi hutun wata guda ne zai koma gidansa da yake bayan fata kusa da gidan Salmanu Faris. Sun mishi murna da fatan Alkhairi. Bayan sun yi sallama da su Salamanu Faris ya kawo shi gidan. Shi suka shiga cikin gidansu sannan shima ya wuce na shi. Washi gari kuwa ya dauki Jasrah kasancewar Ita Yar Garin Gombe ce, bayan sun karya wurin mai babbar daki, suka yi sallama zasu Gombe. Zama Mai Babbar daki tayi a cikin uwar ɗakinta tana ji kamar an lullube ta da danyen Nama, wani irin abu yana taso mata. Idanunta cike da kwalla, tafi awa biyu mikewa tayi ta shiga ban daki ta dauki butar da take alolan da shi ji tayi kamar an fisge butar wanda yayi dai-dai da bugun zuciyarta salati ta shiga yi sannan ta fito jin wayarta yana ringing. Tana fitowa wayar na tsinkewa sake kiran aka yi ta dauka. "Mun gama da daya da iyalinsa, saura biyu haka zamu bisu daya bayan daya muna tura su ga Attahiru yayari yanzu zaki san abinda ake kira Fansa ni nan na fito surukanki kuwa mun turawa Yaranki da al'umma da Ubanta hoton bidiyo tsiraicinta, ba wannan ba ne abin burgewan kin ji yadda muka dauki muryan danki yan ihu ceton rai.!" "Innalillahi wainnalihir rajoun, Innalillahi wainnalihir rajoun Ummi Yaya Sadauki, Mai Bauchi ku zo ku kawo mana dauki Ya Allah ka kawo mana dauki!" Can ta ji muryan Jasrah ranka faɗin "Dady ka taimake mu wuta dady!" Idanunta ne suka daina gani ji da ganin sun tafi lokaci guda.......
(Maybe next page ku sha mamaki abubuwa dayawa zasu faru a ciki kuwa har da abinda kuke ta jiran ayi.muku 😅😂🤣🥺🤔Allah sarki ajali ya kawo Mai Kano)
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 63
Tashin hankalin da Ahalin Yayari suka shiga ciki babu wanda zai gansu yayi tsammani zuciyarsu zata farfaɗo domin wani irin gigita suka yi lokacin da aka samu mai Babbar daki a sume, a lokacin Aneesah ta kawo rahoton abinda ka tura mata don gulma da tsugudidi, shine tana zuwa ta ga mai babbar daki kwance, kuma ta ga videon, amma ita kanta Mai Babbar bata ga wani abu ba, wannan yasa ta shiga ihun Ikhlas ce ikhlas ce.
Tun da aka kawota asibiti har yanzu babu wnada yasan Abdullahi ya rasu, ga Khairat da take jikin Daulah tana ajiyar zuciya saboda ganin Mai Babbar daki a kwance. Karfe daya da wani abu. Mai Napep ya sauke ni, tun a gida da abin ya bazu Abba ya ce kada a bari na sani, ina kwance jikina ba karfi sai ga kiran Uwais, ya ce min. "Autar Maluma kin ga abinda yake faruwa?" Tashi nayi zaune ina faɗin. "Ni da bani da lafiya mai zan sani?" "Ok amma Tabbas akwai abinda ake boye miki matukar Abbanku bai gaya miki ba." Gajiya nayi da jin zancensa na kashe wayar na kira Yeemar. "Ya jikinki?" "Me ake boye min wani abu na faruwa ne?" "A'a ba kome kai ban sani ba;" "Yeemar don't try fool me, idan na ji wani abu na faruwa ba