Showing 195001 words to 198000 words out of 304445 words
ya cika min idanu. "Ban gane ba? Dole sai da ni za ayi nadin Sarautar? Dole sai..." Shiru nayi saboda yadda ya tawo tare da fisgo ni jikinshi, na dirko daga gadon kamar xan fad'i kasa, murmushi yayi sannan ya ce min. "Kika kara d'aga min murya sai na yanke harshenki, na gaji da rashin kunyarki!". Shiru nayi saboda yadda naji tafin kafana akan kafarshi, which mean ya daura ni akan kafarshi, saboda kada na taka kasa, d'ago kai nayi a hankali ina kallonshi. Tab'e wuyata yayi a hankali naji kome ya tafi ban kara sanin kome ba.
Kwantar da ni yayi sannan ya riƙe hannuna, "Na rantse da Allah ni nafi kowa sanin gaskiyarki, amma dole na bawa ahalin masarautar Zanzabira kariya da kuma ke, kiyi hakuri da abinda zaki gani ko zaki ji daga gare ni, rayuwarmu ce tana cikin wani irin kulli. Idan kome ya dawo dai-dai zan rayu dake har abada amma a yanzu dole na saka katangar karfe a tsakaninmu!" Ya furta a hankali yana sumbatar hannunta, anan ya kwana ya sha kira a wurin Ijlal domin tunda abin ya faru ta gama sakawa a ranta Ikhlas ta gama zama da shi, haka a duk lokacin da ta nufi Mai Babbar daki, kukan Munafunci da nuna mata tana jin ciwon abinda Ikhlas ta aikata, Mai Babbar daki bata gani ba amma yadda ake fadar abin yasa tayi kunnen Uwar shegu da su, sannan ta kira Baffanta ta gaya mishi. Murmushi yayi ya ce mata. "Ban san me Allah ya shirya a zamansu, amma ki ji a ranki su din kamar rayuwa da mutuwa ce, dole mutuwa ta fatauci rayuwa, haka dole rayuwa tayi ta fadi tashi domin ta rayu kin ga kenan dukkansu ababe ne da Allah ya wajabta wanzuwarsu a bayan kasa zuwa wa'adin da Allah ya diba musu, don haka ya rage gare ki. Ki yi hakuri sannan ki toshe kunnenki, itama Yarinyar tana fama da kanta ne, jinyarta sai shi domin Matsafa suna bibiyar lamarinta, sannan wani abu da nake ta son gaya miki ki zo Farin ƙasa."
Shiru tayi kafin ta ce mishi."Baffa zuwana farin kasa kamar wasa ce da rayuwata, ana Bibiyar lamarina da na iyalina." "Shi kenan amma. Allah ya rufa asiri akwai abinda na ke son gaya miki dangane da abubuwan da suke faruwa ne, wasu daga cikin gidan sun nime na saka baki kada ki saka kanki cikin rigimar da aka fara kwanaki ban samu na kiraki ba amma tabbas haka yana da nasaba da mutuwar Bawan Allah!" "Na jima da sanin haka, sai dai ban san me Allah ya shirya ba . Allah yasa mu dace!" Suka yi sallama, shiru tayi kafin ta ce a hankali. "Baffa ya san zasu kashe Abdullahi amma bai gaya min ba, wato ina shuka a idanun makarwa abinda Adade ta gaya min kenan ban fahimta ba ., tabbas akwai dalilin bibiyar Ikhlas imma Baffa ya sanar musu da wani abu akanta ba zai yiwu daga waje ake Binta ba, daga cikin gidan nan ne? I miss something!" A hankali take zaga gidan tana kara nazarin me ta manta a cikin abubuwan, "rundunar shaidanun tsakiyar birnin, da wasu daga cikin gidan sarauta sun hada kai, wanann a cire Rilwanu da Nafi'u ba iya su kad'ai bane abin zargi, tun daga lokacin da aka sumar da Ikhlas ya dace ta dasa ayar tambaya amma bata yi wani abu a kai ba. Sai yau magana Baffanta yasa ta tunawa she miss spot Mai muhimmanci. Ko jiya da Malam Junaid yazo ya gaya mata a yanzu kada ta yarda da kowa kada dogon magana ya haɗa ya hadata da kowa, kenan hatta bayin gidan da sauransu akwai wanda bakinsu ɗaya. Wani irin sanyi jikinta yayi abu daya kawai ta sani Yaranta da iyalansu dole ta bawa rayuwarsu kariya musamman Ikhlas bata damu ba da duk abinda za a fada tayi taki mai da hankali akanta ne gudun kada wani abu ya kara faruwa domin suna farautar rayuwarta, burinta yanzu Salmanun Faris ya karbi kujeran Mahaifinsa.
Bayan addu'ar Uku da yake an zo ta'aziyar rasuwar Abdullahi din manya mutane ciki da wajen kasar musamman da aka san kanin Famous Doctor Faris Attahiru Yayari ne, sannan mahaifinsu ma an san wani babba ne, haka yasa aka yi ta zuwa ta'aziyar har tsawon kwanaki uku da aka yi addu'ar uku.
Karfe goma na safe ya shigo cikin wata hadaddiyar shadda Dark blue, ya zauna a gabanta yana gaishe ta, murmushi tayi tana faɗin.."Ina yarka?" "Tana wurin Daulah ban ji muryanta ba." Jinjina kai tayi sannan ta ce mishi. "Ba zan maka dole ka zauna da Ita ba. Amma ni idan da ina da iko da xan zo ka zauna da ita, mace irinta ake bukata kawai idan aka cire rashin kunya da wasu abubuwan mace ce da ake bukata, Matar Ubanta Hajiya Turai tazo min da wani al'amari da ya bani mamaki, Amma kuma sai na ga hakan ba kome ba ne a sha'anin rayuwa. Ga wannan takardan na saka abokan aikinka su nima min kuma Alhamdulillahi sun samo min shekaranjiya da suka zo ma musu magana, jiya ba ka zo ba suka kawo min shi cikin girmamawa." Tura mishi takardan tayi. "Ina son ranar da Abdullahi zai cika kwana arba'in zaka tabbata Sarki a cikin garin nan bakiɗaya!"
"Ummi!"
"Na yanke hukuncin kuma idan aka yi la'asar na saka Mai Bauchi ya tura musu sakon nan da wani lokaci Emirate council board zasu bukace ka. Ba iya shi ba na sake zubawa kifi abinci domin nayi babban kamuwa, wanda i don't care to sacrifice my own life akanka!" Ta fada tana nad'e hannu a kirji, "sign!" Ta nuna mishi takardan. "Ummi akwai hatsari!" "Ai tunda suka kashe min d'a aka kawo min gawarsa ka ga nayi kuka? Na razana babu karya amma ya mutu a matsayinsa na sadauki kuma Uba, idan da za a bani zab'i da zan zaɓi ya rayu na mutu domin duk lokacin d ana kalli yarshi zan ji my fail as gran Mother, na gaza kare iyayenta. My duties is not about alumma harta Yarana na cikina dole na kare rayuwarsu zan yi yaki da kowa domin rayuwarku ta yi tsawo!" Yadda tayi maganar zai tabbatar maka daga kasar zuciyarta ce ba daga waje ba ne, tsaf ta shirya domin isar da sakon da take bukata..
A cikin kwanakin aka sallame ni, gidanshi na dawo, nan ya dace mu karasa. Don haka na mai da hankalina akan lafiyata, sai dai kuma yadda nake rayuwa a cikin gidan akwai damuwa domin dakina dai yana son ya gagare ni, bana iya barci ga zazzaɓi da yawan mafarkai. Haka yasa na gaya mishi, amma abu daya ya gaya min. "Mutumin da ya manta da Allah ba dole ya ga rayuwa ba, hala baki tsayawa ki yi ibada tsakani da Allah ne ya janyo haka." Sai na ji na tsani kaina da kaina. Na kalle shi nayi murmushi tun daga ranar nake yawan sallahn dare da kodayaushe zaka same ni da Alqur'an, haka yasa ko barci nake da karatun Alqur'ani haka ya samar min da nutsuwa da kuma saukin mafarkan da zazzaɓi, wannan rashin jituwar yasa na fahimci yadda Ijlal take amfana da shi ga Nady ta koma ganin likita, sau rayuwar ta koma min kamar xan mutu ga wulakanci ga na shi ga na matarshi idan nayi magana ya ce min. "Ita biyayya take min, saboda iyayenta sun isa da ita akan me zan hanata karban kanta. Idan kin matsu ki wanke kanki!" Ya fada yana cigaba da aikinsa.
Haka na cigaba da hakuri ranar da na gaji na bishi dakinsa, Matarshi tayi ta ihu tana faɗin zata mutu, haka dai ranar ka hakura da shi, sai ya kasance duk ranar girkina haka take min, saboda cikinta ya girma shi kuma yana biye da ita. Satin Nady uku sai gata ta dawo daga yanayinta na fahimci anyi nasara, ni ta fara gayawa. "Sun ce dashen yayi kodayaushe zan iya daukar ciki! Allah yasa na samu Baby Boy na saka sunan Abba! Ya min abinda ko iyayena basu min ba. I'm sorry Zainab ba iya rayuwar Prince kika bawa taimako ba hatta ni kin taimaka min, ni dai koda na haihu kece zaki rike min Yarana!" Dariya ta bani nayi ta dariya har kamar xan tintsira! Na kalle ta ina faɗin.."Hmm tow Allah ya kawo yan biyu!" Rashin zaman lafiya ta da Prince sai ya sake haɗe kanmu da shi, haka yasa Ijlal take ganin kamar muna wani abu bayanta. Wanda daga ni har Nady harkan gabanmu muke, saura sati Abdullahi ya cika kwanaki Arba'in ya kawo Yarinyar Nady ta ce ita fa she is not babysitting, kuma da gaskiyarta nata ma tana faɗin idan ta haifa Nanny uku zaa dauka daya mai yi da safe daya dare, daya wuni. Dariya nake mata don haka wurina aka kawo Yarinyar ba sai ga Ijlal tana Bala'i an kawo Baby Khairat an hanata ba, yarinyar nan rigima har gaban Mai Babbar daki. Kallo daya ta mata cikin mamaki ta ce mata. "Ke yanzu da renon cikinki zaki ji ko da Renon Khairat? A wannan lokacin da kike dama da kanki? Don Allah ki yi fama da kanki bana son Magana ita Zainab bata kome bata da kome zata fi kula da ita!"
Cikin jin haushi ta ce mata. "Ina matar da take bin wasu mazan a waje zata kula da Yarinya har ta mata tarbiyya?" Kallonta Mai Babbar daki tayi ni kaina naji kunya, balle ita murmushi tayi ta ce mata. "Ita mace mai bin maza bata iya zaman aure ne? Sannan ina shaidarki?" Shiru tayi can ta ce mata. "Zainab kin amince da abinda ta faɗa ko kina niman hakkinki!" Kaina a kasa nace mata. "Ummi a bar maganar sai ta haihu zan nime hakkina!" "Shi kenan Allah ya kai mu! Zaku iya tafiya." Haka ta sallame mu yana parlour muka fito shima ya shiga tare da yarsa. "Ka ji tsoron Allah, idan ka san kana zaluntar Zainaba ka daina domin na ji kamar akwai abinda take hangowa kada ka saka na ji kunyarta wata rana da zata bude baki tayi magana!" Kunya ce ta kama shi, ta ƙara da cewa. "Tsakaninka da Allah ka tab'a kamata da ha'intar aurenka?" Girgiza kai yayi alamar a'a, "Me yasa matarka bata da kima a idanunta? Hmm!" Ta ce tana mishi alamar ya tafi kawai.
Bai yi magana ba, amma yadda ta tara mu a parlourn ya mana kashedi da mu daina cutar da juna ya bani dariya, yana gamawa ni da Nady muka bar parlourn, a ka'ida nady zai yiwa kwana biyu, amma kwana ɗaya yayi mata ya koma dakina, nima kwana ɗaya yayi ko nace a dakin Ijlal yayi shi domin ihun da take yi sai da suka tafi asibiti, idan ka zauna da kishiya makira sai ka yi da gaske domin ba zaka tab'a yin fari a idanun namiji da danginsa ba, haka ranar Addu'ar ya kusa aka kira shi aka mishi duk wani abinda ya ya da ce, sannan suka ce idan aka yi Addu'ar arba'in zasu nad'a shi sarki washi gari ranar laraba, sai bakiɗaya da labarin ya zo muka shiga wani irin yanayi n afarin ciki da kuma bakin ciki. A kaf tarihin rayuwata zan iya saka Umminsa a matsayin Jarumar Uwa, domin sai da ta gana da manyan mutane har zuwa fadar shugaban kasa, haka ya bawa danta lasisin kafa shi, sannan ta kuma janyo manyan dattawan Zanzabira da suke siyasa ta cusa musu ra'ayin marawa danta baya ko yau aka dauke shi bata yi yaki a banza ba, ana saura kwanaki ƙalilan ya tafi yayiwa shugaban kasa aikin ƙwaƙwalwa ba shi shugaban ba dansa Rufa'i ba sai ga shi an yi nasara ba, Mai Babbar daki tana da hanya tana da sani Mijinta bai mutu haka kawai ba sai da ya shigar da Matarshi cikin manyan mutane, sannan ta kuma janyo kungiyoyin lauyiyon kasa jikinta kasancewar Shugaban lauyoyi mata, Madam Alhaja Kudirat Obafemi Oloyokayemi kawarta ce tare suka yi makarantar bodi har zuwa kwalejin ilimi na kasar kafin suka rabu a matakai na rayuwa sun hadu da ita ta kuma mata alƙawarin matukar tana raye zata bata gudummawar a duk buƙatarta domin A lokacin ita Mai Babbar daki ta janyo musu mutunci da kare kai domin sai da aka san suna tare da Princess sannan kuma wacce ake kyautata zaton zata auri crown prince,haka yasa har suka gama makaranta basu fuskanci matsala ba, sannan ba a wulakantasu ba sannan ita bata zuwa amsar abinci sai dai a kawo mata, wanann yasa suma suka zama yan gata, sai gashi ta zama shugaban ƙungiyar lauyoyi na kasa.
Shima yana gama aikin ya dawo gida, ranar talata aka yi addu'ar arba'in din Abdullahi, aka raba kome na shi Mai Babbar daki ta cewa Barisater Sham'au yar Kanwata Mariyah kuma kawar Jasran ta saka hannu, domin ta zama shaida ta barwa Khairat dukiyar da aka cire mata, sannan ta ware wasu kuɗaɗen ta saka a cikin na Abdullahi ta barwa Yarsa da yake ya saka kome na shi yarsa ce, kin dinsa sai gashi ya bar wasiya da kome nashi a cikin dairy dinsa aka yi amfani da shi aka barwa Yarsa har zuwa girmanta.
Bayan isha ina gaban Madubi na bar Khairat a wurin Jadda wato kakanta, muka dawo gida yanayin ya bada kalar za ayi ruwa, ga wani zafi da ake yi haka nayi wanka na fito daure da towel, shi kuma ya shigo kenan, Haba Malam ya zo yin rashin mutunci sai ya same ni ina shafa mai a cinyata da bayana. Mantawa yayi da abinda ya kawo shi ya dauke ni cak yayi gado da ni, ba nace ban yi kewar yadda yake sarrafa ni ba domin jikina da zuciyata sun azabtu da rashinsa, ni kaina jikina rawa yake. Na amince yayi kome. Ihun Ijlal muka ji tana faɗin wayyo Allah zata mutu, haka yasa muka rabu, sannan ya fito na saka kayana ai tasan a wurina take ina jin Nady tana faɗin. "Wanann iskancin baki tashi yinsa sai ranar girkin Zainab zaki gamu da Allah munafuka kawai!" Dakinta kaita suka kare a can.
Kwana nayi ina juyi domin zuwa yanzu ina son naji duminsa amma ba hali, haka nayi ta kuka kamar raina zai fita, dakyar barci yayi gaba da ni, wurin karfe uku na tashi nayi sallah dare, na gayawa Allah kukana.. kafin na kwanta, washi gari sai da na makara domin hayaniyar mutane ya tashe ni, haka nayi sallah a gurguje na shiga kitchen na cigaba da aikin cake din da na yi tun jiya duk da babu wani shagali. Amma hidimar da muka yi ba na wasa ba ne.. har gida aka zo aka yi mana hoto har da shi, kowacce anyi mata biyar da shi kala daban daban, sanye da kayan sarauta.
Ina aiki na gama hada zufa na tuna alƙawarinmu yau zai cika, haka yasa na gama kome akan lokaci kitchen dina na rufe a can bayan waje ana ta girki.
Saura awa biyu a tabbatar da shi Sarkin Zanzabira, haka ya bani kwarin gwiwar cika alƙawarin da muka daukawa juna, duk wuya zan bashi goyan bayan har ya samu damar tsayawa akan kafarshi, shi kuma zai bar ni na tafi ga Ya Uwais. Haka yasa na tashi a tsannake ina kallon madubin dakina,.ina gyara zaman rigar jikina, sannan na nufi waje, tun a babban parlourn na ga taron yan uwansa suna ta shewa. Cikin girmamawa na gaishe su kasancewar dayawa sun girme ni, wasu sun amsa da daɗin rai, wasu kuwa ko inda nake basu kalla ba, haka ya bani damar wucewa a tsanake. Ina cilla jelar mayafina a hankali, ina jin yadda suke kwashewa da dariya, haka bai wani dame ni ba. Shi dai da yace ya ji ya gani wurinsa zan nufa, basu gabana Allah na tuba rayuwar da na gani a cikin gidan ai yanzu sai dai ya ji kome ya fita a kaina. Lokacin da na shiga parlourn shi Madam Ijlal na samu da me kwalliya, yadda ta haɗe rai ya kara bani damar dauke kai,.ban ma kalli inda suke ba, na nufi bangaren shi ita ta sani. A bakin kofar na tsaya ina sauke ajiyar zuciya nayi na nufi cikin dakin da sallama, babu haske a dakin sai yar side bed lamp. Mai dan duhu abinda ya faru shekaranjiya ne ya dawo min kaina da sauri na kunna wutar dakin, hango shi nayi kwance da gefen gadonshi, daga shi sai farar wandon shadda, ga kayan da zai saka a kan gado, wandon ne,kashe wutar dakin nayi na nufi inda yake, da dan hasken yake haska fuskarshi. Zama nayi akan gwiwata a dan hasken naga yadda fatar idanunshi ya motsa. A hankali nace mishi. "Yau alkawarinmu zai cika!" Mika min hannu yayi, na mika mishi janyo ni yayi ya kwantar da ni a jikinshi ya ce min. "Ina ta jiranki je ki yi alola ki zo ina jiranki." Ba musu na mike na shiga ban daki nayi alolan ina fitowa na samu ya mike, sallah ya ja mu na raka'a biyu sannan yayi addu'a a tunanina murnan wannan ranar yake anan shi mutumin bashi murnan daban, rike kaina yayi ya min addu'a kafin ya janyo ni jikinshi ya tambaye ni.."kin ci abinci?" "Eh na karya!!" A hankali ya juya gefen gadon ya mika min madaffen madara ya ce min. "Sha." Ba musu na sha tas na mika mishi kofin, yadda ya janyo ni yana min wasu salon yasa na ce mishi. "An kusan fa!" Bakin shi ya haɗa da nawa ya shiga tunatar da ni yanayin da muke, a hankali abubuwan da nake tsammanin zai wuce minti goma zuwa sha biyar suka fara zungure minti talatin, sai da