Showing 1 words to 3000 words out of 304445 words

Chapter 1 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

128

[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: A ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍

*Wannan littafin mallakata ce, ban yarda wata ko wani ya juya min shi ta wata hanya ko kuma ɗaukar wani bangare na labarin, domin yin haka zai kai mu ga tsayawa a gaban kuli manta sabo*


Warning 🔞🚫
_Ban yi don cin zarafin kowa ba! Idan yayi kama da rayuwarki ko naka, a dauka arashi ce gari da sunayen da za a ambata kirkira ce! Don haka a kiyayye fassara labarin ta kowani siga na daban!🔥_



*Shimfid'a*
_Cikin tsananin dare wanda ake kira sulisin, wanda baka jin motsin kome sai na kwari da duhu me tsananin gaske! Anyi ruwa gari yayi tsit baka fahimtar kome. Takun mutane ne dasu ka haura goma karti majiya karfi da lafiya. A gaban wani tsohuwar mota suka tsaya! Kasancewar wutar motar tana kunne! Fitowa wani mutum yayi! Ya tsaya a gabansu! Zubewa suka yi a gabanshi tare da dukar kirjinsu! "Mun mika rayuwarmu da mutuwarmu gare ka Gwaska dakare!" Suka fada tare da dukar kirjinsu! "A kashe shi a shafe min tarihinsa" ya fada kafin ya koma cikin motar ya zauna sannan aka tashi motar daga dajin! Sai da ya bar wurin sannan suka mike sannan suka nufi gaban bukkarsu! "Me yasa kuka kama ni? Me kuke so nayi?" "Shamuwa kai da Ungulu ku karasa kome!" "An gama dokaji!" Daukar shi suka yi suka fita sai da suka yi tafiyar awa uku wuraren asuba. Abokin tafiyar ya rike shi da wanda suka dauka ya ce. "Shamuwa idan muka yi haka bamu yi adalci ba! Eh an yi mana laifi amma kashe Yaron nan ba shine mafita ba, mu kyale shi ya rayu amma kada ya dawo Zanzabira!" A razane ya ce mishi Shamuwa ya ce mishi. "Hauka kake? Kashe mu zasu yi!" Dariya ungulu yayi ya maida mishi da cewa "Allah ba zai basu nasara ba! Kashe Yaron ba shine zai bamu yadda muke so ba!" Musu ce ta kaure a tsakaninsu. Yana jin su, "tow me kake so mu yi?" Inji Shamuwa "Yawwa kasan me zamu yi? A gaban kaɗan akwai inda iyakar Zanzabira da kasar Chiyya! Mu san yadda zamu yi da shi!" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mishi! An gama_


01..
Life or death ☠️

Yau ma kamar kullum cike da so da kauna suka tashi don iya wannan lokacin suna jin kamar sunfi kowa sa'a da dace ne, domin tun farkawansu sallah asuba ya tafi massalaci, ya batar a dakin bata tashi don yin sallah ba, ta cigaba da barcinta, bai shigo gidan ba sai karfe bakwai saura domin daga massalaci jogging ya tafi duk da kasancewar shi likita ya san abinda zai yi ya kara mishi lafiya da kuzari, bude kofar dakin yayi ya samu tana ta sharar bacci son ranta, zuba mata idanun yayi yana jin babu dad'i. Sai dai bai san yadda zata amshi bakon lamarin da yake tun karo su ba. A hankali ya ja kofar dakin sannan ya nufi study room dinsa, ya bude tare da shiga dakin, zama yayi yana kallon tarin littattafai da suke makare a dakin. Hade hannunsa yayi wuri guda sannan ya daura fuskarshi akan hannun yadda zai bashi dpamar tsayar da fuskarsa a kan hannun. Nazari yake yana kara son warware rikicin da ya kunno kai, wanda sanadin haka abubuwa ne dayawa. Mahaifinsa yana can kwance dai kwaikwai mutu kwaikwai. Alhaji Saddam ya rasu, a sakon da ya shigo mishi watanni baya, sakon mahiafinsa ne amma murnin da ya bashi yayi mishi nauyi, haka yayi yadda ya ce. Sai dai kuma madadin dawowar ta zama alkhairi sai gashi yana fuskartan wata irin tafiya da bai san yadda zai iya daukar ta ba. Idan ya fahimci mahaifinsa abinda ya roka a gare shi Rayuwar Malam Junaid Gobir zai kare bayan ya tsaya an daura auren da ya kasa gane da waye da a daura. Shafa kanshi yayi yana me juyawa ya fuskanci window dakin, ana tsammanin ruwa kowani lokaci, don haka ya mike ya bude window dakin, ya tsaya yana hango bayin gidansa da na can cikin gida. Komawa yayi ya zauna yana kallon window, karar tawowar mota gidan ya sa shi mamaki da sassafen, amma bai yi mamaki ba don da ya tabbatar Fulani karama da Mai Kano sun bar garin ya samu nutsuwa, iskar bakinshi ya fesa, buga kofar dakin aka yi cikin jiran umarni, ya ce. "Na'am!" "Prince kayi bako!" Shiru yayi na wasu dakikai, kafin ya ce mishi. "Waye?" "Dattijo Salama ne." Shiru yayi na wani lokaci kafin ya ce mishi. "Kai shi parlour!" Ya fada yana me mikewa daga kujeran dakin karatun, ya fito a hankali ya nufi hanyar koridon da zai kai shi parlour, ta huji-hujin ya hango fuskar dattijo Sallama, a hankali ya isa dattijo Sallama ya mike tare da cewa. "Barka da asuba ranka shi dade, likita bokon turai." Bai ce mishi ci kanka ba, ya daura ɗaya kan daya yana kallon sallama. "Meke tafe da kai?" Salmanun Faris ya tambaye shi, yana kad'a kafarshi. "Dama akan maganar yar gidan Junaid Gobir ce na zo a wasiyyar da Mai Martaba ya bada ne ya ce na kara tuna maka ka tabbatar ka." "Bayan nan fa?" Ya cilla mishi tambayar, "Hmm Allah ya kyauta dama ina son na gaya maka ne ka yi nesa da Junaid domin ana zargin yana da hannu a rasuwar Saddam da kuma matsalar Mai Martaba. Sannan ya fito da batun auren Mai Martaba da Yarshi kowa ya ji haka yasan da lauje a cikin nad'i" D'ago kai yayi ya zuba mishi idanu, sannan ya ce. "Na gode zaka iya tafiya!" Yana fadar haka ya mike zai bar parlourn. "Tow na gode." Jin kalmar bata yi mishi kama da wanda yayi godiyar ba, ya juya yana kallon shi. "Da akwai magana ne?" D'ago kai yayi zai magana, amma kwarjinin da Prince Salmanun yayi masa sai ya tsinci kanshi da cewa.."A'a babu kome Allah ya baka nasara!" Duk da ya fadi haka amma ya kasa fita daga cikin gidan, murmushi Prince Salmanun yayi kafin ya ce mishi. "Da wani abu ne?" Zubewa yayi akan gwiwarshi duk da shekarunsa ya ce mishi. "Allah ya baka nasara." Takowa yayi yana me isowa gabanshi. Hannunsa daya a cikin aljuhun wandonsa ya ce mishi. "Baba Salama ban san me kake bukata ba? Sannan asalima ban fahimci inda ka dosa ba. Ko zaka iya fada min meke faruwa?" "Wato abinda nake son ka fahimta, shine kada ka amince da Malam Junaid Gobir, domin munafiki ne." Yayi shiru yana zare idanu kafin ya kara da cewa. "Tunda Saddam ya rasu, mai martaba yana halin jinya shi kenan bawan Allah nan yake fita daga duk wata alaƙa da wadannan bayin Allah, duk da naso na gayawa mahaifinka halin da ake ciki amma na kasa samun nasarar haka, domin yaki fahimtata. Gani yake kamar bana son Junaid!" "Na gode sosai!" Ya fada tare da juyawa yayi tafiyarsa. Shi kuma Baba Salama Faruq ya fito ya tisa keyarshi waje. Zama yayi ya yana juya kujeran study room din. Shigowa Faruq yayi yana me fadin. "Ya tafi ranka shi dade!" "Ina son ganawa da Imam Junaid Gobir!" "An gama yanzu ko yaushe?" "Ka tuntube shi tukun!" "An gama!" Juyawa yake a hankali. Zaro waya Faruq yayi ya kira Layin Malam Junaid Gobir. "Waalaikumunsalam, Malam eh ni ne.". Daga can ya ce mishi. "Masha Allah ya mai gidan naka?" "Lafiya lau dama shi yake niman alfarman ganawa da kai!" "Masha Allah ka ce mishi, mu hadu karfe biyu na yamma a bakin kofar gidan gonar Mahaifinsa." "In sha Allah zan gaya mishi." "Tow na gode sosai!" Kashe wayar yayi yana faɗin. "Ya ce ku hadu gidan gonar Mai Martaba, kamar yadda ka ce." "Shi kenan zaka iya tafiya." "Na gode ranka shi dade!" Fita yayi yana me jan kofar a hankali ya rufe, sannan ya bar cikin gidan zuwa kofar shiga gidan. Anan yake tsaye kafin ka shiga cikin gidan sai ka fara ji da shi ko ya ji da kai.

Prince tashi yayi a kujeransa ya shiga zaga parlourn, yana nazarin wasu abubuwan da suke zuwa mishi da bai saba gani ba. Hannunshi dukka biyu ya zuba a cikin aljuhunsa ya d'aga kai sama. Yana nazarin yadda lamarin amma sai yake ganin abin ya fara wuce tunaninsa sai ya hadu da Imam Junaid Gobir zai ji meke faruwa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya nufi waje, daga yadda yake jin motsi a kitchen yasan suna aikin hada abin karyawa ne, wucewa dakinsa yayi har lokacin tana barci wurin karfe takwas. A hankali ya buga wurin kwanciyarta bude kananan idanunta tayi masu zubin na yan japanese, tayi tare da gyara kwanciyarta. "Wake up!" Ya ce mata, mika tayi wanda ya janye bargon da take lullube da shi, wani munafikin rigar barci ne wanda bai da banbanci da babu. "Prince jiya!" "Je kiyi sallah!" Shiru tayi tana faɗi a ranta. *Limamin madina ashe shi yasa yake hade rai* ta mike tana faɗin. "Sorry Baby kasan ban yi barci ba ne nayi ta jiranka." Shiru yayi yana me cigaba da haɗa kayanshi na zuwa office, ban daki ta nufa. Sai da tayi wanka tayi alola sannan ta fito ta dauki jallabiyarshi ta saka, kafin ta gabatar da sallah asuba, bayan ta idar shi kuma ya shiga wanka daukar towel din tayi ta cire rigarshi sannan ta nufi ban dakin yana tsaye ruwa na zuba a kanshi, sake towel din tayi tare da rungume shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda ruwan yake zuwa a kasa. Nadiyyah Jamil Chiroma. Ya ce ga tsohon gwamnan Jos, kuma uba ga jigon siyasar kasar nan, Nadiyyah Jamil Chiroma, yar boko ce uwa Uba irin matan nan ne da kansu yake azabar hayaki, amma kuma ita duk da kasancewarta fitacciyar yar gwagwarmaya a wani fuskar tana takunta daidai wa daida, domin a da can feminist ce kasancewar Uwarta baturiya ce rabin rayuwarta tayi shi ne a California na jahar LA, an can ta girma gaban Kakarta. Wacce ta kasance mai kamfanin kayan kwalliya da ado. Nadiyyah ta rike matsayin sarauniyar kyau ta California, sannan ta rike na kasar bakiɗaya, kana ta kuma rike na duniya haka yasa ta goge tare da sanin wasu abubuwan da ba kowacce mace take da shi ba. Nadiyyah tana da degree biyu, a fannin industrial and texture, kamfanin kakanta Mrs Annada ya buga hotunanta a jikin mayuka da turare da sauran kayan kwalliya, sannan manyan jaridun kasar Amurka da Birtaniya sun sha buga hotunanta. Sai dai wani abu da ya kara bawa kowa mamaki lokaci guda ta haukace akan son Salmanun Faris, tun daga lokacin da suka hadu da shi a wani bikin abokinsa da ya kasance daya daga cikin wnada suka bada labarin rayuwar abokinsa, ta hauka ce. Haka tayi ta bibiyarshi har ta gano yana karatu a daya daga cikin jami'ar California ne, haka yasa ta cigaba da binsa ba dare ba rana. Kuma babu abinda ya dame ta gaya mishi take ina sonka. Haka yayi ta share ta kasancewar yana da nashi damar. A lokacin yana degree dinsa na uku ne a fannin ƙwaƙwalwa da aikinsa ƙwaƙwalwa, don haka baya jin akwai macen da zata shiga rayuwarsa. Sai dai yadda tayi ta addabarshi yasa shi ya fito mata a mutum ya ce baya sonta. Sanadin haka yayi yunkurin kashe kanta, domin an kawo ta asibiti ne a haukace, kakaninta suka yi ta rokonsa ya aureta. Idan ya ce ya ji dadin haka yayi karya amma a halin da take ciki mahaifinta da yake matsayin gwamnan ya iya zuwa haka yasa shi amince ya aureta, zuwa yanzu ba zai ce yana sonta ba amma kuma yasan samun mace irin Nadiyyah dace ne, tasan yana da shi kuma yana da abinda zai yiwu kansa amma zai iya kirga yawan abubuwan da ta saya mishi da kanta wanda haka yasa shi jin sonta. Bata damu da ta kashe duk abinda take da shi akansa ba, domin shi dai idan ya dauki kudinsa tow sai dai ya raba sadaka da kuma biyan masu musu girki, hatta gidan da suke ciki a can California nata ne, tunda ya aure ta ba zai ce ga abinda ya saya ba domin duk abinda tasan zai bukata tana mishi. Wannan ita ce Nadiyyah Jamil Chiroma. Fisgota yayi yana me hada kirjinshi da nata, "kin san bana son wasa da sallah!" "Am sorry!" Ya fada tana kasa da kanta, d'ago habbatar yayi ya lashe bakinta. "Jiya me yasa?" "Sorry aiki nake!" Ya fada yana ɗaukarta cak. "Kin san yadda nayi missing dinki?" Murmushi tayi tana me sakala hannunta biyu a kafad'arshi. "Make me screaming, fu**ck me crazy, let me cry please I miss your rough drive!" Matseta yayi yana sumbatar wuyarta.....

***
Unguwar Malamai.

Kusan yau wata guda kenan. Tun rasuwar Baba Saddam, gidanmu ya koma kamar jannama. A da can muna cikin zuri'a masu farin cikin da nutsuwa duk da zaman gidan nan sai a hankali. Sakamakon kishin Mommy Turai da Umma, Maluma babu ruwanta da su, amma tana kokarin yin adalci a zaman gidan duk da mun fahimci cewa Mommy Turai yaranta kawai ta sani. Abba yana kokarin hade kansu amma su fa sai a hankali.
Karfe bakwai saura minti goma, na kalli agogon da yake makale a tsintsiyar hannuna. Siririn tsaki na ja, ina hada kayan da zan bukata a in da nake attachments wato gidan Radion Jahar Zanzabira, takaici ne ya kar kamani jin Ya Nawwas yake faɗa kamar ni daya ce a gidan nake makara a gidan, bawan Allah nan bana kaunar naji labarin zai zo hutu domin kuwa yana zuwa yayi ta addabar rayuwata kenan da fada da masifa wani lokacin ma ya ce zai make ni.
Hey ban gabatar muku da kaina ba, Sunana Zainab Junaid Gobir, mahaifina bagobiri ne daga Katsinar Maradi, mahaifiyata kuwa Buzuwa ce daga Agadz, nice ta hudu a dakinmu, asalima ni ce auta a dakin Maluma. Wato mahaifiyarmu. Gidanmu duk da gidan Malamai ne akwai wani irin yanayi mara daɗi wanda baka isa kayi magana ba, kishin Maluma da me sauki ne domin a wuri guda zaka fahimci tana da zafin kishi shine akan Abbanmu, tow amma Mommy wato Hajiya Turai ita kamar ta kashe su take ji, Umma Bahaushiya ce daga kasar kano ya aurota, duk da suna kishin Abba amma zai yi wahala ka ji sun yi koda sa'in'sa ne tun da aka haife ni har yau ban tab'a jin fadarsu ba, amma Umma da Mommy Turai har dambe anyi ita Hajiya Turai bafulatanar Zanzabira ce, ban san yadda aka yi Abba ya auro ta ba, domin masifaffiya ce ga fada kamar rina, Mommy Turai taba son muna mu'amala da Yaranta, haka zalika bata kaunar ganin Abba ya haɗa mana kome dasu Iram domin tasha gayawa mana ita Iram da Tauhid ta haifa bayan nan bata da wani alaka damu, haka yasa mu dakinmu mu hudu ne, Ya Abid, Ya Nawwas, Ya Yunus, shi nake bi, sai dakin Umma Ya Nuraim, Yaya Nu'aymah, Yaya Sajida domin ta girme mu sosai, yanzu haka maganar aurenta ake yi. Dakin Mommy Turai kuwa Iram sai Tauhid, su kenan a yadda nake jin su Yaya Nu'aymah suna fada wai haihuwar ma dakatar da ita tayi da karfi don bata shirya tara Yara dayawa ba.

"Allah ya shirya ki, amma kin san yana da abun yi ko." Inji Maluma ta fada a hankali, d'ago kai nayi na kalleta, nasan yanzu ina fita zai shiga korafinsa na fama. "Maluma ki ce ya tafi kawai Malam Babangida zai kai mu." Shiru tayi tana kallona kafin ta ce min. "Ikhlas baki da gaskiya, me yasa baki son Nawwas ya ajiye ku?" "Ni kuma Maluma? Ni fa ban ce wani abu yanzu muka bishi zai ta mana korafi mun saka ya dauko mu shi ba drivenmu ba ne." Yadda nayi maganar a shagwab'e da yan matan hawayena, yasa jikin Maluma yayi sanyi ta kalle ni kafin ta ce min. "Ai shi kenan!" Ta juya, tabbas Maluma tana taka rawa a rayuwata yadda duk abinda na ce shi take min..

Ina daki nayi yana faɗin. "Maluma kece kike biyewa Ikhlas take yadda take so fa, shi kenan na kara jin ta kira ni na rage mata hanya ko ta rasa abin hawa sai na karya kafarta." Ya fada yana barin parlour kamar jira nake na mike zubur na dauki jakata, ina sauke ajiyar zuciya na fito kallo daya nayiwa kaina ina fatan Allah yasa kada na hadu da Ya Nuraim ko Ya Yunus, yanzu ustazancinsu ya motsa a kaina. Duk da ba wani shiga nayi me muni ba, riga da wando ne a jikina wando palazzo ne sai rigar iya kuguna, sai after dress da na daura wanda kana iya fahimtar shigar da nayi, murmushi nayiwa kaina saboda yadda na dauki wanka babu inda ba zan shiga ba. Rolling kaina nayi da Jersey veil, peach colour. A hankali nake tafiya kamar mara gaskiya, na fito har zuwa parlourn. Ido hudu muka yi da Ya Yunus sai da hantar cikina ya kad'a, amma na aro jarumta na haɗe rai ina me gaishe shi. "Gidan Uban waye zaki da wannan shigar?" Bai rufe baki ba sai ga Iram cikin gajeren sallama ta shigo. "Ki zo mu tafi!" Ganin yadda ta sha Jalbab yasa naji haushi ya kama ni. "Ke don kaniyarki ina zaki da wannan sunan shigar? Wallahi kika sake na tashi sai na karya ki mara kunya!" Da sauri na koma daki na sauya kayan abaya na saka bayan na cire riga da wando, na fito ina kumbura baki. "Wallahi na kara ganinki da kananan kaya sai na karya ki!" Haka na fita ina tura baki. "Babe haushina kike ji na makara ko?" Banza na bawa ajiyar ta muka shiga mota, "Khlas yau fa zan fara aiki a ministry of


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login