Showing 264001 words to 267000 words out of 304445 words
dukkanmu kanmu a kasa, haushi fa sun ji, musamman Ijlal da ita labarin cikin sai da ya saka ta kusan faduwa, wannan abin bai mata ta dadi ba, ya zo mata bazata. Itama Nadiyya mamaki kamar ya kashe ta, ajiye min kular da Ijlal tazo da shi tayi a kan darduman dakin. "Ga shi na san zaki so cinsa! Zan koma na bar Amirah a gida!" Ta juya tana me barin dakin, Nadiyyah da bata iya boye abu a ranta ta ce min. "Dama kin san kina da ciki ne baki fada ba? Sai dai kawai muka ji abu daga sama!" Murmushi nayi ina faɗin. "Nima haka nake ji a bakin mutane ban san da shi ba!" "Ikon Allah ga inda ake niman shi ana kaf-kaf da shi ya zo inda ba san da shi ba, ko irin zazzabin nan baki yi bane?" Shiru nayi na kalli sama kafin na ce mata. "Ban yi kome ba!" "Zata kara magana Mai BIabbar daki ta ce mata. Ki wuce gida!" Haka ta mike itama tana ajiye min kudi da tazo da shi!" Ta fita tana b'ata rai, bayan fitarsu Mai Babbar daki ta ce min. "Da gaske baki san da shi bane?" A kunyace na ce mata. "Allah ban san da shi ba, kawai abu daya na sani ina ciwon ciki, bayan wannan rashin lafiyar da nayi ban kara wani ciwo ba, sai ciwon kai da nayi ta fama da shi, shima idan ya dame ni zan sha magani!" Kamar zata mai dani cikinta ta rike hannuna cikin wani irin kulawa da yanayi take cewa. "Kin san yara uku kika rasa?" Kaina a kasa ina murmushin dole, a hankali nake jin kuka na zuwa min. "Ummi ban sani ba, sai da ya gaya min Ummi ban san me yasa a ranar na razana da ganinshi cikin tashin hankali ba, wanda haka ba sabo bane idan har akan gidansa, Ummi taya zan iya daurewa, Ummi kewar Yaran da basu rayu ba nake." Na fashe da kuka a hankali, matan da suka yi bari kaɗai suke iya fahimtar yadda rashin yaron da baka san da shi ba, musamman ni da Ijlal take min gori a kai a kai. Yadda nake kuka itama sai da ta share kwalla, Maluma itama fa ta shigo, ganin yadda nake kuka yasa ta fita ta bar asibitin ma zuwa gida. Daki ta shige tayi kuka sosai, don zuwa yanzu tausayin Yarinyarta take itama don dai Malam yaki bata goyan baya ne, da ta riketa n a tsawon sati biyu.
Sai dare aka mai da Mai Babbar daki, Umma taxo muka kwana. Dama ita ke kwana, shima dai ashe anan ya kwana biyu nan, suna ta hira da Umma jifa jifa ina shan kankana ta ce mishi. "Ya naka jikin?" "Da sauki Umma!" Ya fada yana kallona. mikewa tayi tana faɗin. "Bari na leka dakin farkon nan akwai wata class mate dina da aka kwantar da Yarta, dazu ina zuwa naga ta fito daga dakin na tambaye take gaya min yarta ce ba lafiya!" "Umma kada ki dade, ina jin tsoron zama ni daya shima tafiya zai yi ai!" "Ke kasararki, ba ga Mijinki ba, bana son gulma!" Ta yi min zagi da Hannu bibbiyu, dariya nayi kawai ta fita abinta. "Fushi kike ne?" Kallonshi nayi a hankali kafin na cigaba da shan kankanan. "Lafiya muka rabu na dawo ga kin sauya Zeey gaya min me aka miki?" "Yaya ka tafi gida kawai." Na fada mishi a sanyayye. "Wani irin na tafi gida? Mai aka miki da zaki kullace ni?" "Ni nace kayi min wani abu ne? Yaya don Allah ka kyale ni!" Na fada da karfi, zuba min idanu yayi kafin ya riko hannuna. Cikin tashin hankali ya zo gabana ya durkusa. "Gaya min me nayi miki?" "Tell me me nayi?" Hawaye ne ya zubo min, na ce mishi."yaya ka tafi sai da safe!" Na ajiye bowl din na kwanta. Umma ta gaya min musababbin tashin hankalin, kawai na gaji ne da halinsa. Haka ya fita ya tsaya a bakin kofar, na cigaba da kuka har na wani lokaci kafin na kwanta barci yayi gaba da ni.
Ban san dawowar Umma ba, na ganta da asuba tana sallah, ban daki na shiga nayi wanka da ruwan dumi nazo na kwanta. Bayan na karya don da wuri nake shan magani na kwanta, barci ya sake d'aukata. Shigowa yayi da sallama ya gaida Umma, sannan ya ce mata. "Ina ga yau zasu sallame ta tunda jikin da sauki. Mun yi magana da Abba ya ce zaki iya zama da ita zuwa lokacin da ta warware!" Kanshi a kasa kafin ya ce mata. "Umma ki bata hakuri." Kallonshi tayi kafin ta ce mishi. "Kuskure fa anyi shi, idan aka yi laifi bincike ake shi yasa Allah ya saukar da wasu ayoyi masu tufka da warwara, ita kanta Zainaba bata san me ya faru ba don ko jiya da nake tambayarta bata sani ba, ka san me? Zama da mata sama da biyu kana bukatar zama namiji jajjirtacce a cikin gidanka, wanda idan kayi tsawa a za a ji ka, amma ka sake suka fahimci ba zaka iya dakatar da wasu abubuwan ba zasu kulla kuma kai ka fada cikinsa, maganar da Maluma tayi ranta ne ya b'aci, domin Zainab ita ce mace a tsakaninmu kuma Allah ya kawo ta cikin wani irin yanayi na rayuwar girman da aka bata dole ya tab'ata, kayi hakuri ka tsaya a gidanka!" Sannan ta cigaba da addu'arta, haka ya mata sallama ya bar dakin. Kome ya tsaya mishi cak.
Lokacin da ya isa gidansa, jikin Nadiya a mace ta same shi zata mishi magana ya nuna mata hanya, ba musu ta bar parlourn amma ranta yana mata wani. Karfe goma Aunty Shukrah da Aunty Sajidah suka zo suka gyara min gida. Abinci Aunty Nu'aymah ta kawo min. Da yake an gaya musu za a sallame ni. Karfe sha daya na rana aka sallamo ni, daga Ijlal har Nadiyyah sun fito sun tarbe ni, na yi farin cikin dawowa dakina, haka muka wuni cikin kulawa har yamma suka watse, Umma sosai take kula da ni, abinci abun sha, lokacin da zan kwanta.
Kwanaki sun ci gaba da tafiya, har tsawon sati biyu cib, Umma ta min nasiha da kuma nuna min yanzu zan kara mikewa akan kula da mijina, Maluma ta min aikan kayan gyaran jiki sosai, kuma na amsa na fara sai na ga kyan shi, Fulani Nana ta min aika sosai ta gaya min yadda zan yi amfani da shi, haka na hada nayi ta amfani da shi, don na samu damar gyaran jiki sai na nisanta kaina da shi ta hanyar kin amsar girki, yana magana nace xan koma gida ni gara can zan nutsu, jin haka yasa shi kyale ni ya fita harkata.
Kusan wani ikon Allah sai na fahimci, ashe ana wani irin shegen kishi ne a cikin gidan, na farko idan Ijlal ta kwana turakarshi, Nadiya ba zata kwana ba sai an yi gyaran cikin gidan kamar hauka, wai kada ta saka mata wani abu, fada kuwa idan suka hadu sai sun yi sa'in'san, ranar da Yamma na bawa Wildat kular Ijlal abinda ta kawo min Mai Babbar daki ta zubar da shi, Allah ba tuba me zan yi da abin da ya fito hannun Ijlal idan ba Tsautsayi ba. Haka nayi ta kallonsu daga nesa, namiji da gulma sai gashi wai yana son nima na nuna mishi kauna yadda suke nuna mishi, rike bakina nayi ina faɗin. "Allah na tuba ka dai zauna da matanka dai a haka ni yanzu ta kaina nake." A zamana a asibiti har yan office dinmu sun zo gaida ni, haka Yeemar tunda ta ji labarin sai tazo.
Ranar da na amshi girki, na saka aka yi min tuwo a kitchen din waje ni kuma nayi miyar shi, can ma suka yi miyar. Da isha ya shigo cin abinci, yana ci yana kallona ganin yadda na saka rigar sanyi saboda ruwan da aka gama dazun yasa ni sakawa saboda sanyi, tashi yayi a gaban abinci ya so ya dafa goshina, fita yayi can sai gashi da abin gwada zazzaɓi, ya gwada sannan ya rike hannuna yana kallon yadda nake dan yatsina fuskana. "Ina ke miki ciwo?" "Babu Yaya sanyi nake ji kawai da jin wani irin abu!" Sai duk ya rud'e, haka ya kira Munirah ya gaya mata, ta tambaye ni ko ina jin wani alama ne ba wani ciwon na gaya mata ni sanyi nake ji, tambaye ni ko akwai mura? Nace babu, sannan ta ce na bashi wayar, suna gama wayar ya kashe Ac din parlourn ya fita ya dauko room heater, ya saka min kafin wani lokaci parlour ya dauki dumi, ruwan zafi ya kawo min na sha da magani na, a anan na kwanta barci yayi gaba da ni, abincinsa ya karasa, sannan ya mai dani dakina ya kai min heater din, sai da ya bi dakunan su sannan ya shigo ɓangarena...
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 87
Ban san yadda abin ya kasance ba, ni dai da wuri na tashi, bayan ya dawo masallaci. Ya same ni ina azkar zama yayi a kusa da ni yana kallona. "Ya jikinki?" Shafa addu'a nayi na ce mishi. "Da sauki sosai!" Kwanciya yayi akan kafana, ya daura kafaffunsa a saman gadon. "Zaka karyani!" Na fada ina janyo Alqur'ani na fara karantawa, kusan a tare muke karatun sai da rana ya fara fitowa barci yayi gaba da shi, bakwai daura na dasa aya. Na zuba mishi idanu, a hankali na lallaba na kwantar da shi,sannan na dauko pillow na d'aga kanshi na saka mishi. Kafin na kwanta a a gefenshi, zabura yayi ta d'aga ni can muka koma gadon, ya ja mana mayafin gadon barci ya dauke mu bakiɗaya. Bude yayi yana kallon yadda nake shashekar kuka, ko daren jiya ya ga wannan mafarkin kukan da nake, hawaye shar-shar nake zubarwa. A hankali ya shiga hura min iskar bakinshi, ina sauke ajiyar zuciya har na samu na daina kukan, gyara min kwanciya yayi a kirjinshi. Yana tofa min addu'a barci ya kara ɗaukarmu.
Karfe daya na rana, yunwa ya farka da ni. Yadda nake makale a jikinshi na shiga ƙoƙarin tashi ya bude idanu. "Ya dai?" "Yunwa nake ji!" Na furta a hankali. Murmushi yayi yana faɗin."sai ki farka haka!" A hankali ya zare ni daga jikinshi ya shiga ban daki ya haɗa min ruwan wanka da brush ya fito waje, kitchen ya nufa ya dauko tuwon jiya ya kunna gas ya daura akan wuta, sannan ya ciro miyar a frij. A hankali yake, yake daureye wasu abubuwan da ya b'ata, kafin na fito ya gama dumammenshi ya juye a wani katon tire, ya bude drower na kitchen din ya ciro kwalbar manshanu da yaji ya ajiye sai da ya kawo min abincin daki. Sannan ya koma ya dauko yajin ya haɗa tea mai kauri ya kawo min, lokacin da ya shigo na fito ina goge jikina, dauko riga yayi da pant da bra ya mika min na saka, sannan ya janyo ni tare da zaunar da ni muka ci tuwon tare, ina kurban tea. Drower magani ya janyo ya dauko min magani na, ya fara bude min ina sha ina ji kamar nayi kuka. Haka na gama sha, shima ya mike tare da nufar ban dakin yayi wanka, kafin ya fito na gyara dakin tas, sannan na fito Parlourn na buɗe masu aiki suka shigo aka fara gyara dakin, aka kawo min abin karyawa. Kosai da kunu suka yi, tun jiya Uwar tuwo ta tambayi Jakadiya, ita kuma ta tambaye ni nace su yi kosai tunda akwai kome a store, kallon kunun nayi ya bani sha'awa amma na mikawa Wildat da take ta aiki na ce mata. "Idan zaki tafi ki je da shi!" "Allah ya kara miki lafiya!" Waya na dauka na dawo parlourn na zauna na kira Matar Sarkin Gombe, muka gaisa don tunda abin nan ya faru take kokarin kirana, nima kuma haka. Sannan Babbar abinda nake son magana da ita shine masu aikin gyaran jikin. Ai kuwa mun jima har ya fito ya same ni ina wayar kashe kiran nayi na mai da hankalina gare shi. "Bari na sauya kaya yau kin makaran da ni sai azhar zan tafi fada!" "Sorry Yaya dama maganar masu gyaran jikin baka ce kome ba!" "Eh kuma na manta na gaya miki na tuntubi Nadiyyah ta ce itama tana son dama ta buɗe!" "Yaya na hakura ta bude kawai!" Na fada ina wuce shi. "Ban gane ba dawo mu yi magana!" "Yaya ai naga gaya maka gaskiya na hakura!" "Ok wato ke uwar son kai na lura da suna bin ki amma kina share su me kike da shi ne haka?" "Yaya bana son Magana ka ga bamu kaɗai ba ne kayi kasa da muryata don Allah!" Na fada kamar xan yi kuka. "Ki je ki yi duk yadda kike so na yanke hukunci." Ya fada yana mai son zai fita, a hankali nake sauke numfashi, juya yayi ya ga yadda nake fama da matsanancin numfashi, da sauri ya rungume ni. "Baki da lafiya ne?" Yadda yake shafa bayana, ya sha na fara jin numfashina ya fara dawowa daidai. "Jiri nake ji!" Kwantar da da ni yayi a dogon kujera, yana shafa bayana. "Ki huta bayan la'asar zamu asibiti!" Ya fada ranshi a haɗe. Sannan ya bar parlourn. A hankali na lumshe idanuna, lokaci yana tafiya dakyar na yi sallah azhar sannan na samu yau shinkafa da miya suka yi ban leka ba, Amma Jakadiya ta gaya min. Shinkafar suka diba min, na yi miyar da nake so.
A can Bangaren Nadiyyah jidali da masifa take akan me zai kwana a wurin Zainab bayan ita da tsohon cikinta take binsa turaka da yake ya kwaso haushinsa, ya daka mata tsawa. "Gidana ne, kuma ina da yadda nake so nayi. Idan mace ba zata iya zama dani ba tayi waje, abinda ita Zainab din bata da shi kenan tayi kishi ko bakin ciki akanku sai kune kuke a kanta, na kira wata ta zo min turaka? Nace lallai dai wata tazo turaka na ne? Na muku dole ne wata tazo! Ya ishe ku haka idan zaku zauna da ni ku zauna idan ba zaku zauna da ni, ga hanya ba zan kara sakewa wata ta min iskanci ba!" Ya juya ya barta nan tsaye da cikinta, fita yayi bangaren shi ya saka kaya sannan ya nufi bangaren Ijlal, ganin yadda fuskarshi tayi Jajjur bata sake ta takale shi ba sai ma tambayar shi tayi. "Abbyn Amirah ya Mammyn Amirah da jikin da fatan dai lafiya? Na ga baka fito da wuri ba, ina tason na kiraka ina tsoron kada nayi laifi!" Wani irin burge shi tayi ya ce mata ." Da sauki ya Princess da jiki? Da fatan tana barci dai?" " Da sauki Abbyn Amirah baka ce kome ba!" "Da sauki sosai, tana can ma tana hutawa!" Ajiyar zuciya ta sauke a fili kamar da gaske. Kafin ta shiga mishi hira, yana wasa da Amirah biyu saura ya ce mata. "Me nene babu an jima a kawo."
"Akwai kome ina ga sai na leka store." "Ok"
Ya saka kai zai fita ya shafa kumatun yar da take kan keken wasan yara, amma fa kamar irin a saka itacce a kan abu ne domin a sandare take, dawowa yayi ya ce mata. "Ki daina sakata a kekenan na saka a kawo mata keken su." "In sha Allah ba zan kara ba!" Ya faɗa, kallonta yayi yadda tayi laushi kamar ba ita ba. Haka ya saka shi jin lallai ta shiryu. Sannan ya fita, murmushi tayi tana faɗin.."Sai mu ga yadda zaka yi zaman auren da ita, ba sai da lafiya ba?" Sannan ta sake dariya, "ita kuma Nadiyyah bata ga kome ba."
***
Sai da aka yi sallah la'asar, ya samu Mai Babbar daki da maganar yadda Ikhlas take kwana da kuma yadda numfashinta yake fita. "Ka je ka gayawa Mahaifinta zai iya taimakawa, matanka dai su ji tsoron Allah domin kishi ba hauka bane, idan suka sake Malam Junaid ya juya gare su sai sun yi danasanin abinda suke aikatawa!" Yadda take fada kamar ta rufe shi da duka, haka ya gama zamanshi ya dawo gida, ina kwance ya shigo, tashi zaune nayi har nayi wanka na sauya kaya cikin orange colour, murmushi yayi. "Kin san kalar da nake so! Saka mayafi mu fita!" Tashi nayi na nufi daki na dauki hijab na fito, muka fita da shi ya rufe kofar. Gidanmu muka zo da shi, ina shiga parlourn Abba na kwanta a dogon kujera. Maluma da kanta ta shigo ta ganin kwance, sama sama ta amsa mishi. Tana ƙoƙarin d'ago ni idanuna yayi luuuuu yayi sama! "Ke Ikhlas!" Ta shiga jijjiga, zuwa yayi ya dauke ni zai fita da ni Abba ya ce mishi. "Ajiye ta babu wani asibitin da zata" ya fito daga dakinsa. Kwantar da Ni yayi a tsakiyar parlourn. "Fulani Babba! Ce maka aka yi wasa ne matsayinta? Yara uku fa tayi barinsu? Sai dai basu san waye Uban Zainaba ba ne." Ya fada yana mai komawa kujera ya zauna. "Ko matanka basu hanaka zama da ita ba, akwai waɗanda basu kaunar ta zauna da kai saboda lissafinka da nata daya ne! Me ya faru a yan kwanaki nan?"
"Daren jiya tana barci sai na ga tana kuka, sosai take kuka. Haka yau da safe tayi kukan!"
A hankali ya tashi ya fita sai gashi da wata allon karfe ya zauna, yana kallon Umma da ta shigo. "Kawo min wuta a kasko!" "Malam kada ka yi haka!" "Kinsan Me suka mata ne? Rabona da nayi aikin nan