Showing 186001 words to 189000 words out of 304445 words

Chapter 63 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

68

sunanta ina dafe kirjina tare da fashewa da kuka wiwi. "Don Allah kada ki wannan addu'ar don Allah kada ki raba ni da shi wallahi shine rayuwata farin cikina, bani da madadinsa." Murmushi tayi tana kallon ƙasa kafin ta ce min. "Kin zata zan yi haka ne don bana sonshi? Ina sonshi son da nake mishi ya shafe ki, nake jinki kamar shi." Ta fada tana murmushi kafin ta ce min. "Kwanta ki huta!" Daga haka na kwanta bayan ta wanke hannunta, alola tayi ta zo ta fara gabatar da sallah nima tashi nayi na yi alolan na zo na fara bin bayanta, bani na kwanta ba sai karfe hudu na asuba, shima Mai Babbar daki ta ce na kwanta saboda na tashi sallah jiri ya nime yar dani, haka yasa tace na kwanta, sai da karfe biyar da rabi yayi ta tashe shi, nayi sallah asuba abinda ya fara fitowa daga bakina shi ne. "Ummi sun kira ki ne? An ce ya farka?" "Sallah nace ki yi." Ta fada tana cigaba da addu'ar da take yi, jiki a sabile na nufi toilet nayi alolan na zo na gabatar da sallah amma na ga bata nan, ina zaune can sai gata nan dauke da mug na hadaden shayi ne da soyayyen kwai. "Ummi!" "Sha!" Ba musu na kurba a hankali ina kallonta ina cin kwai, tas na cinye, ruwa ta mika min tana addu'a sha nayi ina kallonta ko zata bani labarin ya farka ai kuwa ta hade rai kamar bata tab'a dariya ba, agogon wayarta ta kalla sannan ta cigaba da addu'a. "Bana son ana kallona!" Shima ya tab'a fada min haka. "Ummi!" Wani d'ago idanun tayi tana kallona a hankali, kafin ta ce min. "Me?" "Yana kama da ke, duk abinda yake yi kamar a wurinki ya dauko!" Yadda nayi maganar hawaye na zuba min, jan pillow tayi tare da ajiye min ta mika min PCM ta ce min. "Sha!" Ba musu Na amsa na sha a hankali, ina kallonta can bayan minti goma ta ce min. "Kwanta ki huta!" Ba musu na kwanta. "Ki yawaita addua da niman tuba, sannan ki kasance mai yawan karatun Alkur'ani waraka ce." A hankali na fara karanta Alqur'ani musamman suratul bakara, tana zaune itama tana bina muka karantun, a nan na fahimci daga boko har addini mai babbar daki ta kwashe sai dai muce abar mata kayanta. Har barci ya dauke ni, ita tana karatun.

Barci nayi mai sunan barci domin jiya tunda na farka daga sunan da nayi ban sake barci ba, lokacin da na farka naji ana cewa. "Ki kula da hannunki!" A hankali na bude idanuna. "Yeemar?" Na kira sunanta. "Yaushe kika zo?" Yau kwana biyu kenan ina zuwa ai ashe haka lamarin ya faru?" Kallonta nake ina kallon dakin da nake tabbas asibiti ne tow me ya faru? Turo kofar da aka yi na kalli kofar itama ta juya, Maluma ce da Abba tare da su Aunty Sajidah. "Abba Mai yasa aka dawo da ni? Ba na warke ba?" Murmushi yayi ya ce min. "Da sauki ashe kin farka!" Shigowa mai babbar daki tayi tana faɗin. "Sannu ya jikin naki?" "Da sauki shi fa?" "Alhamdulillahi!" Ta fada , a yadda na fahimta yana can kenan, hawaye ne suka ciko min idanuna. Na bude baki xan yi magana aka turo kofar, kafe kofar nayi da idanu. Hawayen ne suka zubo min, na cire ƙarin ruwan tare da dirka a gadon na nufe shi, fadawa jikinshi nayi ina kuka. "Me yasa zaka min haka? Kasan yadda na damu nasan halin da kake ciki? Yaushe ka farka?" Na d'ago kai ina kallonshi. Shima kallona yake bai ce min kome ba yanayinsa ba yabo ba fallasa. "Yaya gaya min yaushe ka farka? Me yasa aka kawo ni asibiti?" Rike hannuna yayi ya dawo da ni bakin gadon sai lokacin Nady da Ijlal suka shigo. Rike hannuna yayi da kyau. "Zaki iya tuna me ya faru lokacin da aka buga miki abu a kanki?" Shiru nayi ina kallonshi girgiza nayi. "Yaya!" "Ki min shiru!" Ya fada a dan tsawace, shiru nayi ina kallon mai babbar daki. "Ummi waye ya same ta a kwance?" "Sailuba ce!" Shiru yayi yana kallona. "An jima za a mai da ita a duba kanta, domin jinin da ya taru!" Yana gamawa ya mike zai tafi rike hannunsa nayi. "Yaya baka gaya min meke faruwa ba?" Cire hannunsa yayi yana faɗin. "Ku kula da ita a bata abinci!"
Saka kai yayi ya fita daga cikin dakin, Faruq na biye da shi. "Diban jininta aka yi ke nan?" Faruq ya tambaye shi, cak ya tsaya. Idan haka ne akwai saka hannun na gida. Ya furta a ransa ya juya ga Faruq, "Kana tunani da kyau!" Kafin ya cigaba da tafiya, har zuwa office dinsa a hankali yake duba rahoton binciken da Doctor Mu'azzam da Doctor Jacob suka ba shi.
Bai san me yasa ba yake jin shi kamar ba shi ba, ya kamata a ce yana hutawa ne, amma sai yaji aiki yake son yi akan Zainab, yana ta aikinsa yana kallon computer. Jini ne ya digo daga hancinsa, ya saka tissue ya toshe hancinsa. Yana zaune a wurin can ya juya yana kallon wayarshi da take ƙara. Dauka yayi ya saka a kunne. "Prince ya jikin Ikhlas?" Walid Mamman yayari ya tambaye shi, shiru yayi kafin ya ce mishi. "Kana da matsala ne da ita?" "A'a ban ce ba kawai daga tambaya, dama na ji wani gulma ce!" "Kari ke abarka!" Ya kashe wayar, shi mutum ne da yake da ra'ayin kansa baya son a saka mishi magana ko a mishi wani iyayi, haka yasa shi ya cigaba da aikin gabanshi. Kiran sallah Magariba ya fito da shi har lokacin Faruq yana tsaye a jikin kofar. "Faruq!" "Na'am ranka shi dade!" Shiru yayi yana kallon kasa kafin ya ce mishi. "Ina ji kamar akwai wani abu a cikin gidan nan!" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Duk yadda kace sir!"

Dakin Ya dawo ya same ni, ina kuka ya cewa Umminsa da su Nady. "Ku je Faruq ya ajiye ku a gida." "Ummi baku gaya min me ya faru da ni ba" mika min kofin tea din hannun Maluma yayi ya mika min don naki sha sai kuka nake. "Amsa ki sha!" Ba musu Na amsa ina kurba, iya kalamai ukun nan yasa naji kamar umarni ya bani cikin sanyin jiki na amsa har na shanye tas. Ban daki ya shiga yayi alola sannan ta fito yana faɗin. "Ki shiga na tara miki ruwan wanka!" Ban dakin na shiga na cire kaya nayi wanka, ina dawowa Maluma na samu itama ta shiga tayi alola tayi ta gabatar da sallah.
Kallon Maluma nayi na ce mata. "Me ya faru da ni?" Na tambaye ta bayan na idar da sallah. "Ke kanki baki san me ya same ki ba sai ni? Ki tuna da kyau akwai abinda ya faru." Bakiɗaya na ƙasa tuna kome, shigowa suka yi da Abba tare da Ya Abid da Nuraim sun kawo abinci. "Abba me ya same ni?" "Zama yayi a kujeran dakin ya ce min. "Zan baki labarin abinda ya faru, amma kuma zaki iya tuna abinda ya faru kafin ki yi barci?" A hankali na d'ago kai, wani irin sarawa kaina yayi na rike kan da hannu bibbiyu, isowa gabana Nuraim yayi, take ya rike shi tare da cewa.."kada ka motsa gabanta. " "Zainab me ya faru?" A hankali na shiga sake kaina da yake bala'in ciwo kamar zai rabe. Sannan ka kalle shi da idanuna da suka ji jajjur na ce mishi.."Ban sani ba wallahi!" Abba yayi shiru kafin ya ce min. "Bayan mai babbar daki ta barki kina barci aka dawo aka same ki, a sume!" A hankali na d'ago kai ina kallonshi, kamar ina son tuna me ya faru. Sai kuma na rufe goshina musamman inda aka yi min bugun. Na ce mishi.."wata mata ta shigo, ina cikin barci na bude idanuna cikin barci amma kuma ban san me ya faru ba,.na ji kamar ta buga min abu a kaina?" Na rike kaina da nake ji kamar yanzu kafa yi abin. "Baki tuna yadda matar take ba?" "Da nikab a fuskartar!" A hankali Abba ya ce mana. "Allah ya kyauta, duk wnada tayi haka ban san meye ribarta ba." "Jininta aka diba!" Ya nuna mishi dantsena ya cigaba da cewa. "An dibi jininta ne saboda wani bukatar kai da kai. Sannan na gama lissafina ban san waye yayi haka ba!" "Allah ya kyauta. "Amin Ya Allah!" Sallama suka mana sannan suka tafi shima fita yayi bayan kamar minti goma sai gashi, tunda naji an kawo maganar jini tsoro ya kama ni, shigowa yayi ya zauna yana kallona. Mika min magani yayi na amsa na sha. Shiru nayi ina zaune can barci ya fara daukata, "tashi kiyi sallah isha!" Haka na tashi da kyar nayi sabon alola, na ba gabatar da sallah ina addu'a na bingire barci yayi gaba da ni, daga nan ban kuma farkwa ba, sai karfe biyu ya kwanta a kusa da ni, ajiyar zuciya na sake ina jin wani irin tausayinta kaina, kwantar da kaina nayi a kirjinshi barci mai nauyi ya dauke ni. Tunda abin ya faru, dalilin da yasa faruwa al'amarin kiran Mai babbar daki da aka yi, akan ya farka ta fita ta barta akan su Sailuba suna aiki a kitchen, tabbas idan kana kitchen din Mai Babbar daki matukar ba magana zaka yi ba babu me sanin akwai mutane. Sannan basu shiga turakarta kai tsaye sai da dalili mai karfi. Basu ji lokacin da aka shigo ba har aka yi abin haka basu fitar mai laifin ba, sannan lokacin da abin ta faru Nady da Ijlal suna gidansu. Shiru yayi yana kallon yadda take barci a jikinshi. Tausayinta da wani irin kaunarta ya kara cika zuciyarshi. Yadda yaji labarin kukan da tayi ya musu dai da ya saka shi jin lallai Zainaba ta sauya. Yana zaune yana gadinta har aka kira sallah farko sai da aka kusan shiga sallah ya tashi so tafiya amma sai kawai bar gamsu ba, don haka yayi Sallah a cikin dakin yana idarwa ya tashe itama yayi sallah. "Yaushe zaka sallame ni?" D'ago kai yayi ya kalle ni kafin ya ce min. "Kin gaji da asibitin ne?" Gyada kai nayi.

Karfe uku na rana aka sallame ni, koda muka iso gidan na ga an ta gyara alamar za ayi baki a cikin gidan. hidima sosai aka yi, lokacin da na shiga part dina na samu Iram da Ikram kallon juna muka yi ta mike, "Ya jikin naki?" Niman wuri nayi na zauna ina kallonsu. "Da sauki!" "Akwai wani abu da kuke bukata ne?" Ya tambaye su, shigowa Ijlal tayi tana min wani irin murmushi. "Gaishe ta suka zo yi fa?" Kallonta yayi daga sama har kasa idanunsa a wani irin hargitse. "Nayi dake?" Yadda yayi maganar da wata kausasshiyar murya ya sani jin kalamanshi har cikin jikina, fuskarshi tayi ja kamar ja. "Nace da ke yi?" Ya buga mata tsawar da ya sani tashi tsaye. Jikinta ne ya shiga rawa. "Ina wasa dake? Don ina aurenki sai ki rena ni?" Ya kara daka mata tsawa da yasa ta jin kamar an buga mata wani abu a kai. Zubewa tayi akan gwiwarta. "Allah ya baka hakuri ban san ranka zai b'aci ba ne!" Bai kara bin ta kanta ba. "Idan Zainaba ta je gidanku yar uwarki ce amma ki shigo gidana kuskure ne, daga yau na haramta miki zuwa min gida kin ji ko baki ji ba?" Iram da itama jikinta yake rawa ta ce mishi. " In sha Allah!" Sannan ya juya ga Ikram. "Me kike so?" Girgiza kai tayi tana mai sunkuyar kanta a kasa ta ce. "Babu ranka ya dade!" Matsa musu a bakin kofar yayi ya nuna musu hanya ba musu suka fita da sauri. Zama yayi yana huci har lokacin ina tsaye akan kafana, hawaye na zuba min. "Zauna ki sha magani!" A yanzu ya sauya ba wanda na sani bane wannan cike yake da kome. Abincin da yasa Faruq ya karbo wurin Mai Babbar daki ya zuba min na fara ci. A hankali yana kallon yadda nake ciki ya zauna nazarin yadda nake ci. Da sallama Nady ta shigo hannunta dauke da kula. "Prince Barka da hutawa!" Bai amsa mata ba, zama tayi tana faɗin. "Zainab ga abincin nan na dafo miki!" Kallonshi nayi na ce mata. "An kawo daga wurin Mai Babbar daki!" Shiru yayi yana kallonta. "Kin yi anfani da maganinki?" "Eh!" Ta ba shi amsa, daga nan ya cigaba da zama har aka kira la'asar ta fita shima ya tafi massalaci. Ban daki na shiga nayi alola, tunda nayi alolan jikina yake wani irin rawa jikina ya fara kafin na isar da sallah la'asar, jikina yayi wani irin zafi hawaye na zuba a idanuna ga kaina da ya koma kamar gungunmemmen dutse. Dakyar nayi sallama na kwanta a wurin, kafin wani lokaci jikina kamar za ayi gashin masara, domin har na fara jin kamar numfashina zai bar jikika. Sai gashi ya shigo hango yadda nake yi ya sashi shigowa da sassarfa. D'ago ni yayi kafin lokacin na suma, yadda ya ji jikina abin ya bashi bala'in tsoro, haka ya kira Nurse Nabila tazo har gida aka saka min ruwa, sai dai kuma yadda take saka min ruwa bata ga alamar jini ba ta ce mishi. "Doctor ko zaka duba al'amarin nan ne?" Ta nuna mishi tafin hannuna da yayi fari tas. "Babu jini kenan?" "Ga zahiri Doctor!" Shiru yayi kafin ya saka hannu ya dauke ni, yayi waje da ni. Asibitin aka kara mai dani, abin ya bawa kowa mamaki har da mai babbar daki da take jin abin ya mata nauyi da girma, kawai zarginta sai ya bata ko Abinda aka min a dakinta ya haifar da haka, wasa wasa sai da na sha jini leda biyar, shi ya bada leda biyu, Ya abid leda daya Abba Leda daya Ya Yunus leda daya, sai a lokacin na samu kaina, amma duk da haka nayi wani irin lalacewa kamar mai cutar HIV domin ni daya nasan yadda nake ji.
***
"Kace wani abu ya bayyana a gare shi? Har ya ambaci sarki Shago?" Dan dodon da ya samu kanshi bayan ya sha jinin Ikhlas yayi tattul yanzu da yake zaune nan nan karshen da aka bugawa Ikhlas yake lasa jinin da yake jiki yake lashewa wanda yayi sanadin tsotsar jinin jikinta, sake lasar abin yayi, ya juya can ya juya nan tsoro ya bayyana akan fuskar shi ya ce musu. "Ku fito da Gwaska Rilwani kai da Nafi'u ki fitar da Dakare na, ya haɗa Rundunar shaidanun tsakiyar birnin, maza ayi haka amma waye ya tashe shi? Yau kimanin shekaru talatin da ya kona ni, shine a jikinsa, shine ya bayyana shi ya kona ni, ku fito min da Dakare na;" ya fada da karfi bakiɗaya ya razana. "Tabbas kunci da nadama ya dawo da shi, ya dawo ne ku sannan yadda zaku mai da shi barci cikar buri hade da kafaffin alƙawarin mai wanke da izzar mulki zata fara aiki Rilwani kai ka tashe shi kai ne,.kusan sannan hanyar da zaku kore shi domin sai ya budewa Yaron nan idanun da zai hallaka mu......
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 62
A matuƙar rud'e suka shiga tashin hankali, tunda dodon da suka yi imani da shi, ya rasaza tabbas akwai wani abinda basu sani ba. Don haka suka shiga damuwa da rud'ani, Alhaji Nafi'u ya ce da yake ganin Salmanun Faris bai wuce su yi loma daya da shi ba, ya ce. "Me kake nufi ? Kai da muka dogara da kai ka sare mu fa?" D'ago jajjayen idanunshi yayi ya ce mishi. "A'a Shago kasan dalilin sunansa? Shine sarkin da aka haife shi da karama, sannan ya kasance daya daga cikin sarakunan da Uwar Bokaye Ajuji ta bashi sa'a, shine sarkin da bai tab'a jin tsoron aljanu da fatalwai ba. Idan baka manta ba,.farkon zuwanmu garin nan Yaron nan ya min wannan ta'asar idan har yana yaro inuwar take bin shi har yayi min wannan abin tow ba makawa an haife shi ne domin cikar mulkin Zanzabira. Idan kuna tunanin ba gaskiya ba ne mai yasa Attahiru bai ji tsoron sadaukar da rayuwarshi ba domin yasan waye dansa,mai Maryam bata ji tsoron don ta rasa shi ba. Tabbas inuwar da take binsa tana cike cikin ƙaddaransa. Ku san yadda zaku kawar da inuwar da suke tare da shi domin ko kun yi nasarar korar daya tow daya sai ta farka da daya."


"Dama an tab'a yin sarki ne irinsa ne?" Wani irin guguwa ce ta tashi tare da kashe wutar tsafinsu. Komawa cikin raminshi dodon yayi. " Shekaru dari hudu da suka wuce an yi sarki irinsa, sannan tun bayan shudewarshi ba a kara sarki irinsa ba. Ance an hada baki da Matarshi ce aka kashe shi, idan har aka ne kofar mu a bude take!" Inji Alhaji Rilwanu Yayari. "Tabbas anyi haka ku tafi ku nime hanyar da zaku toshe shi, kafin nan ga wannan ku zuba mishi a takalminsa idan ya cire!" Ya basu wata jaka karama me dauke da wani abu.

***
Tattara kome na dakin yayi yana gyarawa, domin ya bar Ikhlas a tare da iyayenta, duk abinda yake zargin yana dakin bai gani ba, amma tabbas akwai dalilin rasa jininta. Komawa saman gadon yayi ya kwanta. Mafita yake nima, zuwa yanzu yadda take asibitin an saka mata jini daga jiya zuwa yau amma fatattar kamar ana tsotse shi,.domin sai wani tsotsewa yake yana yankwanewa yake, wato motsewa. Tashi yayi ya fita zuwa Parlourn shi ya zauna Muryan Ijlal ya ji tana wasa kasa kasa, yayi mamakin yadda yake jin muryanta amma kasa kasa baya fahimtar me take faɗa. Tashi yayi ya nufi dakin ya samu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login