Showing 237001 words to 240000 words out of 304445 words

Chapter 80 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

119

dogarai yaso yayi min waje da wadacan yaran, su bar min Hajiya Mardiya!" "An gama ranki shi dade!" Ta fita da sauri, na kalli Hajiya Mardiya na nuna mata kujera. "Zauna!" Yadda nayi maganar sai bata yi musu ba, a dai-dai lokacin da Sarkin dogarai ya shigo yayi waje da kowa na parlourn na kalli sauran jama'ar a parlourn. "Don Allah ku bamu wuri!" Ba musu suka wuce daya parlourna. Na gyara zamana ina kallonta da kyau. Murmushi nayi na kalleta da kyau kafin na ce mata.."Ba kuskurena bane ko na ƙaddara da ya shigo da Ijlal cikin gidan nan, sai dai kuskure ne da kika shiga harkata ko kike saka tana shiga harkata. Tsaknina dake bani da wata matsala. Amma abinda kike so a cikin gidan nan ba zai yiwu ba. Kome kika ga yana faruwa bani da lokacin duba shi, amma kina shiga harkata. Ijlal bata aikata kome sai da saninki, abu daya xan gaya miki Mai Martaba yana hutawa sannan kuma bana son a kirkiro tashin hankali, na kara fada domin ki fahimci abinda zai wargaza farin cikin Yarku, ta kula da yarta da yarta shine matsalar, gidan nan iya ruwa ne fidda kai, ni ina tausaya mata domin ita ta same ni, na kuma san tabbas aiki yana gabanta. Domin Tabbas idan ban kuskure jiba Mijinta aure zai kara, shin dani zata yi kishin ko da ita wacce zata zo, Maman Amrah ban shiga sabgarta ba kada ta shiga nawa. Sannan ki ja mata kunnen Allah subhanahu wata'ala ya ce ku shirya makircinku shine mafi sanin kowacce makirci. Idan tayi min ta sha gobe ban san inda za ta yi ta sha ba zaki iya tafiya!" Haka ta fita har zata kai bakin kofar na ce mata. "Mijinta ya gaya mata abincin da za ayi a walima ya biya ayi kome hatta inda aka kai nawa da nata da bambanci, ki tambaye ta hala ta boye muku ne!" Juyowa tayi tana kallona cike da mamaki, gyada mata kai nayi ina nuna mata hanya. "Zaki iya tambyarta! Ki ja mata kunne idan ta ce zata yi dani zata wahala ma gaya miki ne a matsayinki na Uwa, kuma a matsayina na Fulani Babba, ba umarni ba ne shawara ce kyauta" Fita tayi a fusace, sannan na tashi na nufi parlourn dole na tsaya da kafana dole na kwaci kaina. Ni ce kaina nice zan tsayawa kaina dole naso kaina na koma ki kowa idan ina son na zama nice a filin. Ina shiga na samu suna ta hiransu kamar irin sun saba da junansu for long time. "Ku fito!" Muka dawo parlourn, a hankali gidan ya fara samun baki matar Salim da Abdulhafiz suka zo, Mai Bauchi ma na ji da shi aka yi radin sunan kafin wani lokaci an cika bangarena har waje, Nady dama tun haihuwar muke waya da ita har take bani labarin gorin da Ijlal ta mata, wai ai ita da haihuwa sai dai tayi kashi a masai. Murmushi nayi nace mata Allah ta kyauta. Taso ayi sunan da ita na ce mata a'a tayi zamanta muna bukatar cikinta da ita kanta.
Bayan anyi la'asar na sauya kaya, wata kamfala na saka daga Dakar aka kawowa Mai Babbar daki, ana gab da za a fara walimar ta aiko mana ni da Mai jego da kuma na Nady aka kai bangarenshi, ita mai jego taci buri akan kayan sunanta musamman da aka gaya mata nayi wanka anyi min Makeup, fitowa aka kara gyara min kwalliyar da daurin dan kwalin, a kalla kudin kampala zai kai Naira dubu dari da wani abu ban da aikin da aka mishi. Ina da takalmi da jaka da na saka a kan kayan na yafa mayafi, muna shirin Fita Faruq ya zo. "Yana son ganinki!" "Ok?" Na gyara zaman mayafina da jakar na rike don pose ce a hankali na fito daga cikin gidan ina take mishi baya, a harabar gidanshi na same shi da ita da mai daukar hoto sai yan uwansa. Wani ikon Allah sai ya kasance duk lokacin da muka saka kaya ana samun code dress da ni da shi, haka yasa ina zuwa kayan jikinshi skyblue ya shiga da Kampalar jikina wanda shima fari ne da ratsin skyblue. Mayafina fari ne haka takalmin channel ne fari. Sai white gold da na saka a wuyata da sarka da abin wuyar. Hoto aka dauke mu, mu uku sai ni da ita tunda na lura bata son bani babyn, yana rungume da Babyn aka mana da shi na daura kaina a kafad'arshi na lumshe idanuna. Sai wanda nayi ina dan kwance a kirjinsa ina kallon fuskarshi, ina wani murmushi. Da kuma wanda aka min ina kallon babyn ina gyara mata bam dinta, ba sai Mai jego ta koma gefe ta zama yar kallo ba, ai wallahi ni da ita babu shi babu gani. Wani hoton da muka yi da shi mun dan hade goshinmu da shi. "Best couples for year!" Inji Bilqis tana mai gyara hoton ta daura a kan IG dinta, kafin wani lokaci an shiga mata like da comments, kafin ta daura na mai jegon. A can ƙasar comments din wata ta ce. "Kutumar Uba, Ikhlas de troublemaker ta cinye yarinyar nan wanka, wayyo Allah my friend kun ga Amira Kuma Head girl ta kankarowa Brighter children model school daraga sai dake Troublemaker!"
A hankali wasu side suka fara Comments wata ta ce, "ba ita aka sake hoton nude dinta ba kwanaki?" Wata ta ce mata. "Da alamu tsohonki ya ajiye kudin beli na masarar da zai ci na tsawon wata uku zai kare a tsakanin kotu da police station."
"Toh dai ku rufa mana asiri, Princess Billy ce ta daura kada ku ja ayi trace number mutum har kabarinsa!"
Wato lokacin da video ya fita Princess Billy tana cikin wanda suka saka ai yi ta kama yara ana cin ubansu, ita fa mulki a jininta yake shi yasa bata shiga harkan kowa haka ta saka a page dinta na Tweet inda aka gwabza wata arniyar turanci tare da kiran kiran Fulani Babba da lambar yabo da iya sanin kanta.
Gajiya nayi na ce mishi. "Zan koma ku karasa da uwar Baby!" Ina fita ta fashe da kuka, takaici ya sa shi barinta nan ya mikawa Bilqis babyn ya shige, Daularh da Kubrah suka ja tsaki suka barta nan tare da kiranta munafuka, idan dai Ikhlas ne bata ga kome ba don kaniyarta.

Ilham da take rike da jakarta ta bata tissue ta goge hawayen tana fada mata. "Idan kika cigaba da nuna rashin hakurinki kowa zai juya miki baya. Yana da kyau ko zaki nuna yanayin an miki laifi ba ta kuka ba shima zai gaji da bin bayanki sam baki iya acting ba gashi kowa ya fara ganin laifinki wallahi wacece Ikhlas da zata saka ki kuka?" "Amma kina ganin abinda tayi min ta kwace min mijina da Y'ata!" "And so what? Idan kika ci gaba da rashin hakuri zata kwace kowa da kyawawan halaye."

Haka suka fita kowa ya ganta yasan tayi kuka, kowa mata Babyn aka yi suka ta hoto kafin Malamar da aka kawo tayi nasiha, tayi nasiha sosai har da maganar bin bokaye. Tayi magana akan illar shigar mata mugun yanayi wanda yake kawo a haifi yara wrong path.
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 78
Yadda ta nuna mana kuskuren da mata ke yi akan namiji yasa ni jin tsoron Allah ya kamani, na kuma saka a raina namiji ba zai zama sanadin shigata wuta ba. Haka tayi wa'azi mai shiga jiki. Tana gama nasihar aka fara raba abinci, hankalin mutane ya dawo jikinsu. Inda nake aka kawo min Babyn cikin girmamawa. Na juya ina kallon Yeemar. Matsowa tayi tana min magana."ki yiwa Aunty Shukrah da Nu'aymah magnaa su kawo kayan nan!" Haka ta wuce wurinsu, ta gaya musu aka shiga cikin gidan aka fara fito da kayan da nayi na Amiratul Zaitunah. Ana kowa min na nuna mike a hankali na isa gaban Dangin Ubanta. Na mikawa Bilqis Yarinyar cikin mutunttawa na ce mata. "Gashi nan a mata ado da kwalliya da shi, Allah ya rayata tafarkin addinin Muslunci." Aka shiga ajiye kayan a gabanta. Bayan na koma mazaunina itama ta mike aka bata mic ta ce min. "Mammy muna godiya domin kin cancanci a kira ki da Mammy domin ba kowa bane yake iya ajiye kome ya rungume alkhairi domin a zauna lafiya. Gaskiya matuƙar aka cigaba da zama haka gidan Dan uwana kuma mai martaba ya samu tubali mai kyau da har karshen rayuwarshi zai yi alfahari da samun mace irin haka. Irin wannan alkhairi da yawa haka! Mun gode sosai." Sannan ta juya ga kayan su da aka fitar ta ce. "Baya ga wannan, Mai Babbar daki ta bawa Amiratul Zaitunah, gida a sabon unguwar GRA, wato new g.r.a, sai kyautar zunzurutun kudi naira miliyan daya ga Uwar Amiratul Zaitunah, sai sai Fulani Hadizatul kubra ta bawa Amiratul Zaitunah kyautar fili ga takardun da kudi dubu dari biyar, sai Fulani Balkisu ta bawa Amiratul Zaitunah kyautar shanu biyu da raguna biyu babban gidan gonar kifi a tsohuwar Fadama! Sai Fulani Zainab Fulani karama ta bawa Amiratul Zaitunah Kyautar kudi da sarkan gold da kudinsu ya kai miliya daya da rabi. Wannan sune abinda iyayen suka bada wannan akwatinan kuma namu ne muka hada sai na Baban Amiratul Zaitunah gashi nan guda goma sha biyu, na mu goma goma gasu nan, sai na Fulani Babba itama guda uku Allah ya raya Amiratul Zaitunah. "

Wani irin dad'i ya cika ran Ijlal ko ba kome an kankaro mata darajarta, haka yasa har aka gama taron Gimbiya Bilqis ta ce na tashi mu zaga na gaida iyayensu. Mikewa ina gyara zaman mayafina, ta fara gabatar min da Yan uwan babansu mata, ina gaishe su tare da mika musu Yarinyar wai a bisa al'adar masarauta nice zan zagaya da yarinyar ana saka mata albarka,, ina godiya nan uwar jinjira ta sake cika tana batsewa, har muka gama aka dawo da yarinyar muka mai da ta wurin Uwarta da take hararana ita da fukafukanta, haka aka yi taron lafiya da za a tashi aka bi ko wani table ana raba musu kayan suna wai ita kanta Mai jegon bata sani ba, tsakanina da Uban Yarinyar aka yi da faruq, jaka ce da turmin atamfa mai hoton babyn ita ɗaya sai hoton Ubanta a kasa, nan suka yi ta zagina suna ganin na tare kome tow ko ita bata san cewa zai yi wannan abin ba, kuma ai ya bata kudin da tace zata yi abin rabo, gaskiya a cikin jakar har da takeaway da kayan makulashe, sai gift kala kala, ana haka sai ga yan uwanta suma sun dauko na wurinta suka yi ta rabawa. Dama ni tun da aka kawo Faruq ya cire min ya ajiye a wurin mai gidan, shi yasa da aka zo rabo nace kada a bawa yan gidan mu, amma ita don zallamar mutanenta har akwai masu karba, bayan an tashi na tabbatar an sallami kowa Hajja sai mita take tana faɗin. "Fisabiilillahi Abu baki da imani, haka kika mana asarar takwai nan idan da kirista ne yayi haka sai a ce don baya kallon gabar ko bai da imani amma kina musluma kika ci amanar addininki tow dai kada ki zama wacce aka saukar da ayatul munafukai akanta. Wannan ai rashin mutunci gara da ban gayyato Tarasulu ba domin da na muzanta gashi na gaya mata har da takwai dinta zan kawo mata kada ta ji kome domin mijin jikata aka yiwa haka!"
Daulah kuwa ta ce mata. "Gaskiya ba a kyauta miki ba, ina laifin a baki naki tun kafin a fara rabo, sai ta ce kada a baku yanzu don Allah meye ribar haka gaskiya wannan ba halin muslmin kwarai ba ne " "Yo ko kirista na kwarai ba zai aikata wannan tuggun ba, domin ina ganin lokacin da take kyafta musu idanu tana musu alama da hannu, tow buni ya tabbata da mai zunde mai rad'a irin gani shagirigibau kada a bani na ce a kara min ina ganin wanda aka basu guda goma ma!"
Shigowa naji Daulah tana ƙara faɗin. "Gaskiya ayi miki adalci!" Da yake wasu suna sallah itama Hajjar sallah tayi take ta rigima, da sallama ya shigo suka amsa mishi, Faruq ya shigo da babban buhu, cikin niman rigima ta ce mishi. "Salamunu faransa, fisabiilillahi akwai adalci cikin lamarin takwara kuwa? Ace anyi rabon arzikin a gidan nan haihuwar Gimbiya Zaitunah amma a hanani takwai, gashi ja gayawa Tarasulu da kawayenta zan kawo musu takwai da kayan dadi da aka yi a gidan jikata. Amma yarinayr nan da yaƙe babu Allah da Annabi Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, a ranta yarinyar nan ina kallon take zunde da yafice da kyafce wai duk kada a bani. Don Allah ka gaya min gobe na sake zuwa gidan nan idan an yi haihuwa? Ni jikar mai kalwa!"
Murmushi yayi yana kallonta ya ce mata. "Matar karfe shine baki nimo wani ya kawo ko bangarena ba? Ai wannan dole na miki adalci, saboda Allah dai ba a kyauta miki ba, an nuna miki rashin Adalci!" Gyada kai tayi tana faɗin. "Kun ji dai da yake shi adalin sarki ne ai gashi nan ya fadi gaskiya kaf duniya babu wanda ya kai ka gaskiya domin adalci dai gashi nan ka yi min shi, ni jikar Mai kalwa."
Juyawa yayi ya kalle ni ina kwance a dogon kujera ina fara da kaina ya ce min. "Fulani me yasa kika hana a bawa Hajja takeaway?" Juyawa nayi ta kalleta idanuna a matuƙar gajiye na ce mata.."Hajja yaushe na ce kada a baki abu?" "Laahalilallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Takwara kina nufin karya na miki?" Sai ta mike tana me gyara zaman hijab dinta. "Tunda abin ya koma yar haka gara na koma gidan Junaidu kafin yarinyar nan ta karyatani da girma da tsufana!"
"Ayya Hajja me yasa kike haka ne? Abin nan bata hana ba cewa tayi ta ajiye mana, a sallami mutanen arziki da taro ya haɗa!" "Asma'u ni bana cikin mutane arziki kenan? Gaya min a gayyar sod'i nazo kenan, ka gani Salamanun faransa, daga uwar har yar sun mai dani gayyar sod'i!"
"Faruq!" Ya kira sunanshi yana dariya tare da juyawa yana faɗin. "Gaskiya ba a kyauta miki ba, duk wanda yayi haka dole a hukuntashi." Babbar leda aka ciro wanda ya fi wnada aka raba Faruq ya mikawa Hajja, sannan ya ce mata. "Kaka abokanki su nawa ne?"
"Kaga akwai Tarasulu ita ta min ƙawancen aurena da Malam Gobir, akwai Jumai yangwan, akwai Laraba mai kunu, akwai Sodangi mai koko!"
"Hajja don Allah ki daina kunyata ni!"
Juyawa yayi ya ce min. "Malama mind your business!" Kamar tasan me ya fada ya ce mishi. "Atow midan yi guzinan ya fada, hala ka gwabza mata turancin nan bai shakuwa ne ko?"
"Hmm ina jinki Hajja!" Bai rufe baki ba aka buga kofar katon tire aka shigo da shi wato Sarkin dogarai ya kawo nama ce gasashiya tana wani irin kamshi aka direta a parlourn, kamshi ya cika ko ina. Ya kalli Hajja cikin kulawa ya ce mata. "Ina jin ki matar karfe!" "Hmmm Allah ya jikan Malam lokacin yana ji da ganiyarshi, haka zuwa tukuban dan na ayee ya sayo min..." Tari na fara ina buga kirjina kamar na kware, kowa yasan dakatar da Hajja nayi bana son abin kunya, amma kuma sai na fahimci suna jin dadin dadin maganarta.

"Sannu ba dai ganin namar yasa kika kware ba zaki kwashewa namar kurwa tun baki ci ba, salon muci ya kasa wucewa wuyarmu!" Aunty Nu'aymah da ta idar da sallah ta cewa Umma. " Ya kamata mu wuce gida dare nayi!" "A'a ga nama nan yanzu za a kawo fura da nono." "Ai wato Abbanku zai yi fada ne!" "Asma'u kada ki yiwa Malam sharri domin shi waliyn Allah ne Gara kawai ki jira muci mu tafi!"
"Ba kome bari Baby ta muku park dinsa sai ku tafi da shi!" Cikin jin haushi Hajja ta ce mishi. "Wacece bebi? Ba dai jarirayar da aka yi suna ba?" Sam ya manta a gaba waye yake, ya shiru yana mai mikawa ya ce mata. "Takwaranki!" Rike baki tayi tana salati. "Innalillahi wainnalihir rajoun, Allah mun gode maka da ba ka kawo mana tashin alkiyama nan kusa ba, wato ita ce bebi Allah ya wadaran naka ya lalace tow fulunbotu idan dai bakin cikin bai motsa ba tashi ki yanka mana! Bana son hassada! Sannan ki yanka har da nasu Tarasulu!" Kamar bakin ciki sai kashe don don takaici kallonta nake ina hararanta amma matar nan tayi kamar bata san ina yi ba, sai da na kawo wasu container na yanka musu na zubawa kowa, Faruq ya shigo ya yiwa yan uwansa magana na mike tare da shiga kitchen na dauko kular abubuwan da na ajiyewa mai babbar daki da za a kai mata, abubuwan da nayi da kaina na cire musu da turaren wuta da na jiki abubuwa dayawa na hada har da wasu material da na siyo a Scotland, na hada musu bakiɗaya har da na Aneesah, na bisu da shi har bangarensu na kai ina musu godiya yaransu na basu zavin yan 1k guda goma, ina kara godiya. Bayan fitana ya ce musu. "Da fatan kome ya tafi daidai!" "Alhamdulillahi kome ya tafi dai-dai!" Suka tab'a hira ya basu nasu jakar, wani abin mamaki shine Ijlal bata basu jaka ba, ko haushi ta ji ko me, yayiwa yan uwansa bayani yadda kome ya tafi da sanin mai babbar daki.
Wannan yasa Aneesah kunya ya kamata, haka suka bar gidan suma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login