Showing 288001 words to 291000 words out of 304445 words

Chapter 97 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

61

tsaya mishi a rai, addu'a yake Allah ya bawa Ikhlas ciki idanunsa sun cika da kwalla. Yadda take abin very emotiona, and so touching heart, yadda nake yiwa yarinyar sai ka zata ni ce na haifeta yarinyar kamar ta fado a kan cinyar Uwarta, takowa yayi ya dauke ta, ya tawo gabana ya mika min, wani irin ihu tayi tare da zuba min yawu tana murna wani irin abu ba gani cikin idanunta na farin ciki da jin dadi. "Amimina!" K'amk'ame ni tayi tana dariya. QMikewa Uwar tayi ta rike hannunta. Yana girgiza mata kai yana kallon yadda yarinyar take ta murna ina biye mata, haka muka gama wasarmu na mika musu yarsu, suka tafi sai a lokacin ne ya juyo yana faɗin. "Zamu tafi Us ne ganin likitan Amiraah, Nadiyyah tana can itama !" Murmushi nayi nace mishi. "Allah ya tsare!"daga haka na cigaba da karyawa ni kaina nasan cusawa nake amma saboda karfin hali da kada ya gano lagona yi kamar bai dame ni ba, shi fa lamarin namiji kamar shafar Aljanu ne ko nace kwaya a lokacin da kuke dinkewa yake ji dake a lokacin da baya yi da ke tsohuwar motar a kori kura ya fi ki daraja irin wanda yana tafiya yana k'ikar k'ikar, idan nace bana kishinsa da wadannan matan nayi karya kawai Allah ya so ni ina cikin matan da suke da bala'in zurfin ciki da boye abinda yake faruwa ko yake ransu, kuma nasan ba kome ya koya min haka ba sai aure domin da na taso kamar wata sakarya ce yanzu da nayi aure na gamu da zaman gidan miji yasa na bude idanuna.

Ina son Yara, ko ba nawa ba haka yasa bayan tafiyarsu da yamma can aka kawo khairat daga Gombe, kasa boye farin cikina nayi ina murmushi hawaye na zuba min, na rungume ta ina jin son Yarinyar, musamman Mahaifinta, a hankali nake shashekar kuka. Mai Babbar daki ta ce min. "Ban cire rai da samun ciki a gare ki ba, ko wani mutum yana da tashi yanayin ne Allah zai kawo!" Gyada kai nayi, tun daga ranar fa na daina zaman kadaici, gani da abokan hira gidan ba kowa Wildat ma nan ta dawo da zama. Yarinyar nan haka xan kaita spa dinmu a mata lalle da kitso, nima haka. daya daga cikin matan da suke min aiki take zoyalata da cewa. "Da alamu kina son gyara kafin Oga ya dawo?" Dariya nayi nace mata. "Akwai Maman Hidaya and khairat,kankat ce wurin kayan gyaran jiki bana shakkar maganinta, kwana biyu da bana sha ma ai naga yanayin sauyi daga gare shi. Gyada min kai tayi, da ta gama min gyaran na dauki Y'ata muka fito a hanya na kira Maman Hidaya and khairat n ace mata. "Baiwar Allah sai ki bar maraniya a gantale, don Allah a min hadin kayan sa mai gida tsalle." Murmushi tayi ta ce min. "Ran Fulanin Zanzabira ya dade ai manya irinku bama musu shishigi yanzu ka ji ana cewa gyara kintsi!" Dariya nayi na ce mata. "Kai Maman Hidaya, ina son kaya Royal parkage za ayi min wanda zan gigita dan mai babbar daki!"
"Fulani Babba an gama in sha Allah jibi a je a karba miki a tasha!" "Zan tura miki sako yanzu in sha Allah!"
"Na gode sosai!" Na kashe wayar na tura mata sakon, sai da na gama wayar na shiga motar domin ba isa. faruq ya ji abinda ya nake ba ya ɗauka asiri nake yiwa ogansa. Yanzu da bikin Ilham ya kusa ba karamin busy muka yi ba, ranar da dare ina kwance da Khairat ina koya mata azkar, Ilham ta shigo hankalinta a tashe kamar zata haukace sai kuka take tana faɗin. "Fulani ki gaya mishi ba ni ba ce, ban tab'a lesbian ba ni da ko samari bani da shi don Allah ki rufa min asiri ki gaya mishi ban tab'a zina ba balle lesbian!" Rike ta nayi na zauna da ita a gefena na ce mata. "Meke faruwa?" Nan ta gaya min abinda ta sani da abinda ya turo mata. Saurayinta mai suna Abdulrazak, na amshi numbershi na ce ta je zamu yi magana gobe, kasa tafiya yai ta ce min. "Annan xan kwana ba zan iya tafiya ba idan na tafi gawata zaku ciro a dakina!" Nuna mata wuri nayi na ce ta kwanta kawai na kira shi. Yana ɗauka na ce mishi. "Barka da dare Malam Abdul!" "Barka dai Fulanin Zanzabira!" "Dama kana da number ta ce?" "A'a true caller ya nuna min haka." "Allah sarki , dama kira nayi akan kanwar mai martaba!" Jim yayi kafin ya ce min. "Na gaya mata mu rabu!" "Kana da shaidar ta tab'a aikata abinda aka tura maka?"
"Amma mutuncin iyayena!" "Akwai inda ya kai gidan da tafi to mutunci? Sai gidan Annabi Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, bayan wannan gidan babu wani gida da ya kai shi daraja, ba kiranka nayi akan lallai ka so ta ba, amma yana da kyau kafin ka yanke hukunci ka fara nazari, idan da Ilham zata yi zina tow tabbas sai an samu Mahaifinta ko Yayunta mijina da yan uwansa sun kasance mazinata, babu kazamta a cikin ahalin Yayari legendery family ne wanda ake kiransu da Ancient kaga kenan ba zasu yi zina ba, tun fil azal masarautar bata kasance cikin dattin zina ba,so zaka iya cewa zaka rabu da ita for same reason amma ka ce akan videon da aka tura ni, gaskiya kayi kuskure domin nima victim ce akan irin wannan videon, sai dai yau ina amsa sunan Fulani Babba ce saboda mijina da danginsa sun yi believe da mutuncina nazo gidan, idan zaka rabu da ita kai tsaye kace ba zaka aure ta ba, amma batun ayi wani abu aka turo ba hujja ba ne, akwai maza da yawa da suke sonta, sannan ita din ba kowa ta yarda da shi ba sai kai Please take it easy and kayi bincike." Daga haka nayi mishi sai da safe ban yarda ya yi wani magana ba, na kashe wayar, kallona tayi na ce mata. "Shiga kiyo alola ki zo ki yi sallah in sha Allah idan Alkhairi na cikin auren nan kafin nan da kwana uku zai motsa idan babu alkhairi Allah zai kawo wanda ya fishi. Daga haka muka bar zancen, tayi ta kwanta nima na kwanta
***
LA
Ashe tun bayan gama case din mu Nadiyya ya korata gida, tayi yaji kuwa bata tsaya ba sai America, tana kuka take gayawa kakarta ya tsaneta ya daina kula da ita, ita kuwa kakar saboda son da take mata yasa ta hau bayanta musamman da Nadiyyah ta ce ciki ne da ita, abin ya bawa kowa haushi kawayenta na can kuwa suna zuwa suka ganta nan aka shiga daura hoton Yarinyar a social media, musamman da yarinyar kyanta yayi sosai yanayin fatarta kamar irin na yan lati American, kafin wani lokaci manya kamfanonin pampers da irin su abincin gwagwani suka fara yiwa Uwar tayin tallar yar, a jikin mayukan shafarwa Yara da pampers...
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 95

Lokacin da Faruq ya ga abin ya nuna mishi, bakin ciki da takaici ya hana shi magana ya zuba mata idanun, sai gashi Ijlal tayi ta damunshi akan matsalar Amiraah haka yasa shi babu shiri ya shirya tafiya can, ya bar Faruq anan ya kula da wasu abubuwan da suke ta musu tafiyar hawainiya. Wannan abin ya dame shi, kawai hakuri yake domin yadda yake saka idanun akan Yaranshi Allah kaɗai ya sani. Sai booking din ganin likitan da zai ga Amirah kasancewar yana da damar niman alfarma bai nima ba kai tsaye yayi video call da shi likitan da ita yarinyar, ya nuna mishi yadda take, don haka ya ce a zo da ita cikin watan zai duba matsalar. Haka yasa suka fara shiri ya musu Visa a lokacin dangin Ijlal babu wanda ya tab'a zuwa wata uwa duniya sama da Amrah haka aka yi ta bata sako a whatsp bata saka zancen ganin likita ba cewa tayi second Honeymoon. Haka yasa suka ta mata fatan Alkhairi da ya gani ta sha masifa ya ce tayi wasa zata zauna a gida ya haɗa yarinyar da Ikhlas baya son hauka. Shi kuma ya fadi haka ne don ta rage rawan kai, ai kuwa ta kame kanta tsaf ta rufawa kanta asiri.

Tunda suka isa anyi hoto tun a airport, ake baza Capacity. Bai kulata ba har suka isa babban hotel suka huta dama ya lura ita bata damu da sallah ba, bayan sun huta har washi gari da yamma suka shiga Asibitin suka ga likitan amma yarinyar taki yin wani abu da zai saka a san stage dinta. Haka dai suka yi ta jelle har na tsawon kwanaki goma cib a ranar na sha ɗaya ne, wani hikima ya zo mishi ya kira Ikhlas da darare wurin karfe biyu agogon Nigeria, wnada yayi daidai da agogon can karfe uku na yamma, ya kirata suka yi magana ya gaya mata case din, ai kuwa suna isa asibitin ya kira Ikhlas, video call. A hankali take kallon wayar likitan yana kallonsu shi da wasu abokan aikinsa. Ta ce mata. "Amimi!" Wani zillo tayi tana nimanta, ta ce mata. "Nunu!" Ta fara wani irin kara tana kiranta. "Mammi!" Sauran likitocin na aiki tare da hada wayar da tv office din sai ga hoton Ikhlas da farin hijab ta ce mata. "Lulu!" Ta saka hannu a kirjinta tana wani girgiza mata kai, itama yarinyar tayi ta giggile tana kamar zata shiga tv,. "Amimina!" "Mammi!" A karon farko da tayi wani irin motsin da basu zata ba duk da kan yana kwance amma haka ta d'ago tare da mika mata hannu tana faɗin. "Mammi!" Yadda na kashe nata idanu ina jijjiga kai, itama sai ta kama yi tana kai hannunta kirjinta. "Mun gode sosai, Mrs kin yi abinda mu likitoci ba zamu iya ba, bamu san lokacin da kika dauka kina mata haka ba amma da alamu an samu kyakkyawar fahimta da dangantaka na musamman a tare da ku, mun gode idan muna bukatar wani abu zan miki magana." Sannan suka datse wayar, kafin likitan ya koma kanshi ya fara mishi bayani. Yadda wasu abubuwan zasu tafi ba tare da an samu matsala ba, sannan ya ce mishi. "A iya gwaje-gwajen da muka yi babu wani ciwo a tare da ita bayan na cutar ƙwaƙwalwar, shine amma idan aka son tayi amfani dole sai ana barinta da wannan da suka yi wayar, domin ita data ce zata iya kula da ita da rayuwarta." Sun yi magana Sosai da yake Ijlal bata office din, bayan sun gama ya fito kai tsaye ya yanke hukuncin da ya dace. Har ila yau bai samu ganawa da kakar Nadiyyah ba, ta maki barinsa ya ga Nadiyyah sai biyu suna zuwa tana hana shi shiga gidan, itama Nadiyya karfin hali ce amma tana son Mijinta. Tun daga nan ya tattara ya watsar da su, shi yanzu babu macen da ba zai iya zuba mata idanun ba, tunda Itama Ikhlas ta iya shiga tsakaninsu da mahaifiyarshi baya jin akwai wacce zata kara mishi wani abu ya ji zafi.

Haka da yayi kuwa yasa Ita, itama Nadiyya tunda tasan yana ganin ta kasa hakura tayi ta niman hanyar da zata ganshi amma ina yaki yarda su hadu. Wasa wasa suka kwashe kwanaki, itama Ijlal ɗin ba wani nuttsuwa tayi ba domin yau tana can gobe tana nan, sayayya kawai kafin su gama cinye kwanakinsu ta gama da kudin hannunta, ta fara zare idanu. Yana sane ya ki bata ko sisi bai aikata kashe kuɗinta ba, haka suka fara shirin dawowa gida ana saura kwana biyu sai ga Nadiyyah da shirgin kayanta, ta samu kudi ba na wasa ba, haka yasa tana zuwa ta fara yiwa Ijlal kyautar kuɗi mai yawan gaske ai kuwa mahaukaciya ya shiga zugata tare da gaya mata ai sai sun tashi tsaye kan Ikhlas don ko da yazo kullum sai ya kirata idan suna tare, kuma karya ce kawai da zalunci irin nata, ana ma sai da ta haɗa karamin fada sannan hankalinta ya kwanta. Ai kuwa tana jin Nadiyyah tana mishi diban albarka. Bai kulata ba, sai dai ya kula a ransa ba zata dawo mishi gida, haka suka kwana biyun nan suna rikici.. kafin suka dauki hanya.

Ita fa Nadiyyah kaf duniya babu wacce take sonta kamar Ijlal, itama Hajiya Mardiya take kara nuna mata hanya tunda suka san cewa asiri da tsafinsu ba zai yi tasiri ba, suka koma asalin makirci da tuggu, sannan ita Ijlal tana nuna mata ita bata kishi da ita sai Ijlal, wannan abin ya janyo Nadiyyah kara kaunar Ijlal.
****
Zanzabira
Mun cire rai da Abdul zai dawo ga Ilham, kada ku manta itama sunanta Zainab. Sunan Fulani Amaryan mai babbar Zainab duk matan sai da ya musu takwara. Haka yasa ake kiranta da Ilham, ranar da suka cika sati biyu babu feedback, ni har abin ya fara bani tsoron yadda ta shiga damuwa sai da na tambaye ta ko sun yi kazamin soyayya ne, abu daya ta fada wallahi sau daya yayi kiss dinta shima ranar da aka yi baikonsu ne, kawai Allah ya daura mata sonshi ne da son auren, amma ita babu wani abu bayan haka, ranar da suka cika kwana goma sha shida da asuba ya turo mata text. *My sorry, na gama binciken da zan yi ban san, yadda zan gaya miki ba.* Wurga min wayar tayi tana kuka. Dauka nayi ina karantawa na fashe da dariya. Kallona tayi na tura mata sai da hawaye ya zubo mata sannan ta bude sakon. *Ko a gidan karuwai na ganki, zan zauna da ke ba Virgin nake bukata ba mace nake bukata daga gidan Mutunci ki yiwa Fulani Babba godiya domin ta gaya min abinda na kasa ganewa, tabbas ko rike hannunku da kiss din da nayi miki sai da kika yi sati kina kin min bori wannan ya kamata ya isa na yarda kece uwar Yarana da zasu zo next generation na gode da Allah ya bani mace irinki!* Saka wayar tayi a kirji tana faɗin. "Aunty Fulani ina sonshi like crazy!" "Da sauki tunda baki haukace ba*, dariya muka saka, daga ranar muka kara shiri sosai ake gyarata kayan Maman Hidaya da Khairat kamar hauka musamman masu kyan da nake kara bata, sai Sabayar da take ta sha tana kara cikowa ta ko ina, domin ba wani kiba ce da ita ba sai tsawo kamar isha!

Sati Uku suka kwashe cib, sai gasu shi da Ijlal. Cikin gida suka zauna aka yi ta hidima da su. Lokacin bana nan mun shiga kasuwa duba wasu kayan kitchen da muka rasa. A matukar gajiye na shigo wujiga-wujiga, turus nayi ina kallonshi. Kamar munafuka haka yake bina da wani mayyen kallon kallo, ina shiga parlourn na cire Jalbab din jikina, na ajiye a gefen kujera na nufi kitchen abinci na zuba ban tsaya amsa gaisuwar Wildat da Sailuba ba na fito waje, na zauna sanye nake da riga da wando milk colour na zauna ina cin abinci. Sai da na nutsu na ce musu. "Ya hanya?" Wata Uwar harara ya watsa min yana dauke kai, "Sailuba ina Ummi?" "Tana parlourn Baki!" Sai yanzu na tuna ashe za a kawo lefe, amma ni da Bilqis muka shiga kasuwa. "Yaya kun sha hanya har ka ga yadda ka ajiye belly pot kuwa? Kambu ina ruwan gobe suna!" Banza yayi min ya cigaba da harkan gabanshi, a hankali nayi ta zoyalarshi da yake Amiraah tana barci nace mishi. "Yaya me yasa kake wani haɗe rai?" "Dalla Malama ki mana shiru kina ta abu kamar sakarya, idan kika tasar min Y'a fa?"
"Ke jahilar ina ce? Akanki take maganarta? Ko tayi dake ne? Kin san Allah ki fita idanuna!" Ya fada yana kara hada rai yayi na koma gefenshi da kyau, na shiga tab'a sajenshi, kafin na kai hannu kan cikinsa ina faɗin. "My Namamajo gaskiya ka fara motsa jiki lamarin ba zai min kyau ba Allah ka fara ajiye teb'a!" Yadda nayi maganar sai ya janyo ni tare da cizon kunnena, ƙara nayi na ce mishi. "Wallahi dai na rama!" Na mike tare da barin gabanshi. Sai da nazo bayan shi na sunkuyar na mishi chakulkuli. "Ni kika yiwa wannan abin.." ai mikewa yayi ta rike hamnunsa. "Binta zaka yi?" "Matata ce fa!" Ya fauce hannunsa, ya wuce ciki ni nasan zai biyo ni sai nayi pretend kamar ban san zai zo ba, na tsaya cire kaya kawai ya d'aga ni sama cak. Wani ƙara nayi tare da faɗin" don Allah ka bari yaya!" Sauke ni yayi yana kallon yadda na ciko tare da cewa. "Baby baki yi kewata ba ne? Ki ga yadda abokaina suka cika kirji, wayyo i miss you guys!" Ya fada yana kara kamo su, biye mishi nayi muka shiga motsa jiki da zukatarmu. Burum muka ji an shigo Ijlal ce, wani irin takaici ne ya kama shi, tunda ta shigo akan me zan saka na fasa ai kuwa na fara jan shi ganin bamu fasa ta ja tsaki ta fita kafin ta fita na ce mishi. "Babu na bude maka V ka sha?" "Karuwa kawai!" Motsi tayi kamar zai fita na rike shi, muka cigaba da sha'anin mu. Sake ni yayi a galabaice ya ce min. "Ki taimaka mu koma gida kin ji!" "Hmm na koma ka cigaba da lalata min rayuwar da kwanciyar hankali kabar ni a inda ake sona kawai!" Lallabani yake amma ina bokare mishi, ganin haka ya sa shi zuciya ya fita na bishi da gwalo. Wurin Mai Babbar daki ma ba sauki tace a'a ba zata ya koma wurin matansa..

Haka yayi ta jele tunda suka koma zai zo sau uku a rana daga fada ma ba gane kanshi suke ba, kwanaki da aka yi taron sarakunan daular Uthmaniyya, bai sani ke ba sai ma kara mantawa da wani zance a raina nace mayye zaka gama ka kyale min muriya, itama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login