Showing 111001 words to 114000 words out of 304445 words
ki kyamace ni, ina jin tsoron kada na rasa abubuwa dayawa. Ina son zama dake Zainab!" Tsoron da na hango sarewar da nake gani akan fuskarshi yasa ni jin babu dad'i, ba wai don ina sonshi ba, amma tausayi da jin kai wajibi ne akanshi. Katse min tunani yayi da maganarshi muryanshi tana rawa ya ce min. "Bakya sona na sani amma kuma na yi alkawarin!" Hannuna nakai bakinshi na ce mishi. "Ya isa haka!" Idanunshi yana rawa, ina ganin yadda idanun suke rawa. "Waye kai?" "Suna ta min dariya wai ba zan iya aikin ba, suna faɗin min kome!" Rike hannunshi nayi cikin nawa na ce mishi. "Waye ya isa ya maka dariya? Kai ban gansu ba, bana jin an haifi wani da zai kalli kyakkyawan gabana ya ce zai mishi dariya zaka yi nasara zaka da ce, majinyacinka zai samu lafiya har ta shi da kafanshi amma ka yarda da Ikon Allah, babu meye sai Allah." Kanshi a sunkuye yake yana wasa yatsuna. "Idan na gama aikin gabana zan gaya miki waye ni!" Takaici ne ya kama ni da yasan yadda nake son jin gulma da gurmi bawan Allah nan ba zai tab'a ce min haka ba,kun san yadda yan jarida suke Bala'i kaunar kanun labarai kuwa? Wayyo Allah na, kamar na rufe katon nan da duka, haka na wuce daki na kwanta ina mai lumshe idanuna, tsaki nayi tare da juya baya yasan ba bani labari zai yi ba ya zauna yana bata min lokaci kamar na rufe shi da duka haba don Allah, hararan kofar na kara kunna karatun.
Ban san lokacin da ya shigo ba, and the next day after sallah asuba, da na ga baya nan barci na koma ina tunanin mai ya ci? Don na cookie din yana dayawa. Sunkuyar da kai nayi sannan na wuce kitchen na hada abin karyawa wurin karfe tara saura takwas da minti talatin, kiran wayarshi nayi, sau biyu ina kira ba a dauka ba sai da na kira na uku dab zai yanke aka ɗauki kiran. "Assalamualaikum! Barka da aiki!" "Amin waalaikumunsalam Alhamdulillahi." Ya fada yana magana da wata kamar nurse ce. "Scaple?" Mika mishi aka yi, sannan ya kara da cewa.."gaze!" "Ka karya kuwa?" "Eh na tawo da plast din nan!" "Har da cookie din?" "Hmm!" Ya fada min yana cigaba da aikinshi. "Pad jini yana zuba duba min lita nawa ne ya zuba?" "Na ji kana aiki mai kake so a dafa maka? Sannan a kawo maka ko a jiraka da shi a gida murmushi yayi ina jin suna faɗin. "Doctor please a kawo mana!" "Ki min nawa su ma suna son cin girki amarya kawo musu?" "In sha Allah! Idan na gama zan gayawa Faruq ya so ya dauka!" "Shi kenan!" Aka kashe wayar.
A lokacin da ta kira wayar.
Yana bude kan mutumin ne, wnada ya ke yiwa aikin cire ƙari akansa, lokacin da ya bude murmushi ne ya kwace mishi, ganin ƙwaƙwalwa dan adam yana saka shi jin wani irin kauna da duk wani abu a ransa, yau da yake aikin sai yake ganin kamar bai tab'a ganin ƙwaƙwalwar mutane ba sai yau, a hankali ya kai hannunsa tare da shafa kan yana jin wani so da kaunar ƙwaƙwalwar, girgiza kai yayi cikin wani irin shauki da dad'i yake ji, shafa inda ƙarin yake yayi yana mai saka aska ya bare ledar da take lullube da ƙwaƙwalwar farko, sannan yayi na biyu. Murmushi ne mai cike da kauna, asalin kauna da soyayyar brain din mutane ya cika mishi zuciya, jin shi yake kamar ya dauke ƙwaƙwalwar ya boye yana gani yana jin dadi da nutsuwa. Kamar yadda nurse idan sun ga vein suke jin dadi har da kwadayin soka mishi allura haka Faris yake hadiye yawun bakinshi yana jin wani irin dad'i mai haɗe da gardi, baya jin a duniya za a mishi abinda zai saka shi ya bayyana kanshi kamar ace mishi yayi aikin ƙwaƙwalwar bil adam, har wani jan nishi yake irin na yaji dadin da bai tab'a ji ba, gyada kai yake cike da annashuwa. Haka ya bude ledar ya saka pad da sauran audiga ya kashe jinin sannan ya fara ƙoƙarin cire ƙarin, yana yi yana kallon jinjiyoyyin da suka samar da ƙarin, a hankali yake cire duk wani jijjiyar jini yana raba shi da ƙarin, a hankali kamar yana wasa da kan har Allah ya taimaka ya cire ƙarin daya daga cikin likitocin suka dauka, sannan ya koma daya bangaren shima ya cigaba da aikin cirewa kafin ya cire bakiɗaya, murmushi yayi yana kallon wurin a hankali ya dauko wani irin na'ura ya fara kona bakin jinjiyoyyin yana saka musu abin kamar yana kona su, sannan ya sake saka gaze ya kwashe jinin tashi yayi yayi mika sannan ya koma ya zauna ya cigaba da kona jijiyar, kafin ya shiga tashin inda ya kwanta yana kallon aikin dinke jinjiyoyyin kan yayi sannan ya kalli daya daga cikin assister dinsa ya ce mishi. "Ka mishi magana muji!" Ya fada yana juyar da wuyarshi. Taɓa mutumin yayi ya ce mishi.."Alhaji ya sunanka?" Lumshe idanunshi yayi ya kuma buɗe sannan ya ce mishi. "Alhaji Hamisu Abdulrahman!" Da yake yayi gyara zama yayi ya ce mishi. "Shekaru da iyali?"
"Alhaji shekarunka nawa?"
Shiru yayi,.a hankali ranshi ya motsa, duba kan yake yana son ganin me yasa bai tuna shekarunsa ba? "Shekarunta sittin da takwas, ina da mata biyu Yara goma sha uku, uku suna aiki biyu sun kusan gama jami'a, guda hudu bana zasu gana secondry school, guda uku suna aji daban daban na primary,sai daya da yake shan nono ba a yaye shi ba!" Gyada kai yayi yana cigaba da aikin. " A ina yake aiki?" "Alhaji a ina kake aiki?" Nahco hukumar alhazzai na jahar zanzabira." "Ku saka alluran barci mu karasa aikinmu!" Haka suka cigaba da aikinsu. Har wurin karfe hudu saura.
---
04:30pm
Na kwashe mishi tuwonsa da nayi,.yayi laushi yayi kyau sai kamshi yake yana tashi, dirin mota da naji na zata faru ne sannan bakiɗaya na manta ban bude kofar shiga gidan ba, ina ji ana buga kofar tare da kunduma Ashar na fahimci dangin Ijlal ne, ban yarda na fita a haka ba sai da na dauko hijab dina sannan na saka na kuma rufe kofar dakin kafin na dawowa na bude kofar, ban saurare su ba na juya ina me barin wurin, don kada su min abinda zai bani haushi na musu rashin mutunci. "Ba dole ba, wani yayi rawa balle dan kaɗi an zauna sai asiri ake anan niman miji da dangin mijin!" "Ai dole an gama ihun ba a son miji tsoho da tsohuwa na can na bin halara!" Babu amfanin biye musu akan me xan saka ma biye musu ma? Kwashe abincin nayi na saka na mai babbar daki, da nashi da Faruq, sannan na koma na juye kome na rufe na wanke kayan da na bata wurin karfe biyar na kira shi. "Assalamualaikum! Ya aikin?" "I'm done!" "Alhamdulillahi congratulations!" Na faɗa ina jin wani dad'i yana ratsa ni ko na kome yayi nasara, don haka na ce mishi.."na gama zo a ɗauka!" Na faɗa na kuma karawa da cewa. " A ci a hankali domin yanzu na kwashe!" Murmushi yayi yana jin dad'i.
Ina cikin aiki ina jin habaicin da suke min da ba'a, haka bai saka naji haushinsu ba tunda ko sunana suka kama ba zan kula su ba, ina zaune a kitchen Faruq ya iso haka na yi ta fito mishi da abincin na ce mishi.."kafin ka isa ka tsaya ka bawa mai babbar daki na ta. Wannan kuma naku tare !" Wani zare idanu yayi yana faɗin.."yau kin gama da ni wallahi!" Dariya nayi na ce ya kai zasu ci zan gaya mishi, yana fita na wuce kitchen na tura mishi sakon.
_Abincin nan kai da Faruq ne! Kada ka cinye a hana shi_
Na tura mishi can kuwa sai ga sakonshi ya dawo min shida.
*Akan me zaki hada ni da shi? Salon ya rena ni! Ni na hakura da abincin*
Akan me xan bashi hakuri sai na tura mishi da cewa.
_Ok ka ce ya ci ya bar sauran zan ci dama ban diba ba_
Turo min da jan emoji ya yayi ya ce min..
*Hauka nake da zaki ci abincin wani kato? Ki ji da kyau cinyewa zamu yi min wanke kwanikan*
Da dariyar na wuce dakin bayan ba rufe kitchen da key, Ijlal ce ta tawo gabana tare da tsare min kofar. "Zan shiga ne?" "Akan me? Bayan abinda kika yi ya kore ni, yanzu ma bai ishe ki ba sai kin kara min da Wani?" "Kin ga ni ma ban san hujjarshi na rufe dakin ba, bani wuri na wuce." Tasowa yan uwanta suka yi, muryan mai babbar daki ya ratsa mu. "Kul nace mara kunya idan bata zauna dakinsa ba a ina zata zauna? Dakinki zata zauna bayan abinda ya kama ki kin aikata shine bari ki sake aikata wani? Yau zai zo ya kawo mana karshen rashin mutuncinki!". hakuri suka fara bata tana fada inda take shiga banan take fita ba. Ta ce mata. "Ba tone-tone ya kawo ni ba, na zo na gaya miki ne idan zaki wanke zuciyarki, ku buga kishi mai tsafta Bismillah idan kuma kina da wani abu a ranki ga hanyar, bana son tashin hankali kece karama kece kullum ake samun matsala dake, haka ta gama fadar sannan ta juya zata fita ta ce min.."duk wata mace jaruma ki binciki tarihinta bata samu kome ba sai da ta sha gwagwarmaya, ita kamar kanwa ce a gare ki , kiyi hakuri da ita ki kauda kanki zaki sha mamaki" fita tayi na bi bayanta har waje ina mata godiya harara ta tayi cikin murmushi ta ce min.."Mara kunya kamar da gaske."
Tana tafiya na dawo basu daina habaicin ba, tunda na shiga na rufe kofar ban bi ta kansu ba.
*
Faruq yana bawa abokan aikinsu abincin, ya koma ya kai na Ogansa office, daidai fitowarshi daga wanka kenan, murmushi yayi yana kallon kulollin abincin cike da shauki, yana ganinsa yana cikin farin ciki amma duk ranar da yayi aiki a can baya ranar hatta hiransa na daban ne, saka hannunsa yayi yana zagaye kular abincin. "Sir tare da ta zuba mana!"
"Idan baki fa?"
"Yau kana cikin alkhairi dumu-dumu, ba zaka yi haka ba!" "Au haka ne? Tow yau rana ta ce kai ma haka ka min wancan lokacin da ta zuba maka naka kai ɗaya nima ni daya xan ci!" "Sir ta ce zata kira ta gaya maka!" "Eh ta gaya min ban yi niyya ba ne!" Ya fada yana kashe mishi idanun ɗaya. Mai abu sarki, amma bai ga laifinsa ba. Duk wani likita yana matuƙar tsoron a mutu akan table dinsa, haka yasa yake jin wani farin ciki, shi Faruq ba sabon abu ba ne ganin shi cikin farin ciki asalima haka yayi mishi dad'i. Haka dai yayi ta jawa faruq rai da yaƙe shima kwadayayye ne, kuma duk laifin Ikhlas ne da ta haɗa wannan rigimar ta haɗa musu rigimar sai da Faris ya gama ikonsa ya bashi abincin shima a tare suka ci abincin. Ya fita ya kara duba mara lafiyar ya samu yana ta barci, sai da ya gama duk abinda ya dace sannan suka fito, zuwa gida.
Lokacin da suka iso kallon.Faruq yayi ya ce mishi. "Ka huta gobe maybe sai jibi da yamma zamu shiga asibitin domin na gaji yau!" Tun farkon zamansu duk abinda yayi ya samu nasara tow ranar yana dogon magana har yayi ta dariya. A saninsa haka ne musamman yau da yayi aikin farko,.fita Yayi da kayan abincin yayi ta shiga da shi cikin gidan, sannan ya mishi sallama, kafin ya wuce abinsa. Ina kwance ya shigo parlourn, tashi nayi ina kallonshi. Don ban zata shi ba ne yana ganina ya zauna a kujera karban kayan hannunsa nayi na wuce dakin na hada mishi ruwan dumi, na kawo a karamin roba na saka kafarshi, kwantar da kanshi yayi da kujeran yana sauke numfashi. "Na gaji sosai! Ruwan zafi nake so sannan xan yi barci!" "An kusan shiga sallah kake kiran barci? Ba wani barciin da zaka yi sai anyi isha!" "A gida xan yi su. Domin xan iya faduwa a massalaci." Ya fada da gaske ban daki na wuce na hada mishi ruwan dumi na dawo na kalle shi," ko zaka yi wanka Ijlal tana jirnka." Bude idanun yayi ya kalle Ni kafin ya tab'e baki ya ce min. "Tayi miki hauka ne?" Girgiza kai nayi na ce mishi. "A'a sai kace wata mara hankali bata min kome ba, asalima fitowa nayi na ganta a parlourn!" "Nayi karya don bana son kallon da yake min irin nayi shagirigirbau, "karya kike munafuka, baki gaya mishi rufe min kofar da kika yi ba ? Anya zaki gamu da rahamar Allah kuwa? Mata sai munafunci ke ba zan ce miki mata ba ma yarinya...
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: AKunya ce ta lullube ni, kallon yadda nake rarraba idanu yasa shi dariya. "Zo ki min tausar wuyana Please!" Ya fada yana kallona. "Ni kuma fa?" Inji Ijlal tana kallonshi, ban san me ya mata ba don ni dai kaina yana sunkuye kunyar abinda ta min yasa na kasa d'aga kai na kalle shi. "Zo ki zauna anan!" D'ago kai nayi ina kallon abincin gabanshi, abinda na fahimta shine ijlal ni ce ya dace na yi kishi akanta, amma sai ita take kishina duk da Mai Babbar daki tana ji da ita amma bata gani, kusan haka zaman gidan ya kasance ya kwana da ita yazo wurina ya ci abinci har zuwa lokacin da Nadiyyah ta dawo, yadda ta tafi bamu sani ba, haka ta dawo bamu sani ba domin farkwa muka yi muka ganta, a lokacin da ta lura da na koma dakinsa da zama bata iya boye kishinta ba. Ta rike baki cikin mamaki take cewa. "Amma nan kika gama ihun bakya sonshi, me ya dawo dake dakinsa? Munafika " da yake bata ji kunyar gaya min magana ba, nima sai ban ji kunyar mata yaren da ya dace ba, na ce mata. "Na zo na dauki abinda kike dauka ne, naga duk abin wa dodo daya mukewa tsafi!" Nadiyyah yar jidali ta fara ihu da masifa da tijara, wucewa kitchen nayi. Don ni dai bani da lokacinsu, ina kan maganar mai babbar daki ne, abinci na daura don yanxu ma baya gari sun tafi Maiduguri akan wani workshop tunda yayi aikin nan yake yawo a tsakanin likitoci da sauran teams kuma wani ikon Allah sai gashi babban Ministan lafiya yana shirin kawo ziyara zanzabira, sannan zuwan da ministan lafiya zai yi zai shiga fada sannan zai gana da shi kanshi Salmanu Faris, bayan nan zai tattauna da wasu likitocin ƙwaƙwalwa a nan zazzaɓi da gwamnatin Zanzabiran bakiɗaya, a wannan lokacin bai gayaawa kowa ba daga ni sai Mai Babbar daki, domin da zai gaya mana daukata yayi muka tawo gidan da dare, muna zaune a ɗakinta. Tana kishimgid'e ta kalle shi tana faɗin. "Sadauki." Kallonta yayi yana juya lamarin, na fahimci bai iya bada labari ba ne sam. "Ummi ministan harkokin lafiya zai zo ganin asibitin nan!" Kura mishi idanu tayi kafin ta kalle ni, "ina jinka!" "Dama!" Sai ya fara sosa kai yana nazarin ta yadda zai bata labarin, data ma bude na fara duba BBC Hausa shafin su, labarin rangadin da ministan lafiya zai yi zanzibara ya ke page dinsu.."Mai Girman ministan lafiya, Alhaji Umaru Ghali Dawanau, zai kawo Zanzabira wata nasara ce ga shi kanshi Babban likitan ƙwaƙwalwar da ga marigayi Attahiru Shehu Yayari." Na karanta ina kallonta. "Congratulations!" Na faɗa ina kallon yadda yake dan murmushi. Zai matuƙar wahala ka hango wani abu a fuskarshi sama da murmushin nan sai ka nutsu da kyau zaka fahimci fushi da b'acin rai yana ninke bisa idanunsa. "Dama ku na gayawa kawai!" "A'a dole ayi yar walima!" Ware idanu yayi na d'ago hannuna na kai idanunsa bai janye ba, sai ture hannuna da yayi na ce mishi. "Allah na zata baka tsoron idanunka ne." Na faɗa ina kokarin mai da hankalina kan maganar mai babbar daki. "Ke ki ajiye sakarci ki fadi abinda ya dace." "Ummi ya ce a'a a tafi kawai a haka tunda baya so nima bana so!" Na faɗa ina kallonta, amma tsokanarshi nake ina yakushinsa da kafana gajiya yayi da abinda nake ya janye kafar. "Allah sai ka kai ni wurin Maluma!" "Dare yayi!" Jan rigarshi nayi nace. "Ummi ki ce ya kai ni naga Maluma!" "Tashi tayi ta shige ban daki ta ce. "Idan kun gama rashin kunyar ku bar min dakina barci nake ji." Ta fada tana jan kofar. Kunnena ya riko yana faɗin. "Baki jin magana!" Ya mike rike da kunnena. "Allah ka sake min kunnena." "Idan ban sake ba fa?" "Zaka biya ni ne idan ka cire min kunne!" Dariya yayi yana faɗin.."Sai ki yi kuma!" Haka muka dawo, sannan labarin ya fita, ai kuwa Mai Babbar daki sai da tai yar walima, Ijlal ta zo gidan tare da Nady, ni ban samu zuwa ba kasancewar makaranta mun fara exam.
Haka suka yi hidimarsu bana nan, ina dawowa na shirya sannan na zo nima, anan nake ta ganin iskanci kala-kala, dakin da na zauna na shiga na zauna abuna. Lokacin da na shiga Mai Babbar daki tana tare da baki, duk da a kishimgid'e take amma sai da ta tashi zaune ta saka a kira Mata Daularh, ina kwance rub da ciki, sai ga Daularh. "Lafiya kika shigo nan?" "Yunwa nake ji!" "Baki san hanyar kitchein ba ne?" "Dibo mata mana, ta dawo makaranta ga yunwa!" "Mai Babbar daki yarinyar nan kina saka mata pampas!" "Eh ba kome!" Ta fada tana kallona tana fita ta harare ni. "Dube ta yaushe zaki girma? Kawai kina ganin mutane kin