Showing 273001 words to 276000 words out of 304445 words

Chapter 92 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

90

kafin na ji sanyi a raina na tsira daga wannan mugun abun. Ba kowa a parlourn dakin Ummi na wuce na samu tana sallah, nima fitowa nayi na shiga daya dakin nayi alola na zo na fara sallah. Lokacin da na isar na koma na samu itama ta idar waya take da Aneesah daga yadda take fada na san ita ce. Sai da ta gama muka kara gaisawa. Ya mai jegon?" "Har muka tawo dai tana barci!" Gyada kai tayi tana faɗin.."Allah ya tashi kafada!" "Amin!" Na gyara zama sannan na ce mata. "Ummi baki zo asibitin ba?" "Allah ya yaraya ko nazo mai zan muku?" "Ki ga sabuwar baby mana!" "A'a haka ma ya isa, tunda ko gobe zan je!" Can yazo suka tab'a hira sannan ya ce mu wuce gida.

Muna isa wurin Ijlal ya wuce ni kuma na wuce bangarena, washi gari tun asuba ya gaya min ta farka..na ce mishi zuwa an jima zan duba su kafin na shiga wurin aikina. Haka aka yi na kira Jakadiya ta musu kome sannan aka tura Faruq da ita da bayin Nadiyyah da Juliet, ni kuma da na gama lokacin Faruq ya dawo. Shi ya kai ni asibitin, na samu Doctor Munirah tana kanta tana mata tambayoyi tana bata amsa, sai da suka gama na gaishe ta amma tayi kamar bata ji ba sai da Hajiya Altine ta ce mata. "Baki ji ana gaishe ki ba ne?" "Ayya lafiya Ikhlas!" Daga nan ta cigaba da yatsina fuska, ban ce kome ba na juya nayiwa Hajiya Altine sallama kafin na isa wurin Babyn. "Hi princess!" Na kai hannu zan tab'a budar bakin Uwar ta ce min.."Kinga tana barci kada ki tab'a ta Please!" Cak na dunkule hannuna, ban tab'a kumatunta ba na juya na kalli Nadiyyah, murmushi nayi ta kuka cigaba da cewa. "Nace kada ki tab'a min y'a tana barci." Kasa kasa ta ce. "Idan mutum bai san yadda wahalar daukar ciki yake ba ina zai san zafin yankar cire d'a!" Na jita na kuma kalle ta, wani irin mamaki na ji ya tsaya min a kahon zuciyata. Na zuba mata idanun da yake hankalin Hajiya Altine baya tare da damu. A hankali na sake murmushi. Sannan na bar dakin bayan ta bi ni da rakiyar tsaki da harara, haka na ji wani abu ya tsaya min a wuya, har na isa gidan radiyo babu wanda ya gane kaina. Gashi yau muna da program akan yadda ake samun matsalar mace macen auren da kuma yadda wasu abubuwan suka lalace.
Haka na hada nutsuwata, muka fara program cikin nasara da yake mun bude wayar sadarwa, a cikin wannan tattaunawar muka tsinci wasu bayanai na yadda yan mata da wasu zawarawan suna bude grps da sunan koyawa mata dabarun zaman aure, a yadda muka yi ta tattaunawa har wata ta kira take cewa. "Ni abinda ban gane ba anan shin ita budurwa tana ta san dabarun zaman aure? Idan ba yar bariki ba taya ta san yadda zata rike miji a hannunta? Sannan idan bazawa tayi haka ba zai bani mamaki ba, shin ita budurwa idan dabarun zata koyar mai yasa bata saka saurayinta ya turo aka aura musu juna ba, wannan abin a bayyane yake yan mata sun rasa kunyarsu a da can muna yan mata Bama zama cikin matan aure da manya amma a yau budurwa idanunta ya bude bata san kome ba sai rashin kunya da rashin hankali, sai anyi auren daga baya ka ga aure ya mutu ita me koyawa wasu darasi amma ta kasa rike Mijinta, Allah ka shirya mu.
A tambayar da na mata na ce mata bata ganin zamani ne ya zo da haka, ta ce a'a rashin tarbiyya ce idan har mace ta isa mace a kame aka santa ba a watse ba.bayan ta fita ne muka shiga tattauanawa Da Yeemar da yadda take hango gobe da irin matsalar da gidajen aure suke samu ta ce min. "Fulani Babba, idan kika duba maganar matan nan akan gaskiya yake, ya kina mace da ta shekaru goma sha a gidan miji wacce bata tab'a auren ba ta ce zata koya miki yadda zaki ci kwalar Mijinki?, Fulani Babba kada ki manta ita bata yi auren ba balle ta san wani irin hali mijin da take aure yake da shi ba, amma ta zauna tana gayawa wasu matan da suka san good side and bad side na mazajensu...
Ita da take niman shiga ina ita ina kirkiro abin da ba ita isa wurin ba, hmm Yan mata ko nace Hajiya ki sani ba fa zaki iya da halin wadancan jinsin ba, domin wallahi kaf duniya babu wanda zai iya da su sai Allah ke dai ki nime yarda Allah amma batun namiji ya ko kama shi a hannu ai ko danki ne sai kin haɗa da rokon Allah balle katon da kika ganshi da girmanshi, idan har halin sa na banza ne tow kenan naki mahaifin haka yake, Fulani Babba bayan ga Uba da Yayu maza babu wani wnada zaki fadi halinsa, shi mahaifinki kin ga yadda ya tafiyar da gidanku. Yayunki ma baki isa ki bada shaidar halinsa ba. Sai abokansa, Miji kuwa wallahi karyan kasa mace yace ta san halin shi. Idan muna son mu zauna lafiya sai mun mika lamarinmu ga Allah sai a zauna lafiya, shima zai shiga lamarinmu, naji Malam Adam disina ya ce idan har mace tana son Allah shiga lamarinta, ta shiga lamarin Addini ta shiga cikin addini, Allah zai shiga lamarinta, Allah zai sota, Mala'ikun Allah zasu sota. Al'umma zasu so ta. Sannan miji da danginsa zasu sota. Wannan rayuwa bai da fa'ida ka nisanta kanka ga Ubangiji. "
Yadda Yeemar take magana sai nake gani kamar da ni take maganar wani irin dad'i da nutsuwa nake ji maganar suna sauka a kaina da rayuwata take magana haka da muka gama program din na ke gaya mata gida zan wuce, haka muka fito aka dauke ta anan nake gaya mata haihuwar murmushi tayi ta ce min. "Zan zo na duba ta!" Haka muka rabu cikin dadin rai aka ajiye ta a gida, nima muka dawo gida. Na same shi a harabar gidan yana hutawa har an kafa mishi inda zai zauna shan iska. Karasawa nayi wurin na zauna ina kallonshi. "Ka leka asibiti ba ne?" yar shiririta tsaki ya ja, ya kauda kai yana kallon inda aka kewaye. Ya ce mishi. "Daga nan zuwa zan zuwa can, kiwon zaki zan yi!" Kallonshi nayi a razane. "Zakin lafiya? A ina aka tab'a haka. A'a wannan lamarin bai min ba!" Murmushi yayi, ya ce min. "Zainaba!" Kallonshi nayi kafin na sunkuyar da kai. "Me nayi na laifi a tsakanin Matana?" Shiru nayi ina kallonshi wanda na fahimci duk yadda aka yi an bata min shi rai ne. Murmushi nayi na ce mishi. "Babu kome, sai alkhairi da kake ta mana da kyautata mana!" "Tow me yasa idan na ce ga yadda xan yi kowacce take ce ba yarda ba!" "Allah ya huci zuciyarka!" "Ke daya ce bakya musu da ni me yasa?" "Saboda ba haka aka koya min ba!" "Me yasa ban isa na samu girmamawa daga sauran ba." "Kayi hakuri zamu gyara!" Yadda yake mita ina rarrashinsa, har ya hakura sannan na wuce ciki,wanka na shiga yi sai ga oga yazo nace mishi Barka da zuwa, tunda nayi barin nan ban sake fama da ciwon ciki ba, bayan barin wannan shine zuwa na biyu da yayi min. Haka yasa nayi wanka na gyara jikina sannan na fito, kitchen na nufa na zuba abincin da aka yi shinkafa da miya ne da salat Wildat ta shigo ta zube a gefena.. "Allah ya baki nasara takawa ya turo da Nama, kamar yadda ake yi duk wata na saka an gyara kome an saka su a inda ya dace, Malam Faruq ya amshi duk wani list na cefane na rubuta mishi, Allah ya baki lafiya da nisan kwana, Fulani na yi duk abinda ya dace saura ki duba ne!" Murmushi nayi na ce mata. "Na gode sosai! Allah ya bawa Ummarki lafiya ya jikinta baki zo da maganar amsar magani ba!" Gyara zama tayi tana faɗin.."ai tun ranar da kika bani a gaban Mai Martaba, ya dauke kome har ganin likita take yi yanzu, ai babu abinda xan ce sai godiya!" Haka yayi ta godiya na sallame ta.

Da dare ya ce na shirya muka nufi asibiti, ya same ta tana cika tana batsewa da alamu, sun yi wata yar tankiya ce ni ban sani ba. Daukar yar yayi ya gama mata wasa sannan ya ce zai mika min cikin fada da masifa ta ce mishi. "Kada ka bata y'ata wallahi ka bata zaa jimu!" A hankali na sake murmushi. "Kyale mata yarta!" Na furta a hankali, amma kasan raina wani irin ciwo nake ji. Ajiye yar yayi ya kalleta sai kuma yayi shiru. "Wannan shine godiyar da zaki mata?" Hannuna na kai bakinshi. Ina girgiza mishi kai. "Duk wanda yayi abu don Allah ya yarda da Allah ne kuma Allah ya yarda da shi yasa yayi haka kada ka lalata min ladana wurin Allah!" Wani irin bakin cikin ne ya cika shi.. ya sake hannuna daga bakinshi yana kallon Nadiyyah da take dariya ta ce mishi. "Kowa fa bukata yake bukata ya biya, don me za a saka min idanun? Idan da ace IVF aka min kin Isa ki ce zaki yi min wani magana ne? Da yake ku malaman tsubu ne kun saba ayi muku reward din abinda kuka aikata kada ki kara tab'a min Yarinya kuma ki gaya mishi, wallahi ya janye sunan da ya saka mata ko kuma wallahi ya shafa ya ji na ware da y'ata!" A fusace yayi kanta. Rike shi nayi nace mishi. "Sai me? Wallahi Nadiyyah bata kai ta bata maka rai ba, sam kada ka damu ai an fada zata mana butulci ban yi mamaki ba,tayi Yarinya kuwa ka janye mata sunan ka saka mata wacce take so!" Daga haka na bar musu dakin bakiɗaya. Idan na cigaba da tsayuwa raina ne zai ta b'aci, haka yasa koda na fita barin asibitin nayi na je can na zauna, wannan ne butulcin da zata min dama? Haka nayi ta sakawa da kuncewa.. ji nayi ya rufe min idanuna, zama yayi na kalle shi na ce mishi. "Ya sunan Babyn!" "Safiyyah wai sunan sister dinta ce da ta rasu suna Yara!" Murmushi nayi na cigaba da wasa da yatsuna. Mun jima a haka sannan ya juyo da fuskana ya haɗa da bakinshi, mun jima sosai a haka kafin na janye bakina, na ce mishi. "Dare yayi!"....
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 90
Na fada ina cire bakina a na shi, haka muka dawo gida babu me magana a cikinmu, wani ikon Allah babu wanda ya kara taso da maganar a wurina ya kwana, washi gari juma'a ba zan je aikin na. Ina tsaye ina ta aikina..ya shigo yana mai taya ni shima. Murmushi na mishi, na ce........
"Da fatan ka tashi lafiya!" "Alhamdulillahi!" Ya furta yana taya ni aikin har na kammala, ana kawo abin karyawan cikin gidan na duba masa ce tun jiya na gayawa Uwar tuwo, kuma tayi abinda ya dace, miyar da nayi daban na zuba mishi. " A kai musu abincin asibiti nasan dukka gidan aka yi ko?" "Eh!" Na fito na cewa Ijlal ta je maza ya haɗa na asibiti a kai musu. Koda aka hada aka kai musu ni ban kara zuwa ba,.kuma shima bai min dole ba, kwanta biyar aka sallame ta. Ai ni na je tow Ijlal tsabar kishi ko bakin ciki bata je ba, tunda suka dawo ban kara shiga harkansu ba, sannan wani abu da na kara yi shine raba yin abincin gidan, kowa tayi nata. Haka yasa babu wanda na gayawa Mijin shima ya ji dadi an kashe rigima, Ita kuma Ijlal har yanzu tana hade da na gidan baki ɗaya hankalin kowa yana kan Nadiyyah ita kuwa sai wani fisga take, na tattara shirginsu na watsar. Da yake ana saka sunan sai bayan sati biyu, Bilqis tana zuwa ta ga yadda take wani fisga. Da yake bata da sauki itama ce mata tayi. "Kina wani abu kamar a kanki aka fara haihuwa? Kin manta muna da Amirah ne? Ko kin manta itama Ikhlas din Uku ta rasa? Ki daina haukar da kike yi idan har kina son a shirya dake tow ki watsar da wannan haukar!" Yadda tayi maganar yasa sai jikinta yayi bala'in sanyi ta kara da cewa. "Yara maza biyu mace daya ta rasa ba kin dauka don kin haifi mace sai mu yi ta rawan jiki akan ki ne? Ki sani bana tsoron kin rike yarki kin saka mata sunan da kike so but ki sani muna tare da macen da take kwantar mishi da hankali ne kina cewa zaki d'aga mishi hankali zamu tattara ki a gefe, mu kanmu muke so da Yaranmu son da zamu yiwa yarki shi ne zai cece ki!" Tana gama fadar haka ta fita ko yar bata taɓa ba. Wannan abin ya saka Hajiya Altine ta kira Ubanta ta gaya masa abinda yake faruwa, ya ji bakin ciki da b'acin rai don haka ya ce mata kada ta sake ta zo mishi gida da sunan ta rabu domin bai shirya ta masa zawarci ba, shi ba zai iya facing Iyayen Salmanu Faris ba.

Abin da Nadiyyah tayi yasa kowa ya janye, babu wanda ya shiga harkan dangin miji da danginta suke suka tsaya akan aikin dama ban da gulma ina kishiya irina zata cusa kanta, na ga yadda ta sauya kafin suna. Mai Babbar daki ta kira ni tai ta bani hakuri, murmushi nayi ban ce mata kome ba, sai take gaya min me ya dace ayi a sunan. "Ummi ina ga zuwa yanzu ya kamata ku fahimci Nadiyyah bata bukatar shigana cikin al'amarin sunan nan ku tambaye ta ita ya dace ta sani!" Shiru Daulah tayi kafin ta ce min. "Yana da kyau ke ki sani da sauran abubuwan da za ayi amma tunda abin ya koma haka, zamu bata zabin yadda take so!" Da wannan na samu kaina na kuma samu nutsuwar zuciya, kamar yadda na gaya musu su same ta haka suka same ta. Ai kuwa ta ce zata musu bayani. Kawayenta suka taru aka tsara kome, abinci ma ba a gidan za ayi ba. Abu daya ya zo min da shi ya ce min fada zai yi yar walima. Na ce mishi ya samu Mai Babbar daki, sai ya hau diri da masifa har da kiran Umma wacce ban san yaushe suka zama aminai har haka ba. Mika min wayar yayi na amsa jikina a sanyayye. "Ki amshi aikin ki mishi sai na turo masu taya ki da aikin kin ji Good girl!" "Tow Umma!" Na kashe wayar na mika mishi. "Me zaki min kenan?" Duk da nasan na gayawa Maluma sai ta kusan zuwa da kanta tayi bala'in da zai saka Itama Nadiyyah ta ji tsoron sake shiga sha'anina. "Duk abinda kike ganin zai fitar da ni kunya!"
"Ayi masa da sinasir, sai a gasa maka nama irin wannan lokacin, sai kunu ko fura da nono!" "Shi kenan dama akwai matar da take yin fura zan saka a mata Magana ke kuma sai ki ji da nonon ko? Amma kafin nan ciro min wannan na kirjin na sha kin ji?" Bude hannunsa nayi sai da ya saka na yi murmushi. Duk yadda naso hana shi haka ya hana ni sakat,.da tsotsa kafin ya kyale ni na ke gaya mishi ni fa ban dawo sallah ba. Sai da ya duba ni. Sunan zai zo lokacin bude wurin spa dina sai na sake Kai da hankali akai musamman da Aunty Shukrah da Aunty Nu'aymah suke kai, ba ko ba gani Mai Babbar daki ta dauko min Aunty Yanah ta zauna kafin a kawo matan da aka ɗauki hayarsu daya daga Indonesiya ce, daya kuma daga Sudan sai wata yar kasar habasha, da na tambaye shi ya ce min. Zasu nada horo da aiki na tsawon shekaru biyu ne, zamu dauki masu kokari a cikin mutane su basu horo, a cikin su kuwa na jefa Wildat itama a cikin domin zata kasance mai sanar min da wasu abubuwan, Yarinyar tana da hankali da sauri daukar abu haka yasa na zabe ta. Kuma nasan zan samu biyan bukata. Sannan ta san inda take zaune. Za'a bude shagon da kwana biyu kafin suna. A wannan lokacin na shirya gaya mishi maganar kudin Dracula, da kudin da suke account dina da wanda na tab'a. Bayan sallah isha muna zaune na matsa kusa da shi na zauna na fara jan shi da hira a hankali, kafin na sako zancen. "Gaya min ya miki wani abu ne?" Girgiza kai nayi ina rike hannunshi. "Bai min kome ba Yaya, kudin da yake account dina ne nake tsoron ina ta amfani da su!" Murmushi yayi ya ja kumatuna yana faɗin. "Ki ci rabonki ne shi yasa Allah ya kai ko can, oya kashe su kina da miji irina da zai kara miki dubunsu!" Daga haka ya kashe zancen.
Haka na tattara hankalina na bawa wurin da zan bude, domin a kudin da yake hannuna ya kara bani shawaran na hada da su Abaya da sauran shi zai min hanya da wasu kamfani a China, haka Abaya ya ce zai min magana da hada ni da wasu kamfani uku daya a dubai da daya a Cairo sai na Saudiya, na zata kawai fada yayi. Haka aka bude wurin bakiɗaya ni aka fara yiwa gyaran jiki, sannan aka samu wata aka mata gyara wata model ce Lateefa Elmustapha, ita ka yiwa gyaran jikin da farko naji ance Mutuniyar Nadiyyah amma yarinyar ta san kanta domin duk barkan kudi tana tare da shi. Haka yasa suka tsawaita kwantaragi da Yaya sannan ya biya ta. Lokacin da aka bude shagon ya zaga social media, kada ku manta ni din


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login