Showing 228001 words to 231000 words out of 304445 words

Chapter 77 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

42

nake so masu kyau gashi nan zan turo kuɗin!"
Ai kuwa ta amsa min cikin mutunttawa tana faɗin. "An gama Fulani Babba, mata a gidan Sarki Salmanu Faris!" Murmushi nayi tare da kashe wayar. Na tura mata kudin kayan da na delivery. _(Ga masu buƙatar kayan masu kyau da aminci ku tuntubi Maman Hidaya and khairat a wannan number 07043372978)_

Lokacin da muka isa unguwarsu, kofar gidan Aunty Sajidah ya cika ana ta hidima bayan shekaru goma sha biyu sai yanzu za ayi suna, bude mana gate din aka yi muka shiga har cikin gidan, tunda aka ce gani nazo Yayuna suka fito cikin farin ciki har da Mai jegon, ni dai nasan ya bani dubu hamsin, amma cikin wani kashe ni da mamaki sai ga kwati guda Faruq ya fito min da shi, tare da wasu kayayyakin, dogarai suka dauko ana min kirari. Duk sai kunya ta kama ni, Maluma da take gidan sunan da Auntynmu da ban san da zuwnata ba Aunty Murja sai Aunty Kulu kanwar Umma suka fito tare da faɗin. "Sarkin dogarai an biya wannan kirarin da ake mata!" Ya ciro kudi ta mika musu, wasu maroka da suke kofar gidan suka fara nasu, Aunty Kulu itama ta basu naira har da CFA. Murmushi Yeemar take tana faɗin.."An gaida Fulani Babba," muka shiga cikin gidan, ana ta murnan ganina. "Kina zuwa kallo ya kare!" Suka fara suna min dariya, zama nayi a kasa ina gaida iyayena da yayuna, suka yi ta murna musamman yadda Yeemar take faɗin.."Allah na tuba Anya ba zaki koma Scotland da zama ba can yafi dacewa da ke!" Dariya nayi nace mata. "Rufa min asiri sanyin garin a takure nake!" Aka yi ta hira ana bani labarin cewa ya zo jiya. Fuskana da mamaki nake kallonsu. "Nifa bai gaya min wallahi!" "Ya zo jiya da yaji Hajja tazo yanzu ma wai gwagwaronta ne ya warware ta tafi sabon unguwa wurin kawarta Tarasulu don ta san tana da shi!" Dariya nayi na ce musu.."ita matar nan ko a Maradi ma ba zama take ba mata sai ka ce shanshani!" "Kaniyarki tare da kafar uwaki, Mansurah ta Agadaz!" Tura baki nayi ina kallon Aunty Kulu da take min dakuwa. Ita kuma Aunty Murja me zagina. "Sai na gayawa Abbana wallahi!"
"Sai ki yi!" Inji Maluma, aka fara ciro kayan akwatin, kayan jarirai ne fa da naga irinsu nayi ta imagine idan da Aunty Sajidah zata haihu ina garin zan saya mata, sai gashi ban saya ba shi kuma ya saya mata. "Nifa ban san ya saya kayan nan ba, na san mun je wani store na can Scotland diin naga kayan nace ina so na saya mata amma ashe ya saya!" Kasancewar unsex ne sai kayan suka.dace da Yaron. Sai kuma na rike baki na ce musu. "Ya Allah kayan Magaji ya kawo muku!" N a kwashe da dariya ina basu labarin abinda ya faru. Rike kunnena Aunty Shukrah tayi tana faɗin."Umma yarinyar nan bata jin magana kin san ranar da kishiyarta ta haihu ta mare ta?!"
Aunty Nu'aymah ta buge hannunta, tana faɗin. "Wallahi da bata rama ba, da nace ba Hajja ba ne kakarmu,.mai sayan fada da kuɗinta balle kuma an tab'a nata."
Dariya aka yi na basu labarin abinda ya faru, sai gashi suna faɗin.."kin kyauta wallahi ai hauka ne ki kyaleta."

Hidimar suna aka yi ta yi aka ciro cake dina aka hada da na sunan da suka yi..
---
Wanka ta sha ta shirya cikin wata abaya mai shegen kyau da ɗaukar hankali ta bar musu babyn ta fito bangarenshi yana tare da faruq da ya koma suna tattaunawa ta shigo. Kallon mamaki ya mata domin bai ga dalilin zuwanta ba. "Lafiya?" Mikewa Faruq yayi ya bar parlourn. "Taya matarka tasan zamu zo bata kai mana abinci ba, fisabiilillahi...........
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 75
"Muna da hakkin ta bamu koda a ce b azamu ci ba, ai ta fita amma ta barmu ba na.karyawa ba na rana yanzu har an tafi la'asar ka duba Lamarin nan Allah ya baka nasara!" Yadda take maganar yasa shi zuba mata idanu, jinjina kai yayi ya dauki wayarshi. Ya kira Zainab. "Maisha me yasa ba a kai abinci bangaren Fulani karama ba?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Shi kenan ki dawo akan lokaci a kai masu na dare zan saka a musu oda! Na rana!" Bayan sun yi sallama yadda yayi maganar ba haka ta so ba, amma kuma ko ba kome ya nuna kulawa. "Ina shalele?" "Tana wurin Gwaggon Zubaida. Ta fada tana wasa da hannunta. "Ki koma bangarenki jego kike!" Haka ta koma, tana shiga ta samu kanwar Mamanta Aunty Fa'iza ta iso. Tana kallonta. Domin yadda ta dawo a wani hargitse bayan tsayawa tayi ta goge kwalliyar fuskartar. "Yanzu zuwa kika yi ya tab'a ki da danyen jikin?" "Tow ya zan yi? Ita wancan matsiyaciyar ta tafi nata harkan gaban. "
"Ai wannan yarinyar zaku sha fama ke dai kada ki kara yadda ta dake ki! Tunda alamu ya nuna ta fiki gaskiya sannan ban da wawuya ce ke irinsu ba ayin kishi da ita ta fada sai ta kasa."
"A'a Fa'iza kada ki daurata ta wahala domin akan Matarshi na.ga zai iya fada da kowa!" Nan suka rufe kanwar Ubanta da fada, tayi shiru bata yi magana ba.

Bayan fitar Ijlal ya kira Ikhlas yayi ta faɗa ashe da sharewa yayi a gaban Ijlal yanzu yayi ta masifa da jidali, bata amsa mishi ba sai hakuri take bashi cikin kaushin murya ya ce mata. "Ki dawo maza domin suna bukatar abinci!" "Allah ya kai mu gani nan a hanya!" "A'a ki jira Faruq zai zo ya dauke ke ki!"
Wurgi da wayar yayi ya kira faruq ya shigo. "Kaiwa Jakadiya magana ta tura yara bangaren Fulani Babba zata zo su yi aiki! Sannan ka dauko ta yanzu!"
"Sir ko minti arba'in bata yi ba!" Kura mishi idanun yayi kafin ya ce mishi."me kace!" "Allah ya huci zuciyarka, an gama!" Har ya mike ya ce mishi. "Kada na ji maganar nan a wurin mai babbar daki!" "An gama!" Ya juya ya fita zuwa waje, kamar yadda ya umarce shi haka yayi har ya dawo ya gaya mishi. "Ka saka Aminu Sarkin fawa ya kawo rabin saniya yanzu nan! A cire cinyar bayan a cire zallar tsoka a gasa." "An gama takawarka lafiya."
Bayan tafiyar Faruq ya zauna shiru, kiran Sarkin dogarai yayi ya zube a gabanshi. "A kira Jakadiya a dauki wancan kwanon abincin a kai bangaren Fulani karama!" "An gama!" Ya fita can sai gashi da Jakadiya suka gaishe shi, sannan suka kwashi abincin aka kai musu, don zalinci an kawo abinci daga cikin gidan wurin Mai Babbar daki, amma da aka kawo nashi suka hada baki daya suka ci, har suna faɗin. "Shegiya ta iya takunta ga girki ga karuwanci!"
**
Tunda ya kira ni ban san lokacin da na fashe da kuka ba, musamman kiran bayan da yayi min yana ta faɗa kamar zai dake ni ta wayar abinda bai tab'a yi ba, sai na ji kuka ya zo min na ce mishi Allah ya huci zuciyarka, in sha Allah ina hanya gani nan. Bayan mun magana na mike ina hada kayana ina kuka. Murmushi Maluma tayi ta ce min. "Zaki ci sunan Fulani Babba ne ki zauna lafiya? Duk wacce kika ji an kirata Fulani Babba ko mai babbar daki, to ba a duba girma da shekarunta, abinda aka sani ta kula da duk wani abinda ba sai ya kai ga sarki ba, sannan idan har abinda ya kira yayi fada akai gaskiya ce baki kyauta ba." D'ago kai nayi ina kuka na ce mata. "Na ga da yan uwanta me kuma zan basu?" Dariya suka saka bakiɗaya ta ce min." Ke zaki basu abinci har bayan suna ai bata isa tayi girki ba, bata isa ta shiga wurinsa ba, dole kece zaki tsaya akan kome kai ko ba zaki yi ba, ki zama mai bada umarni akan kome na gaya miki kin yi laifi daga yau kada ya kara kama ki da laifin hana kowa abinci koda kuwa za a zubar zasu yi a saka musu idan shi mai gidan ya gani zai yi abinda ya dace, kada ki manta tsawon shekaru ya dauka kafin Allah ya bashi haihuwar nan kina tsammani ba sai a ce kishi kike yi da haihuwar ba? Balle yau aka sallamota ko yaya zasu so cusa miki haushi da takaici don Allah kada ki sake ya gano gazawarki akan wannan lamarin, na san kina ƙoƙarin amma akara a na da, sai yanzu na fahimci dalilin da Marigayi Attahiru ya bukaci aurenki da shi mai Martaba na yanzu domin ita wancan baturiyar ba zata iya ba, kece Bahaushiya kuma yar amininsa ya ga haka zai iya zama wani hiyana a rayawar dansa don haka ki rike matsayinki da girmanki kada ki yarda ta Amshe shi yanzu burinta ta haihu da shi. Burinta shine ta Amshe Fulani Babba, don haka ku rike kambunki Allah ya baki ita kuma ta rike matsayinta, karamin misali gata nan yar uwarki sai da ta shekaru goma sha biyu Allah ya bata haihuwar nan, don haka kada don baki haihu kice zaki ji haushin Yarinyar, shi da da dukiya ba ayiwa mugunta, sannan ki rike Allah wallahi ba zaki ji kunya ba, domin muna tsaye da Addu'a akanki ba dare ba rana, b adai mutum ba sai ta Allah. Duk wanda kika ga yayi hakuri bai ci riba ba, tow ba hakuri yayi ba idan kayi hakuri sai ka ci riba!" Yadda suka hadu suna min nasihar yasa ni nayi ta kuka. Sannan Maluma da kanta da su Aunty Murja suka rako ni har wurin mota, aunty Kulu ta haɗa min maganin mata sosai ta mika min jakar, tun a hanya nake kuka har muka kusan isa gidan. Ya tsaya cak. "Please ko zaki daina kukan nan, kada su rena mana ke. Ki yi hakuri don Allah!" Share kwalla nayi nace mishi. "Ba kome Dan uwa." Muka karasa gidan a lokacin da muna isa ana kawo rabin saniyar bayan an cire na gashi, ina shiga kallo daya nayi mishi ba dauke kai, tasowa yayi yana faɗin. "Fisabiilillahi baki kyauta ba!" "Na sani kayi hakuri!" Na faɗa na wuce kitchen na cire nuna musu inda za ajiye min namar, sannan na koma daki na sauya kaya na fito na fara aiki, ba ji ba gani Wildat da wata baiwa Sa'ida muka cigaba da aiki, tuwon shinkafa nayi sai miyar kubewa busashe da farfesun nama saniyar da ya kawo, ina ganin aikin ya hau hanya na wuce muka yi sallah, muna idarwa, muka fito kuma cigaba da aikin kafin karfe shida, aka shiga kai musu abincin sannan aka fito da kular cikin gidan aka kawo min, murmushin takaici nai na shiga wanka, ina fitowa na gyara jikina na gabatar da sallah Magariba.

Ina idarwa kawai na cigaba da azkar, yana dawowa na kai mishi na shi na zuba mishi, sai anan na lura da yana da walwala ashe chat yake da Nady, na ga ya mai da ni yar iska na tashi na barshi anan, nan sallah isha nayi na kwanta. Bayan nayi dogon karatun Alqur'ani don ina jin zafin rai sosai sai na koma karatu. Wurin karfe daya saura ina tsaka da barci ya tashe ni. "Ko zaki samu yi mana kunun kanwa, wai yarinyar tana ta kuka babu ruwan nono sai tasha ruwan nonon zai zo."
Gyada kai nake ina kallonshi baki a bude, ina ga da zagina yayi da yafi saukin na ji shi na bawa iska ajiyarshi. Gyara kwanciyata zan yi ya ce min. "Baki ji bane?" Kasa mishi musu nayi ina kallon agogon wayata da nake kalla. "A wannan lokacin fisabiilillahi?" Shiru yayi can kamar wanda yayi zuciya ya mike tana faɗin. "Nadiyya da kika mata ina don niman gindin zama kika mata?" Shiru nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Ni ce mai niman gindin zama?" A fusace ya juya ya fita, zura kafana nayi na sauko na nufi kitchen na zata zai bar bangarena ne sai na ga ashe yana nan, haka yasa na wuce kitchen Allah ya gani ban iya kunun kanwa ba, sai nayi amfani da salon tuwon masara da ake saka mishi sawa, amma ban bari yayi kauri ba, na tsinka shi kafin karfe biyu na gama na juye a wani jug na fito parlour na ajiye na juya dakina, alola nayi na gabatar da sallah nafilla,har lokacin bai saka kafa ya dawo ba, nima kuma ban nime shi ba, haka na gyara kwanciyata, sai naji babu dad'i amma da na tuna haihuwa fa aka mishi.
Sai asuba ya shigo ya kwanta, zai fara addabata. Nayi maza na tashi tare da daukar hulata na nufi waje. Shima ya ji yadda naji, ina shiga kitchen na fara aikin hada wannan sauke wannan kafin ayi kiran sallah farko, na wanke wanke na markad'a, kasancewar bangarenta mutum biyu ne da ita na uku sai shi da faruq anan, sai masu tayani aiki.
Da na daura kunun shinkafa, sai da ya dauko nuna, na rage mishi wuta sannan na wuce daki, har lokacin yana kwance bai fita ba, alola n a shiga nayi sannan na dawo na tadda sallah, shima jin za a shiga sallah ya tashi ya shiga ban daki ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, ina sallah ya zo ya wuce, lokacin da na idar su Wildat suka shigo, kosai suka buga min na fara soya, sai farfesu da nayi bayan na gama na kalli Wildat na ce mata."ki tafi wurin Fulani karama ki amso kayan da zan zuba mata abincinta da kayan jiya!" Haka ta je ta amsa kayan har da kunun yadda aka kai haka aka dawo min da shi, murmushi nayi na hada abinda xan hada, da na fuskanci so take ta mori kayana n acewa Wildat. "Ki je ki ce ta kawo inda zan zuba mata abincinta." Can sai Kanwar Uwarta sun zo tana ta karewa kitchen dina da ko ina kallo tana yatsina fuska. "Zaki iya ajiye ko sai kin gama bawa idanunki abinci?" Sai kuma ta dawo hankalinta na zuba mata kome, yadda ta d'ago kullar tana tab'e baki yasa ni maza na haɗe rai. "Akwai wani abu ne?" "Wai gani nayi yayi mana kaɗan mu uku!" "Ok xan kara muku idan na ga kwaya daya ya fito billahi azim sai na warewa kowani dan kutumar bura uba hankali!" Ina fadar haka na ga ta nutsu, na zuba mata ina faɗin.."idan ba iskanci ba tsakiyar dare a hanani barci sannan a ce an dawo min da abinci ba aci ba ga yar iska? Ga baiwa? Tow wallahi shege kafasa!" Ina fadar haka na tura mata kome suka fita ita da Yaran, ina gama shirya na table, da ya dawo masallaci bai shiga ba, sai da ya shiga yayi wanka ya dawo ina wani haɗe rai ni kuwa na aro agadabuna, na daura a gaban goshi ba ta samu kwana biyu yana bin ta ba, sai gata nan ta sha kwanta cikin riga da skirt na atamfa ta shigo tana baza kamshi, ga nonon nan yayi tumtum.." My King kai ne kace dole a cinye abinda aka kai?" Ina jin shi juyawa yayi ya kalle ni ranshi a soshe, na haɗe rai ina shan kununa. "Ban gane ba?" "Matarka tana ta ma kanwar Mamana fada akan abincin da ba kawowa tayi daga gidan Ubanta...." Nata marasa ba, na wanke ta da mari cikin isa ina kallonta. "Akan me zaki mare ta Zainab?" "Akan me zata zagi ubana? Da nake girkawa ina bata ka gaya mata kayan gara nane da har yanzu bai kare ba? Ki ji inga miki ubanan ba rago ba ne, manomi ne sannan abinci kuwa ba zan kara ba ai ke mace ce ko danginki mata suka rako duniya? Basu iya ba sai dai a dafa a basu, su. Bude wagegen baki su ci!" Buge min baki yayi yana faɗin.."Na gaji!" "Nafika gajiya!" Na faɗa da ƙarfi ina kallonta da ta daina kuka tana murmushi, abinda tazo nima ta samu. Ina rike da bakina na kalleta tana murmushi ta ce mishi. "Shi kenan na ji ki yi hakuri, ba za a sake kawo miki sauran abinci ba, amma idan bai miki ba zaki daina zuba mana ma yayi!" Ya fita tana dariya kasa kasa. Tana fita ya hayyako min na fasa mishi ihu na fara watsar da kome na kan dinning table din, kamar mai aljanu haka nake watsar da ke haka yasa shi yayi maza ya rungume ni, na fashe da kuka. "Sake ni ka je wurinta tunda ka buge min baki saboda Matarka!" "Look!" "Look for hell!" Na faɗa ina kuka, daki ya wuce da ni, Allah ban san ta yadda kukan ya tafi ba, ikon Allah fadar ya kare kenan. Bamu fito da shi ba sai karfe sha daya saura ya wuce fada, ni kuma na kwanta huce gajiya, tuni barci yayi gaba da ni. Hayaniyar mutane. Tashi nayi na fito na ga Jakadiya tana tsaye ita da Sarkin gida. "Lafiya?" "Ai Fulani Babba wai yan uwan Fulani karama ne suka zo rama mata marin da kika mata."
"Sai su zo ai tunda bakinta bai da linzami nima hannuna bai da hankali!" Na wuce abina. Ina parlour sai Yanzu abinda tayi ya kara dawo min rai, "assalamualaikum!" Mai Babbar daki ta shigo ranta a b'ace. "Tashi!" Ta fada tana me nuna min hanya muka fita da yake mayafina yana kaina. Waje muka fito ta ce musu. "Gata ku kashe ta!" Sai suka yi tsuru-tsuru. Bata kara magana ba ta wuce ta bar gidan, babu wnada yayi yunkurin motsi sai dai kuma cikin abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login