Showing 132001 words to 135000 words out of 304445 words

Chapter 45 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

74

lips dinsa yayi tare da lashe bakinsa a hankali. "Zaki yi ko ba zaki yi ba?" "Ba zan yi ba!" Na bashi amsa sannan na kashe wayar. Sako ya turo min don ya cusa min haushi.
*Ina da wata matar don baki yi ba*
Nima na tura mishi har da emoji. _So what? Shi yasa nace ba zan iya ba! Tunda ai ba daya gare ka ba rami biyu gare ka, ka dangwala can ka dangwala can😏_

Can kuwa ya sake turo min da wani sakon. *Allah yana ganinki idan kika karya min azumi*
_Saboda ni ce na nimo ka ba?_ daga haka na kashe wayar na cigaba da abinda nake.
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 43
Akwai wani abu da aure ya gadar guda biyu, dabi'u ne na farko ma'auratan da suke tsayawa juna idan wata matsala ya same su, na biyu ma'aurata da suke mantawa da matsalar junansu. A nazarin Nady sam Salmanu Faris bai damu da halin da take ciki ba, tunda Ijlal tana da a cikinshi, amma maganar gaskiya ba haka ba ne, asalima shi ba mutum mai lallai sai ya san me yake faruwa ba ne, yana iya zama da kai ba tare da ya nuna ya damu da kai ba, amma kuma kome idan yana tare da shi yana bibiyarshi sau da kafa, ita ce bata sanshi ba amma shi yasan su bakiɗaya. Ko a yadda ya ga tana murmushi ya kyaleta bayan ya ga hawayen da take, bayan ya rakota, komawa asibitin yayi domin tana shiga ban daki ya buɗe jakarta ya dauki takardan ya gani, murmushi yayi ya dauki hoton takardan. Sannan ya juya ya koma ban daki yana jin yadda take kuka sosai. Murmushi yayi a karo na biyu, sannan ya fita ba zai hanata kuka ba amma me yasa ta boye babban al'amari haka? Tana ganin ba zai damu da ita ba ko? Murmushi yayi. Lokacin da ya koma ya samu likitan suka gaisa ya gabatar da kanshi ba tare da ya gaya mishi sunan shi da aikinsa ba, kallonshi likitan yake kafin ya ce mishi. "Kai ne Dr Faris Neurology MD na jahar Machigan?" Inji Balaraben ya tambaye shi, jin haka yasa shi amsa mishi cikin murmushi da kulawa sake hausawa yayi. "Masha Allah, mun jima muna son gayyatarka ko zaka taimaka mana ka duba mana wasu marasa lafiya!" Girgixa kai yayi yana faɗin.."kuyi hakuri ina da mara lafiya nima, Matata ce ta zo da case din haihuwar nan!" Kallonshi likitan yayi kafin ya ce mishi. "Dr ya aka yi abin ya ci bututun da kwayoyin halittarka zasu shiga jikinta?" Murmushi yayi wanda take karawa fuskarshi kyau ya ce mishi. "Ƙaddara! Ban da ƙaddara babu abinda zai kawo haka, don Allah ka taimaka mata tana son itama ta haihu." Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Mu mata aikin farko bayan wata shida idan bata sami cikin ba zamu mata dashen kwayoyin halittarka mu ga abinda Allah zai yi!"
"Na gode sosai!" Suka gaisa sannan likitan ya ce mishi. "Likita kai amma kana da lafiyar ko?" Yar yake yayi ya ce mishi. "Su uku ne dayar ta ukunsu tana da cikin wata biyu!" "Ah Masha Allah!" Suka kara gaisawa. Sannan suka yi sallama.
Tura mata sako yayi da cewa. *Ban san me yake damunki ba! Amma Please ki ci abinci ki kwanta! Kafin na dawo* wannan sakon da ta gani ya mata dad'i don bata dauka zai dawo gare ta ba.
Tunda ya shiga Makka a daren ranar, bai rintsa ba domin ko kiran da yake yi na yayi abinda yake a waya ya kasa, Addu'a yake ba ki ba gani. Sannan ya kara mika lamarin Matanshi Allah ya bashi sa'a da iko kansu haka yasa bakiɗaya yake ƙara addu'a da mika lamarinsa ga Allah, tsawon kwanakin da yayi a can addu'a yake, sannan yaki komawa don ya bata damar nutsuwa don kullum ya kirata zata ce tana lafiya.

***
Ana jibi sallah, muna aikin cin-cin da cake, sai ga sakon Nady. _Ki taya ni da addu'a za a shigar dani aiki!_ yadda ta turo min sakon nayi maza na mai da mata da cewa. *Allah yasa a dace Maman twins* lokacin da ta ga sakona, kirana tayi tana shashekar kuka ta ce min. "Thank you, da sunan da kika kira ni da shi na gode sosai. Amma shi Allah ba a mishi dole yasa ina da rabon ganin nawa gudan jinin!" Murmushi nayi na ce mata. "In sha Allah! Zaki gani idan muna raye!" Da haka muka yi sallah, anyi min dinki sallah Telan mai babbar daki yazo ya amshi kayana don ni da Sailuba da Faruq muka je gida, na kwaso kayana masu yawa na ajiye akwati guda na ajiye mishi. Mai Babbar daki ta shiga daki ta kawo min wasu lace guda biyu, daya Austaraliya daya kuma China ne, ta ajiye mishi tana faɗin. "Wali duba kayan nan a hada da shi." Size dina na bashi, a cikin kayan da na dauko har da takalmi da jaka na, sannan gyale da hijabs dina, duk da ta tura an yi min jalbab masu kyau. Yaranta haushina suke, ana sallah saura kwana uku Mazan gidan suka fara zuwa ganina a dakin Mai Babbar daki, lokacin da suka shigo gaishe ta domin wannan al'ada ce kafin su gaisa da iyayensu mata ita suke fara gaisawar sannan su fita. Ganina sanye da hijab na fito Salim ya ce min. "Kina nan ne? Masha Allah zamu kwashi arzikin abinci. Yau kwanona a nan yake don Allah a yi da Ni!" Murmushi nayi ina mai kallon Mai Babbar daki da take bata uzurin amma kuma tana aiki jin mu. "Ka tambayi Umminmu!" "Mai Babbar daki zan zo cin abincin bude baki." "Nima haka!" Inji Abdulhafiz. "Gaku ga kukun nima sammin take." Duk suka saka dariya sannan suka fita. "Ki kara sanwar;" "in sha Allah!" Na faɗa ina sunkuyar da kai. "Kina shan maganinki kuwa?" Gyada kai nayi don kunya nake ji. "Gara dai a daina jin kunyata, domin dai nasan." Da sauri na koma kitchen, mun yi abin buɗe baki har da su alale da dan wake, Masar shinkafa da miyar taushe. Don tin jiya muka yi, bayan na gama aikin bude baki, na shiga nayi wanka turaren wutan da na zo da shi na saka. Ina shiri na tura fa dazun na bawa Faruq ATM dina ya ciro min kuɗi zan bawa su Sailuba da Wildat. Ina cikin shafa mai suka shigo don nace idan sun gama su gaya min. "Gimbiyar Zanzabira, zan tafi kin san Ummata bata da lafiya." "Ayya baku tafi asibiti ba ne?" Sosa kai tayi bata gaya min ba, na ce mata. "Ki samu Faruq idan an sha ruwa ya kai ku asibiti, sannan ki turo min shi idan kin ganshi. Wannan kuma kudin kayan sallah ne na bada kayanku ke da Sailuba ga telan mai babbar daki, wannan ki sayi abinda kike bukata!." Zubewa tayi a gabana tana wani irin kuka da godiya, domin bata kawo zan mata kayan sallah ba, a matsayinsu na bayi su ba ayi musu kayan sallah masu dan samu ne suke yiwa Yaransu. Tayi ta godiya karshe koranta nayi ta ishe ni da godiya. Sannan tana fita ta zube a gaban Mai Babbar daki tana mata godiya, murmushi Mai Babbar daki tayi tana kara hango yadda Yarinyar take amfani da kome nata domin na kusa da ita, ko shekaranjiya kayan sallah da ya haɗa da hijabs da turame kusan kala hamsin hamsin ta bawa mai babbar daki a kai can wurin danginta na farar kasa, a raba. Sannan ta haɗa da wasu amintattun yan uwan Mai Babbar daki guda uku, Hajja Mariya, tana auren Dan malikin Zanzabira, Hajja Kulu tun aure a azare na jahar Bauchi, sai Hajja Auta tana Abuja, kuma tasan zasu zo zanzabira sallah musamman Mariya da auta, da ta gaya musu sakon Ikhlas cikin farin ciki suka ce ta tura musu, su dinka don zasu saka.
Haka yasa aka tura Faruq ya kai da sassafe tasha. Wannan abin ya matuƙar kama zuciyarsu, sannan ta kara da tuna mata Yarimar gabas uban rikon Ijlal Menless ta saya mishi da turarukan, aka kai mishi inji matar Salman, wannan abin ya mishi dadi, uwa uba duk wani babba a fadar sai da Mai Babbar daki ta saka tayi mishi hidima har kishiyoyin Mai Babbar dakin, wannan yasa masarautar aka ɗauki gulma da gutsiri tsome.

Ana gobe sallah Abbana ya turo min da kayan sallah, cikin akwati guda a dinke har da na mai babbar daki, sannan ya haɗa min da danyen nama, kaji da hatsi da zunzurutun kudi naira dabu dari, nayi hidimar sallah, ana kawowa Mai Babbar daki ta bada dan aikanta dubu ashirin tukwaici, Dama kunsan mutumin da kaunar 20k anya ba aljanu suka kama tauhid ba yana son dubu ashirin. Kirana tayi na zauna a gabanta. "Ga kayan abinci me zaki da shi naji akwai wasu a gidanku, akwai wasu anan?" "Madadin haka a rabawa iyayen fada na cikin gidan nan da waje, inji Dr ba?" Kara tambayarta. "Kin tambaye shi?" "Ummi aikin alkhairi ba a jiran izini ko sa hannun wani idan aka yi haka kamar ya san me ya faru ne!" "She kenan ki cire wanda zaki yi abincin sallah ki kai musu." "Tunda akwai a can a barshi sai na idan ya dawo!" Kun san me nayi ƙoƙarin na tafi gida nima kamar Ijlal, kiri-kiri Mai Babbar daki ta ce idan na tafi gidan zai zama empty don haka na zauna anan mijina zai ji dadin duk da yasan ina gidansu. Kada ku ce abincin sadaka ya tsaya fa ana kan yiin shi ta hannun matar da Nady ta dauka da faruq ake rabawa shi ne dalilin da bai bi uban gidansa ba kenan, haka muka sake raba kayan da aka kawo min ban da hatsi don su Wildat da Sailuba na bawa, suka yi ta godiya har da danyen nama da kayan miya da mangyada suya.

Ban yi lalle ba, sai dai da dare ana gobe sallah kenan, aka min don mun yi snack sun kai kala goma wuni muka yi ana aiki. Na gaji ranar sallah da safe kafin mu tafi Idi muka tashi da aikin masar sallah, da sinasir wanda Mai Babbar daki ta hada min kulun, ni kuma nayi miyar egusi sai tuwon shinkafa da fried rice , sai salat da nayi da fruit salat. Duk mun hada muka shirya bakiɗaya aka tafi massalaci, muna dawowa ni da Abdullahi da Mai Bauchi muka rakoni gida na kwashi manya kulollina, muka wuce gidan masa dama tun asuban fari muka fara suya, kafin shida mun gama, sinsir ne muna shigowa muka fara suyarshi kafin karfe sha ɗaya mun gama, masu jiran abinci kuwa tea na dafa musu da ya sha kayan kamshi na hada musu da masa, na koma na cigaba da aikina. Dubulan da nakiya da alkaki da wasu cimar Mutanen Borno Mai Babbar daki ta bada aka mata, ni kuma nayi su cincin da cake. Duk kafin karfe sha biyu mun jera abincin domin Mai Babbar daki ta gaya min zuwa karfe biyu za a fara zuwa gaishe ta, ciki da wajen masarautar. Sai abincin da muka kai sassan gidan aka raba..sannan ya gaya min zai dauki kwana uku ana abincin sallah don haka na saka a raina aiki ne ja a gabana. Lokacin da na fito da kayan kayan karshe ina sanye da wani karamin mayafi akan lace din da mai babbar daki ta dinka min, kusan irin nata ne, na ji ana ta hayaniya. Ashe wai suna video call da shi ne, ina fitowa suka juya mishi ni. Kallo daya yayi min ya dauke kai yana faɗin. "Barkanku da sallah! Bari na duba Nady!" Kashe wayar yayi, na ajiye kome na wuce dakina. Ina shiga naga kiranshi. Ina dauka wato yadda yake faɗa da Bala'i kamar na mishi wani abu. "Don rashin mutunci, sai ki saka dan karamin mayafi kina yawo cikin mazan da babu Muharramanki, Allah yana ganinki hakkina da ake takewa wallahi. Domin na san har da rawan jiki yi kike tunda kin zama mara kunya da rashin sanin darajar aure, ki ga wani mayafin da kika dasu. Allah ya gani ba don ke bace da ba miki Allah ya isa domin ji nayi kamar zan mutu har Faruq ya ganki a haka waye ya san iya adadin mazan da zasu ganki a haka, wallahi kin zalince ni zuciyata kamar zata buga, ki nime Yafiyar Ubangiji domin matukar ban yafe miki ba zaki sha tsinuwar Mala'iku, yawwa gobe ki saka Hijab har kasa, sannan idan kika fita kallon hawan Sallah wallahi ban yafe ba, kin mai dani Dan iska ina magana kina jina." "Tow me zan ce maka? Kace baka yarda ba kace kaza kace kaza me kake so nayi maka don Allah? Tunda baka so ka gayawa Ummi zan koma gida kawai, tun kafin sallah na ce zan koma ka ce baka amince ba ya kake so nayi? Don Allah ka daina addabar rayuwata." Na faɗa ina jin wani irin kuka yana zuwa min, hadiye kukan nayi na ce mishi. "Allah ya huci zuciyarka!" Tsabar kishi ne ya rufe mishi idanu, ina zaune a dakin na kasa fitina naji muryansu Ijlal, ban fita ba, na shiga ban daki na wanke idanuna na dawo na gyara zama a gaban madubi, na tsara makeup, domin mun yi da Yeemar itama ana saukowa idi zata zo, na gyara zaman dham din wuyana, haka hannuna da kunnena. Sannan na gyara dakin na fito na gaida mutanen parlourn na wuce kitchen. Ina jin muryan Hajiya Mardiya tana faɗin. "Mai Babbar daki, ai ina ganin kokarinta kwana take tana fama da zazzaɓin, ga rashin cin abinci. " Ka ji wani karya na fada a raina. Sannan na fito tana ta kara bayaninta. "Yeemar din ta iso ne?" Murmushi nayi ina faɗin. "A'a Ummi tana hanya!" Na kai kayan daki, ina dakin naji Parlourn ya kara daukewa da hayaniya, daidai lokacin da naji muryan Yeemar tana gaida da mutanen Parlourn fitowa nayi na ga Abbana Ya Abid, Ya Yunus, Ya Nawwas, Ya Nuraim da Tauhid. Komawa da baya nayi,kuma sai na fito da gudu ina ihu. Dariya Mai Babbar daki tayi tana girgiza kai. "Wayyo Allah na, Abbana Wayyo Ya Abid!" Na fada jikin Abba ina kukan murna, tun kafin azumi ban kara ganinsu ba, gara Tauhid yana kawo min sako. Tsakiyar su na shiga, aka yi ta daukarmu hoto na tashi da rawan jiki na zuba musu abinci suka ce sun koshi, Mai Babbar daki ta ji dadin yadda nake murna, duk da taga alamar kamar kuka nayi dazun sai Ijlal ta zama yar kallo, wato ita tana ganin yar so ce sai ya ga ashe iyayen Ikhlas bakiɗaya ita ce duniyrsu ga wasu mayun warms da aka kawo na abincin sallah, Mai Babbar daki tayi godiya ta bawa Tauhid goran sallah Yaron nan mayen kuɗi ne amsa yayi yana ta godiya, sannan suka tashi na raka su, Yan uwana bakiɗaya suka bani goran sallah. Sannan suka tafi hotunan da muka yi Tauhidi ya ce idan ina son ya turo min sai na tura mishi 20k, daga nan na tura mishi sannan ya ce na jira zai turo min, Yeemar da na bari a daki na koma wurinta muka nutsu a daki muna hira. Tare da bawa juna labarin, anan nake gaya mata rigimar mu da shi na safiyar nan nan Murmushi tayi tana faɗin. "Kishi ne ya motsa sai ki saka hijan din tunda baya son yana ganinki haka, kuma da gaskiyar shi. Ina dalili!"
Ya faɗa tana dariya bari na gaya muku Yeemar yar iska ce. Idan nace muku dilaliyar yan iska ce kada ku ce karya ne. Don haka na tashi ina nufar waje jin ana tambayar Mai Babbar daki ni, tayi shiru ashe haka da nayi kuskure babba. Domin ina fita na ga wata dattijuwar Mata, zaune fara ce tas baka ganin kwayar idanunta. Saboda wannan farin da ya lullube idanun.
"Maryamu ki ce Faris ya samo macen da ta dace da gidan. Tabbas ita ce Lu'lu'a yarinya zo nan!" Kallon mai babbar daki nayi ta zuba min idanu kafin ta min alamar na koma da baya. "Adade don Allah bana son abinda kike min, Ke koma dakinku." Maza mata tayi ta kamo hannuna kamar tsafi tayi sama da kanta na tsawon minti goma kafin ta juya ga Mai babbar daki. Murmushi tayi tana dariya. "Burina ya cika, an haife ta. Jinin ya dawo." Yadda Mai Babbar daki ta fisge hannuna a cikin na matar tana mai rufe ni da alkyabbarta. "Adade ki fita kafin na saka a wulakantaki!" Ta fada da wani irin tsawa, dariya tsohuwar take tana faɗin. "Karni zuwa karni jini bayan jini yaki zuwa yaki shekaru zuwa shekaru, baki isa goge zanen ƙaddaransu ba. Ko yau na mutu tarihin Zanzabira ya zanu kuma ya tabbata. Maryamu jini zai ta zuba sadaukarwa akan sadaukarwa ga duk mai numfashin da zai huda katangarsu.

Rantsuwa ce da jinin rauhanai, dare ne mai cike da duhuwa. Wanda ya haɗa wayewa da kusufin dare. Guguwa Mai Karfi ta taso daga tsakiyar birnin zata lullube samaniya zata haifar da gagarumin rinjaye na zubar da jini. Za a haifar da annoba mai rinjaye. Attahiru yayi shuka a idanun makwarawa, yayi barci ana mishi minshari zan tafi domin mutuwa na dab da cimmani. Yarinyar idan gudu ya zo kada ki gudu ke daya riƙe hannun damansa ki gudu tare a shi. Nagani a kaddarar baya amma ban gani a ƙaddararki ba. Miyagun shaidanu mutane zasu lullube samaniya, zasu zo gab da cimma shi amma sai kin bada tazarar da zasu samu nasarar haka. Dariya take tana tafiya tare da dogara sandarta tana wani waka da wata mitsitsiyar murya.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login