Showing 105001 words to 108000 words out of 304445 words
ni wannan shine kukan da tawa Uwar tayi."
Ikhlas
Ina kwance karatu nake kaina yayi zafi, na ji wayata tana ringing. Dauka nayi ina daga kwancen. "Mamana!" Tashi zaune nayi ina raba idanu nace mishi. "Abbana!" "Na'am yar abbanta!" "Abba yaushe zaka dawo?" "Kin gaji da zaman jirana ne?" "Eh Abba!" Na faɗa ina kallon tv parlourna da yake kara na rage karar na ce cigaba da cewa. "Ina kewarka Abba!" "Ga Mijinki!" "Hmm!" Na faɗa ina tura baki. "Abinda zaki yi, ki burge ni shine ki zauna lafiya da shi, wata rana a kawo min Yaranki na ganku cikin farin ciki, kina murmushi tare da mijinki a gefenki, shine kawai abinda zaki yi ki burge ni." Shiru nayi don maganar da kamar wuya. "Allah da gaske nake, Allah ya albarkaci rayuwarku da zuri'a dayawa yadda xan kalle ki ma na yi alfahari da kuma" "Abba!" "Ki min alƙawarin zama da shi da zuciya ɗaya!" "Abba!" "Alfarma nake nima a wurinki don Allah!" Da sauri na ce mishi. "Abba in sha Allah, zan maka." Murmushi yayi mai sauti yana faɗin. "Allah ya cika rayuwarki da albarka." "Amin Ya Allah!" Sai na fashe da kuka, bai yanke kiran ba, sai da nayi sosai sannan na fara ajiyar zuciya. "Ki min alƙawarin zama da shi no matter how!" "Nayi Abba!" Na faɗa ina kallon tv. "Ki min alƙawarin zaki zauna da shi at any cost?" "Nayi Abba!" "Zainab ina kara niman alfarman don Allah kada ki wulakanta Mijinki don Allah! Da ina gabanki da zan zuba gwiwata a kasa, ina niman alfarman ki taya mijinki yakin da zai taso miki da iliminki da baiwarki don Allah ki min wannan alfarman ki taya shi ta kowani fuska." Kuka nake tare da kifa littafina a fuskana ina kuka kamar an yi min.mutuwa, don yau nake ji kamar Abba ya daure ni da igiya, sai nake jin kamar ya cika min kasa a gwiwata na kara jin kamar kaf duniya babu wanda ya tab'a niman abinda Abba ya nima. Haka yayi ta rarrsshina kafin ya katse kiran sannan, na cigaba da kuka a hankali, har barci ya dauke ni. Ji nayi kamar ina yawo a sama, bude idanu, daidai ya shiga da ni dakin. Dan hasken da ya ratsa dakin yasa ni kai hannun na kai fuskarshi. "Why you?" Daga nan barci yayi gaba da ni, kwantar da ita yayi ya kwanta a bayanta, ya rungume ta a hankali. Bai san kalmar kiyayyar mace ba, amma a idanunta yana hango kiyayyarshi da mishi kallon son kai, kalamar ta na kashe me yasa kai? Sauka yayi daga gadon ya koma parlourn wayarta ya dauka a hankali ya shiga bincike, shine har Whatsp dinta, bibiyar wayar yayi a hankali ya dauki wayar ya tafi dakinsa yayi linking what'spp dinta da laptop dinsa ya bude, 😁 backup din kome nata tun daga bude Whatsp dinta, murmushi yayi lokacin da yake hango wasu abubuwan da take whatsp, a rayuwarshi da ya gamsu ko kashe shi zata yi bai biya tarbiyyar da ta samu ba, abu daya tsaya mishi a rai shine chat dinta da Uwais kafin ya zo har wanda tayi blocking dinsa, kallon kofar dakin ya juya yayi yana mamakin yadda ta iya dakatar da kome ba tare da kowa ya sani ba. Google account dinta ya shiga ya duba history dinta, murmushi maganar Paul ne ya dawo lokacin da suka kebe ya ce mishi. "Yanzu ya dace ka fara tunanin Yara, kada ka girma yaran suna kanana ba tare da sun taimaka maka, ka duba lamarin!" Nady, Ijlal, yasan suna shirya maganar haihuwa, amma ita fa? Lumshe idanun yayi, yana jin wani irin feel deep serious, amma ita kaɗai yake jin wannan kwadayin akanta yasan sauran ya san yadda suke mishi. Mikewa yayi ya nufi waje bayan ya nufi Ijlal, ya same ta sanye da wasu tsinannun kayan barci wanda basu da bambancida na yan iska. Murmushi yayi dukkansu biyu sun san kan karuwanci. A hankali ya isa gabanta tare da damke gashin kanta ya d'agota tana kallon shi ta ce mishi. "Ni baiwarka ce, zan jiyar da kai a wannan duniyar nan, kayi yadda kake so da ni, ka min abinda zan kai sati ina cikin shauki!" Kallon yadda take magana da yanayin jikinta, duk da farkon auren bata kai Ikhlas ba, amma kwana biyu nan da tayi ta wani hada jiki al'amar hankalinta ya kwanta, murmushi yayi tare da sake kanta ya nufi ban ɗakinta, yadda ya ga tarin pants dinta da bra yasa shi juyowa ya kalle ta yana cizon lips dinsa ya ce mata. "Ke da Nady kazamai ne! Common innerwear dinku baku iya kulawa da shi!" Ya fada yana jin duk wani jarabarshi ta kau, dakinsa ya nufa sai lokacin ya lura da dakin ma yayi kura. Zama yayi akan stool yana jin wani irin kyakyamin dakin har jikinsa. Kayan da zai saka ya nufi bangaren Ikhlas, ban dakin daya dakin ya shiga tsaf-tsaf, kamar a saka abinci a ci a cikin bayin. Wanka yayi ya nufi asalin ɗakinta, ya leka ban ɗakinta wasu pants dinta da bra dinta ya gani ya dauki bra din da suke kamshin sabulun wankin, sai kamshin riyal don ya rike kamshin ko tafiyarshi Abuja sai da ya shiga Sahad store ya duba ya sayo mata, murmushi yayi, bai yarda da bata sonshi ba yasan zata so shi zai gina mata Soyayyarsa a ranta. A hankali ya nufi waje ya samu kamar an shigo parlourn, a hankali ya tsaya kasancewar parlourn da duhu, kallon ko ina yayi don fitowarshi ya fahimci an shigo don parlourn da yanayin kujerar da kuma kofar da aka bari a buɗe. Kunna wutar parlourn yayi sai gashi an zuba ruwa wani irin ruwa a jikin kujeran parlourn har da kujeran parlourn, dakin ya shiga ya dauke ta cak, yayi waje da ita har lokacin barci take hankalinta kwance kamar ba ita ba. Haka take da nauyin barci musamman yau da ta wuni tana aiki. Dakin shi ya ajiye ta, sannan ya fita yana me jin wani irin abu na dukan ranshi, a daren Ya kira Faruq, suka shiga aiki a gidan har kujeran aka fitar da su aka kai car wash, duk a daren, a daren ya kwaso mata kayanta ya ajiye a dakinsa. Wurin karfe biyu uku ya dawo dakin ya zauna yana aikinsa, har karfe uku ya tashi yayi sallah sannan ya kwanta a parlourn, kiran sallah farko ya tashe shi, ya tashi yana fita ya samu Faruq alamar a gidan ya kwana masallaci suka wuce, nima a can dakin shi mafarki nake mai dad'i, sake kiran sallah ni, kamshin turarensa na shaka na fahimci kamar ba a dakina nake ba, bude ido nayi dakyar tare da janyo wayata, yanayin warm din dakin ya kara fahimtar da ni, tashi daga gadon nayi ina duba jikina, na nufi waje, sannan na wuce dakina na ga kofar a rufe, juyawa nayi dakinsa ban kawo ya dawo min da su dakinsa ba, na shiga niman kaya, wani jallabiyarshi na gani a wardrobe na ga bakiɗaya kayan wurin Jallabiya's ne don haka na saka wata ash colour. Na wuce nayi alola sannan na zo na gabatar da sallah, shima hirami na yafa, ina idarwa kuwa sai gashi lokacin ina addu'a, tsayawa yayi yana kallona daga bakin kofar, sai da na gama na mike tare da juyawa ina kallonshi, yadda kuka san an sakawa katako kaya haka nake yawo a cikin kayan, murmushi yayi ya ce min. "Kin yi kyau!" Ya tako inda nake, ya ce cire min hiramin ya daura min a hankali, sannan ya kai ni gaban madubi. "Haka wasu daga cikin matan Larabawa suke sakawa, idan sun fita yawon shan iska " ya fada a daidai kunnena yana kai bakinshi kunnena a hankali na janye kunnena ina juyawa fuskarmu ya kusan haduwa da juna na ce mishi.."Me yasa ka dawo da ni dakin nan!"lashe lips dinsa yayi yana zungure goshina ya ce. "Mafarki nayi wani kamar dodo ya zo ya dauke min ke!" Ya kai hannunsa kuguna yana me dafa min su.
Buge hannunsa nayi na wuce na ce mishi. "Bani key ɗin dakina?" Na mika mishi hannuna, zuwa yayi ya sumbaci hannun yana faɗin. "Babu!" Ya koma gaban wardrobe din ya fara cire kayanshi, sai da ya kwabe daga shi sai gajeran wando, iya cinya dauke kai nayi naki kallonshi, can na kara kallonshi kirjinsa a murde yake irin na cikakken namiji, hadiye yawun tsoro nayi, dauko wata Black single yayi yana mai juyowa ya kama ni ina kallonshi. "Na burge ki ne?" "A'a!" Na faɗa ina tura bakina, "ok zo ki taya ni barci juya kin hana ni kwana da matata!" Ya fada yana mika min hannu. "A'a ni dai!" Na faɗa ina juya bayana. "Allah ya shirya ki!" Ya fada yana mai cigaba da kwanciyarshi. "Ki zo ki kwanta." Ya fada min yana juya min baya. "Zan kwanta a parlour kawai!" Juyowa yayi ya ce min. "Kin san bana wasa da ke!" Ba musu na nufi gadon na kwanta, ina tura mishi bakina, naki cire kayan ina kallon bayanshi ina gudun kada ya juyo. "Ki bar kallona!" "Ni yaushe na kalle ka!" Na fada ina hararanshi. "Yanzu ma harara na kike!" Shiru nayi naki kallonshi. Juyowa yayi yana kallon yadda nake tura baki, don a takure nake. Lumshe idanuna nayi can na ji shi ya matso min, nayi saurin bude idona, nima nayi baya. "Meye haka?" Murmushi yayi yana kara matsowa kafin nayi wani yunkuri ya riko kwalar rigar ya matso da ni jikinshi, kafin ya saka hannu bibbiyu ya yaga rigar jikin har ƙasa. "Don Allah kada ka min haka im not ready!" Na faɗa ina zare idanu. "Me yasa baki shirya ba?" "Please ka barni na bude zuciyata, idan ka min haka ka tabbata mara adalci ba zaka tab'a zama adali a rayuwata ba, zan ta maka kallon tsana da kiyayya ka bar ni na bude zuciyata, wallahi bana jin kome akan ka don, wannan rayuwar al'ummar baya ne suka yi. Duk wata rayuwa ana ginata da aminci amma idan ka ga zaka iya ka yi amma kayi hakuri ba zan tab'a kaunarka ba, kuma ba zan tab'a mantawa da abinda ka min ba, zan rayu kana sauke hakkinka amma duk lokacin da ka bukaci haka mutuwa ce tafi cancanta da rayuwata, koda Allah zai hada jininmu ta zuri'a zan rayu ina tsanarsu har karshen rayuwata." Ma faɗa ina kokarin danne hawayen da yake zuba min, sannan yadda nayi maganar cikin sanyin murya, yasa shi kallona na cigaba da cewa.."kayi hakuri ni ba sonka ko kaunarka ce bana yi ba, kawai bana jin kome akan ka ne, taya zan ki halittar da Allah yayi, ko farce aka ce na halitta ba zan tab'a ba, amma idan ka kyale ni zan rayu ina jin ka a matsayin shugaban kuma zan kasance mai maka biyayyar har iyakar rayuwata, kawai lokaci nake bukata Please ka bani lokaci ka ara min lokaci a cikin wanda kake da shi a yanzu!" Na faɗa ina shafa kanshi. "Ka fahimce ni ba gudunka nake ba, amma ina son samun nutsuwa ina bukatar nutsuwa, ina bukatar duk abinda na.baka ba zan ji zafi ko ciwo ba, bana son ayi ta tsanarka, ban san me yasa Abba yake bayanka ba, a duk lokacin da na ganka Abba nake gani a gefenka, don Allah kada ka min haka ka yi hakuri ka ji, zan zame maka bango a duk lokacin da ka ji zafi ko b'acin rai ka tuna ina nan domin ka, amma a yanzu ka yi hakuri ban san yadda xan dauki lamarin ba, kayi hakuri ka yi hakuri ka yi hakuri Kayi hakuri Sadaukina." Na faɗa hawaye na zuba min, sannan na shiga shafa bayanshi don yayi min rumfa. "Da ciwo a rayuwarka, ka bani damar fahimtar irin ciwonka, a idanunka babu soyayya haushi da takaici nake hangowa, na fahimci haka ne tun daga ranar da muka hadu, akwai ciwo akan fuskarka, fushi da fusata suna cikin nan dinka, ka bude min na ga yadda zan shiga sai na baka kome amma ka sani idan muka rayu a haka har abada zamu ta tsanar juna, ni Salmanun Faris Attahiru Shehu Yayari na aura, ba wani na daban ba. Kai kanka kana bukatar ganin likitan ƙwaƙwalwa domin" rufe min baki yayi ya kwantar da kanshi a kirjina yana sauke ajiyar zuciya a hankali nake shafa bayanshi, yadda yake hakki ya sake matse ni sosai a jikinshi na kara fahimtar magana ta ce take huda duk wani lungu da sako na jikinshi, maganar Abba na jiya har da wannan sannan shi ya tirsassa ni bin wannan hanyar idan har da gaske Faris bai da lafiya tow akwai matsala....
08130269641
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Yau ita ce farko a rayuwata da nake kwance da namiji, kuma a jikina abin ya zame min sabo ko nace banbarakwai, sai dai haka bai dogara da abinda zuciyata take hakaitowa ba, ta fi raja'a akan waye mutumin da yake kwance jikina, a hankali na kara cusa hannuna cikin gashin kansa wanda yake tarawa har ya wuce yadda muka saba gani, sai dai dayawa likitocin ƙwaƙwalwa zaka samu suna tara irin wannan sumar, wasa da gashin nake ina jin wani irin nauyi a zuciyata da gangan jikina ba nauyin kwanciyar ba, yadda zan boye kaina har na iya saka shi dariya. Kalaman Abba ya sake dawo min sabo. _Ki daina kuka haka! Alfarma na karshe da zan nima shine don Allah ki min alƙawarin zaki saka shi ya bude zuciyarshi, akwai jinya a tare da shi amma dole sai kece zaki iya jinyarshi don Allah ki min wannan alfarman don Allah ki bude mishi zuciyarshi. A yanzu baya jin kome a ransa hatta sauran yana zaune da sune ba don yasan me yake tafiyar da rayuwarshi ba, yana tare da su amma bakiɗaya bai san makomarsu ba_
Ajiyar zuciya na sauke tare da jin nauyinsa ya karu, haka yana nufin barci ya dauke shi. Nima gyara kwanciyata nayi muka kwanta a haka. Wurin ƙarfe goma na safe naji wuyarshi tana ƙara, bude ido nayi ina jin karar wayar, motsin da yayi ne yasa na saka hannu a hankali na janyo wayar na saka a kunne na. Ban duba sunan ba kawai na saka a kunnena. "Haba Babana, me yayi zafi da zaka kori Yarinyar da sassafe haka?" Kasa kasa na gyara murya na ce mata. "Barka da safiya Mai Babbar daki, ki yi hakuri amma yana barci idan ya tashi." "Yana barci?" Yadda ta tambaye ni, sai ya bani mamaki. Na ce mata"eh!" "Kashe wayar bakiɗaya." Kashe wayar nayi kamar yadda ta ce, nayi shiru kafin barci yayi gaba da ni. Barci sosai muka yi daga ni har shi, kiran sallah azhar ya farka da ni,har lokacin yana barci gyara mishi kwanciya nayi, na zuba mishi idanu.
"Bana son ana kallona!" Ya fada yana rufe gefen fuskarshi da hannu ɗaya, zura kafa nayi zan sauke ya ce min. "Me kika min dazun nan?" A dan karkace na zabga mishi harara na wuce hanyar fita. "Kayanki yana dakin nan!" Cak na tsaya ina mai juyowa na kalle shi. "Anan kuma?" Tashi yayi ya nufi ban daki yana me rufe min kofar bam. Takaici yasa kamar na bishi ban dakin na kamo shi nayi ta kwala kanshi da kasa. Kwafa nayi na zauna sai da ya fito kallo daya nayi na dauke kai, sannan na wuce ban daki amma sai da na dauki kayana kafin na wuce ban daki na shirya bayan wanka na fito na samu yana saka takalmi, gyara gadon na fara na share dakin, parlourn shi na dawo na gyara kafin na wuce ban dakin na gyara na ga ya ajiye innerwear dinsa na saka a washmachine da yake ban dakin na wanke na maka a inda na ga alamar ana shanya ne, kafin na fito. Na same shi yana zaune a parlourn alamar waya yaƙe. "Waye yace ki kashe min waya?" Kallo daya nayi mishi, na wuce waje, kitchen dina na nufa na hada abin karyawa kunun tambrau na hada na zuba sugar kaɗan sai fan cake da nayi na, ina gama soyawa, na dauko date Honey na zuba a kai, na dauki nashi na nufi parlourn shi na waje na kai don naji muryansa da Nady, shiga parlourn na ga abinda suke yi dauke kai nayi na ajiye mishi sannan na wuce ban kula su ba. Da na fito na nufi bangarenshi na karya ina nazarin yadda zan fuskanci matsalarshi, fita yayi ban kara jin duriyar shi ba, na gama na koma kitchen na wanke kayan da muka b'ata. Ina main parlour na ji motsin Mr Brandy, shiga kitchen din nayi, na gaishe shi kafin na nemi wuri na zauna murmushi yayi ya ce min. "Ina ji a jikina kamar wa'adin aikina ya zo karshe!" Ya fada yana kallona. Murmushi na mai da mishi na ce mishi. "A'a wa'adin zamanka bai kare ba, sai dai zaka bar gidan nan, idan ya so sai ka bude gidan abinci na musamman a cikin garin nan!" "Why?" Ya tambaye ni, cizon lips dina nayi kafin na ce mishi. "Yana da kyau ka fahimci girma da daraja na addinin Muslunci, mu mata muslmai muna da iyakar da ya dace wasu mazan su shigo gidan mu, sannan idan na ce ka bar gidan nan lokaci guda ban maka adalci ba, amma idan kayi tunani da kanka zaka ga abinda ya dace." Na mike zan fita ya ce min. "Shekaru goma sha biyar ina aiki da shi." "Ba laifi ba ne, zai iya binka waje ya ci a can nan gidan matan aure ne." Na fita, ban gayawa mai gidan ba don nasan zai iya kin amincewa, haka yasa na zubawa Brandy idanu, haka kawai gidan matan aure wani kato ya zo yana mana girki, itama Nady ta nime wanda zai na mata girki amma ban da namiji.
kofar