Showing 21001 words to 24000 words out of 304445 words

Chapter 8 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

122

Ka kasan asarar da zan yi?" A matuƙar gajiye ya ce janyo ta jikinshi tare da rungume ta. "Ban san asarar da zaki yi ba!" "Tow ka bar ni nayi yadda nake so, na gaji da fitinar nan kullum cikin gasa min gyad'a a hannu wannan project din yau kwana biyu kenan da na kawo maka amma baka ce kome ba." Shiru yayi kafin ya nufi wurin kujera ya ajiye ta a kai. Karamin firji din da yake dakin ya bude ya ciro ruwa ya bata. Ture ruwan tayi tana faɗin. "Bana bukatarshi." Murmushi yayi ya ce mata. "Idan har zaki amince, ki hakura da project din domin babu alkhairi a cikinsa, akwai project din da nake nima miki, saura kaɗan a cimma nasara zaki samu kuɗin da." "Ni zaka gayawa zan samu kuɗi? Ni zaka gayawa yadda zan saita rayuwata? Kada ka manta da rayuwata ka same ni, don haka abinda na saka kaina shi zan yi ko kayi approved ko kada ka yi na rigada na saka a raina zan yi kome domin kaina."
Daga haka ta mike tana me ƙoƙarin barin dakin, kallonta yake ya ma rasa me zai ce mata, maganar gaskiya bata jin maganarshi. "Na fito daga cikin bloodlines na Royal family ne, don haka ba zaki yi ba." Ya fada mata a hankali, juyawa tayi murmushi kafin ta juya ta fita.

The next.
Ya shirya cikin ya nufi asibiti, yana shiga office ya dauko face mask ya saka sannan ya nufi ward na mahaukata mata, bin gadonsu yake yana duba files dinsu, yana tambayar Nurses din da suke gaya mishi cigaban da aka samu, gaban gadon wata mata suka zo, tana barci ne sakamakon alluran da suka mata. Duk da an daure ta amma idan da zata farka sai su ga sarkan da suka daureta da shi a warware su bakiɗaya don haka sai sun sake mata allura. "Wannan yaushe?" "Yau kwana biyu kenan Dr Bashir ya amshi case dinta, ana tunanin za a mai da ta gida ma don case din ba ta asibiti ba ce." "Yarima Salmanu Faris Attahiru Shehu Yayari." Kallon matar yayi ya ce mata. "Na'am!" "Akwai yarinyar da aka haifa da jinin nasara da sa'a, wacce ita ce mafarin raba kan amana huɗu, ka nimo yarinyar ka mallaketa, koda wasa ba zaka tab'a faduwa ba,.akwai yan baiwa da yawa da suke kasancewa haka, kayi sauri kada ka rasa wannan damar. Wancan tana can tana faffutkar fadawa wata rayuwa. A hankali zaka fahimta domin an juya kome! Daga sama zuwa kasa."

A hankali ta koma ta barcinta, murmushi yayi yana me rubutu. "Dr Faris, dama kai ne Royal Prince din da yake aiki a cikin asibiti?" Hannu ya kai bakinshi. "Shiii!" Daga haka suka kama dariya, "but why doctor, babu amfanin." "I want to live like some ordinary people. Don haka ayi shiru a bar maganar anan!"

Sai da suka gama ganin marasa lafiya mata, kafin suka koma wurin sauran marasa lafiya maza yan iska na asibitin mahaukata. Musamman wadanda suka samu matsala ta hanyar shan kwayoyi. "Likita yau ma kazo? Jiya da na ce mata zan baka miliyoyin Naira ina baka dawo ba, ni zan baka gangaliyo trillion tare da zillion na naira." Kallon Nurse din yayi ya ce musu. "Kuje zan zo yanzu!" Sannan ya nufi kan mutumin kama kunnensa yayi ya murd'a. "Gaya min waye ke sayar muku da kayan maye?" Yadda ya murd'a kunnen sai da mutumin ya sake fitsari. "Khalifa da Ahmad Rilwani Yayari." Murmushi yayi sannan ya ce mishi. "Good Boy!" Ya fita daga ward din, kiran wayarshi aka yi. "Sir everyone is ready, muna jiran ranar ne!"
D'ago kai yayi yana kallon hasken rana, "done!" Yana kashe wayar ya mai da cikin rigarshi. Office dinshi ya nufa a babban parlourn ya hadu da sauran likitocin. "Golden spoon!" Inji wani likita. Kwashewa da dariya suka yi. "Kai dai Dr Mikel kana da matsala." "Eh mana mu anan shekaru goma sha biyar muka dauka muna hada degree da master, Golden spoon kuwa shekaru goma zai dauka ya haɗa master da Phd, kaga kuwa skill is rather than degree." Wucewa yayi office dinsa bai ce musu kome ba, "ka lura kuwa ance a fadar sarki yake zaune maybe irin Yaran dangin nan ne!" Nurse Amina da Nurse Nana kallon juna suka yi, Nurse Nana ta ce musu. "Hmmm kuna abu a jahilce!" Rike mata hannu hannu Nurse Amina tayi mata tana girgiza mata mata kai. "Kada ki ce kome."
Basu kara magana ba, kiranshi aka yi ana nimanshi. Can kamar minti goma sai ga Dr Bashir, office din ya nufa ya kalle shi. "Dr ka yi hakuri, kiran gaggawa ce." "Haba Yallabai, akwai abinda zaka nima na gaza maka, yau ina tsaye ne a matsayin likita ta sanadin Mahaifinka, don Allah ka je ni zan kula da su." Mikewa yayi zai magana Faruq ya turo kofar. "Mutumin ashe kana nan?" Dr Bashir ya mikawa Faruq hannu. "Ina nan aiki ne baya kawo ni nan!" Inji Faruq yana mika mishi hannu, bayan sun gaisa ya dauki jakar Prince ya fito sai da Salmanu Faris ya fito shima rufa mishi baya tare da Dr Bashir, sai godiya yake yi yana jin dad'i. Har Addu'a yake Salmanu Faris ya kira shi ya rike mishi aikinsa wannan ai babban abin farin ciki ne, sannan idan wata yayi wani irin mahaukatan kudi ake zura mishi, tunda Salman ya fara aiki a asibitin har yau bai san.iya adadin kudin da ake bashi domin yayi wani abu da za a ga laifin Salmanu din ba, amma ya kasa domin shi mutum ne mai amana, bayan ya dawo daga raka su Dr Mikel ya ce mishi. "Loyalty dog!" "Duk abinda ka gadama kace, amma ka sani wannan asibitin mallakarshi ce." Mikewa Dr Mikel yayi "what!" "Yes aikin da kake yi a karkashinsa kake yi, wanda ka gani rike da jakanshi shine mataimakinsa idan ya saka jan biro akanka tow takare maka, albashin da ake bamu asibitin gwamnati bai kai allowens din da muke samu anan ba, ka sani kowani mutum yana da abin da yake so ko yake ki, shi ƙwaƙwalwar mutane ita ce abinda yake so idan har ka sake ya juya gare ka tow ba makawa zaka sha mamaki."

***
Cikin gida
Kai tsaye bangaren Mai Babbar daki ya nufa, anan ya samu Hajiya Kilishi wato Hajiya Balkisu wacce take bin Mai Babbar daki,da Hajiya Turaki, wato Hajiya Hadiza wacce take bin Hajiya Kilishi. Sai iyayen Nady sai Nady da take zaune. Sai Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari da Baba waziri Alhaji Mamman Abba yayari sarki mai rikon kwarya, sai Alhaji Kabiru Hamud Yayari. Zama yayi a ƙasa kanshi a sunkuye, a rayuwar zamansu ba a tab'a mishi abinda Nadiya tai ba. Da addu'o'i aka bude taron. Kafin Mahaifin Nadiyyah ya ce musu. "Naso da kun kira Imam Junaid Gobir domin shi na bawa amanar Nadiyyah, lokacin da Mai Martaba yasan Faris ya auri Nadiyyah, and akan me zai na cutar da ita? My daughter ta tashi cikin aminci da nutsuwa taya za a kawo ta cikin inda bata tab'a mafarkin rayuwa ba ace tayi abinda ake so? Haka zai faru ne? Ai haka ba zai taba yiwuwa ba, shi yasa idan don arziki ne Faris bai isa ya kai kafarshi inda Nadiyyah take, amma ya zauna yana juya ta."
"Kayi hakuri, amma mu Royal family muna da limit dinmu da muke tsayawa, sannan shi yasan dalilin da yake dakatar da ita ko Son!" Ciwon lips dinsa yayi tare da dunkule hannunsa. Kanshi a sunkuye ranshi yayi bala'in b'aci. "Idan har dai haka ne gaskiya tow zan tafi da Yarinyata, domin ba zan iya ganinta a wulakance ba, kafin ya aure ta ai har yarjejeniya suka yi babu batun rabuwa amma yanzu zan dauke ta idan ya bukaci tayi yadda take so fine sai ta dawo." "Kayi hakuri duk da mai martaba baya nan amma ina mai baka hakuri da abin da ya faru, baa kyauta mata ba sannan, shima za mu mishi faɗa."
"Hajiya Maryam bai da ce a yanke hukunci bangare daya ba, domin idan aka yi haka babu adalci a cikinsa. " "Alhaji Mamman wannan shine adalci, tayi hakuri." "And akwai wani labari da yake yawo na cewa ana son Salmanu Faris ya kara aure?" Tabbas Mai Babbar daki ta fadi haka. "Tow amma ku sani idan har aure zai yi ina ga lokaci yayi da zai sawwake mata." Shiru duk wurin ya dauka still dai ita mai Babbar dakin ta ce mishi. "In sha Allah ba za a mata kishiya ba, Alhaji kayi hakuri."mikewa yayi zai bar parlourn. "Ina zaka ka bawa surukinka hakuri!" Juyawa yayi yana kallon Mahaifiyarsa. "Ummina ai kin bashi hakuri idan sun rena naki shi kenan su yi duk abinda suke so!" Ya saka kai ya fita, "Ummi ba sai ya basu hakuri ba, Dad ai ka hakura ni dama kawai a samu masalaha shine bukatata!" Ta fada tana bin bayansa, "ai kun ga irinta mata da miji kenan haka suke gashi zasu daidaita kansu."
Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari bai so haka ba, idan har da Salman ya yi zuciya ya ce zai rabu da Nadiyyah tow shi zai nimawa kanshi Nadiyyah, zuwa yanzu da ake hasashen Alhaji Jamil Chiroma zai iya zama next shugaban kasa haka zai bashi dama da ikon biyan buƙatarshi. Kyaututtukan da aka yi ta shigo musu ne, wasu irin manya kwati ne kowa da na shi kudi ne na fitar hankali mazan kenan, matan kuwa kayan kawwa ce danginsu zinari musamman Mai Babbar daki da taji babu zancen yiwa Nadiyyah kishi matukar tana raye. Da aka suka watse suma suka koma garin Jos dama a can suke da zama.
Da dare da ya shiga mata sai da safe nan ya samu sabon nasiha har da mishi iyaka da wata mace, matuƙar ya ce zai yi aure sai ta mishi Allah ya isa. Wannan abin ya tsaya mishi a rai.
Dalilin Mai Babbar daki kuwa Mahaifin Nadiyyah yana da karfi, zai iya amfani da karfin domin karawa da kowa a bawa Salmanu Faris kujeransa. Haka yasa dole su hakura da Nadiyyah.

Koda ya koma da wasu kayan barci ya same ta, ajiye mishi file din tayi ya dauka ya saka mata hannu sannan ya wuce dakinsa,domin mai Babbar daki ta gaya mishi Nadiyyah da iyayenta sune damarsu ta karshe don Allah kada ya ce zai yi wani abu da zai shiga tsakaninsu yana rabuwa da Nadiyyah kamar mulkinsu ya rasa.
Abinda Mai Bauchi ya fada yasa ta fusata yana faɗin. "Tow idan Nadiyyah ta mutu fa Ubanta zai cigaba bawa Yaya goyan baya ne?" Dakuwa tayi mishi tana hararansa..

Washi gari, sai da Nadiyyah ta zo ta gaishe ta sannan ta ajiye mata damin kudi ta ce. "Ummi a rabawa masu tayaki hira." "Bakya gajiya ne?" "A'a Ummina dama nace idan ba zan takura Aneesa ba ita da Dawla zan biya muku umara sai ku tafi ku yi ibada tare da yiwa mai Martaba addu'a." "Ikon Allah, Nadiyyah!" "Ummi albarka zaki saka min kawai!" "Tow Allah ya miki albarka."

Fita tana jin dad'i, Babanta yayi gaskiya da ya ce mata, suna da ikon ja da kowa amma Salman ba zai tab'a musu biyayya kamar yadda suke gani a wurin kowa ba, idan suka janyo danginsa suna kashe musu kudi da da musu hidima zai batar tayi yadda take so domin ko bar ta ba, danginsa ba zasu tab'a barinsa ba.
***
Friday


Ikhlas Junaid Gobir
Tun da Hajja tazo kullum sai Abba ya raba Fada a tsakanin Hajja da Iram.
"Junaidu nazo gidanka ne bakin ciki ya kashe shi? Yarinyar nan Irak kaga yadda take min kallon banza, wallahi ba zan yarda ni da gidan d'ana ana min kallon uku saura kwata."
"Iram me yasa baki jin magana ne?" "Abba!" "Munafuka yi min shiru." Inji Hajja. "Ni dai gaskiya ba za a saka min Ya a gaba ana cutar da ita a banza ba, ka jawa Hajja kunne ko a ji mu da ku."
Murmushi Hajja tayi ta ce mishi. "Ai dama nasan mara kunya sai kin yi magana, tunda nayi magana. Yarinyar nan shiru-shirunta na munafunci ne." Fisgar hannun Iram tayi tana faɗin.."Allah kaɗai yasan karatun kurma." Daga haka ta wuce. Irin wannan rigimar bata karewa a gidanmu..
Shigowa Hajja tayi tana faɗin. "Kilas baki ga sauyi a tattare da yarinyar nan Irak ba?" Girgiza kai nayi nace mata. "Ban ga kome ba Hajja!" Na faɗa ina hada kaya zuwa office. Wayata ce tayi ƙara na ɗauka ina sakawa a kunne. "Yeemar!" "An gaya miki labarin yau garin kamar za a samu wani karamin crisis?"
"A'a gani ina shirin fitowa ne?" "Gaskiya kada ki fito, domin ana tsammanin ba lafiya jiya an samu gawarwaaki wasu mutanen da ba sani ba. And an saka Curfew." "Curfew? Gaskiya zan fito kada ki damu na samu damar yin wani bincike ne. " "Ikhlas kada ki fito fa!"
"Sai kiyi! Na kashe wayar, na dauki jakata. "Ke kilas baki ga sauyi a tattare da yar uwarki ba?" Juyawa nayi na kalleta kafin na ce mata. "Hajja don Allah ana zaman lafiya a gidan nan, kada ki rusa mana zaman lafiyar da muke yi Please!" "Tow shi kenan amma ni nasan abinda na gani yar nan!" "Ke iya idanunki kaɗai zai ni mu kuma abinda zuciyarmu yake dauke da shi zamu gani." "Ina zargin tana da juna biyu...

Bononza bononza matan kwarai masoya gyaran sunan kunada lbr sallah promo kuwa wanda mayan mata wada sukashahara tawajen bada magani tazomuku d promo datakeyi duk shekara nakayan dahu hjy kisaya kihada dakanki inamasuso cicibin da nakayan cikin dana tsuka yanka 9 dana bindi saniya to gamagani kisaya kihuwa kema kiji me akeji ne 🤙 lahiya yazo kemakizama tauraruwa agidanki 🥰 dakudinki kalilan promo 1 cicibin magani promo 5k ,,7k
2 bindin saniya 8k 10k
3 natsuka yanka 9 3500 2500
4 nakayan ciki 3k 2k
5 nakaza 4k noml 6k
7 nasoya koyi 1000 2k
8 nasawa kowani kalan cukudin magani shikuma 3500 yadaukan abudayauwa ummu rayan inagodiya m zee 🫶
Kar ayibake don sallah akayi wanan saukin

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.



*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*



*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍

*Hala so kuke na wangale muku labarin kafin na kai karshen labarin kowa ya san me zai faru 😉🙄🤣 a tow ba dani ba gad'a a makabarta*


07

Ban san lokacin da kayan hannuna ya kwace suka zube a kasa ba, a birkice na kalle jikina yana tsuma. "Hajja kin san me kika faɗa?" Fuskarta bai nuna damuwa ko kaduwa daga tambayar da na mata ba, sai na wani confidence da na gani akan fuskarta. "Ikhlas ina jiranki!" Iram ta fada daga waje. Wanda ya nuna alamar ta ji maganar Hajja. "Ai ba karya na mata ba, gata can a waje ki tambaye ta." Fitowa nayi ta ce min. "Yau garin babu lafiya, ina ganin an saka Curfew!" Yadda tayi magana na fahimci kamar ranta ba dad'i. "Hmmm don Allah kada ki damu da Hajja kin san halinta."

"Wai kin yarda da abinda ya faɗa ne? Kin ga nayi kama da mai ciki ne?" Kallonta nayi a mamakance kafin na girgiza kai, sai yanzu na lura da sauyin da nake gani a tattare da ita na saka katon hijab ko da a cikin gidan ne. Yanayinta ya sauya sosai amma da yake bana son shaidan ya ci galaba a kaina nayi maza na kore shi nace mata. "Kodaya." Shiru tayi kafin ta ce min. "Muje Mommy tana kiranki." "Tow bari na ajiye jakata." Na mai da dakinmu na bi bayanta, daga ni har ita babu wani wanda ya kara magana bana mantawa muna Yara ita dasu Iman da Ikram zan gansu suna wasa amma basu barina na shiga, dama dama Ihsan tana jana a jiki. "Mommy gata nan." Sai lokacin na bude baki na ce mata. "Ina kwana Mommy!" Kallona tayi sama da kasa. Kafin ta ce min "lau!" "Zauna nan!" Yau ni ce Mommy Turai ta ce na zauna a kujera bayan a duniya ko parlournta bata kaunar na shigo, kai naci azaba a hannun matar nan, karfi da yaji na koyi fada da rashin kunya wanda ya bi jikina. "Zainab abinda na saya na kira ki, dama na ji ko kina da saurayi ne?" Kai tsaye na ce mata. "Ya Uwais ne bamu gama shiryawa da shi ba." Gyada kai tayi tana kallona yayinda na lura tana hararan yarta da wutsiyar idanun, nima sai nayi kamar ban gani ba. "Ikhlas dama tambayarki zan yi yaushe rabonki da ki ga Iram tayi al'ada?" D'ago kai nayi na kalle ta, ni dai nasan duk wata tana daukar saniteria pad bayan nan tana kwashe kamar kwanaki bata sallah sake maimaita min tambayar tayi na ce mata. "Mommy ko cikin watan nan na ganta bata sallah sannan tayi amfani da pad


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login