Showing 150001 words to 153000 words out of 304445 words
da ni a daidai lokacin da nake bukatarshi ya tafi ya bar ni!" Matsawa nayi ina kallon yadda take kuka. "Daga can kike?" Ta nuna min Zanzabira daga inda nake tare da ita. Gyada mata kai nayi, "ki min alƙawarin zaki dawo da shi hanyar da zai kwace mishi. Ni da su zamu sadaukar da kome namu domin kiyo nasara. Kada ki sake su kawo ki nan domin tasirin ki zai gushe kamar nawa. Kiyi yaki kamar ba gobe ki tabbatar da kin tashe shi daga barcin da yake shi din da yake can ya manta Asalinsa ya...." Wani irin iska ne da guguwa ya tashi, karar fashewar abu daga can birnin ya tashi. "Na shiga uku waye zai kawo mana dauki sun shiga cikin masarautar rundunar shaidanun tsakiyar birnin, wayyo ke ki gudu!" Kukan dawakai hade da takun sawunsu. Suka tunkaro inda muke, da gudu kafin su iso kasa ta hadiye matar da yaran bakiɗaya yadda suka d'aga takobinsu na saka hannu xan kare kaina tare da kwala ihu da karfi sai da na'uran da aka saka min suka shiga wani irin ƙara suma, na mike zubur ina mai kare kaina. "Wayyo Allah na, Wayyo Allah na, Wayyo Allah na!" Yana shigowa ya ga yadda suke dambe da ni, ture kowa yayi ya rungume ni. "Gani ina tare da ke!" Kuka na saka mai cin rai sai yanzu na tuna matar da yaranta yadda kasa yake hadiye su, hawaye na zuba a idanunta. Nima kuka nake ina kara rungume shi. *Kada ki manta damu, ki tuna da mu ki toshe shi domin ya tuna da mu!* Shafa bayana yake yana bubuga bayana, allura aka min domin sun gano bugun zuciyata tana fita bibbiyu, kwantar da ni yayi yana shafa bayana a hankali..har alluran yaci karfina a hankali na ce mishi. "Baka kewar wani abu ne? Baka jin like you miss someone else? Baka kewar ko Yara ne?" Daga haka nayi shiru domin maganar ba zan iya ba barci yaci karfina. "Ina tare dake kewar mai zai yi?" Kafin na gama rufe idanuna yanayin wancan Sarkin da na tab'a mafarkinsa ya bayyana a gabana. Rike hannuna yayi yana kallon yadda nake lumshe idanuna daga nan shi kenan, so nake na ce mishi tana jiranshi so nake na gaya mishi suna kewarshi, amma duk na kasa duk na kasa cigaba da tunanin kome.
***
A cikin duhun dare, mace ce gaban wani tubalin wuta tana sake ingiza wutar yana tashi. Wani mutumutimi ta dauko ta kara a jikin tubalin ta shiga watsa mishi jini, a hankali wutar take tartsatsi har zuwa wani lokaci kafin ta fara magana da karfi. "Aojana ki dawo ga baiwar ki nan ta zo gare ki, Aojana bayyana a gaban baiwarki tana niman ta gomashin albarka a gare ki, sasaarin da aka dauke Awatif lallai zai balle Aojana ki bayyana labulen satara wanda ya tashi a daren sha biyu ya dauka a daren sha hudu ya lullube, har yanzu rundunar shaidanun tsakiyar birnin basu bayyana ba." Surutu take tana ƙara ƙarfi har wutar ya wani irin tashi da karfi kafin ta razana ta koma can, wani irin jan hayaki ne ya fita daga cikin wutar ya zube a can kamar ruwan dalma, mutuwa yayi murus kafin wani farin hayaki ya bayyana a gaban matar cikin surar mace kyakyawa daga iya cibiyarta take mace. Amma kasanta wuta ne da baka iya gane tana da kafa ko babu. Tana tsaye a hankali take bin dakin da ido, kafin ta sauke akan matar da take gabanta a durkushe.
Takawa tayi tana mai isa gabanta. "Barka da haihuwarki, ranki shi dade!" Kallon hannunta tayi a hankali tare da kallon kanta. "Kina bukatar gangan jikin da zaki rayu? Kina bukatar kusantarshi domin ki rayu uwar gijiyata nuna min hanyar da zan tayaki niman wanda zai sadaukar da kanshi dominki?" Shawagi ta fara akan iska tana faɗin. "Tabbas ina buƙatar gangan jikin da zan rayu amma ba wanda ya mutu ba, na fison rayayyen wanda zan biya a cikin inuwarshi. Bana bukatar matacce domin zai iya zame min tarko. A duba min gangan jikin da yake da kusancin haifaffen sarki!"
Daga haka ta koma cikin wutar da aka tashe ta a cikinsa.
***
Mai Babbar daki zama tayi tana nazarin littafinta da Baffanta ya turo mata, a jikin littafin a rubuta *KUNDIN ZANZABIRA*
Juyawa tayi tana sauke numfashi, ta duba tun daga shafin farko rubutu ne da aka yi na alhini.
_Mai yiwuwa wannan shine karon farko karanta kundin Zanzabira kayi shiru domin girmama ga Mata magabatan na masarautar da suka sadaukar da rayuwarsu! Musamman Lu'ulu'u Awatif wacce aka binneta da Yaranta biyu! Tarihi ba zai manta da jarumtar ta ba, wacce ta bada rayuwarta domin kare Sarkin na tara wanda aka boye sunansa na asali aka bayyana wanda ya samu bayan zuwan wata addini daga wasu bakin haure daga wata nahiya na daban! Fatan Alkhairi ga Awatif tare da ahalinta da suka yi imani da Mai Martaba sarki Allah ya jikansu ya musu rahama domin sun amshi tafarkin addinin Muslunci tafarkin gaskiya!_
*Kada ka ci amana domin ita amana takan ci wanda ya cita ne!*
Inji Sarkin yakin Zanzabira
Bargaga ⚔️
Wani abu ne ya gifta akan Mai Babbar daki,ranar da Adade take cewa Faruq Bargaga, wani irin faduwar gaba ta ji, ta cigaba da bin wani rubutu a cikin littafin.
_Abin da muka sani sarki Shago ya kasance daya daga cikin sarakunan da suka amshi ragamar shugabancin masarautar a shekarunsa na sha takwas, ya girmama faɗin masarautar zuwa manyan biranen har zuwa gabashin ciyyah! Sannan a arewa maso gabas ya haɗa har zuwa borno! Kafin ya sarara inda yayi ta yakar kananan ƙabilar da bata da karfi domin kara karfinsa! Sai da ya kai shekaru hudu yana wannan yakin wannan shine abinda n asani_
Prof. Hamis Jikan Baida'u
Na jami'ar dan fodio.
Bude sabon shafi tayi a hankali ta ci karo da wani farin hoto wanda taji zuciyarta kamar zata dirko daga kirjinta! Salmanu Faris ne sanye cikin shigar sarauta! A kasan hoton an rubuta rubutu kamar haka..
_Tarihi ba zata manta sarki Shago ba! Ba zata manta da gwagwarmayar shi ba! Sarkin da ya zagaye wasu nahiyar ya tawo da wasu bakin haure masu wata irin shiga da tufafi! Sarkin farko da ya koyi harshen wasu ƙabilar bayan harshen Hausa! Ya kuma shigo da wata addini bayana addinin bautar iskokai_
Dr James Alexander
Na Jami'ar Oxford department of arts and historian.
Rufe kundin mai babbar daki tayi tana zare glass dinta, hawaye da karya na kamata. Kenan masarautar ta wanzu da karfin muslinci kafin zuwa Shehu Usmanu danfodiyo?.....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 49
A hankali ta rufe littafin ba zata iya karantawa ba, domin zuciyarta cike yake da tsoro. Sannan idan ta ce zata cigaba da bibiyar labarin ba mamaki ta iya ganin abinda zai dame ta, haka yasa ta rufe labarin yadda zuciyarta ba zata ji ba balle har ta kai ga son karantawa. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon window dinta a ƙasar zuciyarta kuwa wani irin tunani take, idan har dama can haka ce to kuwa maganin kada ayi kada a fara, idan ba haka ba Ikhlas ce zata wahala. Wani abu ta ji yana tsingulinta tana son ta karanta ta ji me ya faru. Kurawa Kundin tayi tana jin kamar ta hakura kada ta hango abinda zai dame ta, amma wani bangare na zuciyarta yana tursasawa ga zuwa ga Kundin ta ji me ya faru. Da har yake barazana ga rayuwar d'anta, wani irin tsoro da tashin hankali take ji mai karfin gaske, wanda ya haifar mata da jin wani abu kamar yana motsi a gadon bayanta.
Bude kundin tayi ta isa kan shafin gaba bayan na hoton Sarki na tara na Zanzabira! _Ya kai mai karatu idan wannan shine farkon karanta wannan labarin ka sani zaka so jin mai yasa aka damu da sarki na tara? Me yasa sarki shago? Biyo ni a hankali ka isa ga kundin ka ji irin gudunmawar da ya bawa al'ummarshi._
Mulkin zamanin maguzawa
Kundin tarihin Zanzabira.
Ƙarni na sha shida
Farin dare
Ranar Biyar ga watan Maris
Kaiwa da komawa unguwar zoma suke wanda suka cika bangaren Sarauniya A Maza wacce ta kasance y'a ga Sarkin Yakin Zanzabira, Mata ga sarki Ilu, wanda ya kasance sa maza gudu, shi kanshi Mai martaba kaiwa da komawa yake yana kallon kofar shashin Amaza, wacce tun safe take kan gwiwa. Har zuwa wannan lokacin da ake ganin haihuwar tana gab da zuwa amma sai a samu matsala kan Yaro ya koma. "Mai bishiyar tsamiya da bishiyar kuka, Ya mai muradai na aljanu sha ji na gamji mai tubalin yaƙi! Kai ne mai Sarkin rafi da Sarkin kutaren aljanu! Ina mika sakon jajjantawana akan sarauniya Amaza ba gazawa ba ce, isa ce ta saka Yarima kin fitowa yana bukatar jini yadda zai sami damar fitowa!" Inji wata mata wacce take sanye cikin baki da ja na yadi, fuskarta bakiririn kanta cike yake da layyu da wuri, idanunta jajjur ta saka kwallin da ya kara fitar da muninta!"
A tsume ya kalleta ya ce mata. "Bokanya Ajuji, idan kin san cewa Yarima ba zai fito ba a kashe Amaza a fitar da shi da karfin tsiya ai ba kome ba ne face sadaukarwa!" "A'a Mai Martaba, ba iya shi Sarauniya zata kara wasu Yara mazan da ba a san iyakansu ba!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Ayi duk abinda za ayi matukar bai fito ba, tow ba makawa zuwa gobe da safe sai dai ta hakura da rayuwa shi ya rayu! Ko daidai da zira'i bana kaunar makiya su yi barci so nake a wayi gari an girgixa musu zuciya yadda tsoro zai saka su fitsari a wando!" "A'a tana gare ka! Amma fita yaki safiyar gobe wajibi ce! Domin ga mashaya can daga farin birni sun tunkaro filin dagga." A fusace ya juya a gare ta! Kafin ya ce mata. "Na miki kama da wanda yake tsoro? A daren nan zan farmake su nayi daga-daga da ruhinsu da namar su, na watsawa ungulu su ci su koshi." Ya fara yana gyara tsayuwar shi. "Na rantse da iskokai a yanzu haka na ga wasu khadiman masarautar nan a waje suna gudu! A farmake su a kashe ai a dawo da gawarsu!" Ta fada da karfi. Fita yayi zuwa fada ya saka Sarkin busa ya buga tamburan fadar, yana tsaye Bokanya Ajuji tazo ta tsaya. "Maza a shirya mahaya gilla su nusa dajin karnakato ga Khadiman masarautar can suna son su isa ga abokan gaba!" Buga sandarta tayi da kasa wanda ya haifar da wani irin yanayi ta d'ago kai ta kalle su. "Na yanke muku nisan tafiyar zaku iya tafiya ku kawo su a raye. Domin Yarima yaki fitowa sai an yi mishi wanka da sabon danyen jikin ma fita amanar Masarautar!" Wata kofa ce ta bude suka fita bakiɗaya. Ya dauki tsawon lokaci domin a lokacin farin wata yana kara haske da washewa cikakken daren goma sha huɗu me dauke da yanayi mai albarka, kafin wani lokaci an kawo manyan Khadiman masarautar gudu uku. Gambo na jikin shugaban rundunar Bamayi, Dan Tani kani ga Shamakin Tanko, sai Chindo dan uwa ga shi kanshi Sarki Ilu. Gurfanar da su aka yi. "Kun manta waye ni ce?" Bokanya Ajuji ta tambaye su, murmushi tayi ta ce musu. "Naci dubu sai ceto!" Ta fada tana komawa gefe ta fara yan tsubbace-tsubbacenta a hankali.
"Idan aka sare kansu wata zata yi jajjir kuma zaka yi nasara har zuwa shekaru aru-aru, jininka zai cigaba da gudana, idan aka barsu tabbas wasu zasu kashe su domin ko an tambaye su ba zasu buɗe bakinsu ba! Su kansu danginsu ba abin yarda ba ne." Zubewa Chindo yayi yana faɗin. "Tuba nake Dan uwana, ba cin amanarka muke shirin yi ba, mun tafi mu ga yadda rundunar take ne."
D'aga mishi hannu Sarki Ilu yayi ya ce mishi. "Ajuji mai kika ce?" "Idan aka hukunta su kowa zai ji shakkar aikata wani miyagun laifi kowa zai shiga hankalinsa. Sannan shamaki da Shugaban runduna a kawo su a musu hukunci na cin amana, domin kafin watsewa mutane a fada an sanar da yadda yakin zai tafi amma suka zari jiki bayan Sarkin Yaki Yaro na can.!"
"Ya batun Sarauniya Amaza fa?" " Daren nan zan ayi aikin wanka da jinin farko domin wanke mishi hanya." Ya nuna Chindo dan uwa da sarki ya ce mishi. "Sadaukarwa ce bashi damar amsar hukuncinsa!" Haka dakaru suka kama Chindo aka safe kanshi, Bokanya Ajuji ta mika wata kwarya jinin da yake zuba ya shiga zuba cikin ƙwaryan. Haka aka cika kwarya har biyu sannan ta wuce hanyar cikin gidan, tsayawa tayi rike da ƙwaryan. "Iskokan yamma iskokan arewa, iskokan gabar iskokan kudu, maza ku zo ga godiyarku ta gaza maza ku zo ga baiwarku ta nuna gazawarta, ina kuke na kan tudu da na gangare ina kuke masu ruwan nasara, Zanzabira ta ku ce ina ruwan rauhanai nan ba ta Aljanu ba ce, ina kuke masu amana da jinin mutane maza ga sabon sarkinku yana hanya." Sannan ta nufi dakin ta watsawa Sarauniya Amaza da take durkushe jinin nan, wata irin guguwa ce ya turnike sararin samaniya har sai da hasken wata tayi ja. Kafin can jariri ya callara kuka.
An haifi shi cikin cikakken daren sha hudu wanda ya zo daidai da jan dare wanda jar guguwa ta lullube sararin samaniya. Washi gari asubar farko sarki Ilu ya dirka sansanin yakin inda yayiwa abokan gabanshi zube.
Bayan ya musu barna ya kashe su,.sannan ya yanko kan sarkin Kaita wanda da shi suka yi yakin ya nufo zanzabira da rayukansu, yana isowa ya saka aka kafe su a kofar zanzabira, sannan ya shiga cikin masarautar bayan ya tara Khadiman masarautar aka yi liyyafa, domin yaki bai wani tafi so far ba aka yi nasara, don haka daga yau za a fara liyafar zuwan sabon magajin garin zanzabira. A cikin wadanda da suke Fadar da Shamaki, da Shugaban runduna. Jikinsu a matuƙar sanyayye domin sun san daren shekaranjiya an kashe yan uwansu. "Idan na ce muku! Mulkina cike da izza take sai ku ce haka ne! Eh haka ne amma tabbas mulkina cike da alfahari take domin jinin zanzabirawa da yake gudu a jikina. An haife min da namiji bayan cire tsammani, yau gashi har an kwashi kwana biyu, nasara kan nasara ya lullube duniyata kuma duk akan wancan kujeran masarautar! Na ciyar kuma na shayar da guba a gare ku." Yana fadar haka ya mike tsaye yana gyara zaman alkyabbar shi. Yayinda shugaban runduna yake rike da wuyarshi yana kakarin mutuwa, haka ma Shamaki, wani irin tsoro ne ya shiga zukatan dukkan mutanen cikin fadar ya zauna daram ya kuma samu mafarkar siyasa. Yadda babu wanda ya isa ya kara ja da mai martaba, haka yasa mulkin ya samu tagomashi.
Sati da haihuwar Yarima shago, aka yi suna na ban mamaki, wnada ya haɗa ko ina da kuma kowa. Kasancewar Sarki Ilu bai tab'a haihuwar da namiji ba duk Yaransa mata ne har zuwa lokacin da ya samu D'a namiji. Haka masarautar ta cigaba da fuskarkantar wasu irin yanayi na barazana da mulki na zalinci domin sarki Ilu yana da wani irin goyan baya da mulkin zalinci daga Bokanya Ajuji, wacce kaf zuriyarta ita ce bokanya mace. Zamani aka ce riga idan aka cire wannan a ajiye wancan haka zamanin yayi ta tafiya a lokacin da Shago ya cika shekaru goma sha shida.
Sarki Ilu ya fara wata irin jinya wanda ya d'aga hankalin kowa domin ba karamin tashin hankali suke ciki ba. Domin ko bokanya Ajuji tayi matukar ƙoƙarin gano mai ke damun sarki Ilu amma ina haka jinyar tayi ya cinye shi tana kassara shi, sannan yayi ta fama da hauka bayan wannan jinyar da yake bibiyartashi. Abu na farko da Ajuji ta boye shine Sarki Ilu ya boye karagar da aka kireta da takutu da azurfa, tare da ruwan zinarin asali wanda ita ce Zanzabira bakiɗaya, masana tarihin na can baya sun tabbatar da ita kanta karagar wasu rauhanai aka biya suka yi ta, sannan duk wani sarki da ya jibanci zalunci a masarautar dole ya hau ya zauna domin ta haka ce za a iya tantance asalin jinin masarautar! A wani kauli ma ance Sarkin da ya saka aka kera kujeran ya bada Yaranshi mata uku, da matarshi domin a lokacin Zanzabira tana fuskantar yake-yake da aka yi a birnin kasar hausa, wannan yasa aka dauke kujerar a boye da sahalewan sarki Ilu. Dalilin da yasa aka yi haka shine ya hango wani Babban al'amari da zai faru a nan gaba kaɗan.
A lokacin da Bokayan Ajuji ta fahimci haka, take ta yi kokarin a boye kujeran yadda babu wanda zai bincika sannan a rufe tarihin masarautar yadda babu wanda zai so ya san me ya faru. Haka aka cigaba da jinyar Sarki Ilu har