Showing 156001 words to 159000 words out of 304445 words

Chapter 53 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

79

domin basu yi tsammanin wurin haka yake ba, duk Sarkin da dai hau mulki bai san makamar yaki bai cancanci zama sarki ba, domin Sarki Shago matashin Sarkin da bai wuce shekaru ashirin da uku a duniya haka ya dami katin maza masu tozo da tsokaki ya takura musu ya addabi rayuwarsu yayinda shi Bargaga yake gefe yana kallon irin bajintar abokinsa, kuma shugabansa. Da a ce ya iya bada labari tabbas da ya zauna ya zama makarancin domin ya gaya musu irin aikin da yayi, da ya basu labarin irin tabargazar da yayiwa mutanen nan domin ba a haifi wanda ya tab'a shi, kamar yadda yayiwa dan uwansa alƙawarin, sai da ya gama da su sannan ya cire kawunansu ya zuba a raga ya janyo shi suka sauko kasa, farin ciki da mutane suka shiga yasa suka shiga bikin murna tare da tatsar madaran saniya mai dumi suka mishi wanka da shi, tare da girmama shi a matsayin Uba a gare su.

Sannan babban waliyin karnin da babu kamar shi, a daren ranar suka bar garin kafin wayewar sunan Damina wacce wasu suke kiranta da Gimbiya Marka, ya iso fada tare da alƙawarin da ya cika. A lokacin da ya iso nan ma bikin suna ake yi, koda Balarabe ya ga tarin kawunan yan fashin sai da tsoro ya kama shi wanda yasa Sarki Shago dariya domin ya jima bai ganshi a firgice ba, sannan shi kanshi Sarki Shago baya son zargin da yake Ya tabbata gaskiya, domin yana tsoron kada dan uwansa ya zama boyayyen makiyansa, saboda mulki, haka yasa yake ganin kamar akwai wanda yake son ganin bayansu. Juyawa yake ya tukararshi amma zuciyarsa ya kasa nutsuwa dole ya saka a kira mishi Ajuji, ta dauki lokaci kafin ta iso fada, tana isowa ya mika mata abin amsa tayi ta rufe idanunta, a hankali take ganin wasu abubuwan masu girma a cikinsu har da sace abin da aka yi. Murmushi tayi ta ce mishi. "Ranka shi dade! Wannan abin sacewa aka yi. Duk da haka ina kira da ka zama me lura da kowa domin zamani ya zo da wnada kake tare da shi dari bisa dari shi yake iya kashe ka"
"Zan duba!" Zata kara magana ya d'aga mata hannu haka yasa tayi shiru dole sannan tashi mishi sallama ta bar fadar tana tsoron gaya mishi ya kula da bayanshi.....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 51
Ya sani, ya san me take shirin gaya mishi. Yasan abinda ita bata sani ba, saboda baiwar da yake da ita. Yana yawo a nahiyoyi domin samun ilimi yana mu'amala da mutane ma bambanta domin niman ilimi. Haka ya sa shi jin lallai akwai wani abu da zuciyarsa take son bayyana mishi amma kuma haka ba yana nufin zai yarda da ita ba ne, jini ba wasa ba jini yafi ruwa kauri, baya tunanin akwai wanda zai iya dabba mishi wuka a baya cikin sauki.
Bayan an gama taron suna, ya shiga bangaren Aojanah ya zauna a bakin gadon yana kallon yarshi hannunshi ya kai ya riko Hannunta a hankali ya zare hannunsa ya saka yatsarshi a cikin nata, rike yatsar shi tayi yana kallon yadda take barci, a hankali ya zuba mata idanun wani irin tsaftacecciyar kauna yake ji a kan Yarshi da yake ganin kaf duniya babu na biyunta, shi soyayyar d'a ga mahaifinsa daga ranar da ya fara jin labarinsa yake fara kaunarshi har zuwa ranar da zai yi tozali da shi, haka ya kasance ga Shago, asalin soyayyar da yakewa Yarshi na dabance, uwar kuwa bai tab'a jin ko sau daya ta burge shi ba, ko me zata yi abu daya ya sani ya sakar mata wasu damarmaki dayawa, daga cikin haka har da hana shigo da bayi mata duk ya bata wannan damar domin Aojanah mace ce mai tsananin kishi, wanda kishin yasa ko Sarauniya Amaza bata yarda ta bar wata baiwa a bangarenta matukar Aojanah zata shigo cikin gidan saboda yanzu zata fusata ta ce zata cutar da baiwar.

Kwanaki sun cigaba da tafiya yayinda suke rikid'ewa zuwa makonni, mako ya juya izuwa watanni, haka watanni suka bada tazarar shekaru masu yawan gaske wanda a cikin shekarun Aojanah ta haifi Yara mata hudu, wanda haka ya dasa mata wani irin zafin kishi da baƙin ciki. Tare da firgici me yawan gaske domin Sarauniya Amaza ta fito da kulafucinta na son Jikoki maza ko don su gaji masarautar. Sai dai duk yadda Sarauniya Amaza ta so haka bai samu ba domin sai an gama maganar aure Aojanah zata lalata kome tun ba a gano ba har aka fahimci tana lalata kome ne don ta gayawa Sarauniya Amaza ita matar Sarki ce, tana da ikon hana shi zama da duk wata mace da taso, ba wanda suka so ba. A wannan takin sai gidan Sarautar ya koma kamar filin dagga domin ita Sarauniya Amaza tana son nuna ikonta da danta ne ita kuma Aojanah ta nuna mata ita matar Sarki ce uwar Yar da yafi so. Haka aka yi ta rigima sai da Ajuji ta shiga tsakani ta fito kiri -kiri ya gayawa Aojanah. "Tabbas zai haifi magada, sai dai yadda kika saka a aranki baki haifa ba babu wacce ta isa ta haifa, magada za a haifa ba Magaji ba."
Wannan kalamar Ajuji ya bugi kanta kamar ya dawo da ita daga duniyar mafarki ne,.haka yasa tayi ta shiga da fita tana niman hanyar da zata hana shi aure, sai dai a lokacin dai bata isa ba, don Shago ya cigaba da mulki da yawon shi nahiyoyi har ya cika shekaru arba'in a duniya, ya zama cikakken namiji da duk inda mace ta ganshi zata so mallakarshi, a lokacin ya hadu da Awatif wacce ya kirata da Lu'lu'a, kafin wannan lokacin ya fara haduwa da wasu ayari na Larabawa da suka kwadaita mishi Muslunci, abinda ya ja hankalinshi shine, wata rana cikin dare wani shaidanin dabba ya shigo sansanin ayarin fataken, shi kuma yana cikin ayarin. Wannan shaidanin Maciji ne, a karon farko da suka hadu da macijin sun mishi magana ya tafi kada ba zasu cutar da shi ba, amma haka macijin mai girman maisa. Ya kara dawowa a cikin daren sau uku suna koranshi yana dawowa. Na hudun da suka dawo babba cikin fataken ya dauki dutse ya karanto wasu abu ya tofa ya jefa mishi, ya kara tofawa ya jefa mishi, sau biyu ya ce mishi. "Mun naka shawara kada ka dawo amma kayi taurin kai, tun farkon ganinka nasan kai ba dabba ba ne ka rigada ka girma ka manyanta amma ka ko gane abinda nake nufi mu addininmu ya tabbatar mana da muyiwa kowa adalci amma ka ƙi ji! Don haka ga ayar Allah zai ji da kai." Wannan abin ya bawa Shago mamaki haka yasa shi kara saka idanun a jifa na uku ne macijin ya kone kurmus, sannan suka cigaba da zamansu, washi gari kafin su bar wurin ya so ganin mutumin ya samu suna ibada, ba yau ya saba ganin irin wannan ibadar ba, amma kuma na yau sai yaji yafi mishi koda yaushe shiga zuciyarsa.

Haka haka suka idar ya gana da shugaban ya gaya mishi daga inda ya fito da bukatarshi, Mutumin yayi maraba da shi, ya gaya mishi kome akan Addini, bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa duk da imanin da yayi da bokanci da kome amma ya bar kome a ranshi, domin idan ya fitar za a iya samun rabuwar kai a cikin masarautar, haka ya cigaba da dawainiyya da addinin da ya amshe ta amma bai san yadda zai yi da ita ba, kwatsam sai ya hadu da Awatif Lu'lu'a, a lokacin da ya ganta ya samu itama bata san kome akan Addini ba. A yadda ya nime aurenta ya dawo masarautar Zanzabira aka tafi aka nimo mishi aurenta, abin ya matuƙar tab'a Aojanah domin tayi hauka tayi bori, amma duk a banza, haka yasa koda aka yi auren Awatif, Aojanah bata daina tashin hankali ba, ita kuwa Sarauniya Amaza ta amsheta hannu bibbiyu, haka yasa Aojanah ta kara tunzira.
Idan za a bada labarin soyayya tow kaunar da Shago yayiwa Awatif wacce irin kauna ce mai matuƙar tsayawa a rai, domin yarinya ce karama, kuma baya iya boye kaunar da yake mata haka yasa Aojanah take kara jin bakin ciki da damuwa, haka lokaci yayi ta tafiya har itama Awatif ta samu ciki, a lokacin Sarki Shago ya bayyana mata addinin da yake yi a boye, goya mishi baya tayi tare da mishi fatan nasara. Wannan soyayyar ya matuƙar tab'a Aojanah.
A hankali kiyayya da kishi mai zafi suka rikide zuwa gaba mai muni, domin Aojanah niman hanyar da zata kashe Shago take wanda ya sani ba wai bai sani ba, kwatsam Balarabe ya shigo cikin tafiyar inda ya yaudareta da cewa ya jima yana sonta su hada kai su ga bayan dan uwansa, ita sai ta gaji sarautar ya gaya mata kadan daga cikin shirinsa, ita kuwa bata ki ba amma ta gayawa Mahaifinta shi ya tsara mata yadda zata yi amma ya nuna kada ta yarda ta nuna mishi wani ya sani. Domin su nasu shirin idan aka yi juyin mulki shi kuma zasu gama da shi.

Haka suka dauki tsawon watanni suna kitsan shirinsu, Bokayan Ajuji bata sani ba sai a cikin daren da rundunar shaidanu tsakiyar birnin suka fara turo sanarwar zasu farmaki masarautar da karfin tsiya, kuma abin mamaki shine sun yiwa masarautar kawayan, a ranar kuma Awatif tana nakuda, rike hannunta yayi ya ce mata. "Idan kin ga gari yayi haske al'amari ya ritsa da ni ne, idan kuma kika ga gari yayi duhu, ki jira ni zan nime ki dare da rana har sai na iso gare ki." Ya fada mata bayan ya mata alƙawarin zai zo gare ta. haka yasa aka fitar da ita ta wata kofa da take karkashin kasa, wanda Bargaga da wasu mutane suka fitar da ita waje, sannan ya koma masarautar, ashe fitar da aka yi da ita Balarabe da Aojanah suna kofar, ganin halinda take ciki suka kyale ta zasu kashe ta amma sai sun samu labarin juyin mulki suka koma masarautar suka barta da dakaru. A can masarautar kuwa Ajuji ce ta hango abinda ya faru, da kuma wanda yake shirin faruwa, don haka ta isa ga Sarauniya Amaza ta mika mata wata mayafi. Sannan ta bata wani abu ta ce idan ta isa wurin ta jefa tayi maza Awatif ta kusan haihuwa. Haka kuwa ta isa wurin daidai tana haihuwar, jefa abin yayi ta isa gare tana faɗin. "Ki yi hakuri!" Girgiza kai tayi Ta ce mata. "Ki gudu ranki shi dade, kada su zo su cutar da ke " "A'a nazo taimakonki ne!" Ta fada tana shafa kanta bayan ta samu ta haifi daya da na farko, haka ta kuma wani yunkurin ta haifi na biyu. "Ki tafi da daya zan rike daya ya ce zai zo!" Ta fada tana kara rike Sarauniya Amaza, a karon farko a tarihin masarautar da aka haifi Yara maza uku, ta mika mata daya tana kara tallafe daya. Ta ce mata. "Zan jira shi, ya ce min zai zo ba zan shiga ba sai da izninsa!"

Sarauniya Amaza ta rike jinjirin ta ce mata. "Sun yi gallaba a kanshi har da yan'uwansa, idan na zauna a cikin masarautar zan rayu da bakin ciki da takaici nayi haihuwar asara," haka ta bar wurin, can kusan tsakiyar dare Aojanah da wasu suka dawo wurin, kallon Awatif tayi tana faɗin. "Na gaya miki shi nawa ne, don haka zan rufe tarihinki;" shiru Awatif tayi tana kallon Yaranta, murmushi tayi ta ce mata. "Ni ba tsoronki nake ji ba, sai dai zan tafi na barshi da girman alƙawarin rashin zuwansa, sannan ni kin ga bayana amma bana tsoron mutuwa domin nasan zan mutu kuma a hannunki. Sai dai abinda zai biyo baya shi yafi muni, nasan zai rayu da kewa mai yawan gaske. Ke kuma zaki kasance cikin dimuwa mai yawa mara iyaka, zaki kasance cikin walagigin so koda za a haife ki sau dubu ne, ba zaki tab'a cin ribar so ba, zuri'arki zasu ji kunyar wanzuwarki, zaki ta rokon ki mutu amma ina mutuwar ba zata zo miki ta sauki ba, idan har na auri Salmanu Faris domin duniya ce Allah da ya dogara da shi zai isar miki idan kuma na aure shi ne domin so da kauna Allah da muka dogara da shi, ni da shi Allah nan zai isar mana zaki tab'e zaki banu zaki lalace, ki saka a ranki karni zuwa karni ba zaki tab'a rayuwa cikin yanci da Salama ba zaki rayu cikin kunci da bakin ciki zaki so tsinuwar nan ta kyale ki amma ina aljanun da suke zagaye da ke zasu ta maimaita abinda kika aikata har zuwa ranar da zamu haɗu a gaban Ubangiji Salmanu Faris, Rantsatsiyar zuciyarshi da ya killace ta domin mace irina Allah zai dawo da ita ko da bai dawo da ni, zai kuma hada shi da macen da zai so sama da ni, ki kasance a cikin tsinuwa ƙarni zuwa ƙarni, ko da zai hadu da mata dubu sai ya kara haduwa da wata Lu'lu'a yarinyar da zata kamanta abinda nayi ki sani kin tab'e tun yanzu ki saka hannu a kanki ki fara kuka da ihu domin lokacinki ya fara har zuwa karshen zamani." Mari ta kwad'a mata tare da cewa. "Ku daure ta da abinda ya haifa a binne su!" Dariya Awatif take tana nuna ta da yatsa ta ce. "Kin makara Jinina yana raye!" Karfe suka saka sannan suka ja ta har cikin sahara suka binneta da jaririnta.

A lokacin da suka koma Masarautar, ta samu ayi wani irin yaki me kad'a hanta, Mahaifinta da Balarabe gasu kwance cikin jini, Bokayan Ajuji itama tana cikin jini. Bargaga da ya tare harbin da aka yiwa Sarki Shago yana durkushe a gaban Shago. A hankali ya ce mishi.
"Kada ka ci amana domin ita amana takan ci wanda ya cita ne!" Ya kara rike hannunsa. "Kayi nasara! Amma." Aman jini ya shiga yi, a hankali ya zube yana me kallon sarki Shago da yake zaune jini na zuba a raunin da aka ji mishi. "Alhamdulillahi! Nayi addu'a tun basan Allah ba ya amsa min, Allah ya kara Amintar da amintarmu a kowacce rayuwa idan mun hadu, ka sa na kasance bawa a gare shi wanda zai bada rayuwarshi domin kare na Salmanu Faris!" A furta a hankali. Shi kanshi Sarki Shago wanda boyayyen sunanshi ya kasance Salmanu Faris. Hawaye ne yake zuba mishi, hannun damarshi ya tafi ya barshi. Yana kallon Bargaga ya rasu akan idanunsu. D'ago kai yayi yana kallon Aojanah. "Dakaru!" Ya furta a hankali. "Ku killace ta har karshen rayuwarta ku bada labarin mutuwarta. Ku shafe tarihinta" Haka aka tafi da ita, yana zaune yana ambaton har ya rasu a wurin hawaye na zuba mishi na rashin cika alƙawarin da yayiwa Awatif!"

Tarihin Rayuwar Shago ta wanzu a zukatan al'umma, har tsawon shekaru goma sha biyar, kafin Sarauniya Amaza ta dawo da matashin yaron da yaci suna Hussaini, duk da dama mulkin ana tsammanin wani cikin Zuriar zai bayyana tunda Sarauniya Amaza bata mutu ba, sai gata ta dawo da ɗan Sarkin Shago Husaini, wanda ana ganinshi aka tabbatar da cikin da Awatif ta fita da shine ba.a jima ba aka naɗa shi a matsayin sabon Sarki, abinda ya sa tun lokacin basu nad'a sabon Sarki ba akwai wata alama ta tauraron da suke kira jini wanda ya kasance a tsakiyar gabashin masarautar idan har sarki yana raye za a dinga ganin shi shekara Shekara, idan babu sarki kuma akwai jinin sarki a raye zai tsaya ne yaki tafiya har sai jinin sarautar ya hau mulki kuma sun canfa da cewa matukar aka daura wani sarkin zai iya mutuwa.

Haka lokaci ya cigaba da tafiya cikin duhun jahilci da maguzanci, sannan ita kanta Aojanah tana kurkuku, ta tsufa bata da wani fata da ya wuce ta mutu tayi imani matukar aka kara samun wani sarki a cikin masarautar kuma irin Shagonta sai ta san yadda aka cika mata buri kuwa ba abu me sauki ba ne don haka tayi ta dakon lokaci a hankali wata rana aka kawo wata mata ana zargin mayya ce, ita kuma Aojanah da girma ya cimmata ta kalli matar ta ce mata. "Na ji ance ke mayya ce, nasan na kusan mutuwa ina da buri ki cika min ki tambayi duk abinda kike so zan baki daga kai dukiya jini da zuriata."

"Kina da Yara hudu mata ki bani su ni kuma na cika miki burinki!" Kallon matar tayi ta mika mata hannu. "Duba za a sake haifar wani basaraken irin sarki Shago!" Hura wuta matar tayi da harshenta, ya cire kayan jikinta tana rawa tsirara. Juya kai take har tsawon sa'a goma ta zube tana nishi. "Tabbas da kafa daula kuskusa ma kuwa wadanda da zasu kafa daular muslmai ne. Da suke can gabashi duniya. Kuma za ayi mulki ta izza da kasaita! Sai dai da ayi ta kashe juna akan kujeran da kakan Ilu ya saka aka gina mishi, Makiya da masoya zasu wanzu!"
"Ni bana cikin qaddaran ne?" Girgiza mata kai yayi ta ce mata. "Hatta zuri'arki ba zasu wanzu ba, gobe ce mai kyau mai armashi!" Inji mayyar. "Tow na bada rayuwata da na Yarana, a daukar min fansar soyayyata matukar aka wayi gari sarakunan masarautar Zanzabira zasu so mace a haukatatta ko a kashe ta wannan shine burina!"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login