Showing 207001 words to 210000 words out of 304445 words
nake yi a cikin asibiti? Ban san me yasa suke bibiyar duk wani motsina ba." Shafa bayanta yayi ya ce mata.."she worry about you!" Ture hannunsa tayi tana faɗin.. "i fuck worry about me, haka kawai tana zagina tana min abinda taso kace ta damu da ni, kawai ka dakatar da ita. Don wallahi xan saka a rufe min Ubanta!" "Duk bai kai ga haka ba!" Ya shiga rarrashinta domin yasan rashin mutuncin Nady da ita ba, haka yasa shi rarrashinta a rufe zancen. Ranshi a b'ace yake shi yasa bai nemi wani abu a wurin ba, asuban fari suka tashi yayi wanka suka shirya. Wurin Ijlal ya nufa ya samu tana kwance abinta.."Zaki tashi ko sai na bar garin ki fara rashin kunyarki nan!" A hankali ta, mike ta shiga ban daki, wanka tayi sannan ta fito ta shirya tsaf, ta fito parlourn domin ita dai ba ruwanta da wani sallah balle nafilla.
Lokacin da aka kawo Babban motar da zasu tafi a cikin, ta fito janye da akwatinta. Suka bar gidan.
----
Tun jiya da dare bayan ya kai su gida yazo ya kai ni nima nayi sallama da su Abba da Maluma. Ina ganin Iram ta fito tana kallona ina kallonta. "Kin!" "Shiii ki yi ta kanki nima nayi ta kaina!" Na faɗa mata ina mai wucewa wurin Umma na bata sakon Mai Babbar daki......
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 67
Da wannan kwarin gwiwar suka bar gaban boka bayan sun zuba masa kudi mai yawan gaske wanda suka saka a cikin wani kwarya da yake ci da wuta fal-fal, sannan suka fita daga surkukin dajin, kafaffunsu yayi futu-futu musamman Ijlal da bata ki a kashe Ikhlas ba. Damuwarta Ikhlas ta fita a duniyar Faris a yanzu da ya zama sarki ya dace a kirata da giwar sarki, don Ikhlas ta kasance Fulani ai ba wani abu bane, amma zamanta giwar sarki zai saka a kara darajarta da abinda zata haifa. Kallon Hajiya Mardiya tayi ta ce mata. "Umma da Fulani da Giwan Sarki wanne yafi dacewa da ni?" "Mai Babbar daki! Idan kika haifu namiji kin cancanci zama mai babbar daki, sannan aka yi da ce kika kwana arba'in ki koma ki.sake dauko wani cikin tabbas zaki haɗa Mai Babbar daki, Giwar sarki, Fulani Babba. Zaki kasance Mai Martaba yana ji dake a duk inda ya ganki ko ya ga Yaranki, sannan ita wancan juyar bata cikin lissafina kada ki je kina mata hauka, haukarki ya tsaya akan Ikhlas. Domin ita ce kawai zamu iya lalatawa kome ba ita budurwa ba. Sai ta dauki cikin mugani." "Kuma Umma kin gama da yar banza, shegiya tana nan kamar alkoro!"
Haka suka yi ta zagin Ikhlas har suka fito inda motarsu take, Ijlal ta zauna a gefen hanya tana nishi, domin kuwa cikinta yayi bala'in nauyi ta gaji ainun, can suka mike suka shiga motar. "Malam dan ladi makabarta muke so a kai mu a binne wannan abin!" Ya nuna mishi wani abu a cikin bakin leda. "Tow amma makabarta!" "Zan baka dubu dari biyu da hamsin idan baka so muje Malam Yero zai yi!" "Tow Hajiya wannan mai sauki ne!" Haka dauki hanya suka bar garin sai da suka kusan isa gida ya biya dajin da makabarta yake. Maganar Boka ce ta dawo dasu kamar yana ganinsu. "Kada a saka a tsohon kabari a saka a sabo ka ji!" Suka gaya mishi bayan motar ya koma ya bude a hankali ya dauki karfen da suka aikin motar, sannan ya nufi hanyar katangar kafin ya dawo ya amshi dan kwalin Hajiya Mardiya ya goya abin a bayanshi sannan ya haura katangar a hankali ya shiga cikin makabarta yayi ta tafiya da yake namiji ne, haka yayi tafiya mai nisa, amma bai samu isa waje farko farko ba nan ne da sabin kaburruka, ya bude wata kabari da ya ga kamar bata jima ba, ya tona ya hango har likafanin bai wani jima ba, sakawa yayi ya rufe, sannan ya juya a hankali ya koma hanyar katangar ya danneni ya haura ya dirka, yana karkad'e jikinshi ya ce musu. "Hajiya na gama!"
*Ku sani shi kanshi wanda ya binne abin ba zasu barshi ba rundunar mutanen mu zasu bibiye shi, don haka kada ku damu idan ya mutu! Domin al'amari ne na sirri*
Mika mishi kudin suka yi ya amsa yana godiya, a ransa kuwa yana faɗin. Idan ya bari wannan damar ta subuce mishi ba zai kara samun wani dama ba, wannan abin da ya aikata shi ne hanyar da zai na samun na biyan buƙatarshi har suka isa gida. Fitowa Hajiya Mardiya tayi ta ce mishi. "Idan wata buqata ya zo maka, kofar mu a bude yake domin ka mana aiki na musamman, fatanmu bakinka ya san inda zai na furta wasu abubuwan, zuciyarka ta rike Amanar da ta dauka idan baka haka ba, za a samu matsala" "haba ba kome Hajiya!" Ya fada yana dafe yan kudaden hannunsa. Sannan ya musu Salama ya bar gidan. A hankali yake tafiya har ya bar unguwarsu na GRA. Babban titin da zai tsallaka zuwa can ketare ya tari abin hawa zuwa gida ya ji kamar abu ya fada mishi kunne a gigice ya saka hannu a kunne yana girgiza kunnensa, tare da manta inda yake ashe ya hau Babban titin, wani irin ƙara kaka ji... "Kiiiiii gigibi!" Wata babbar Daff tayi sama da shi tare da kara bin ta kanshi kanshi ya fashe kamar yadda ake fasa kwakwa, ko shurawa bayi ba ya ce ga garinku, ya mutu da nufin idan ya gama da kudin dole ya dawo su kara bashi wani kudin, ya mutu da son lallai shima sai yayi kudi a tare da su, sai gashi cikin ikon Allah Mutuwa ta mishi yankar kauna.
Bakin aljanin da ya shiga jikinshi ne ya fito ta kanshi da ya fashe sakamakon shi ya rud'a shi, ya girgiza jikinsa yana kallon yadda jini yake malala a tsakiyar titin motar kuwa mai ita ne ya tsaya tare da fita da gudu ya tari mashin ya nufi office din Yan sanda ya san a banza wasu fusatattu su dauki mataki, yana zuwa kuwa ya bada statement din abinda ya faru, suka tashi yan sanda biyu aka tafi can ai kuwa ana ta nimansa domin an ci alwashin sai an kashe shi musamman da suka ga motar kamar ba musulmi ba ne. Sanin cewa motar kayan wani attajiri ne shi kuma baya daukar asara yasa basu yi kuskuren tab'a kayan ba. Atow baba ma da Babanshi.
***
Ikhlas
Ilham da Iram ne suka zo ina kwance a dakin, nifa tunda nazo gidan kunya ya hana ni fita. Ina kwance wurin La'asar suka shigo, na sake kayan ina sanye da riga da wando, wandon palazzo ne har cikina sai rigar da na daura wandon a kai, ina kwance nayi limo, ni dai ba barci nake ba amma kuma na nace idanuna biyu ba, sama-sama na ji suna gaida Mai Babbar, shigowa dakin suka yi don na ji tana faɗin."tana cikin dakin!" Buɗe ido nayi ina kallon kofar a hankali suka shigo, kallona suke a hankali. Suka nime wuri suka zauna kowannensu da abinda yake kisimawa a ransa. "Ga wannan na kawo miki!" "Na gode ajiye akan can!" Na nuna mata gaban Mirror, "ashe kin ji yadda abin yaƙe?" Inji Iram a hankali na gyara zamana ina kallonta. Ban ce mata kome ba. "Da fatan yanzu dai kin zama yar hannu!" Murmushi nayi mata, ina kara kallonta da kyau. "Baki da baki ne!" Kirarin da muka ji yasa suka mike da sauri na sake murmushi na ce mata. "Yana waje ai, ki godewa Allah kada ya rigaki shigowa idan yayi ido hudu da ke." Murmushi nayi ina kallon abinda ta kawo min, na kira Sailuba ta zo ta dauka tare da fada mata cewa. "Kada ki yi amfani da shi ki saka a cikin shara, amma ki fara sakawa a bakin leda sai ki saka a shara!" Fisgewa tayi tana hararata. Murmushi nayi ina faɗin. "Meye a ciki?" Na faɗa a shagwab'e, fita tayi tana kwafa a parlourn suka samu Mai Babbar daki suka mata sallama, domin bai shigo ba ya tsaya bin dakin matan gidan yana gaishe su. Sannan da ya gama ya shigo parlourn Mai Babbar daki, kallonshi tayi cikin tausayawa, ta kauda kai tana faɗin.."Na saka an shirya maka abincin a wurinta, kusan ita tayi ma." Murmushi tayi ya ce mata.."Na shiga?" Ya tambaye ta, gyada mishi kai tayi,sai da ya gama borin kunyarshi sannan ya mike ya shigo dakin, a hankali ya zuba min idanun bayan yayi sallama na amsa mishi. Babbar rigarshi ya cire ya ajiye sannan ya cire kome ya huta. A hankali ya turawa Nady. *Ina tare da Zainab zan ci abinci a nan!* Itama turo mishi da sakon cewa.. _Duk yadda kake so haka zaka yi. Baka da matsala da mu_
*Na gode giwar Faris!*
_Ina kara godiya da sunan Giwar sarki!_ ganin chat ya dauke mu shi hankali, sai na koma gadon na kwanta, ina kallonshi yadda yayi kyau kamar ba shi ba da alamu yana samun kulawar da ta dace. Dazun naji Mai Babbar daki tana faɗin ta gaji da cin shinkafa wallahi, tasan yana zuwa abinci zai nima shine tana shiga sallah azhar na fito muka daukar tuwo, duk kusan aikin Sailuba ce tayi tare da Wildat, tuwon na tuka da miyar kuka wanda ya ji kayan kamshi da jikin wani, sai gashi kamshi ya cika ko ina, idan Mai Babbar daki ta shiga sallah bata fitowa sai bayan la'asar a dakin ba zaka rasa ta da kayan tea ba, su cake da dangin nama su dambu, haka yasa ko ta fito abinci kadan take ciki, tuwon dawa ce na hada da semo, kamshin turaren tuwon da na saka fefe, sai biski da na mata na tsakin gero da na zuba man shanu a cikinsa, shi kuma Sailuba tayi miyar taushe domin har muka kwashe tuwo bata markade gyadar miyar ba. Haka muka yi aikin kusan tare ina gamawa kafin Mai Babbar daki ta fito na koma na yi wanka na shirya cikin kayan jikina, sannan na saka Sailuba ta kawo min biski din na ci bayan ta gama miyar. "Fulani ba ayi kome na sha ba!" Na manta da wani abun sha domin tsayuwar da nayi akan kafana yasa ina jin ciwon jikina. "Ki haɗa min su kankana da lemo duk wani abu da yake cikin firji ki hada min gani nan!" Tana fita na kara shiga ban daki na yi tsarki da ruwan dumi da mai babbar daki ta bani wani buta sai dai na zuba ruwan dumi, ina fitowa na samu ta wanke kome ni kawai na shiga nikawa, sannan ba kawo brown sugar na zuba na saka a firji na basu nasu na fita da nawa. "Idan mai babbar daki ta fito ki gabatar mata da abinci, na Mai Martaba zai shigo a hada mishi a wancan tiren. " "Tow! An gama ranki shi dade!" Ta fada a hankali na fita zuwa dakin ina ci, ta shigo gaya min ta gama na ce mata. "Na gode!" Fita tayi tana murmushi, sai da na gama na tashi nayi sallah la'asar, ina idarwa Mai Babbar daki ta shigo tana rike baki, zama tayi tana faɗin. "Kina nufin ke kika yi aikin nan,?" Sosa kai nayi ina wasa da yatsuna. "Allah yayi albarka. Sailuba zata kawo abincinshi dakin!"
Wannan ne dalilin shigowarshi cin abinci dakin, ina jin yadda wurin yake zafi na mike a hankali na nufi ban daki, ruwan zafi na tara na shiga cikin na zauna. Ina jin wani dad'i yana ratsa ni, ina gamawa na fito farfesun kaza ce aka kawo daga gidanmu, ya amsa yana ta murmushi. "Yan mata ki ce jego kike yi?" Ya ajiye min yana kallon yadda nake sharfe zufar jikina. "Ba magana ne!" Zama nayi akan pillow da na saukar kasar na fara zuba mishi abincin. Sannan na gama na zuba mishi farfesun kazar, nima na zauna na fara sha ina lura da yadda yake cikin abincin, kara mishi tuwon nayi ya ce min."ina son biski kada ki kara tuwon!". Ya fada yana kallon yatsuna da suka yi haske. "Yaushe za a yi miki ja lallen nan?" D'ago kai nayi ina kallonshi a hankali na janye yatsuna cikin hannunsa. "Zan yi!" "Yaushe?" Kamar nayi kuka yadda yake murzawa yatsuna, "kada ki damu ba zan miki kome ba!" Gyada kai nayi ina wasa da cinyar kazar hannuna. "Ci!" A hankali nake ci duk da abincin ya gundure ni, amma haka nake durawa. Muna cikin haka Sailuba ta shigo dauke da fura da nono. Amsa nayi ina faɗin."na gode!" Biski yaci sosai bayan tuwon, sannan ya koma gefe yana numfashi. "Gaskiya zaka yi kiba kwanan nan gara ka fara motsa jiki." Murmushi yayi ya ce min. "Ni ban hango haka ba!" Ya fada hannunshi a kan cinyata, a hankali na zamar da hannunsa na koma saman gadon na zauna ina jin wani aminci a tare da ni, haka yasa bakiɗaya na koma na takura kaina. Shima dawowa yayi saman gadon, ta zauna tare da cewa."Ummi ta saka a rusa bangarenki, a kara miki girman bangarenki, sannan ta saka a cire kayan dakinki a rabawa mabukata." Kallonshi nayi domin bata gaya min haka ba ko da wasa. "Sai dai a nawa lissafin so nake tunda akwai wadataccen fili a fara ginawa kowacce part dinta babu wacce ta ga wani abu balle ta ce ba a mata adalci ba, sannan ina son na bude wani shafin rayuwa da ke, shi yasa nake son na sarewa kowa bangarenshi, haka zai dauki 2 to 3 month, wanda haka yasa na shirya mana tafiya ni da ke da Nady da Ijlal domin ta haihu a Qatar sai ku dawo gida ayi suna, saura wata biyu zuwa uku dude dinta." "Nima zan tafi wani karo ilmi ne na tsawon wata uku amma dukkan a taren zamu tafi" ya fada yana shafa bayana, "and na manta na gaya miki, Batun deal dinmu ya rushe ina son zama dake har rest of my life, ki bani hannunki mu taka daga duniyar nan har zuwa aljanna, wannan shine bukatata da ke." Ya fada yana jan drower gefena wannan karamin box na gift din ya ciro ya buɗe a hankali sai ga zobe guda biyu masu kyau. Ya ciro daya ya saka min a hankali yana murza yatsun sannan sumbata, kafin ya mika min kallonshi nayi na saka mishi tare da sarkafe hannunsa cikin nawa yayi yana d'aga min gira, a hankali na fara ƙoƙarin zarewa amma na kasa idanuna ne ya cika da kwalla. Ba shiri ya cire yana faɗin. "Sorry ni ba wani abu zan yi ba." Yana durkushe a gabana, jan kumatuna yayi ya ce min. "Na gaji da wannan shirun naki zan saka ki yi magana fa!" "Don Allah ka yi hakuri!" Na faɗa ina matsar kwalla. "Ok I want to chop!" Hannuna na Kai bakin shi hawaye na zuba min, "Ka ga har yanzu da ciwo a jikina, don Allah kada ka min haka!" Sumbatar tafin hannun yake har zuwa wuyana da kirjina. Rike kanshi nayi ina zubar da kwalla. "Don Allah kada ka min haka!" Na faɗa muryana yana rawa, hannunsa ya kai cikin rigana. Kifa kaina nayi a saman goshinsa. Bakinshi ya kai kan nawa yayin da hancinmu suka hadu wuri guda, hawaye ne ya zubo min, a hankali yake min kome a sanyayye, lokaci zuwa lokaci yana birkice min ina ganin zai sake layi ba kwace kauna ina girgiza mishi kai, shi kuwa idanunsa ne suka yi jajjur domin ya gaji kwana daya nan jin shi yake kamar ba shi ba, duk da Nady ta sauke mishi na jiya, amma yanzu bai ki ya kara samun Ikhlas din ba, haka ya gama latsata sannan ya mata sallama, wurin Mai Babbar daki ya koma bayan ya gama saka kayanshi da ya cire nan ya gaya mata shirinsa, sannan ta mishi fatan nasara. Ai ina zaune sai ga Mai babbar daki ta shiga hada min kaya na musamman a ban daki ta ce na shiga na gasa jikina wato idan na fahimci matar nan ita fa yadda danta zai samu sukuni take yi, haka yasa na shiga kin sha tana kawo min zan fara kuka. Har ta gane maganin nake gudu, a cikin kayan maganin da na ji dadinsa kayan Maman Hidaya and khairat, wallahi kayan matar nan na da kyau, domin Yeemar ta kawo min na sha sosai ga gubar da nake ci kafin kwabo na wani irin cika, a tsakanin kwanaki goma na murmure na murje nayi kyau ga mai gyaran jiki da aka kawo min tana min gyaran jiki, kaina har gida aka zo aka min saloon, bayan an gama min muna daki muna hira da Yeemar da Mijinta ya kawo ta, shi kuma ya wuce wurin aiki domin jan shi sosai Mai Martaba yayi yana gaya mishi yanzu fa abokai zasu zama tunda Allah ya haɗa su ta sanadin Matansu, amma Mijinta gani yake kamar ina wannan ba wurin wasan shi ba ne, amma ganin yadda shi Faris yake kiranshi su gaisa har ya tambaye shi yaushe zai kawo Kawar Fulani Babba, haka yasa Yazid ya sake ranshi aka fara harkan arziki idan ta shi ne baya son shiga damuwa, domin daga yadda Yeemar take mishi bayanin wasu abubuwan ya fahimci gidan akwai abubuwan da sai kayi da gaske, idan ya ce Masarautar Zanzabira bata cikin manyan Masarautar da Allah ya tara attajirai yayi karya, Masarauta ce da zai ce duk fadin Nigeria babu irinta sai na kwara.
Lalle ake min ja mai kyau, wanda kana gani kasan an zuba fasaha. Yau din nan wani maganin Maman Hidaya and khairat da na sha nake jin wani abu