Showing 213001 words to 216000 words out of 304445 words
Na san nayi laifi domin kamar zai cinye bakina sai da nayi laushi sannan muka fito turus muka ganta, na kalle shi duk ya shanye jan bakina a bakinsa. "Gaskiya kayi kyau da lips stick!" Na wuce na barta tana bala'in da ta saba, haka na dawo, na zauna ina kara kallon wurin ina gyara zamana, ai kuwa ta sako shi a gaba tana mita. Haka ya zo zai zauna ta zauna tana faɗin. "Wallahi ba zaka zauna ba, sai dai ka je can! Ana shiga hakkina!" Dariya muka saka,mun isa karfe daya na rana, amma sanyin da ake kamar da bakin kwarya yasa aka ce kowani fasinja ya saka rigar sanyi, wani ikon Allah daga ni sai Nady muka zo da shi ita kan Madam tana hakimce, shi ya cire na shi ya bawa Nadiya ita kuma ya bata, ta ce ba zata amsa ba, shi ya bi cewa na Nady yafi girma zata sake da dan cikinta amma ita kishi ya hanata. Haka muka fito a hankali sanyi yana kad'amu wai ma a haka mune muka samu izinin sauka domin aka kakar sanyi sai dai mu sauka a Ingila mu biyo jirgin kasa. Wata babbar mota ce ya zo ta dauke mu, kafin mu shiga cikin harabar airport din wuri me dumi, Ijlal kamar zata mutu, sai da ya cire top dinsa ya kara mata, ni kan Allah yaso Mai Babbar daki ta bani babbar jacket take gaya min zuwan su Kashmir da Mai Martaba ya saya mata, haka yasa take son Jacket din sai gani ta bani, murmushi nayi na ji ina son Jacket din nima.
Muna isa ciki hankalinmu ya fara dawowa jikinmu, coffee aka fara bamu muka sha, naga Nady bai dame ta ba, ta amshi coffee din hannuna ta ce min.."suna da Hot chocolate su bamu;".tana fada kuwa aka kawo mana, ta mika min a wani kori mai kyau na fara sha da straw. Madam ta fara kuka yunwa. Haka suka amso mata pizza da shawarma, ni dai donut da cake, sai Nady sandwich. Shi kenan Faruq kuma fry chips da burge, Oga kuwa shima layinmu ya biyo hot chocolate, muka sha bakiɗayanmu, kafin muka samu nutsuwa, fita muka yi zuwa wurin motar da tazo daukar mu. Hannunsa cikin na shi. Muka isa har wurin ya tsaya sai da suka shiga sannan n a shiga shima ya shigo ya kalle ni. "Fuskarki bata son wannan weather din ko?" Murmushi nayi ya juya ga Uwar Magaji ya ce mata.."Madam ke fa!" "A'a ka gama da Mai gindin zinari" (🤣😂kishi manya) kallon Nady yayi ya ce mata. "Giwata ya dai?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Kasan Dr Munirah ta ce dole na kiyaye saka damuwa a raina!" "Yes Allah ya bamu sa'a!" Har muka isa wani hadadden gida na alfarma. Murmushi yayi ya cewa Nady."ga gidan da nake gaya miki wanda an taya Dalar Amirka Biliyan biyu na ce a'a!" Kasa magana nayi ina ganin gidan kamar irin gidajen tarihin turawa wato castly,gidan yayi kyau a cikin wani unguwa kamar tsibiri, tun daga bakin kofar gidan zaka fahimci Allah ya san dalilin da ya ware masu arziki da talakawa, domin gidan kana gani kasan an ci zarafin kudi, masu kula da gidan tun daga bakin gate suke mishi Barka da zuwa har muka isa gidan wanda tafiyar minti talatin ne cib, Ya Allah. Kallon gidan nake, ga kome na more rayuwa a cikin gidan."uban riko nane ya mallaka min shi!" "Kai kuma sai ka mallalawa Magajinka!" Inji Ijlal daga ni har shi da Nady juyawa muka yi muna kallonta. Budar bakin Nady ta ce mishi. "My lord ka kula kada kana barci a danna maka pillow ko a baka guba!".............(NADY YA DA ZANCEN GUBA KUMA?🥺😏🤣)
₦500
08130269641
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: .70
Like seriously maganar Nady akan gaskiya yake, amma a wurinsa Ijlal wawuya ce da bata iya boye abinda yake ranta, for me Ijlal ta san me take yi, wulakanci ne irin wanda ya samu wuri. Sannan duk abinda take tana sane ba wai bata sani ba ne, tasan yadda take gudanar da kome nata, "mun iso Maisha." Ya ce min murmushi nayi, kafin na saka kafa na fito bakina dauke da addu'ar shiga sabon wuri da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koya mana, gidan ya hadu gare biyu ne kafin mu isa Main house din, kallon gidan nake da idanun basira, duk yadda aka yi Baturen da ya zana gidan ya san me yake yi, domin gidan ya haɗu. "Yau ne farkon zuwana gidan nan." "Inji Nady cikin girmamawa masu aikin gidan suka fara isowa muna tsaye, wata dattijuwar da ta kai irin shekaru hamsin tana zuwa ta gaishe shi cikin girmamawa ta ce mishi. "Barka da zuwa Mai Martaba, ya hanya?" "Mrs Lilly lafiya Lau!" Ya fada yana kallon yadda suka taru. "Na zo ba zan wuce wata uku ba, zan yi wasu abubuwan masu muhimmanci. Faruq zai muku bayani!" Sai yanzu na fahimci dalilin shigar kayan jikin Faruq kullum cikin kaya daya ashe ba daya ba ne, tsanrsar kuka ce da sanin hakkin aiki. Ana sanyi a waje haka ya mana jagora har cikin gidan, ko ina so Masha Allah. Faruq da ya biyo bayanmu domin shi mai gidan yana tare da Mrs Lilly suna magana ya ce mana. "Tun wata biyu da suka wuce ya fada musu zaku zo!" Gyada kai nayi ina mamakin yadda kome yake ajiye a cikin gidan gaskiya masu kula da gidan sun san me suke yi, haurawa sama muka yi tare da nufar cikin gidan sosai, dakinshi shine na ƙarshe daga Nady sai na shi ni nake bin Nady. Dakin Uwar Magaji an gyara mata shi kamar yadda take so an saka mata kome irin na uwar da namiji, wato light blue, ni dai dakina kome na cikin shi pink ne, ina ganin haka na shige abina na Nady ita da yake ta musamman ce kome na unique ne, ban ji kome a raina ba kuma bana fatan na ji jinin domin Matarshi ce tare na gansu, sallah asuba na fara kafin nayi azhar da la'asar, sannan nayi wanka, ina fitowa na dauki wani gucci panty leggings da na zo da shi mai kauri, sai shirt da na saka na dauko normal sweater na saka a kai tare da hula na saka, kafana kuwa safa na saka mishi, tare da gyara zaman hular kaina. Kwanciya nayi domin na gaji, maganar gaskiya na ji ana hayaniya sama kamar ana dambe daga nan ban kuma sanin mai ya faru ba, ina kwance naji kamar ana shafa fuskana. Bude idanu nayi na ganshi zaune cikin ƙananan kaya yayi kyau. "Tashi ki ci abinci!" Tura mishi baki nayi ina ture hannunsa. "Barci nake ji!" "Shida saura!" Da sauri na tashi na wuce ban daki nayi alola, na fito kallona yayi for while kafin ya ce min. "Ban fa ce miki an yi Magariba ba, abinci nace zaki ci."
"Tow muje!" Na faɗa a hankali, muka nufi kitchen wanda yake hade da dinner room, suna zaune kowa nacin abinda yake so, zama nayi na dauki plat zan zuba abinci wata budurwa da nake ganin like maid ce ta ce min. "Kawo na zuba miki!" Amsa tayi na kalle ta. Shigar da tayi bai min ba, wani mitsitsin skirt ne a jikinta, sai wani uban gyara zaman rigar da tayi cikin skirt din. A hankali na juya ina kallon kusan masu kaiwa da komowa a kitchen din manyan shigarsu ta kammala ce, yan matan ne dai. "Gaskiya Waɗannan yan matan sun ci taliyarsu ta karshe, a sallame su." Na faɗa mishi da hausa, "Me suka yi Fulani?" "Kawai basu min ba ne a nimo dattawa sun isa, yan matan shigarsu bata yi ba!" "Ki yi hakuri, tun suna kanana suke aiki a gidan nan, idan na ce zan sallame su waye zai kula da su." Ban gama jin shi ba wata fitsarariyar budurwa ta shigo da gudu, kawai ba sai naga ya mike ya bata wani hug ba, damke cokalin hannuna nayi har sai da na karya shi, na d'ago kai ina kallonshi a hankali. "Na ce a sallame su!" Na faɗa ina mikewa akan kujeran. "Babu inda zasu, sai dai ki mutu amma yanzu suka fara aiki a gidan nan, domin sai sun yi renon Future King!" Ban kulata ba, na haura sama da gudu, Nady ta bi da idanu. Yarinayr ta ce mishi. "Doctor wacece ita?" "matata ce Zainab!" Kallon Nady tayi ta ce mishi. "Bayan ita ka kara wata matar?" Nuna mata Ijlal yayi da uwar cikinta. "Ga third dinsu." Rike baki tayi tana kallon Ijlal karama sosai irin an cutar da Ijlal da aka barta ta aure shi, suna zaune ana ta hira Nady ta mike tana faɗin. "Ya kamata ka duba lamarin Fulani!" Ya wuce abinta, abincin da ban ci ba kenan, sallah nayi ina mai bude akwatina na fara ciro kayan da nazo da shi, na fara ci a hankali. Dambu da kayan suya, a hankali nake ci ina kallon kofar ko zai shigo amma mutumin nan yayi biris da ni, har dare yayi na gabatar da sallah isha, na kwanta barci cike da jin haushi. Ashe kwasar Yan matan yayi suka fita daga gidan basu dawo ba sai karfe daya saura, ƙishirwa ya tashi ni, na fito na ganshi rungume da daya daga cikin yan matan ya wuce wani daki, da yake akwai duhu ban kunna wutar parlourn ba, ina kallonshi ya wuce da su daya bayan ɗaya. Ta karshen ce ta rike collar dinsa tana faɗin. "Amma kasan ina sonka Prince?" Kwarewa nayi na fara tari, haka ya janyo ya kunna wutar parlourn. Muka kalli juna, a hankali na ajiye kofin na wuce su, daga shi har ita yarinyar na nufi sama. Rufe kofar nayi na kwanta, sai dai na kasa barci har gari ya kusan wayewa ina juyi, washi gari ban fito ba domin nasan zan gansu sai na ki fita, ina jin Nady tana buga min kofar nayi banza da ita. Haka ma da rana tayi ban fito ba, karshe naji gidan yayi tsit. Saukowa nayi sanye da wata gown dress, blue block. Kitchen na nufa na samu suna ta aiki da alamar fita ake yi da abinda suke. Cikin girmamawa suka gaishe shi na amsa musu, sannan na shiga tambayarsu me suke da shi a kitchen din, Mrs Lilly ce ta fito daga store na kitchen din. "Sannu Queen jiya mun yi magana da Mrs Yayari ta ce mu kula da ke." Murmushi nayi na ce mata. "Na gode sosai!" Ummi da alamu rashin samuna a waya yasa ta mata magana. "Queen kina bukatar wani abu ne!" "Eh ina son na san mene ne babu a cikin kitchen din." Jagora tayi har store din gidan mai matukar girma da kayan abinci. Ta ce min. "Duk wata ake sabunta kome, wanda aka kwashe gidan marayu ake kaiwa. Koda kuwa ba ayi amfani da shi ba. His Highness, ya ce ana kaiwa can" shiru nayi kafin na ce mata.."Wanann yaushe zaki kai kenan?" "Jibi za a kawo abincin, gobe za mu fitar da shi." Shiru nayi ina kallonta. "Anan kuke da zama dukkanku?" "Eh Ma BQ dinmu yana baya!" Ta min jagora har zuwa Bq ɗin. Ana kiwon dabbobi a wurin akwai shanu, akwai tumakai da awakai irin nasu na turawa sai kaji da wurin kiwon kifi. Sannan abinda na fahimta koda sun yi abincin, sun samu a can akwai kitchen dinsu da suke girki. Zama nayi na ga wata yarinya tana wasa na cewa Mrs Lilly. "Mai yasa baya zuwa makaranta?" "Ai Uwarta bata da halin biyan makaranta, sannan ina jin nauyin yiwa My lord magana ne!" Mika mata hannu nayi ta tawo da gudu, ɗaukarta nayi na ce mata."ya Sunanki?" "Mary!" "Wow! Mother!" Na faɗa mata a hankali. "Mrs Lilly zaman gida ba zai yiwu ba, ace ba zata makaranta ba ai an nakasa gobenta, sannan ta tashi da rashin ilimi akwai matsala." "Wato ranki ya dade, asalin tarihin wannan gidan mu bayi ne. Karni da zamani yasa muka samu yanci bamu zama yantattu ba sai da Mijinki ya mallaki gidan a matsayin na shi, don haka kada ki ji tausayinmu bauta muke don ma Mijinki yana da adalci yana biyanmu kudin da ko gwamnati ba zata iya bamu haka ba. Sannan muna da insurance card, a duk inda muka je bamu da matsala." "Batun abinci fa." Murmushi tayi ta ce min. "Wannan ai mai sauki ne kullum muna girki sannan muna aiki, muna da gona muje ki gani." Haka muka wuce tayi ta nuna min. Har zuwa inda iyakar gidan yake bakin wani kogi. "Anan muke wanki wani lokaci wani lokaci kuma mu yi a gida. Kome da kika gani anan yana cikin aminci da kulawar Mijinki. Da kuma William zai zo ko ganshi." Jinjina kai nayi muka wuce cikin gidansu Mary tana wasa da wani dan babyn akuya sai tsalle yake itama tana biye mishi, dauka nayi ina faɗin. "Na kama miki shi!" "Ma ki bani na dauke shi!" Mika mata nayi, ina zaune a wurin wata mata ban san da ita ba tana zuwa da wani flower a hannunta da ta nad'e shi ta daura min a kaina. "Barka da zuwa Sarauniya!" Ta min irin gaisuwar tsofin turawa, waɗanda suka san yanayin mulki da sauransu. "Sunanta Anna, ita ce Mamar Mimi da Lulu, sai wance ta shigo jiya. Mira Mahaifiyarta bata nan tana aiki a wani asibiti. Akwai Miyaki shinokagara yar Japan ce, da yarta Pretty. Duk muna nan ne!"
Gyada kai nayi ina kallon matan da yake ta lissafo min. "Kuma dukkanku anan kuke raye?" "Yes Ma!" Murmushi nayi na ce mata. "Daga yau abincin da za a fitar da su zuwa gidan Marayu da mabukata, a raba shi gida biyu, ku dauki rabi a kai musu rabi. Idan aka baku dukka ma ba laifi bane amma tunda ana kai musu a raba biyu, sannan idan kun yi amfanin gona irin su timatur madadin a fita a sayo a waje, ku na kawowa William yana saya haka zai kawo muku kudin shiga, babu amfanin ga kaya a gida a yi asaransa, madadin a cire kaso mai yawa a saya a waje gara a inganta na cikin gidan ba sai an fita waje ba, tunda kin ce baku bukatar kome daga waje. Na abinda ya shafi noma. A hankali ana inganta na ciki sai a fara fita da shi tunda ga filin noma. Sannan ita Mary zan yiwa William magana sai a saka ta a makaranta na maka ban samu ganin Mai gidan ba. Da sun fita tare." Cikin wani irin girmamawa suke tafa min, koda ba muslmai bane su bana jin haka zai saka a tauye su, sannan adalci ba iya mu muslmai ya da ce mu samu ba, hatta wanda ba musulmai ba suna bukatar haka a tare da mu, mun gamawa na dawo kitchen, na ga abubuwan da suke da shi nima na rubuta abinda nake bukata. Na cewa Mrs Lilly. "Idan William ya zo ki ce ya samu Faruq ya min magana!" Gyada kai tayi, na saka aka fada min noodle da kwai ina zaune sai ga Mary da wani karamin basket da y'ay'an itace, wato fruit. A hankali na karba ina faɗin. "Thank you Mother!" Da gudu ta fita, na cewa Mrs Lilly. "Bari na wanke!" Don na lura so take ta ɗauka ta wanke. Na wuce wurin wankewa tana faɗin. "Ki rufa min asiri ki kawo na wanke!" Dariya nayi ina faɗin.."Bari nayi da kai!" Na cigaba da wankewa sannan na kwashe a wani bowl, dauka tayi ta yanyanka min su, na ce mata. "Ki zubawa Mother abincin nan!" "Ranki shi dade, ai bamu isa mu ci abincin da kuka ci ba, sai dai ki ci ki rage mata!" Tashi nayi na dauki karamin plat na zuba mata har da kwai na mikawa daya daga cikin masu wanke-wanke da take zare idanu. "Idan William ya san da haka zai rage mana albashi!" Take na haɗe rai. "Ni nace a kai!" Ba musu suka fita, suka kai mata sai ga Uwarta da Babanta sun zo da sauri suna faɗin."kiyi hakuri Ma, wannan kwanon yafi karfin rayuwarmu balle ita!" Dauko ta nayi ta zauna a kusa dani, na saka mata abincin, sai da ta kalli iyayenta, kansu a sunkuye. Sauka zata yi na ce mata. "Idan baki ci ba, nima na hakura da nawa!" Na faɗa ina murmushi, a hankali ta diba tana ci, tana kallon Mrs Lilly da take gyada mata kai. "Tsayuwar me kuke yi a kanta!" Ya fada cikin tsawa. Yadda jikinsu yake rawa suka shiga aiki ba ji ba gani. "Ke waye ya ce ki zauna anan? Waye ya kira ki zuwa cikin gidan nan?"
"Ka fita daga cikin gidan, kuma ka daina mata ihu a kai!" Inji Faruq ya fada yana shigowa cikin gida. "Ita din Sarauniya ce, matar King Salma!" Zubewa yayi akan kafarshi yana faɗin. "Tuba nake ranki shi dade!" Ina cikin abincin ina kallon Mary da take zare idanu. "Ci babu me damunki!" Ina gama ci na juya kujeran yana durkushe.."Faruq!" Amsawa yayi na ce mishi.."ina suka je?" "Sun tafi asibiti ne bakiɗaya!" "Mrs Lilly zata maka bayani, na ce a madadin kai abincin nan zuwa gidan marayu a raba musu biyu su. Su dauki rabi akai rabi can, sauran bayanin zata maka. Idan Mother ta gama cin abinci, a nima mata makarantar, a cire a cikin kudin mai gidan a biya mata, ko yaya tayi aikin alkhairi da ilimin da ya biya zai samu lada! William!" Na juya gare shi ina kallonshi. "Su ma mutane ne, kada ka kara cutar da kowa idan ba haka ba, zan saka a a kama ka da laifin cin zarafin dan adam!" Cikin girmamawa ya ce min. "Ba zaka kara ba daga yau!"
A hankali ta ajiye spoon din ta dauki bowl din