Showing 282001 words to 285000 words out of 304445 words
ta ce ai ita yar Amirka ce kuma ya yiwa mijinta aikin ƙwaƙwalwa, tana fadar sunan mijin, ya rike baki yana faɗin. "Ya yake?" "Mun rabu mun rabu domin ya koma shaye-shaye shine na rabu da shi da yaronmu ɗaya yana wurin Iyayena!" "Allah ya baki wanda ya fishi!" Godiya tayi tare da cewa amin, ta fita can sai ga wasu suna ta shigowa suna gaya mishi sun tab'a jin labarinsa wasu har nuna mishi tsofin videon aikin da ya tab'a yi a public yayi, sai duk ya takura. Rike hannunsa nayi ina faɗin. "A yanzu na fahimci wani abu akanka! Baka da ce da mulki ba, ban san wani abu kake bukata a mulki ba, amma al'umma suna bukatar irinka dan baiwa!" Murmushi yai yana faɗin. "Tabbas mulki ba nawa ba ne, zan yi wani abu ne idan na gama zan koma inda nafi wayo!" Ya shafa kaina yana sumbata, haka muka iso garin zanzabira Faruq ya zo ya dauke mu.
Yadda Ummi take damuwa da ni, yasa take ta cewa a kawo min kaza da kaza, kafin wani lokaci ta cika min gaba da kayan dad'i, shima haka cire kayan zak'in yayi na kalle shi kamar xan yi kuka ya ce min. "Sam baki jin magana kin san dalilin ciwon cikin nan wannan watan ai saboda zak'in da kike ta durawa cikinki ne yaushe zaki girma?" Tura baki nayi na ce mishi. "Gobe da safe!" Murmushi Mai Babbar daki tayi tana faɗin. "Har yanzu da ciwon cikin ne?" "Eh Ummi da ciwon cikin sabida kwadayi irin nata." Dariya tayi tana faɗin. "Kai kuma da ba kwadayayye ba sai ka saka mata idanun!" Haka muka ci abinci, Mai Babbar daki tayi mishi nasiha sosai sannan ta haɗa har da ni, sannan muka bar gidan, bangaren shi Ijlal ta gyara an saka turaren wuta anyi gyara na musamman, ita kuwa Uwar princess ana can ana ta zuba kishi da fushi. Ni dai ɓangarena, na shiga na cigaba da harkan gabana da abinda ya shafe ni. Wasa wasa kafun wani lokaci na kusan gamawa Allah yasa Wildat ta shigo tare muka gama kome, sannan muka daura abinci iya ni da ita ne, haka muka ci abincin dama tafiya ce da miyar sauce....
92&96
Kwana biyu yayi bangaren Ijlal ya bawa kowa tsarabarsu, wani gado me kama da kujera na sayawa Amirah na bashi ya fitowa Uwar da shi yana nuna mata yadda zata saka yarinyar wacce take wata biyar amma har yau babu al'amar zama, a yanzu Ijlal take fahimtar kome na rayuwar Yarta, kallonshi tayi ta ce mishi. "Daddyn Amieerah ko zaka fitar da ita waje ne ko za a dace?" Kallonta yayi sai ya sake murmushi ya ce mata.."babu wanda ya isa ya miki jinyarta ta warke sai Allah, abinda na yi ta so ki fahimta kenan kika kasa ganewa, ciwon Amirah take ba ciwo ba ne da zaka biyewa wasu kayi ta yadda kake so yanzu zaki fahimci yadda abin yake kada ki damu, haka yasa na dawo dake ji yi jinyarta da kanki!" Sai da tayi kuka domin kuwa har wurin wani boka aka kaita ya ce mata bai ga wani abu na sihiri ba, ita ce dai take dab da fadawa hannun wata shaidaniyar ruhi, yarta kuwa abinda ta aikata zata girbeta idan zata zubar da makamanta tow da sauki sai ta fuskanci gobenta idan kuwa ta ki, Uban Kishiyarta yana tsaye tana tab'a mishi Y'a hauka zata yi wanda babu magani yanzu haka akwai wani wasu da suke bin mijinsu suna ta bin shi da asiri, sunyi nasarar tab'a mata cikinta har tayi barinsa, ya ce mata yanxu haka bokon da yayi wannan aikin yana can a kwance cikinshi yana ta cika da jini, ya kara da gaya mata yarinyar da Mijinku rayuwarsu a hade take, idan suka rabu zaku ga masifa iya ganin idanunku kada ki saka kanki akan rigimar kishiyarki don ma na lura kece mai hada kome. Wannan maganar da yayi mata yasa ta kama kanta yanzu ita ta rayuwar yarta take ji amma idan ta tuna da Nadiyyah da yarta ba ta san wannan matsalar abinta.
**
Na koma aiki cikin hukuncin Allah kome ya fara tafiya min dai-dai, an kawo kayana na kuma janyo Tauhid na saka shi a wurin Sai ga Ilham tazo da Matsalarta na gayawa Yayunta da kowa suka kuwa bata goyan baya, haka aka fara kome da ita, cikin hukuncin Allah ta zama min yar talla ina biyanta mahaukatan kuɗi. Kuma Yayunta sun ce idan tayi wani tsalle daga can zuwa can zasu ajiye ta a gida haka yasa kome namu ya tafi aunty Fulani sama da kasa.
An samu wata guda da dawowanmu, a lokacin Nadiya tayi arzikin, ta amshi girki domin tun dawowarmu ta so amsa ya ce ta ji da kanta, baya buƙatarta. Haka kuka tayi ta hauka da Bala'i bai bi ta kanta ba yanzu mutumin nan yayi bala'in daurawa haka yasa kowa ya ga yadda ya sauya sai da ya kama kanshi, tana arzikin ta ce zata koma bai ki ba ya dibi jininta ya bawa Faruq ya je yayi mishi test ya kawo, anan ya dauke ta da dare ya kaita asibiti aka saka mata implan, ai shima da kuke gani ba karamin Bayahude ba ne, haka tayi ta mita da fada da rigima wanda har tana cewa don ni baya haihuwa zai musu mugunta, na toshe kunnena nayi kamar ban ji su ba, haka kwanaki suka cigaba da tafiya duk wata sai nayi saukar Kur'ani da azumi da lafiya ko zan samu cikin nan domin wani lokaci haka zan ta jinta tana dariya da shewa tana waka, Ijlal mata tana fito da yarta waje bayan la'asar sai su shigo bangarena wai sun zo ganin abinda ya zuba. Ni dai ban tab'a cewa kowa kome ba.
Amiratul Zaitunah tana cika shekara daya cib a duniya aka tashi kanmu da hidimar Birthday kasancewar satin da ya wuce na gama service dina, ban san da hidimarsu ba, ina barci ashe har an kira dangi da abokan arziki, sai da Wildat ta shigo nake tambayar ta. "Lafiya kuwa?" "Suna bikin ranar zagayowar haihuwar Amirah ce!" "Ikon Allah!" Haka na shirya na fito na samu ana ta hidimar, barka nayi mata tare da ɗaukarta yarinyar da yake uwar tana kawo ta gidan bangarena da sunan kallon dabbobi wai har ta gane ni, tana ganina tayi ta dariya da juya kai. Tashi nayi na kalli Uwar. "Ban sani ba wallahi sai da naji a hayaniyar Yara!" "Wai tow ki yi hakuri kada ki lalata min shiri na ce ya gaya miki don Allah kada ki ja yazo ta ruguza min shirina da farin cikin da yake idanunta!" Na kalli yarinyar sai dariya taƙe tana son na dauke ta. "Ba zan lalata murmushin da nake gani a kan fuskarta ba, ban kuma shigo don na lalata murmushin can mai tsada ba, ina ga ko ke baki samun irin wannan murmushin." Na fada ina kallon yarinyar a hankali na nufi yarinyar ai kuwa ta damki hannuna, haka na tashi na zare hannuna, sannan na nufi hanya xan fita ina jin wata Yar uwar Hajiya Mardiya tana faɗin. "Ba iya haifa ba sai iua ci a yi kashi!" Naji sarai amma ban kula ba ita Ijlal ɗin ce ta ce Mata. "Don Allah kada ki janyo min masifarshi wallahi ya sake ni a kanta!" Murmushin takaici nayi na dawo bangarena a bakin gate muka hadu da Nadiyyah. Me ya shiga yi a cikin gidana ? Haka na shiga na ga tana murmushi koda yake ai bangaren mijinta ne, a yanzu Princess watanta takwas, yarinyar itama tana ganina tayi ta d'aga min hannu kenan. Kuma haka ya samu asali ne ta wurin Ubansu shi yake kawo min su ayi hira a haraba na, Don haka yaran suka saba da ni. Musamman da nake da lokacinsu nayi ta musu wasa ina jansu da abubuwan wasa. Ko kunsan cewa Amiraah da take cikin wannan yanayin ta san yadda zata kiran sunana. "Mammi!" Abinda yake iya furtawa kenan Uwarta kuwa Na take kiranta, Uban kuwa Da. Wannan abin ya bawa Ijlal haushi wai ina sace kome hatta yaransu na sace zuciyarsu.
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 93
Ai kuwa suka daina yarda ya dauki yaran, kamar hada baki suka yi tun kafin Birthday din Amiraah aka daina kawo su haraba na, Ni kuwa haka bai min ciwo ba domin dai sune a matuƙar wahale, zaman gida ba dad'i, a hankali kome yake zuwa da sauki mall dina bayan ya cika ana zuwa a dauki sari da sayan ɗai-ɗai sai nima na zama busy, tun kafin mu gama service Yeemar ta haihu, muka sha sunan Yarta mace mai sunan Uwar mijinta, ana kiranta Ammi. A hankali kome yayi ta tafiya kamar bamu ba. A cikin wannan yanayin da muke ciki Ilham ta samu miji, kafin ya turo take gaya min tana son ta gabatar da shi ni kuwa nayi ta mata dariya ina faɗin. "Ki gayawa Yayanki kawai." "Hmm baya dariya ta sauki yanzu sai ya kusan halaka ni idan ya ji bayarabe ne wanda nake so!" "Allah ya shirya ki ai musulmi ne tunda yana sonki zasu bashi kenan, kin gaya Fulani ?" "Ban gaya mata ba!" "Yana da kyau ki gaya mata sai muji me zata ce!" Haka kuwa ta gayawa Uwarta, ita kuwa ta samu mai Babbar daki da maganar, itama ta samu danta da zancen, yana zuwa ya fara min mita Ilham guda nawa take da zata yi aure nan kuwa? Kallonshi nayi da kyau cikin renin hankali domin nima ina son zan bi su Maluma Maradi bikin Ihsan naji mijin Yeemar shima ya barta. "Ilham dai ta gama jami'a, sannan tana cikin yan mata da suke cin kudi da baiwarta idan ba hassada kake mata zata je ta ji dadi ba ka saka ayi bincike ayi mata aure bana son bakin hali da hassada!" Biyo ni yayi na falla da gudu ya bi bayana haka ya dauke ni cak yana faɗin. "Bari na nuna miki yadda ake hassada da kyau!" Wallahi na gurzu a hannunsa fiye da yadda baku tunani, kafin ya kyalle ni yana faɗin Allah yasa nayi saiti daidai, buga mish pillow nayi abina, muna ta dariya, anan nake gaya mishi zan tafi biki maradi, bai bani amsa ba ya wuce ban daki nima bin sa nayi muka yi wanka tare sannan na fito na gyara jikina yadda yake hade rai na fahimci baya son maganar sai na share ban kuma magana ba. Haka ya shiga ban garen Nadiyyah.
Haka suka yi bincike akan mutumin da yake niman Ilham, asalinsa dan kwara state, Ubansa Bayarabe ne Mahaifiyarsa bafulatana, ba ayi wani kasa a gwiwa ba aka fara maganar aure, ai kuwa an nuna mana yadda ake hidima, sai gashi Uwar Amaryar yayun Amaryan sun tattara kome sun tura min, mai babbar daki ta ce min. "Girman kenan ai tunda kika dauke ta a matsayin mai talla, muka bar miki ita." Nayi kuka kamar na me, saboda farin ciki sai abin ya zame min abin gori na cusa kaina cikin dangi ana ji dani na sani gara na haihu ko mace ce, kai koda irin Amiraah ce nayi fatan Allah ya bani. Wato abinda basu sani ba Yadda suke wanke shi da sayayyan yaransu haka yake wanke ni da dukiya nima, Omo kin kula Ijlal, sun saka bikin nan da wata biyu, haka ya bani damar zuwa nijar kwana uku, kamar wata korarriya haka na dawo ana tsaka da biki, muka wuce China ni da Bilqis Daulah, da Dijah da ita amaryan sai shi Namamajo da Faruq, muna isa sai da muka huta na tsawon kwana biyu, sannan muka fara fita muna zaga garin kafin muka isa wani store na kayan kitchen, tunda muka shiga na fara sayayya, abin ya basu mamaki nace musu. "Ai na jima da booking tun kafin na zo!" Wayata da take jakar Amaryan tun jiya ya nima mana layin kasar, nayi kuwa saving number shi da Namamajo, cirowa tayi tana faɗin. "Aunty Fulani waye Namamajo?" "Oh my King!" Na amshi wayar na saka a kunne cikin karya murya na ce mishi. "My Namamajo ya kake? Me kake so?" Sake baki suka yi jin yadda nake kiran dan uwansu! Har muka gama suka min caaa da idanu, murmushi nayi nace musu. "Kada ku damu ai shi din haka ne bana cire rai zai cika ta huɗu!" "Kuma sai a kira shi da Namamajo?" Dariya nayi kawai na cigaba da abinda nake yi, har muka gama muka fito, wani store na tsaya kayan Yara na gani, baya cikin lissafina amma sai nayi ina da kwadayin saya haka na shiga na fara sayan kayan, Bilqis ta taya ni itama, muna gamawa muka fito, sati uku muka yi aka saka mata kaya a ruwa, mu kuma muka wuce Turkiya anan muka sayi kayan gado masu kyau, sati daya muka yi shi kam ya koma tun satin mu biyu, sannan muka wuce India anan muka sayi manyan kulollin abinci masu kyau elites na fada a ji. Sannan muka dawo nayi booking kaya electronics a South Korea, musamman LG, musamman da na ga masu kamfanin nasan shi, gayen da ya fito a Marry my husband, ba asalin jarumin ba shashan wnada ya fito a welcome to wikiki, haka yasa na sayi kayan su don gayen number dan ban dariya ne.
Wata guda muka dauka muka dawo a matuƙar gajiye da bukata mijina, muna isowa na samu kyakkyawar tarba a wurinsa, kwanaki uku bai fita fada ba. A yadda na fahimce shi kamar ba lafiya, haka yasa na kame kaina nayi ta binsa ina shafa kanshi da rarrashinsa, kamar wanda aka bude min bakinsa ya gaya min Nadiyyah da Ijlal ciki ne da su. Kusan yadda na ji abin? Kamar diran aradu haka naji abin, jikina wani irin rawa ya dauka da sanyi, na rasa gane tashin hankali nake ciki ko farin ciki, hawayen da nake dannewa ne ya subo min, nayi ƙoƙarin gogewa kada ya gani. .....
Murmushin karfin hali nayi na fara faɗin, "Masha Allah, Ubangiji ya sauke su lafiya!" Daga haka na wuce na bar shi nan rai ba dad'i daga ranar na fita harkanshi wallahi na tsani abinda zai hada ni da shi. Tun bai gane ina gudunsa ba, kwatsama ya fahimci bana son mu'amala ko ta aure ce ya hadamu, a hankali wani yanayi mara daɗi ya kara ratsa tsakaninmu shi ne, haka kawai idan ya shigo ya kwanta bai nima na nima kuma bana nimansa, a haka kuma idan ya fita a buƙace da ni yake dawowa. Ganin halin da na tsoro sai ya kai karata gidanmu, ya gayawa Umma. Da kanta taso tai ta min fada da nasiha, ita kanta da na gaya mata abinda ya faru shiru tayi tana mamakin abinda na ce. "Umma da goyon danye ya musu ciki ita Sadiya shekara daya ita kuma." "Ina ruwanki? Akanki suke? Yau naga jaraba da kishi!" Inda Umma ke shiga ba nan take fita ba har ya shigo ina ta mata ido amma umma tayi kamar bata gani ba ta gaya mishi kome, murmushi yayi yana faɗin. "Allah yana sane da ita in.sha Allah itama zai bata!" Sai kuma ya koma bata hakuri tayi min tas na tura baki ta buge min bakin na fashe da kuka, yadda ta rufe ni da fada yasa shi runguma ni yana faɗin Umma. "Maslaha muke noma ba fada ba!" Ai kuwa ya bani haushi na ture hannunsa na kifa kaina a cinyata. Haka tayi min gargadi da babban murya na sake na kashe aurena zata bani mamaki ita da Maluma. Haka na daure zuciyata ina ta kuka, ai kuwa cikin Ijlal irin mai laulayin nan ne, haka take ta ciwo yau tana asibiti gobe tana gida, haka dai Nadiya itama ba wani laulayi can sai dai ba halin nayi abu zata biyo tayi ta zare min idanu. Ni kuma tsoron basu nake sau uku tana min haka karshe ta gaya masa ita fa cikinta abincina yake so! Shi kuma da yake bai da lamba sai gashi ai kuwa ya same ni a tsini nace ba abincina ba, idan ya diba zai ga tsiya na bar wurin haka yasa shi kiran Ilham ta musu girkin irin nawa, wai ace zuciya lokacin da tazo ta ji abinda nayi ya gaya mata, ta amsa amma ranta bai so ba. Bayan futarshi sai gata a dakina. Yadda ta buga kofar da kirana yasa na fito ina ganinta na dauke kai. "Aunty Fulani, ki bata daga yau ta nime mai mata, ciki ne da ita ko yaya kika bata Allah zai baki lada, sannan kada ki yarda yana jin ba dad'i akan matansa wallahi zai fara jin haushin kamar saboda bake bace, please bana son ki samu matsala da kowa wallahi kaf familyn Yayari suna sonki tun daga ranar da kika yi bari kowa yake son please!" Wannan rokon yasa na fito na zuba abincin ya shigo ya samu tana rufewa tare da cewa."ko ke fa Aunty Fulani!" Dauke kai nayi na ce. " Ni ban ce ta dauko ciki ba, idan abu take so ta shiga cikin gidan ba zata rasa ba a wurin Umma ni ba baiwar kowa bace, aure ya kawo ni itama aure ya kawo ta." Takowa yayi gabana ya tsaya tare da cewa. "Me kike nufi? Akan abincin da kika bada ne kike wannan masifar?" Yadda yake maganar zaka fahimci ba fada yake nima ba sulhu yake nima, cikin takaici da haushi yasa na harara shi, na ce mishi. "Ni da bani da amfani a rayuwarka? Matanka masu haihuwa sun fini!" Na fada cikin kuka, "waye ya ce baki da amfani? Wani azzalumin ne zai ce baki da amfani a rayuwata? Waye ya gaya miki haka?" Dauke abincin Ilham ta yi ta gudu abinta, kafin na