Showing 240001 words to 243000 words out of 304445 words

Chapter 81 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

102

basu bi ta kan mai jegon ba, sai hiran Hajja Bilqis take da suka isa ta bawa Mahaifiyarta nata sakon domin na ware na su suma, ta kalli Mahaifiyar ta tace mata. "Umma yarinyar nan tana da kirki da hankali ga kome nata yana tafiya cikin nutswa da tsari!"
Murmushi tayi tana faɗin. "Eh amma ki kula da kanki kada ki shiga lamarin ki ka sa fita." "A'a ba shiga zan yi ba, kawai sai tana da abinda ya dace duk wata matar sarki tana da shine!"
Bayan an gidanmu sun tafi Yeemar mijinta yazo ta dauke ta, Wildat da abokiyarta suka taya ni aiki tas aka gyara gidan, sauran abinci suka tafi a shi bangarensu, kasan shi yake a key dina don haka na rufe gidan nayi wanka na zuba kafana a cikin ruwan zafin ya gasu sannan na fito a dakin na same shi ya kawo min tea na sha da namar nan. Ina sha ya bani panadol, daga nan na kwanta a jikinshi barci yayi gaba da ni, wurin karfe biyu kiran wayarshi ya tashe mu, ya dauka ina faɗin. "Lafiya?" "Baby taki barci mu kuma mun rasa yadda zamu yi da ita sai kuka take," gyara kwanciya nayi na cigaba da barcina tashi yayi ya fita ina barci na jishi, can sai gashi da babyn wai tana parlourn a zaune ko xan musu wani abu babyn ta yi barci. Tausayin yarinyar da take kuka muryanta har ya dushe, na kalle shi a hankali na ce mishi. "Idan na gaya maka wani abu zaka yarda?" Gyada kai yayi na ce mishi.."ka mai da mata Yarta, sannan ka tambaye ta meye amfanin matan da suke tare da ita? Sai na uku ta cirewa Yarinyar nan kayan nan don Allah, ta mata wanka da ruwan dumi ya gasata ni dai barci nake ji, mu kwana lafiya!" Na ja bargona na kwana. Barci ban bi ta kanshi ba, ai kuwa bai dawo ba sai bayan sallah asuba, ban ce miki cikanka ba. Sai lokacin yake gayawa min yana gaya musu aka mata wanka, amma yadda na ga kamar ransa a b'ace yake yasa na kyale shi na koma barci a cikin barci nake jin yana faɗin. "Taya zata tashe ni karfe biyu, na ce ta bari na kawo yarinyar tace a"a na kawo ta koma tana min labe ba yau ta fara ba Ummi, ta tafi gida tayi wanka sai na bukaci dawowarta amma yanzu babu wani abin da zan iya mata don zan iya rabuwa da ita har abada!" Gyara jan bargon nayi nakara nutsewa cikinsa, idan kana jin baka iya kuka ba uwarka ce bata musu ba.

Idan labe ne ba yau ta fara ba fa, haka suka yi aiki su da bayi aka yi suyar nama, ina kwance suka buga sai Allah ya taimaka Wildat tana nan ta amsa sannan ta shige cikin kitchen da shi, namar a flat aka kawo min ta juye musu. Karfe biyu na rana n tashi nayi wanka na gyara jikina, ana nuna min namar na ce su dauka na basu. Wannan abin ya musu dadi, na jiya ma su na bawa suna juye suna ta godiya.

Karfe shida na yamma ya shigo yana mai faɗin. "Wash!" Kallo daya nayi mishi na cigaba da kallon Arewa24. "Madam babu abinci ne?" "Ban yi ba naga kamar ka koma can ne!" Na fada domin tun da ya fita bai dawo ba kuma bai je fada ba an gaya min yana reno ne, Uwar da yar suna bangarenshi, sai shewa da yayyi take tayi wai ko zan ji, tow naji sai me? Yadda nayi maganar ya ce min.."Amma kin san matata ce?" "Ai shi yasa na ce ka koma can ne?" "Wai ke!"
"Wani Tsinannen ne yake min labe?" Aikuwa ta kwasa da gudu ina jin ta rufe kofar gidan har shima ya ji, tashi yayi ya fita, ban san me ya faru ba gaskiya sai dai yadda ya haukace musu yasa dole a daren aka mai da ta gidansu, nima wai yayi zuciya ban ga kafarshi ba, nace can da su gada ban bi ta kanshi ba, sai washi gari da na tashi da aiki nayi abin karyawa. Ya shigo ya karya ya ke ce min. "Idan Nadiyyah ta dawo kowacce za a ware mata masu mata aiki da girki!" "Tow!" Na ce na cigaba da karyawana, yadda naga yana hade rai haka nima nake hade rai, ya gama ya wuce fada yau kan babu babbar riga shigar turawa aka yi na ce a raina na ce. "Allah ya jikan sarakunan gargajiya!"

Ashe jiyan wani abu ta faru a wani gari na data daga cikin hakiman da suke kasanshi, shine aka chaza mishi kai zai dauke kwandon masifar shi sai Ijlal tayi katari yana kan tsininsa.........
08130269641
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 79
Wato tun kafin rasuwar mahaifinsa da Alhaji Saddam ake fuskanta wani case da a hukumance an kasa warware shi, ba wai babu hanyar da za a warware ba ne, kawai akwai mutanen da suke amfana da wannan al'amarin ne, yankin taski local government na Zanzabira, tana kusa da Farar kasa ce, gari ne mai arzikin noma domin suna da dam wadda ya haɗa da Zanzabira, garin kifi da noman rani da damina, daga garin ake shigar kayan hatsi da kifi, garin suna noma duk fadin yankin Arewa babu inda ya kai su nomar kayan abinci, wanda yake rike kusan kashi saba'in na zanzabira amma wani abin mamaki shine duk sati aka ci kasuwa aka kawo kayan abinci garin idan zasu koma ana tare motar yan kasuwa a kashe a wulakanta su, a lokacin Sarki Attahiru Shehu Yayari yayi magana da gwamnati tun daga kan ta jahar Zanzibara har zuwa ta kasa aka ce za'a magance matsalar amma abu ya ci tura. Sai ya lafa sai ya dawo to yanzu abin ya kai har matafiya ma ana tarewa a kwashe musu dukiya a kashe su, tunda Salmanun Faris ya amshi Sarautar sai aka samu matsala, shi bai san da yadda abin yake ba, har an cigaba da yin mugun barna, a wannan can ne aka kashe daya daga cikin manoman da suke kula da harkokin abincin masarautar, shine ɗan uwansa ya kawo koke cikin fadar dakyar ya samu ganin Salamanu Faris, abinda ya sa haka ya faruwa kafin sunan nan ayita mishi complain kayan abincin da yake store ba Masarautar ya kusan kwarewa kayan abincin da idan aka loda sai ya shekara hudu, bai kare ba sai ma an raba sadaka ga mabukata, shine ya tura sako wurin Sarkin noma Alhaji Naziru Yayari, tunda ya zo yake ta karerayi, haka maganar aka barshi bayan kwana biyu sai ga dan uwan wanda aka kashe, yayi ta sintiri sai da wani dogari ya hada shi da Faruq, anan ne ya samu ganin Salamanu Faris, sosai ya gaya mishi halin da garin yake ciki. Shine ya ki zuwa Fada, ya kuma ki amsa kiran kowa yana kwance wannan nazarin da yake ne munafuka tayi ta shiga mishi da Yarta. Bayan sallah isha suka tsare shi aka yi meeting, yana tsaye a bayan kujeran da ya dace ya zauna. Yana jin su, suna ta mishi bayani. "Kuka ce hukuma ma ta kasa magance Matsalar?"
"Eh ranka ya dade!"
"Waziri kai zamu tafi da kai gidan Gwamna a nima mana izinin ganawa da shi, kai kuma Galadiman daga nan zuwa sati da xan tafi ziyara can zaka kula da Zanzabira har mu dawo ka ji ko?" "In sha Allah!"
A daren da suka nime iznin ganin gwamna Musharraf ya ce a gaya musu baya gari. Ya sani ba zai tab'a saurarensa ba, don haka ya sa Faruq ya nimo Goga, ya bincika musu inda Alhaji Nafi'u yake cikin abinda bai wuce awa daya ba. Ai kuwa da yake dabanci ya aure shi ya kuma shiga jikinsa, sau ga shi a cikin awa guda sai ga kiranshi, yana gidanshi don haka. Ya shirya cikin ƙananan kaya ya nufi gidan Alhaji Mamman Abba yayari, ya dauke shi suka nufi gidan Alhaji Nafi'u, wani ikon Allah sun same shi kuwa, ganin yadda suka yi amfani da karfin security sai masu tsaron kofar suka yi maza suka fada musu ga halin da ake ciki, don haka koda Alhaji Nafi'u ya ji haka ya ce a barshi ya shigo. Murmushi yayi suna suka samu Gwamna Musharraf a zaune a kasa kamar wani almajiri kanshi a kasa. Zama suka ya zubawa Alhaji Nafi'u idanu yana murmushi. "Me ya kawo ka? Bayan kace zaman lafiya kake bukata?"
"Anya zaman lafiyar nan zai samu kuwa?" Shiru parlourn yayi kafin Alhaji Nafi'u ya ce mishi. "Me kake nufi?"
"Taski local government, nasan babu yadda za ayi baka cikin wannan badakalar!" "Me ka ɗauke ni? Waye ya gaya maka kowacce kazamta nake ci!"
"Waye ya sani mutum da ya yi homo ya kuka bi matan aure, meye ya rage maka?"
"Zo ka fita min a gida!"
"Sai na gama abinda ya kawo ni" ya juya ga Musharraf, ya ce mishi. "Tashi ga wuri nan zauna!" Kallon Alhaji Nafi'u yayi yayi kasa da kai. "Kai tashi!" Ya daka masa tsawar da parlourn sai da ya amsa. Ba musu ya tashi ya zauna a hankali yana zare idanu. "Alhaji Nafi'u aurenka yake da kake mishi biyayya haka? Ko shine mijinka bayan ya baka yarsa ko akwai wani abu ne bamu sani ba!"
"Salamanu Faris ka kiyaye harshenka!" Inji Alhaji Nafi'u, "Na kiyayye harshena? Kace me?" Ya daka wani irin tsawa sa ya haɗa da buga center table din da hannunsa sai da ya dagargaje. Tsoron haka yasa kowa ya kare kansa. "Na gaya maka ina son zaman lafiya sai ka bi al'umma kana musu kisan wulakanci!" "Sau nawa xan gaya maka bani cikin wannan lamarin, ka bincika fadar da Emirate council mana sun san kome!" Murmushi yayi ya ce. "Ba gashi ka gaya min abinda nake zargi, hmm sannan ya ce. "Mai Girma Gwamna, zaka bani hadin kai mu duba lamarin kauyen ne ko zaka koma gefe ka bar ni nayi aikin ni daya ne?"
Kallon Alhaji Nafi'u yayi yana zare idanun yaki magana sai da ya sake maimaitawa ya ce mishi. "Zai duba lamarin!" Inji Alhaji Nafi'u.

Saka hannu yayi a kunnensa yana sosa kunne yana faɗin. "Zuwa yaushe? Domin bani da hakurin jira?" "Amma duk saurin unguwar zoma dole ta jira a haihu ko?" Inji Alhaji Nafi'u, murmushi Faris yayi ya ce mishi. "Ni ba haihuwa ba ne, ni mutuwa ce idan lokaci yayi nake ɗauka, bana jiran koda dakika daya ne, idan ya wuce awa ashirin da hudu!" Murmushi yayi yana mai bude sabon goran ruwan da yake wurin ya shanye tare da ajiye goran sannan ya saka kai ya bar gidan bakiɗaya, "Ba kace kome akan mutanen Fada ba?" "Su waye kenan? Ko kana da shawarar da zaka bada ne?" "A'a kawai!"
"Kawai me?" "Ba kome!" Ya fada a hankali, har suka iso gidan Alhaji Mamman Abba yayari suka ajiye shi kafin suka suka bar Kofar gidan zuwa. Gidanshi a jikin motar suka tsaya ya ce mishi. "Ina tsoron zuciyata kada ta cigaba da zargin Mamman Abba yayari!" Shiru suka yi kafin ya nufi cikin gidan Faruq yana take mishi baya, har zuwa bakin kofar. A bakin kofar ya kalli Faruq. "Ba kace kome ba?" Jinjina kai yayi kafin ya ce mishi. "Akwai abu guda da na hango a tattare da Alhaji Mamman Abba yayari, na farko har muka shiga muka fito jikinshi rawa yaƙe, na biyu har ka gama magana bai ce Uffan ba, na uku yadda kake magana har ka gama kanshi a sunkuye yake, waɗannan gaɓɓai ya bani damar fahimtar waye shi ko da ace bai da hannu tow akwai wani abu da ya sani yana boyewa ne kawai."
"Da kyau Faruq dina, dan sanda na musamman na gode mu kwana lafiya!" Ya fada yana murmushi, juyawa yayi ya shiga Faruq na gani ya shiga shima ya juya zuwa waje ya rufe kofar gidan, sannan ya kalli masu tsaron kofar gidan. "Su waye? Anan?"
"Sir Goga ne tare da Simon Haruna!" "Ok! Good Job!" Ya wuce zuwa kofar Ikhlas ya duba masu tsaron suka fadi sunansu sannan ya wuce inda yake zama kafin ya amshi abinci wurin Jakadiya Iyaami ya wuce gidan da yake..
Ina kwance ya shigo, kallo daya nayi mishi na gyara kwanciyata, ina son magana amma bana son tashin hankali, na janye jikina daga tsakiyar gado na koma baya, ina mai lumshe idanuna. Kashe wutar dakin yayi ya kwanta shima babu wanda ya kula, can ya juyo yana kallona. "Ke baki iya bawa mutum hakuri idan kin mishi laifi ba ne?" Shiru nayi mishi tare da sauke boyayyen ajiyar zuciya, na cigaba da kwanciyata. "Baki ji ina magana ba ne?" A hankali na kalle shi kafin na ce mishi. "Barci nake ji Yaya!" Na kara rufe idanuna. Nasan matsalarshi na kula shi ya rage zafin da yake ji ne, ni kuwa ba zai dame ni ba.

Ganin naki kula shi ya matso jikina, ya kai hannunshi zai tab'a na rike hannun. "Please barci nake ji!" Na fada ina sauke hannunsa, janyo ni yayi jikinshi ya fara niman d'aga min hankali. Na fashe shi da kuka tare da sake mishi jikin tunda nasan ina period ne, ganin haka yasa shi kyale ni yana sauke numfashi. "Tow ya isa haka, na kyale ki dole Nady ko Ijlal daya ta dawo ba zan iya kashe kaina ba!" Yadda ya fada nan ya so yaga yadda xan fusata ne sai ya ga haka bai wani d'aga min hankali ba, har nayi barci yana fama. Hannuna ya riko ya daura min akan abinshi. Yana niman na farka bude ido nayi na rike abin, duk da bani da zaɓi amma nayi ƙoƙarin samar mishi da nutsuwa yadda ya kamani ya k'amk'ame, na fahimci ya rage damuwar da yake damunsa wanka ya shiga yayi nima na gyara jikina domin jikina ya amshi wasu abubuwan da yake min, har naji fitar wasu abubuwan, haka ya bani damar yin wanka. Ina fitowa na gyara jikina na saka riga mai kauri yana fitowa ya wuce bangarenshi dama ya zo ya d'aga min hankali ne, sai da ya bar dakin na gyara kwanciya na cigaba da kallon kofar, har na fara barci na ji motsinsa ya kwanta a bayana, a bayyane na sauke ajiyar zuciya. Ina gyara kwanciyata akan hannunshi.

Da asuba da muka farka wanka yayi ya wuce masallaci, ni kuma na wuce kitchen na daura abin karyawa na dawo na gyara kwanciyana, wurin karfe shida na koma kitchen na sauke sannan na baza su ya sha iska da yake doya ce, ina gamawa na koma na kwanta sai karfe Bakwai saura na fito nayi abin karyawa sai tea da dafa yaji kayan kamshi. Sannan na dibi nawa na wuce parlour ina karyawa ya zo.. "ina abin karyawa na?" Ya tambaye ni yana zama. "Gaskiya sai dai ka yi hakuri ban yi da kai ba!" Matsowa kusa da ni yayi ya dauka ya fara ci, haka na tashi na kawo mishi, nawa ya ci nashi ya bar min. "Ya ka ji labarin Amiratul Zaitunah?"
"Suna lafiya dazun Mamanta take gaya min wai bata barci! Sai gari ya waye!" Ya fada yana shan tea. "Ai haka Yara suke dare ne lokacin hiransu, idan irin haka ya faru su kama ta su mata wanka sai a goya ta, zata koma barci in sha Allah haka Umma da Maluma suke yiwa jikokinsu!"
"Yanzu idan kin haihuwa bana tunanin kulawa da Yara zai baki wahala!" Murmushi nayi na ce mishi. "Eh amma ai ita mai jego ana barinta ta huta ne, saboda kada bayan haihuwa ta shiga damuwa, idan na haihu gida zan koma nayi wankan jego domin ba zan zauna ka saka ni a gaba ba." Dariya yayi yana faɗin. "Allah ki saka a ranki ba zaki tab'a zuwa wankan jego ba, muna tare a yadda muka yi cikinmu tare haka zamu haihu tare, Ikhlas ko me kika yi nima sai nayi har rokon Allah nake jininmu ya zama daya yadda kome kika yi nima zan ji nayi!"
Takaici ne ya kama ni na dauki pillow kujeran nayi ta muka mishi ina faɗin.."Ni kake yiwa mugun fata? Yadda kowa ya tafi wankar gida haka nima zan tafi ba zaka janyo min abin gori ina zaman lafiya ba."
"Allah da gaske Nady ma idan ta haihu gida zata koma kece fitilar gidana, kina tafiya hasken zai dauke." Ya fada yana mikewa saboda yadda ya ga nayi shiru. Na ce mishi! "Amma wasa kake ko?" "Billahi azmin ba wasa nake miki ba, ba zaki tab'a zuwa wankar gida ba a nan zamu zauna mu yi cikin tare mu yi laulayin tare mu yi hidimar tashi dakyar zama da kyar!" Shiru nayi ban kula shi ba, shiru nayi ban kara cewa kome ba, na kyale shi ya ce min. "Zo muje ki taya ni shiri!" Ya riƙo hannuna muka wuce wurinsa, muna shiga cikin dakin shi na shiga na nufi wurin laundry basket dinsa, na duba kayan wanki babu ji daya kallona yayi yana faɗin. "Wanan aikin faruq ne!" Kada na kara janyowa kaina bala'in da zan kasa saukewa, na shiga taya shi sauke kayan jikinshi. Ai kuwa sai gashi ya shirya tsaf yana kallona, safarshi da agogonshi na taimaka masa ya saka. Sannan muka fito na saka mishi alkyabbarshi na rako shi waje, kafin ta shiga motar ya san rungume ni. "Sai na dawo!" "Allah ya dawo da kai lafiya!" Sai da ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login