Showing 93001 words to 96000 words out of 304445 words
matuƙar tsorace na rike shi. "Wai me kake nufi da Yaran nan? Ka lalata min rayuwa ne don yau na zama abin dariya a gare ka?" "Nady!" "Kasan abinda na bari domin kai? Kasan abinda na yi domin kai, why? Na ji ba laifi bane kayi aure but why wannan Yarinya?" Ina kallon ya shafa kanshi a hankali kafin ya saka daya hannunsa a cikin aljuhun wandonsa ya ce mata. "Ki jirani!" Ya juya tare da riko hannuna ta daya barin, muka barta a tsaye a wurin, kamar ta ruwa ihu. Ni dai tunda ya kawo ni waje wurin motar ya bude min na shiga, na sauke ajiyar zuciya. Allah ya tsiratar dani. Murmushi sarkin kofa ya ce min. "Ranki shi dade, na ga sai ajiyar zuciya kike Hajiya Nadiyyah ko Ijlal?" Gyada kai nayi ina wasa da yatsuna, murmushi yayi kafin ya ce min. "Haka take da zafin rai, amma bata da mugun nufi! Ba zaki gane ba don kishiyarki ce!" Ya fada min lokacin da yake gyara parking motar. Sannan yazo ya bude min na fita yana me take min baya har part din Mai Babbar daki, tsoron yadda zan ga fuskarta ya sani jin kamar na sake fitsari a jikina, a babban parlournta na same ta, ji nayi kamar zan kifa, nayi maza na zube akan gwiwata. Ina hadiye yawun. Waya ce a hannunta alamar da shi take magana, alama tayi min na tashi, da sauri na tashi na nufi dakin da nake zama, ina shiga na samu an gyara tas koda na shiga hijab dina na ninke. Na wuce wardrobe na shiga jira shi, sannan na dawo bakin gadon na zauna. Shigowa Sailuba tayi da tiren abinci na sakar mata murmushi. "Ki .....yi hakuri na....na saka ....ki matsala!" "Ba kome kawai da aka tambaya ne nace kin tafi dauko kayanki a gidan ne." Murmushi nayi mata ta cigaba da cewa. "Mai Babbar daki ta damu kada wani abu ya same ki, sai ya gaya mata kina tare da shi, haka yasa hankalinta ya kwanta, ki ci abinci." Ta tura min, saukowa nayi na fara ci a hankali, ina jin kamar na mishi wani abu kafin ya tafi, ba wai zuciyata ta dawo gare shi ba ne, sai duk abinda xan yi dole na girmama lamarinsa, mutumin da ya ji ciwo sanadina, sannan Kullum sai ya kira ni ya ji yadda nake, sannan magani idan lokacin yayi ko baya nan, zai turo min sakon lokacin shan magani yayi.
Mikewa nayi na fito parlourn, zama nayi a gaban mai babbar daki. "Wani abu ne?" "Eh!" Na faɗa kaina a kasa. "Ina jinki." "Dama zan yi cake ne da cincin!" Kallon agogon bango tayi tana faɗin. " A daren nan?" "Eh!" Na gyad'a mata kai, "ki shiga ki ga abinda babu sai ki gaya min." "Na gode!" Na nufi kitchen din. Na duba kayan da babu na rubuta na kawo mata, kiranshi tayi ta ce ya turo mata faruq zai je mata aika ne. Ya ce mata shima gashi nan a waje zai kawo abu ne. Kashe wayar tayi can sai gashi, gaishe ta yayi lokacin da na fito na kara zama kusa da ita nace mata. "Ummi ina son kaji biyu?" "Halo dai?" Ta kuma tambayata. "Eh!" Na faɗa ina kallon kasa. "Yana nan ki ɗauka!" Tura mishi rubutun tayi, bayan na tashi. "Gaskiya sai dai ta zo muje ya saya." "Idan ka fita da ita ba dawowa zaka yi da ita ba, nan kusa tunda naka iya boye abinda yake ranka!" Shafa kai yayi yana faɗin.."Ummi ni kuma?" "Eh kai fa!" Ta fada tana kauda kai, kiran Faruq yayi ya bashi aikan. "Which mean ba zaka ba tunda ba zata bika ba." "Ni ban ce ba." Ya fada yana shafa kansa, kafin faruq ya dawo na daura kazar, sannan na haɗa mata kayan kamshi da na dandano, na koma kan kayan cake, ina haɗawa bayan minti ashirin sai ga Faruq yazo yana zuwa na dauki kome na zuba a mixer, na cigaba da aikina yana gama haduwa na kwaba cake din na hada abinda xan hada a zuba a cup dinsu. Cin-cin kuwa Sailuba da Wildat da ta kirata suna yanka min, kafin karfe goma mun fara soya, namar kazan wurin sha daya lokacin da ya leko kitchen din ya samu ina soya dambun na cikin mai, komawa Parlourn yayi mai babbar daki ta ce mishi. "Amma baka da abin yi ne?" "Ina da shi!" Ya kurawa kofar kitchen din idanu, itama bin kofar tayi da idanu. "Sam bana son yarinyar nan zan barka da ita ne saboda zuciyarka da ka bata, ba don haka ba da na saka ka sallame ta don laluran da take fama da shi." "Laluran nan a gidan nan ta same shi." "Eh shi yasa nake son ka rabu da ita, ina tsoron kada abinda ya faru na wasu lokutan ya faru akan yarinyar da babu ruwanta ne." Kallonta yayi da kyau, ya gyara zama. "Ban gane ba Ummina." Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa. "Fulani Atine, takwarar Daularh, ita ce Mahaifiyar Mai Martaba, Allah ya musu rahama. Ance Marigayi Mai Martaba yasota kamar ya bada rayuwarsa domin ta, haka yasa magauta suka yi ta jifarshi amma madadin ya same shi, sai ya fada kanta. Ina tsoron kada soyayyar da nake hangowa a ƙwayar idanunka ya cillata cikin hatsari." Murmushi yayi yana me mikewa ya nufi hanyar kitchein din. Bin sa tayi da idanu, tana girgiza kai ganin su Sailuba a waje yasa ta juya rufe kofar kitchen din yayi ta mike tare da barin parlourn. Ina tsaka da soya naji an rungume ni ta baya, ban san lokacin da na sake ludayin hannuna ba, gabana yana wani irin bugawa. "Ka sake ni kada mai babbar daki ta shigo!" Kanshi ya saka a wuyata ya ce. "Ba mai zuwa na gaji da jan ajin da kike yi min, waye ya aike ki Wannan aikin?" Haki na fara kamar wacce tayi gudun tsare da doki, "ina tambayarki?" "Please!" Na faɗa muryana yana rawa. "Zan kyale ki, amma ina jin yunwa wallahi!" Ya fada a sanyayye. Juyowa nayi na kalle shi, idanuna cike da kwalla na ce mishi. "Please bana son haka, ni." "Bakya sona ba?" Hawaye ne ya zubo min na goge da bayan hannuna, ina jan hancina kafin na juya da sauri na kwashe sannan na zuba wani man, na koma gefe na hada wuta hawaye na zuba min. "Ina jin yunwa?" "Ka je zan kawo maka!" Na faɗa ina jan kukan sosai. "Tow me nayi miki?" "Babu kome!" Na faɗa ina jan kukan, fita yayi na kira Sailuba ta kankare min karas da pies sannan na tafasa su da baking powder, na dauko taliya na karkaya shi kanana na soya sai sa yayi brown sannan na haɗa kayan miya na zuba a karamar pan , na fara soyawa sauran ruwan namar kazar na zuba kaɗan. Na kara ruwa na rufe ya tafasa ina cigaba da suya dambun ina yi ina lura da taliyar, ina ganin yayi na juye mishi a wani tangaran mai kyau Sailuba ta gaya min na marigayi ne wato mahaifinsa, sannan na kai na dawo na nika fruit na zuba zuma da madara na fasa kankara a kai na kai mishi parlourn.
"Ke bana son shegentaka kwanon mijina zaki zubo mishi abinci a ciki? Kada ki sake tab'a min kaya." Murmushi yayi, yana faɗin. "Ko zaki ci ne na zuba miki?" "tasan dani ta zuba maka iya cikinka, sai shi magana ta ce bata sonka, na bi rashin son da gudu." Murmushi ya kara da cewa. "Ni ina son matana haka. Ita bata iya karya ba ne zata gaya maka sai dai ka mutu, macen da zata gaya maka gaskiya bata cancanci k'i ba." Ya fada mata yana zuba mata abincin. "Ni tunda ta zo bata tab'a min girki ba sai kai, bayan a gidana take." "Ba mamaki don baki so bane." Kallonshi tayi cike da mamaki bayan ta kai lomar taliyar bakinta. "Hmm, ta san kanta." Ta fada tana cin abincin, duk da bata son Ikhlas sai dai tayi farin ciki ko ba kome zata ciyar mata da d'a cikin kwanciyar hankali, sannan da tasan haka girkinta yake da ta ci na ranar da aka kawo taki ci Abdullahi ne ya ci shi da Abdulhafiz, tana ci ta girgiza kai tana faɗin. "Junaid!" "Ummina!" "Idan na tuna shi ya kashe mai Martaba!" "Baki da tabbacin haka." Ya fada yana goge bakinsa da tissues din da yake parlourn, ya zauna yana shan drink din yana jin wani nishadi, tashi mai babbar daki tayi tana faɗin. "Ina zaman lafiya kasani cin abincin tsakiyar dare mu kwana lafiya!" "Allah ya kai!" "Kai ka ka wuce gida dai!" Ta fada tana nufar dakinta.
Duba agogo nayi na ga dare ya yi na fito ina me kwashe kayan, jin hannunsa nayi saman nawa na cire da sauri ina kallonshi. "Don Allah ko zaka raka su!?" Na tambaye shi "Tow amma ni waye zai raka ni idan na raka su?" Gyada kai yayi ya ce min. "Su fito!" Ya mike. "Tow!" Na koma na gaya musu, tashi suka yi suna min sai da safe, na amsa musu, suna tafiya na dawo na cigaba da aikina,minti biyar sai gashi nan ya dawo, kitchen din ya zo ya ja dogon kujera ya zauna yana kallon yadda nake aiki har na gama, na fara niman inda xan zuba sai dai babu. "Don Allah idan ka je gida ka duba!" Gyara zama yayi ya ce min gobe sai ki je ki duba don nima tsoron hanyar gidan nake idan kuma zaki raka ni muje tare ko ki juye kayan mu tafi da shi don nasan nawa ne!" "Ni babu inda zanje." Na haɗe rai, murmushi yayi ya fita daga parlourn dakina ya nufa, na tsaya ina kallonshi, kafin nima na shiga, ban daki ta shiga ina hango shi, ruwa ya haɗa sannan ya dawo ya kalle ni, "shiga!" "Ka je xan yi da kaina." Banza yayi min ya fara ƙoƙarin takowa inda nake nayi maza na yi baya tare da faɗin. "Zan yi don Allah ka san inda kake!" Na faɗa raina a b'ace, kafin na ce mishi. "Kawai zan biya abinda ka min ne, har yanzu ina da abinda nake so!" Shiru nayi ina taune bakina, kafin na cigaba da cewa. "Ina da nawa farin cikin, ina da an da nake buri, asalima babu wani muhallin da zan cusaka a raina don Allah ka kyale ni, ka nisance ni zan yi repaying abinda ka yi min ne, bin ka sa nayi da kuma abinda nake yi ina son na gyara alakata da mai babbar daki ne, Please ka je sai da safe kada ka yi kirkiro min wani tashin hankali." "Me yasa baki sona? Waye kike so da aurena?" Ya tambaye ni a tsawa ce, ban san lokacin da na juya zan wuce shi ba, ya fisgo ni da karfi ya mai da ni kan gadon na fadi, bina yayi ya danne hannayena bakiɗaya. "Gaya min waye shi? Waye shi? Me yasa baki sona, ban cancanci a soni ba ne?" Hawaye ne ya zubo ta gefen fuskana, ina me kawar da kaina na ce mishi. "Na gaya maka from the beginning bana sonka , and na kara repeating dinsa bana sonka, ka shafa min lafiya." Murmushi yayi ya haɗa fuskana da nashi yana faɗin.."Ok zan jira ki har ranar da zaki so ni!"
"Never!" Na faɗa ina kallon cikin idanunshi. "Mata biyu kake da shi why me? Ce maka aka yi kowacce mace irin matanka ne da zasu haukace akanka? Ina da buri ina da abinda nake so." Daga haka na fara ƙoƙarin ture shi, ai kuwa ya jibga min nauyinsa. "Tashi a kaina?" Na faɗa raina yana b'aci. "Idan naki fa?" Ya tambaye ni, "Zan maka ihu!" Murmushi yayi ya ce min. "Okay ki yi idan mai babbar daki ta zo zance mata. Kece kika ce min idan ban yi ba zaki tara min jama'a oya wuce ki yi wanka ina jiranki!" Ya sauka a kaina na shige ban daki, da sauri na wuce ban dakin ina haki, wanka nayi na fito lokacin da na shigo dakin baya ciki, kayan barci na saka, na daure kalaba din kaina sannan na koma na kwanta, ina mai lumshe idanuna. A hankali barci yayi gaba da ni. Sosai na fara barci, cikin barcin na ji kamar sanyi sanyi ko ana saka min ruwa a jikina wani irin tsoro ne ya kama ni ba dai wadancan abin ne suka dawo ba, bude ido nayi na kanshi ashe shine ya fito wanka daure da towel,yayi min rumfa ai ban san lokacin da na daka wani tsalle ba na fada can ina haki. Dariya yayi ya gyara wurin ya kwanta, Ban tab'a ganin dariyarshi haka ba, sai yau juyawa baya yayi ya ce min. "Kwanta zan miki tausa." "A'a ni dai!" Na faɗa ina tsaye a wurin, shi ma ganin naki kwanciya ya share ya dauki pillow ya kwanta a kasa, a hankali na kashe wutar dakin sannan na kwanta a hankali, har kusan karfe biyu ina juyi ban san lokacin da barci ya dauke ni ba, cikin barci ya ce min. "Kina ta juyi da mika kina bukatar wani abu ne?" Yunkurin tashi nayi ya mai dani tare da kamkame ni. "Kwanta, na saba kwanciya a jikin Matana." Ya fada yana kokarin matse ni, ai kuwa na yanka mishi cizo a damtse da sauri ya sake ni na sauka karshe haka na kwana a zaune ina jin yana dariya kasa-kasa musamman idan na dungura, tun asuba na farka ina dubawa na ga baya dakin.
Ban daki na shiga nayi wanka da alola, sannan na zo nayi sallah. Ina idarwa nayi addu'o'in da aka bani, sai da rana ya fara fitowa na kwanta bayan na sha magani tuni barci ya fara daukata, naji wayata tana ringing, ina jin matuƙar barci na ɗauka. "Me zan dauko miki ma?" "Ka shiga store akwai wani kwali pink zaka ga container ka dauko kwalin bakiɗaya ka kawo min. "Aikana kika yi?" "Hmm!" Na faɗa ina me gyara kwanciyata, barci yayi gaba da ni. Can wurin karfe tara ina kwance na ji ana shafa fuskana. Bude idanu nayi ina kallonshi. "Kin tashi?" Lumshe idanuna a karo na biyu, sannan na tashi zaune. Matsawa yayi na zuba ƙafafuwa na a kasa, sannan na tashi kan kafana, wani irin jiri ne ya kwashe ni da sauri ya riko ni. "Be careful!" Ya fada yana gyara min tsayuwata. A hankali na janye jikina daga gare shi, na nufi hanyar waje, a parlourn Mai Babbar daki na samu kwalin na shiga kitchen na zuba mishi kome sannan na dawo dauke da su a cikin jakar container din,na ajiye mishi. Kallona Aneesah tayi daga sama har kasa ta ce. "Munafuka nan kike ihun baki sonshi Uban me kike mishi!" Wani irin kallon banza na mata tare da jan tsaki, shine ta biyo ni ai kuwa sai gashi nan ya fito. "Me zaki mata?" "Tsaki tayi min." "Ina ruwanta da ni? Na shiga harkatan ta ne? Tana gidanta ina nawa meye matsala ta da ita da zata ce min munafuka? Na gaya miki ni bana sonshi, so what? Kayan gabar ne da zan ta bi ina yayyatawa ina sonshi? Ba a sonshi sai ki kashe ni." Rike kunnena yayi da karfi na kara fashewa da kuka ina jin zafi.."idan rigima ta hadaki da mutane, ni ban shiga ba ki daina shigar da ni, tow don baki sona mutuwa zan yi? Ki je can da halinki Allah yasa kada ki so ni." Ya suri jakar ya bar gidan bakiɗaya, duk da ni ban yi wani abu na tashin hankali ba, amma a ranar sai da mai babbar daki ta ci mutuncina tare da gaya min ni fa Ubana makashi ne, ranar wuni nayi ina kuka tare da jin kamar zuciya zata fashe da takaici. Wuni nayi ban fito ba, sannan na ki cin abincin da aka kawo min har abin ya dami Sailuba, don haka ina kwance Mai Babbar daki ta shigo da kunu ta zauna tana mika min. "Oya tashi ki sha!" Kauda kai nayi tare da cewa. "Na koshi." "Tashi nace!" Ta daka min tsawa, tashi nayi na fashe mata da kuka, ina me kauda kaina akan kunun, abin ya bata mamaki. "Ki sha nace kafin na kwad'a miki mari, tunda baki ji magana." Dauka nayi na rike a hannuna ina kuka, kiran wayarshi tayi tana faɗin. "Dama kasan haka take ka kawo min ita? Gaskiya gobe zata koma gidanka na gaji da magana." Ya ajiye min wayar ta fita. "Zainab!" Ya kira sunana. "Kin san zan shiga aiki ne? Please ki daina abinda kike yi." Kuka na kara cigaba da yi haka yayi ta magana har ya gaji ya kashe, can ya fara turo min sako. *Don Allah ki kula da kanki! Ki daina kuka rayuwar wanda zan mishi aiki yana hannun Allah yana hannunki, ki taimaka ki nutsu nayi mishi aiki in sha Allah ina hanya*
_Don Allah ku yi hakuri! In sha Allah ranar sallah xan kara muku ɗaya!_
08130269641
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Ina gani nayi banza da sakonshi domin na tsani kayan haushi, kuma na fahimci wani abu daya shine ita Mai Babbar daki akan Yaranta bata da wani katabus. Duk abinda Yaranta suke so shi take yi,haka yasa naki yarda da duk abinda take min, ina jin Aneesah ta kira Daulah a waya suka yi ta zagina, ban fito ba haka na zauna a dakin, ko sun zuga ta ne ina kwance Sailuba ta kawo abin abinci tana faɗin. "Tashi ki ci don Allah!" "Na koshi!" Na faɗa ina ƙara kwanciya. Haka ta fita can wurin karfe sha ɗaya ina jin wayata na kara na duba shi