Showing 78001 words to 81000 words out of 304445 words

Chapter 27 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

71

jikinshi yayi sanyi. Ina shiga parlourn Mai Babbar daki ta ce min. "Ke kam wacce iriyar aljana ce? Ana rabaki da sata sai ki koma sane!"
"Ummina Kaninta ne fa, dan wajen Turai Shaibah!" Juyawa tayi tana kallon Nady. "Dama baki san Kaninta ba ne, kika kira ni ta kawo kwarto gida." Kamar wacce iska zata dauka sama haka nake ji na, har na isa parlourna, zama nayi tare da jin kamar kome ya tsaya min a kaina, goge number Uwais nayi tare da block dinsa daga Whatsp da normal contacts dina. Na koma na kwanta a ranar haka na kwana bana cikin natsuwa abu kasan zan fara tuba ina istigifari..
**
Underworld.
"Har yanzu ka kasa cimma nasara ko Nafi'u, ni jinin Yarinyar nake so kai kuma ka mallaketa shine ake bukata gashi zaka zama wani abu amma dole sai da yarinyar jininku ya hadu wuri guda,kuyi tarayyar saduwa yadda ruwanka da guminka zasu hade da nata, yadda zaka samu kome ka saka a gaba. Domin haka ka cigaba da nimanta ko da jininta ne ka samo ko baka aureta ba zaka samu nasara da jininta.
"Rilwanu yarinyar nan tana da karfi, yadda tazo nan abin ba a magana amma sai dai akwai wani abu da yake bibiyarta, idan muka same ta ni da kai da Nafi'u zamu huta, don haka daga kai har Nafi'u ku cigaba da nimanta idan na samu hali zan taya ku,.ita ɗaya ce kawai zata mana yadda muke so."

Sun jima suna tattaunawa kafin suka bar duniyar suka dawo, gidan bakinshi ya wuce bayan yayi wanka da jinin jarirai. Can ma yana isa akwai wata matar auren da aka kawo mishi ita. Nan ya cigaba da abinda yake yi.
**
Yau ya kasance Asabar, da alamu me musu girki bai samu zuwa ba, sannan Mrs Doris ma haka, haka kawai nake son shan iska don haka na tako zan fita waje, wani irin sauti ko nace gurnani, haka nake ji ina matsowa parlourn Nady ina kara jin sautin, saidai kofarta da zan wuce, ban san lokacin da na sake salati da faɗin. "Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun." Da sauri na juya parlourna. Tare da shigewa uwar daki na rufe kofar na zauna a kasa dabas........ ...
Kun san weekend ne barka da yau)
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Ban tab'a ganin iskanci tsirara ba sai yau, Innalillahi wainnalihir rajoun, dukkansu sun ganni kuma mun yi ido hudu da su, ashe rashin kunyar tasu har ta kai haka. Can wata zuciya ta ce min. "Tow Ina ruwanki?" "Mtseew!" Kuma haka ne ina ruwana da zan damu can musu, na tattara su na watsar. Abin da nake bukata na bar gidan, na rabu da Uwais amma babban damuwata shine barin gidan, wanda ta haka ne kawai zai saka na samu nutsuwa. Duk yadda nayi abin yaki make Sense idan na kara wani abu Abba ne zai iya hukunta ni, gara na hakura tunda aka yi case din Tauhid ban kuma shiga harkansu ba, ita kanta Mai Babbar daki bata kuma wani magana ba, haka yasa na tattara su na watsar.
Da yamma ina zaune a harabar gidan ya fito, sanye da three quarter gashi da tsawo da ɗan kiba, amma a haka yake saka kayan irin wannan, dauke kai nayi ina karanta wani lissafin Wole Sonyinka, hankalina yayi nisa akan karatun. Muryan mata na ji na d'ago kai, Ilham da Ijlal, Ikram Iram. Gaishe shi suka yi Ilham da Ijlal suka shige ina wurin Ikram da Iram suka zo inda nake. "Me kike yi a nan?" Nuna musu book din nayi na cigaba da kallonsu da mamaki. "Me kuka zo yi?" "Kishiyarki ce bata da lafiya!" Kallonsu nayi irin kamar ya? Ganin irin kallon da nake musu Ikram ta ce min. "Ba dai baki sani ba?" Abin da na ga suna yi ne ya fado min a raina. Yake nayi na ce mata. "Ayya mantawa nayi." Na faɗa ina kokarin su manta da zancen. "Ok bari na shiga cikin kafin mu shigo!" Inji Ikram. Bayan tashinta Iram ta kalli bangaren da yake tsaye yana wani aiki. " Soyayya ake yi ne?" Murmushi nayi mata na cigaba da karatu. "Kin ga mishi an tab'a sayar dake a Dubai?" Sake littafin nayi cike da mamaki. Ina kallonta. "Ya kamata ki gaya mishi, domin boye irin wannan al'amarin wata rana zai zama wani abu na daban, idan ma ba zaki iya ba zan gaya mishi yadda zai fahimce ki!" Tashi tana me nufarshi. Wani irin tsoro ne ya kama ni na ce mata. "Zan gaya mishi." Cak ta tsaya bayan ta mishi magana ya d'ago kai yana kallona da nake zaune, domin na d'aga murya sosai. Yadda yake kallona yasa na dauke kai ina haɗe rai. Magana tayi mishi ya mike amma idanunsa yana kaina. Ban ga wani abin mamaki a tattare da su ba sai dai na san Iram bata da hankali kamar saniyar huda take da sauri na taso na same ta. "Ke ba zaki iya rufa min asiri ba ne? Meye ribarki idan kin gaya mishi? So what? Ko an gaya miki am afraid da ya sani ne? Mtseew!" Na ja tsaki zan wuce ta kara da cewa. "Wannan shine takardun shaida faruwar kome?" Kada ku yi tsammanin attention dinsa yana kanta ne, a'a yana kaina da na juya raina ya gama b'aci. "Sai me gaya mishi so what? Amma ki tuna ni yar uwarki ce ko mutuwa nayi bana tsammanin zaki same shi ta sauki gaya mishi an sayar dani da wanda ban sani ba!" Murmushi tayi ta kalle ni. "Ni ba maganar da muke ba kenan, good baby sister kin gaya mishi, magana nake da shi akan wani project da nake son yi aka ce na nimo sahalewan shi. " Ta fada tana murmushi, idanuna ne suka yi jajjur, juyawa nayi a fusace, na bar wurin ita burinta kenan ta yi sanadin da zan fada da kaina. Mika mata takardan yai ya ce mata. "Shine kike saka ta tonawa kanta asiri? Ba ke kika janyo ta zuwa Dubai din ba ne?" Murmushi tayi tana kallonshi. Ya hade rai kamar bai tab'a dariya ba abinda ya kara mishi wani irin kwarjini, yasa tayi baya kaɗan. "Ita matata ce, idan na ji wannan labarin ya fita!" Ya kuma kallon cikin idanunta da kyau. "Abinda Mamanki da Kawunki, da Cousins dinki da ke kanki kuke yi sai ya fita a video episode by episode!" Ya fada yana nad'e hannu yayi a kirjinshi. "Tell me now zaki iya shiru ko sai na fitar da bayanai masu kyau akanki?" Zubewa tayi kasa tare da faɗin. "In sha Allah ba zaka tab'a jin kome a bakina ba." Juyawa yayi ya koma yana aikinsa ya barta nan zube kamar kayan wanki. Dakyar ta mike tare da barin wurinsa.
Ina shiga daki na zauna shiru raina yana matuƙar b'aci, ina jin suna ta dariya a parlourn Nady ban kula abin ba kawai na zauna ne ina tunanin yadda zan yiwa Iram rashin mutunci.
Sai dare suka bar gidan, ita Ijlah din har kitchen dina ta shigo tana kalle-kalle, sannan ta shigo parlourna, anan ta sake bakinta tana kallon kome. Ina zaune ban ce musu kome ba, sannan suka fita.
"Ikram kayan Ikhlas yafi kome d'aga min hankali!" "Inji Ijlal din. "Hmm don baki shiga ɗakinta ba ma kenan. Wai kayan Iram aka bata don ita aka yiwa sayayyar." Shiru Iram tayi tana kallon hanya. "Iram baki ce kome ba." "Tow me zance?" Ta tambaye su. "Kin ce zaki saka a sallami Ikhlas kafin na shigo kuma baki ce kome ba " tana tuki amma zuciyarta yana rawa ta ce musu. "Da farko ki fara samun kan Prince idan aka same shi ita Ikhlas prey dina ce zan ji da kome." "Yawwa Iram!" Daga haka ta kai kowanne gidansu sannan ta wuce.
Ban san me yake faruwa ba, don na kula kwana biyu basa zaman gidan bakiɗayansu nima haka makaranta nake zuwa na dawo da yamma, wani lokacin da safe ko da rana, ya danganta da lokacin da nake da shi, shi kuwa tunda Iram ta yi sanadin fadan abinda ya faru na daina yarda muna haɗuwa. Ranar da na cika wata uku cib, ranar ya kai ni gida daddare. Abba ya min fada da nasiha wanda ya kawo min kissan matan annabawa har zuwa kan manyan bayin Allah, kai karewa babu kissar da ta fi kashe min jiki kamar kissan Nana Fadimatu, da irin gwagwarmayar da ta sha, da yadda ta nime sauki amma Mahaifinta ya gaya mata haka ba zai yiwu ba sai dai idan zata zabi wani abu. "Abba kasan bana sonshi?" Na faɗa ina kuka, "ka yi min hakuri na koyi yadda zan zauna da yan gidan, Abba nasan ban kyauta ba, amma Abba ni zama da ahalin ne bana so! Ka bashi hakuri zan je har wurin Mai Babbar daki na bata hakuri. Abba ka yi hakuri na daina daga yau."
"Ban miki auren da shi don na cutar dake ba, amma kina da lokacin da zaki koyawa kanki zama da shi koda baki sonshi. And ina kara baki hakuri goma juma'a za a daura aurensa da yar gidan Yariman Gabas." D'ago kai nayi ina kallonshi. "Wannan ba wani abu ba ne, domin bai dame ni ba." "Saboda baki son shi ko?" D'ago kai nayi ina kallon Abba a karo na babu adadi na ce mishi. "Ba haka bane!" "Haka ne Zainab kana kishin abinda kake so ne, sannan baka damu da kome zaka yi akansa ba, na ji dadin da kuka nuna bai dame ki ba, duk da nasan wata rana zai dame ki. Kiyi hakuri kiyi hakuri kishi gaskiya ne." Ban san hakurin da Abba yake bani ba, amma na shiga wurin Maluma ko kula ni bata yi ba, abu daya ta gaya min. "Duk ranar da kika kashe aurenki tow ki nemi wata Uwar!" Daga haka ta bar ni tsaye a parlourn. Wurin Umma na nufa tayi min fada da nasiha sannan ta dauko turaren zamani da na wuta ta ce na kaiwa Mai Babbar daki. Gyada kai nayi na amsa ina godiya, "bani na saya ba ni wancan na saya wannan mai yawan Maluma ce ta saya." Allah ya saka da alkhairi!" Ka furta.
Haka na fito muka nufi gida, a motar ya daura min katin daurin auren, a hankali na ture gefe ban ce mishi cikanka ba, har zamu wuce nace mishi.."Ga sakon Mai Babbar daki!" Na faɗa mishi, ba musu ya wuce da ni kofar gabas, nan na samu an cika a gidan ana ta hidima. Yana gaba rike da kayan muka shiga na gaishe da yan parlourn ya min jagora har uwar dakinta. Na samu tana tare da wasu yan uwanta da Aneesa da Daulah, ganin tare muke da shi, yasa suka gaishe shi suka fita, gabanta na nufa na zauna akan gwiwata. Kai na a sunkuye na fara magana cikin nutsuwa. "Umminmu!" Zuba min idanu tayi na tura mata kayan muryata tana rawa na ce mata. "Kiyi hakuri da abinda nayi ta yi abaya, ban yi don na rena ki sai don nayi ne don ki saka ya rabu da ni, amma wallahi ban yi don na zubar miki da darajarki ba, don Allah ki yi hakuri ki yafe min." Na faɗa ina shashekar kuka. "Zan zauna da shi ba zan kara yin abinda zaki ji ba dad'i ba, amma don Allah ki yi hakuri ba zan kara ba." Na faɗa ina kuka. "Ya wuce!" Da sauri na d'ago kallona tayi tana murmushi. "Ya wuce amma ba zan tab'a sonki ba, kiyi hakuri ni Uwa ce dole na rike ki a raina koda zan manta ba zan tab'a sonki, ga kayan fadar kishi can naki ne da na Nadiyyah itama da yake mahaukaciya ce tayi yaji ko? Hmm idan ma wani abu kika shirya don aurenshi ki ajiye. Don babu fashi fa." Wai ya zan mata bayanin ni ko kaɗan bana sonshi, sannan bana kaunar wani abu ya dame ni akansa tura mata turaren nayi nace mata.."Gashi inji Maluma!" "Ki je da shi na gode!" Ta fada tana cigaba da aikinta, yana tsaye bai ce kome ba, a hankali na mike tare da mata sai da safe ta ce min. "Zo ki dauka!" Ba musu na koma na dauka, "kin ci Abinci?" Ta tambaye ni, juyawa nayi na ce mata. "Eh naci a gidanmu!" Daga haka na mata sallama na fita, ina fita Parlourn na samu kannensa ne,.sai hira suke suna ganina suka kwashe da dariya. "Gobe za a daura, jibi zuwa gata za a taru domin tabbatar da budurwa ya kwana da ita." "Ki ce duk wadancan da aka tara holoko ne!" Suka kara kwashe da dariya. "Eh mana mace ake aura ba zawarawa ba." Wata ta faɗa. "Waye ya gaya muku matana zawarawa ne?" Shiru suka yi jin muryanshi akansu. "Tambayarku nake?" Ya daka musu tsawa da yasa suka fara bashi hakuri. "Tambayarku nake a ina kuka ji labarin matana zawarawa ne?" Sai suka yi shiru. Tsaki yayi ya koma daki, ya zauna ya ce. "Idan an daura aure bana bukatar kome a kawo ta bangarenta itama ta zauna, bana bukatar ganin kowa a gidana idan ba alkhiari zai kawo su ba, bana bukata." "Amma ko wuni ba za a yi ba." "Tai a gidansu" sanin cewa kafin ta shawo kansa ba karamin aiki ta sha ba, yasa ya ce mishi. "Shi kenan Allah ya kai mu!" Ta fada a hankali, don haka ya fita daga dakin har lokacin ina tsaye a parlourn amsar kayan yayi muka fita, wani irin abu nake ji na rasa gane b'acin rai ne ko me? Maganar da suka gaya min yana tsaye a raina. Don haka da muka isa gidan, daukar kayana nayi na wuce na barshi a wajen.

Tunda na shiga daki na kwanta, nake juyi da asuba sai da ya buga min kofa, sannan ya tafi massalaci, nima haka ina sallah kitchen na wuce na hada abun karyawa, sai yanzu na lura da sauyin da gidan ya samu, duk da cikin gida gida ne, amma bangarensa yana can, wurin Nadiya da ni kusan wuri guda ne, sai wani dakin da yake gefen nashi shima ciki da parlour ne da dakuna biyu kamar nawa da na Nadiyyah. Sannan kwanaki nan ban tab'a zuwa na samu kowa ba. Amma wani lokaci nakan hango tarkace a wurin trash dinmu alamar an bude sabon abu. Itama da nata kitchen din a wurin, ni dai ban sani ba sai da na gama kome na shirya zan fita makaranta na ga Aneesa da Daulah sun shigo gidan, ko sun tsammanin zan kyale su idan suka takale ni suka fara min maganar banza. "Yawwa zamu kowa wata wacce zata goge miki hadda domin muna son a nuna miki ita ce matar gidan da zata haifa mishi Yara." "Mtseew! Tow ni ina ruwana? Nadiya ya dace ku gayawa domin ita ta aure shi tunda farin sawunsa. Ni fa dan uwanku baya gabana biyayya nake yi amma da zai ce min Zainab Junaid Gobir je ki na sake ki, wallahi rawa zan fara har da gayyato masu DJ, asha bidiri."
"Ke wacce irin mace ce da baki kishin kanki balle Mijinki!" Inji wata mata da take jin mu a cikin masu aikin jere. Murmushi nayi na ce mata. "Sai da so ake kishi, idan babu so gaya min me za ayi kishin? Ni fa bana kwaina sai da zakara, zaman biyayya zan yi ba zaman kishin mata ba." Ina fadar haka na juya na fita abuna, murmushi wata mata tayi ta ce musu. "Itama Auren hadin ce?" "Eh yar gidan Maluma Hajara ce bata da kunya bata ganin kowa da gashi." Inji Hadiza karama. "Ta huta domin bata damu ba balle ayi ta dambe da ita, sannan sai ta gadama zata shiga harkan yan gidan haka yana nufin ko me za ayi baya gabanta!" Murmushi tayi tana me wuce su. "Shi ya dace ya koya mata yadda zata so shi, idan ta fara sonshi shima aka yi dacen yana sonta sauran matan sai sun haukace har da yar mu domin duk da yasan bata son shi ya zauna da ita guess idan ya fara sonta itama ta fara fa?"

"Mu da muke fatan ta bar gidan nan ina zamu yarda ayi soyayya!" Suka fada suna kallon juna.
-- karfe daya na dawo na samu an taru a gidan, ashe yana gidan, domin biyu da rabi za a daura auren, na nufi wurina bayan na gaida yan bikin. Ina jin wata cikin yan bikin tana faɗin. "Ita ce ta biyun ta farin tana can garinsu tayi yaji!" "Ita wannan me ya hanata yajin? Da sun watse Ijlal tayi yadda take so kafin su dawo. "Tow ai ita wannan bata son zaman auren don haka ba zai dame ta ba." "Ai ikon Allah ashe dama har yau akwai matan da idan basu son zaman aure basu damuwa da kome, har na shige ban daina jin maganarsu ba, a ina shiga na kunna wutar parlourn "innalillahi!" Na faɗa ina me dafe kirjina. D'ago kai yayi ya kalle ni yana kwance. A raina nace duk fadin gidan nan ya rasa inda zai kwanta sai parlourna. Kallonshi nayi naga yana zufa. Wuce shi nayi na nufi dakina, na cire kaya, zan shiga ban daki domin na daura towel a a jikina, shigowa yayi a yadda yake tafiya a hankali yasa na fahimci akwai wani abu da yake damunsa. Baya nayi ina me kare kirjina. "Barni da lafiya!" Ya fada a hankali yana komowa gadon ya kwanta. "Tow shine ba zaka gidanku ba ni ya zan yi jinyarka?" Yadda ya kwanta ya sani daukar hijab dina na wuce ban daki na watsa ruwa saboda zafin da ake yi, na fito na dauki kayana, na fita zuwa daya dakin na shirya. Zuwa nayi gaban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login