Showing 114001 words to 117000 words out of 304445 words
shigo dakin kin zauna Kamar wacce aka miki wani abu!" Kwalkwal nayi da idanuna. "Kada ki min kuka, idan Mijinki ya zo sai ki mishi ni dai kada ki tara min mutane !" Ya juya ta fita na ce mata.."Ummi idan yazo zan yi kukan kin amince?" "Kallona tayi tana faɗin.."yaushe zaki girma?" Dariya nayi ina kifa kaina. Girgiza kai tayi tana faɗin. "Ba zaki daura min cutar damu ba." Ta fita shigowar Daularh da abinci ya sani jan stool na ajiye na fara ci ina kallon yadda take ya tsina fuska. "Ke!" Kallonta nayi , can sai ga dan wurin Aneesah yana shigowa ya kwabar da abincin bakiɗaya kamar wanda aka aiko shi. Kamar nayi kuka haka nake kallon abincin.."yanzu an kyauta min?" Na kalli abincin kawai na kwashe na tattara a tiren na fito waje lokacin ya shigo gidan bayan an tashi taron ya kalle ni, ya ce min.."kin ci abinci?" Nuna mishi tiren nayi ina jin kamar nayi kuka na ce mishi.."ya zubar min da shi." Rike baki yayi yana daukar Yaron ya ce min. "Zo muje eatry!" " Na juyawa da sauri na nufi ciki na dauki mayafina da wayata da pose dina na tawo cikin mutane na cewa mai babbar daki. Nayi kasa da muryata bakiɗaya ta bani attention dinta"Bari na raka shi!" Juyowa tayi tana faɗin. "Daga ke har shi baku jin magana, sai ki tafi ai!" Yake nayi, na wuce ina dariya a raina abinda na fahimta mai babbar daki ita fa akan Yaranta bata da wani makiyi kuma kowa masoyinta ne, tura baki nayi lokacin da na tuna bana sonshi. Haka kawai Abba yasa ni zubar da mutunncina, kamar yasan abinda nake tunani ya ce min. "Sorry kina ta pretending akan abinda bai zama dole akanki ba ko?" Da wutsiyar idanun na kalle shi ai kuwa muka hada idanu fuskewa nayi na cigaba da kallon wani wurin har muka shiga mota, shi da faruq suna gaba ina baya. "Kina jin yunwa ko?" Ya tambaye ni, "eh!" Na fada a takaice, shiru muka yi wakar taushi na dan kwairo yana tashi a motar, saita glass din gefenshi yayi yana kallon yadda nake latsa waya. "Me yasa kika sallami Brandy?" Daga shi har Faruq zuwa min idanu suka yi suna jiran mai zance. "Gani nayi ya girma da zama kuku bayan, dukkanmu mata ne kowacce tayiwa kanta girki and ba muharramunmu ba ne!" Ganin zan ja mishi aya da hadisi sai gashi ya ce min. "Sayyadah maganarki gaskiya ce!" Inji Faruq, kallonshi nayi shima ya d'aga min gira yayi, hararansa nayi na murgud'a bakina. Lumshe idanu yayi yana girgiza kai. Dauke kai nayi ina tura baki, ban san ya aka yi ba sai ji nayi ya kama bakina da hannunsa, kwalkwal da idanuna nayi ina kallonshi. "Murmushi yayi ya ce. "Kin kora min Mr Brandy Kuma baki bami wani abincin ba!" Ya fada yana kallon kwayar idanuna, dauke kai nayi saboda ina jin tasirin kallonshi a jikina haka yasa ni sunkuyar da kaina cikin matsanancin kunya ce ta kama ni, naki yarda na kalle shi, wannan shine karon farko da naji kunyar yadda yake min mad'e amma wani bangare na zuciyata ya tuna min. *Ke mutimin da bakya so shine kike mishi dariya idan ya fara tunanin kina sonshi ne fa?" Dauke kai nayi ina haɗe rai, domin kuwa haka kawai naji raina yana ƙara b'aci. Wani shagon abinci ya kai mu, tun kafin mu isa akan san da zuwanmu.
Ashe bayan tafiyarmu, faduwa Ijlal tayi garin ta biyo mu, aka kuwa yi ca a kanta bin nima ya samu. Ai kuwa aka nufi asibiti da ita. Duk da abin ba wani abu ba ne amma yadda ake ririta lamarin zai ka ɗauka wani abu ne haka yasa aka taru zuwa asibiti. Bakiɗaya ahalin Yayari suka cika asibitin, an kira Salmanu Faris ya kai sau goma amma kafin ya ɗauka.
--
Yadda ake kiranshi yasa shi dauka ya fito bayan ya fara cin abincin, naso na tsayar da cin abincin amma sai na cigaba can da na ga bai dawo ba na juya sai naga shima ni yake kallo, yana magana a hankali. Ajiye cokalin nayi ina kallonshi. Fuskata dauke da tambaya, shigowa yayi ya zauna yana murmushi. "Ci a hankali!" Murmushi nayi ina wasa da abincin, "yarinyar nan bata da lafiya ne!" "Ya Salam." Na ture abincin ina me mikewa, rike hannuna yayi ya ce min. "Zauna ki ci!" Haka na zauna ina ci ina kallonshi, ajiye cokalin nayi na goge bakina
.."Na koshi!" Daukar pose dina yayi ya fita, sannan ya wuce muka nufi asibitin. A hanyar asibiti, na kalli wurin da ake sayar da ice cream. "Kina so ne?" Lashe baki nayi ina gyad'a kai nayi. "Mu koma wurin can!" Ya nuna mishi, shan kwana yayi ya je kofar ya tsaya. "Flavor?" "Mint chocolate!" "Brush zaki yi?" Sai yanzu na kara fahimtar shi mutum ne mai matuƙar tsokana. "Wai ta fadi ne?" "Allah ya sawwaka!" Na faɗa ƙoƙarin share zancen, ni yarinyar ai ta bani mamaki..
Faruq na shigowa ya ja motar muka nufi asibiti, ba wani babban al'amari ba ne fa domin mun samu ana ta hira da ita sai bandeji da aka daure kafar da shi, amma tana ganinsa ta fara narkewa tana son yin rashin mutunci, ta hanyar rigima.. nima sai na kauda kaina tare da danna wayata, tunda na ji tana faɗin ya duba ciwon naga yan uwanta sun fara fita nima mikewa nayi zan fita ya ce min. "Baki ji ba!" Juyawa nayi ina kallonshi, "ina zaki?" "Zan je Faruq ya ajiye ni a gida." Kallon idanuna yayi ya ce min. "Ok go for yourself!" Yadda yayi maganar yasa ni fahimtar kamar a fusace yayi maganar, don haka na koma na zauna. Ganin haka yasa tayi ta min abu tare da yi mishi abubuwan da ya biye mata, suka yi ta yi kaina a sunkuye. Ni dai ban san kome ba, but naji ba dad'i yadda yake abu akan idanuna. “please ka kai ni sai ka dawo!" Da mamaki a fuskarshi ya kalle ni, "ki je wurin faruq ya kai ki idan ba zaki iya jirana ba." Lashe bakina nayi kafin na juya na fita, cak ya tsaya sai kuma ya kasa yin kome ya zama kamar abin da take mishi yana gundurarsa, haka ya mike yana faɗin. "Zan tafi sai gobe!" "Ok!" Ta fada tana matse idanunta. Fitowa yayi don yasan Faruq ba zai tab'a tafiya ba tare da ya jira shi ba, nima ina cikin motar ya shigo ya motar, gida muka nufa kamar ranshi a b'ace yake haka da muka isa daki na shiga nayi sallah, ina idarwa naga key ɗin bangarena, na wuce na gaji kayana na kwashe na nufi bangarena, su ci kansu. Tunda na shiga na ga ko ina tsaf-tsaf. Dakina na wuce na cire kaya na saka masu sauki sannan na kwashe ice cream din na kai firj don yayi melt, sannan na jefa dan wake, ina gamawa a kitchen din na ci ka wanke flat ɗin.
Duk yadda ya so ya ga fuskata naki, haka na kwana, washi gari ma na wuce makaranta ban kara yarda mun hadu ba. Har aka sallame ta a daren ina jin suna fada da Nady, ban yarda na kasa barci nayi barci sosai, washi gari ina da exam na fita abuna can dayawarsu.
A hankali watan azumi ya gabato.......
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 37
Ban san ya aka yi ba, ni dai a bangarena ko girki bana yi, amma ashe haka yana mishi zafi, yadda na watsar da lamarinsa shi da Matanshi, abin nasu da har ya kai gaban Mai Babbar daki, ita kanta da tayi musu sulhu sai da ta tuhume shi da laifin rashin kai mata abinci, abinka da babban gida wanda ake jira ayi, a lokacin rasa ta cewa yayi domin rigimar Nady da Ijlal ne ya kai su har gaban mai babbar daki, sannan yadda Nadiya take ihu da masifa yasa kowa yasan me ya kawo haka itama Ijlal, cikin fushi mai babbar daki ta ce su b'ace mata a gaba bakiɗaya su wuce gidan iyayensu domin ita babu macen da zata hana danta sukuni, wurin karfe uku na yamma na dawo a gajiye na same shi kwal a cikin gidan kamar mayye, tunda nayi sallama na wuce dakuna na bude na shiga na ajiye kayan hannuna sannan na wuce, ban daki nayi alolan sallah la'asar, don yin karfe daya muka shiga sai yanzu muka fito. Shigowa yayi dakin ya ga na fito daga ban daki, kallo daya yayi min yana zaune a bakin gadon na dauke kai na shimfida abin sallah, ganin ban kula shi ba har na tashi sallah sai abin ya dame shi , ina sallah wayata ta fara ringing da yaƙe a jaka na bar wayar sai gashi ya dauko ya ciro wayar, ganin yayi na rubuta My Everything, sai da ya kalli inda nake, haka bai dauka ba har wayar ya tsinke, aka.sake kiran anan ne ya dauki lokacin ina zaman tahiyya, yadda ya dauki wayar yasa na fahimci Abba ne, sannan shima ya kama girmama wanda yake wayar. Sai gashi yana gyata karya, lokacin da na idar ya kalle ni cikin nutsuwa don har sun yi sallama. "Malam Junaid ne ya kira!" Ya ajiye min wayar dauka nayi na kalle shi, kafin na ce mishi. "Idan bai ci arzikin Babanki ya kira ba, ya ci arzikin abokin Abbanka ko?" Ina fadar haka na dauke wayata na cigaba da addu'a sai da na idar sannan na koma kan wayar har lokacin yana zaune a wurin bai tashi ba.. kiran Abba nayi don na ga number shi ta gida ne, ina dauka na shiga ihu don ya ce min ya dawo dazun kuma ya kira wayar a kashe ga sako nan ya bada Tauhid ya kawo min, nayi godiya kamar Yaya.
Sannan muka yi sallama na barshi a dakin, ina cikin aiki Tauhid ya iso shi ya shigo da Tauhid din ya kawo min kayan tsaraba, kifi babban kwali, kai kaya kala-kala gasu nan,.haka na wuce da su store na, na turawa Tauhid dubu ashirin don nasan halinsa, shirya kayana nayi sannan na wuce na cigaba da aiki dama tuwo zan yi na dauko babban kifi na fasa a miyar tuni na tashi miyar da gidan, da nayi tuwon mai babbar da na kaiwa Sarkin kofa domin ya kai mata sai na shi, a bakin shi na ji labarin su Nady basu nan dukkansu sun bar gidan, Allah ya kyauta nayi sannan na koma ina shiga na same shi ya daura ɗaya kan daya sannan ya zuba biyu son ranshi ya kwashe kifin, ya zauna yana ci kamar shi ya dafa min, tsayawa nayi ina kallonshi. "Gaskiya kada a kara min haka" na fada ina wucewa na samu saura Malmala biyu kacal ya bar min ban san lokacin da hawaye ya cika min idanun ba, gashi ana kiran sallah haka na wuce nayi sallah da wanka, don fushi nake da shi saboda abinda yayi min a gaban Ijlal. Bayan na fito na samu shima ya tafi massalaci amma wani ikon Allah ya dauke flat din ya kai kitchen, ya wanke kamar ba shi ya ci abinci ba, sai yar rubutu ya bar min a samar kular.
_Please ki bar min abincin nan zan biya ina son ayi min dumammenshi ne!_ lallai ma wato ni bani da rabo a cikin abincin da zan girka da hannuna, daura ruwan zafi nayi na shiga duba garin semo da garin dawa nazo na tankade ana kiran sallah, nayi talge na wuce na yi sallah ina idarwa sai da nayi addu'a sannan na fito na tuka tuwon da garin semo, na fito na gyara wuce nayi sallah isha, ina sallah naji ana ta shewa ashe Ijlal ce suka shigo ake ta shewa. Daga auren dai a sani na sun yi rigima tana zuwa gida na uku kenan. Ko lokacin da na kwashe abincina, ban leka su ba, na kwashe abincin na wuce daki, wurin ƙarfe takwas sai gashi tare da Nady, ina babban parlour ina kallon wani film. Kallo daya na musu sannan aka yi sallah na amsa daga nan na cigaba da abinda nake. "Ke !" D'ago kai nayi na kalle ta , wato Nady bata da hankali amma ganin irin kallon da na mata yasa ta shiga hankalinta. "Ke bakya fada da mijinki ne?" Murmushi nayi shi kanshi jira yake na mishi kwabar da na saba sai na fasa tare da cewa. "Ki tambaye shi Mijinki, ko Bama fada?" Daga haka na cigaba da kallona, sai da ta shiga sai ga shi ya fito. "Na zata zaki ce bakya sona ne." "Dama na gaya maka ina sonka ne?" Na tambaye shi ina gyara zamana, "Wai me yasa bakya sona?" Kallon shi nayi kafin na cigaba da kallona don haushi kawai nake ji, "Ina barcina?" Dauke kai nayi ina cigaba da kallona can dai na gaji na mike tare da nufar kitchen na kawo mishi abincin sannan na cigaba da kallona, fitowar Ijlal tayi turus ganin ta fada mishi jollop din taliya, ya sha kayan dad'i amma ta fito ta samu yana cin wani abu yasa abin ya mata mugun ciwo, bata san lokacin da ta koma ajiye abincinta kan kujerar parlourn ta yi wurgi da flat din tuwon gabanshi, kallo daya yayi mata, sannan ya bi tuwon da idanu, ni kaina ban ji dadi ba, amma sai na share domin Matarshi ce sun fi kusa.."bakar munafika kawai ki kyale min mijina shine zaki zuba mishi abinci ranar girkina?" "Kwadayin Mijinki!" Na faɗa ina tattara kayana. Sannan na barshi a parlourn sun gyara basu gyara na Allah dai ya kyauta. Haka na wuce kitchen na zubar da fasashen flat dina, ina kallon yadda yake a cikin kwandon shara wannan shine karo na biyu da ta min b'arna. Fitowa nayi na wuce dakina bayan na rufe kitchen din.
Washi gari bamu da exam, haka yasa na sha aiki saboda azumi Umma ce ta kara kirana tana tambayata shirin azumi na gaya mata abinda nayi, murmushi tayi ya ce za a kawo min kome. Nan da kwana biyu ana gobe azumi kenan, da yake yana tsaye yaji wayar da muke sai ya shigo parlourn ina da idar da waya ya zauna cikin nutsuwa. "Zainab!" Kallonshi nayi na dauke kai ina cigaba da abinda nake. " "Ina son ki lissafa min abin da kike bukata na azumin da za a fara." Kallonshi nayi kafin na ce mishi.."ka tambayi matanka mana ni kada ka janyo min jakar tsaba a fasa min kayan da iyayena suka sha wuyar saya min." Shiru yayi kafin ya ce min. "Kin kori Brandy waye zai na min abinci?" "Ka dawo da shi idan haka kuskure ne ai ba laifi ba ne." Na faɗa ina kokarin mikewa ya ce min. "Ban gama ba." Zama nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Don Allah ka kyale ni idan baka da abin fada ina da ita ni!" Na wuce abina. "Ina son abincin shan ruwa ne domin cikin azumin nan ina da appointments na aikin mutane, ina bukatar abincin sahur da na bude baki." "Ai kana da mata sai ka saka su." "Wai meye matsalarki ce?" Ya daka min tsawa da yasa nayi shiru. Ganin yadda na tsaya a wuri guda, ya tako yana faɗin. "Idan su sun mai da ni mara daraja Why ba zan yi daraja a idanunki ba? Why Zainab kike min haka? I thought kaf duniya kin fi kowa fahimtatta ashe kuskurena ne? Me nayi miki da zafi da bakya son saurarona? Ki bani damar waye ni a gabanki, amma kin ki ko da yaushe kina guduna. Me nayi miki? Shi kenan naji kin san ba zaki iya ɗaukar nauyin ciyar da ni ba me yasa kika kora min Mr Brandy?" Sai yau naga illar koran bawan Allah nan ko wata ba a yi ba Dan Mai babbar daki yana jin haushina. "Hatta mai Babbar daki ta fahimci akwai abinda nayi miki baki yin girki ki kai mata." Sai na tsinci kaina da fashewa da kuka. "Tow ni daya ce Mace a gidan nan? Ina sai dai ka ci ka kuma yi min wulakanci a gabansu, kai ka sani na raka ka duba Ijlal amma ka kama yin abinda bai dace ba, sau daya da nace xan fita me yasa baka bar ni ba, yanzu kazo kana jin hausuina saboda kawai na fita sabgarka!" Kura min idanun yayi kafin ya haɗe rai. "Matata ce, kuma ina da ikon nayi yadda nake so da Matata, sannan akan me zaki ji babu dad'i ke da kika ce bakya sona? Tow sai me don nayi abinda zai dauke min tunanin wasu matan banza." Yadda yayi maganar tare da nunawa bai yi kome ba, ya kara min ciwo. "Shi kenan tunda haka ka zab'a sai mu zuba ni da kai wanda ya ga ba riba ya janye kalamansa."
"Ok ni nawa mai sauki ne, zan tafi gidan Malam Junaid na dinga cin abincin a can!" Cak naji kukan ya tsaya min na zuba mishi idanu. "Me yasa ka rena min iyayena?" Murmushi yayi sannan ya juya zai fita na ce mishi. "Mahaifina kake kira Malam Junaid, Why ka kira shi Junaid, tunda baka san darajar iyaye ba, kuma wallahi billahi azim matukar kace zaka rena min iyayena ba zan yarda ba." Juyowa yayi a fusace sai da na razana amma ban nuna mishi ba. "Kika ce me? Da kika yiwa Mai Babbar daki rashin kunya na samu wani cikin gidanku na gaya mishi? Iyeee wato ni dan iska?" Kura mishi idanu nayi na ce mishi. "Mu zuba ni da kai wanda ya fasa ya rena iyayensa!" Na juya zan wuce dakina ya fisgo ni.