Showing 153001 words to 156000 words out of 304445 words

Chapter 52 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

52

tsawon shekara daya, yana mutuwa aka nad'a Yarima Shago a matsayin sabon Sarkin Zanzibara, bayan shago yana da kanne biyu dukkansu maza ne, Yarima Balarabe da Yarima Auta, wanda ya kasance cikin laluran rashin lafiya tun haihuwarshi, Yarima Balarabe yana tare da Sarki shago ba dare ba rana domin wani irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninsu maza, haka yasa tunda Shago ya amshi Sarautar Balarabe ke zaune a gefenshi, sannan shima Yarima Auta a yadda Bokayan Ajuji ta fada ai aljanun da suke bautawa masarautar ne suka tab'a shi don haka babu wani zancen ayi mishi jinya ta hana ne zasu bada damar sadaukarwa.


A shekaru goma sha takwas da aka bashi mulki Shago yayi nasara a yake-yake saba'in da takwas, a wannan shekarun nashi ya murkushe masu niman zame mishi matsala, Shago shi mutum ne mai matukar son tafiye-tafiye izuwa sauran ƙasashen duniya na ruwa da na sahara, haka yasa mulkinsa yake cike da mamaki da al'ajabi, sannan gefe guda shi din mafarauci ne da yake shiga Daji domin anranga da manun dawa. A shekarunsa ashirin a duniya ya hadu da Aojana ya ga Babban mai bawa Sarki shawara, a lokacin Aojana ta haukace ta rikice tana sonshi, bugun farko da aka gabatarwa Sarauniya Amaza ta ce sai ta tuntube shi, bayan yayi wani tafiya ya dawo ya sauka a wurinta, yana cin abinci tare da Balarabe, Auta yana gefensu yana ta hidimar haukarshi. Mahaifiyarsu ta kalle shi kasancewar tafi duk matan sarakunan Zanzabira jimawa domin dayawansu mutuwa suke, ita kuma tayi tsawon rai. Cikin kauna mai yawan gaske ta ce mishi. "Mai baka shawara na musamman Dan Tani ya ce yana gabatar da yarshi Aojanah!" Kallon Mahaifiyarshi yayi sosai kafin ya sake murmushi ya ce mata. "Macen da take sona hatsari ce ga rayuwata, haka Ajuji ta gaya min gara wacce ni zan mata so na hakika amma ita zata iya zame min matsala!" Ya cigaba da cin abincin. "Idan da zata zame maka matsala da mahaifinta ya fara zama matsala, Dan nan ina kira a gare ka da kayi aure mutane sai mamaki suke taya har yau baka ajiye mace ba, shin kana da wata alaƙa da iskokai ne?" Dariya yayi yana kallon Balarabe. "Ko ɗaya Ranki shi dade, macen da nake so ba haife ta a cikin masarautar nan ba, Haka Ajuji ta gaya min shi yasa nake fita nimanta, ka ga Balarabe na koyi wata yare ma sannan idan aka kwana biyu wasu mutane dasu shigo domin ganin masarautar mu da irin cigaba da muke da ita." "Da gaske Yaya?" Gyada mishi kai yayi ya fito mishi da wasu fatar bauna da aka yi rubutun Arabic da bakar tawada mai kyali. "Yaya kana ganin idan aka cigaba da haka zaka asamu cigaba ?" Lumshe idanun yayi ya ce mishi. "Kwarai da gaske!" Daga haka ya tsame hannunsa daga cikin abincin ya koma gefe yana duba wasu abubuwan da ya sayo ya mikawa Sarauniya Amaza. Amsa tayi ta saka mishi albarka.

Aojana ta matsala sosai, domin tana bibiyar Sarki shago shi kuma mutum ne mai matukar jan aji da sanin ciwon kai shi har mamaki yake yadda Iyayen Yan mata suke niman ya auri Yaransu amma yana ki don gani ake kamar aljanu sun aure shi tunda a tarihin masarautar akwai wani sarki da har ya mutu bai haihu ba, ashe yana da Yara da wata aljanna ce amma shi bai tab'a fadawa kowa ba, sai bayan an kashe shi domin a gaji sarautar ne sai a sirrin makasan ya tonu domin aljanar ta bi hakkin Mijinta. Haka yasa ake zargin Sarki Shago.
Dakyar da sudin goshi yayi auri Aojanah, sai dai duk yadda ake saka ran auren zai yi albarka da abin mamaki, sai haka bar faru ba domin dai Aojanah tana shiga a daren farko da yazo mata, ba karamin biki aka yi ba domin kunnen kowa yana sauraren daren farkon Sarki Shago, daren da aka kwana ana biki an rubuta a tarihi daren mai daraja ce. Sannan ana yawan tunawa da daren don a cikin daren aka yi ta bin gidajen talakawa ana raba musu shatara na arziki musamman iyayen Aojanah, bayan tsawon lokaci rashin zaman Sarki Shago ya saka basu shaku da Matanshi ba, don yaki bata wannan damar, sai ya dauke ta aba ce ta biyar bukatarshi idan ya gama zai barta nan bai damu da ta ji dadi ko bata ji ba. Kwatsam sai gata da ciki a karon farko da yaji dad'i har ya kasa boye farin cikinsa sai dai daga ɓangaren iyayenta zuwa ga Ajuji fata suke ta haifi ɗa namiji, wanda haka ya saka mata lallai a ranta dole ne ta haifi namiji tunda ko ina ana so, duk da Sarauniya Amaza tafi kowa murna da farin ciki amma kuma jikinta baya bata namiji za a haifa. Amma ta yi shiru musamman ita da irin wannan abin ya faru da ita sai take ganin b'ata lokaci ne zama tayi ta dakon wahalar da ba karewa zai yi ba.

Haka akayi ta kula da cikin, wannan cikin sai da aka saka mishi wani irin tsaro da ko kukan tsuntsu aka ji Mai martaba ya ce a kashe shi, haka yasa hatta tsuntsaye da sauran dabbobi suke tsoron giftawa ta fada. A hankali har cikin ya isa haihuwa daga yadda ake nakudar zuwa Bokanya Ajuji yasa aka fara ganin akwai haske a haihuwar, Wani abin burgewa tun kafin ta haihuwa ake maka ruwan sama mai karfin gaske, wanda yasa ake da yakin Yaron da za a haife yazo da albarka za a samu alkhairi a nomar bana da sauran abubuwan rayuwa zata zo da sauki kasancewar tun kafin ya iso duniya rauhanai sun bada isharan wanda za a haifa mutum ne da al'umma zasu kaunace shi. Haka yasa aka kara saka al'amarin a gaba ana ta murna da jin dadi idan har aka haifi wannan jinjirin ai ba karamin alkahairi za a samu ba sannan su kansu unguwar zomomin suna cikin alkhairi dumu-dumu. Bayan wuni da aka yi ana fama sai can goshin alumuru Ajuji ta fito fuskarta tattare da damuwa, haka ta nad'e jinjiran ta nufi Shago yana tsaye. Zubewa yayi akan gwiwarta ta ce mishi. "Harshena tayi nauyi wurin sanar maka abinda aka samu, gabakidaya wadanda suka amshi ragamar haihuwa suna maau niman yafiya a gare ka, domin ba a rangad'a gud'a na samun karuwa ba. Na cancanci mutuwa ka hukuntani kawai." Ta fada tana mika mishi Yarinyar, murmushi yayi domin wani irin natural love ce tsakanin yar da Ubanta ya amshi ta yana murmushi ya ce mata. "Kuskuren da kika yi Ajuji shine na rashin rangad'a gud'a, maza a ta shi tamburan. Domin yau ma zama Uba! Ga Damina!" Da gudu aka isa sanarwa dama ba a cika buga tambura ba sai abu mai muhimmanci, kuma gashi nan ya faru an samu Gimbiya Damina wacce ya mata lakabi da Sultnanah saboda fitarshi fatauci yaji sunan da ma'anarta.

Ya kuma je ya ga mai jego ganin yadda yake nuna kauna da soyayya akan yarinyar sai ta tsinci kanta da farin ciki dama kuma tana tsoron kada ta ce ba zai yi murna ba, ta shiga uku. haka Mahaifiyarshi tazo ta ga Yarinyar tayi murna. Ana saura kwanaki biyu suna ne alumma wata kauyen naka, gari ne da yake tsakanin duwatsu da koramai, suka kawo agajin wasu yan fashi daga garin sun buwaye su, suna kashe musu maza da Yara maza sannan suna lalata da matansu kana su kashe babban abinda ya tashi yan kauyen shi ne yadda suke iya kwance da ƙananan Yara da mata masu juna biyu, wannan abin ya daki Mai Martaba ya yaji zafi sosai.
5921536136 moniepoint ramlat Abdulrahman
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 50
A masarautarshi a lardinsa, a cikin al'ummarshi ake irin wannan rayuwar? Ana wulakanta mishi jama'arshi, dattawan da suka zo da nufin niman agajinshi suka yi ta sauke kayan da suka zo da shi cikin damuwa da gajiya da wahalar rayuwa wani dattijo ya ajiye mishi duwatsun yakutu da karfen azurfa da aka yi abin hannu da shi ya ce mishi. "Mai martaba, mun ji Gimbiya Aojanah ta sauka lafiya. Muna rokonka alfarman kafin Gimbiya Damina ta yi wanke mana garin Naka daga wadannan azzaluman, idan muka cigaba da ganinsu kullum rayuka ne zasu cigaba da salwanta, alfarma muke nima da rokon zaka agaza mana kamar yadda Iskokai da rauhanai suka tsaya maka! Duba lamarinmu ." Mikewa yayi ya bar Fadar, Yarima Balarabe wanda ya kasance makusanci kuma mai magana da Yawun mai Martaba ya ce mishi. "Sako ya isa inda ake buƙata! Sarki Shago ya ji kukanku koma cikin aminci da salama!" Haka suka yi godiya sannan suka juya domin kuwa sun isar da kukansu inda ya dace.

Bayan rana tayi sanyi likis yana farfajiyarshi, Balarabe ya zauna a gefenshi. "Takawa ina da wata yar shawara!" D'ago kai yayi yana kallonshi. "Ina jinka!" Kamar Dazun ranka ya b'aci da lamarin da suka zo maka da shi. Sannan baka ce kome ba har yanzu." Kallon dan uwansa yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce mishi. "Raina ne ba dad'i! Ina son ma rusa duk wata katanga ta zalinci ga al'ummar mu, na shimfida adalci a gare su amma sai ma tsinci wasu abubuwan ba yadda na so ba, sarakunan baya sun zuba mulki na kama karya amma ba haka yana nufin mu na baya mu halastawa kanmu zalinci ba ne, ina da burin masarautar nan ta kara girma da fadi! Ina nufin mu kasance mun fadadda shi yadda hannunmu zai isa ga talakawanmu, idan muna son hkaa sai mun cire rigar zalinci da cutarwa haka zai saka mu yiwa takakawanmu adalci!" Shiru Yarima Balarabe yayi wani abu da mutane ya kamata su sani Yarima Balarabe ya bambanta da Sarki shago domin shi a idanun kamar mutumin kirki amma a zahiri mugu ne na kin karawa, sannan yana cikin wasu tawaga na musamman masu hatsari, duk da shi bai tab'a yarda yayiwa wani abu da Dan uwansa zai gani ba domin ya boye kansa ne don kada a samu wani damar da dan uwansa zai zarge shi. Amma bakin azzalumi ne,.daga duk lokacin da Sarki shago ya bar Zanzabira zalincin da yake yi ba na wasa ba ne, sannan a gefe guda bai yarda da Bokayan Ajuji ba gani yake kamar ba zata ba shi hadin kai ba, tun mutuwar mahaifinsu Balarabe yake da burin zama sarki haka yasa tun kafin ya bayyana sirrin da yake ranshi Ajuji ta gargade shi da cewa yayi a hankali, domin hannunshi yana cike da jini ta gani ta ga ta ga jikin da ya wanke mishi jikinshi da hannunsa,kada ya sake wani yayi amfani da zuciyarshi ga dan uwansa domin al'amarin ba zai yi matuƙar kyau ba, yana jin kamar Ajuji ta gayawa dan uwansa haka yasa ya kama na shi bokon a can wani kauye mai suna rafin bauna.

Murmushi Balarabe yayi ka ce mishi. "Idan ka amince min ka bani damar zuwa na ji da su!" "Ajuji ta tabbatar min da cewa su din a shirye suke, daren yau xan tafi ga kauyen kafin wayewar gari zan dawo ayi sunan Damina da ni." Inji sarki Shago. A rud'e Balarabe ya ce mishi. "A'a Dan uwana kada su cutar min da kai!" Dariya Sarki Shago yayi ya ce mishi. "Ni daya na tashi alkaryar guda sai tsirarun mutane zasu bani tsoro? Ina da shekaru goma sha tara na fara tasar garin da basu min mubaya'a ba gaya min me xan ba ni tsoro? Ka san yadda ake fada da zaki? Ka tab'a gamo da katar da zaki? Baka tab'a gudun ceton rai da Giwa ba! Nayi tafiya a lokacin tsananin masifa zafi da macizan sahara masu feshin guba sai wadannan da suke kashe min mutanen lardina? Idan na sake suka kwarzane ni tabbas Ba Amaza da Ilu suka haife ni ba, idan kuma na sare kansu, tabbas zan shigo garin Zanzabira dauke da kayunaksu a daure a jikin Jaki!" Ya fada cike da alfahari da jin kai irin na asalin jaruman maza. Duk da Balarabe bai ji dadin haka ba amma ya saka a ransa, zai boye wani sirri me girma da yake yawo a ranshi.
"Tow ga shawara idan zaka tafi zaka dauki runduna ne? Idan ba zaka ɗauka ba mai zai hana ka dauki Bargaga tunda hannun damar ka ne shi, kuma shine Sarkin Yakin Zanzabira sabo, haka zai saka kome ya tafi cikin aminci!" "Zan duba!" A irin wannan lokacin boye abinda ya shafi tafiyarshi, da kuma abinda ya dace. Tashi yayi ya mishi sallama zai koma wurin Sarauniya Amaza. Kurawa bayanshi Idanun yayi yana jin shakkar abinda mutane suke gaya mishi akan dan uwansa kada ya tabbata gaskiya ce. Duk da har kwanan gobe idan ya tambayi Amininsa kuma Sarkin yaki abu daya yake gaya mishi kada ka daka ta mutane, domin zaka iya rasa turmin daka taka, duk da yasan abinda Balarabe yake aikatawa kuskure ne amma ya zabi yayi shiru domin idan yayi magana za a ce don suna takun saka ne da juna akan Sarki Shago, haka yasa yayi kamar bai san me yake faruwa ba. Balarabe abinda ya kara mishi karfi da jin kai haihuwar Damina wacce ta kasance Y'a mace, ai ko babu kome y'a mace ba ta gadon sarauta duk inda za a je a dawo ita din sai dai ta ga ana yi, sannan yasan matukar aka cigaba haka yara mata Aojanah zata cigaba da haifa haka yasa yake jin lallai kome rintsi sai yayi hakuri domin kuwa masu iya magana suna faɗin da kaɗan kaɗan matankadi yake shiga gora. Wannan karatun ya zauna a ranshi sannan duk inda yaje labarin da ake ba shi zai zama Sarki sai dai sai yayi zaman jiran shekaru masu yawan gaske domin ba zai tab'a cimma nasara ba sai da taimakon mace, lokaci yana zuwa da zai ga haka amma ba yau ba, ba gobe ba, ba jibi ba amma tabbas tarihi ba zata shafe ba sai ya shiga cikin jerin sarakunan Zanzabira.

Wannan abin ya zauna a ransui daram kuma ya ji a ranshi tabbas idan da rai da rabo wata rana zai cimma abinda yake bukata.
Present.
Wayar mai babbar daki ce tayi ƙara, da sauri ta razana da sai da kanta ya sara. Dafe kanta tayi ta ajiye kundin tarihin Zanzabira a gefe, a hankali ta dauki wayar ta kalli Son💙 ta ga a rubuce. Dauka tayi ta saka a kunnenta. "Ummina ta farka!" "Alhamdulillahi! Ya ta gane kowa?" "Eh ta gane kowa amma taki kallona! Shiru tayi kafin ya ce mishi. "Don't worry zata kulaka!" "No ai ban damu ba, kawai dai na gaya miki kada ki ga ina share ta ki ce bakyau!" Murmushi tayi tana mamakin irin halinsa yanzu dai nuna bai ji dadin abu ba tana magana sai ce mata shi bai damu ba, wato Yaro Yaro ne ko shekara nawa zai yi ba zai daina wannan Yarantar ba, ta ce mishi. "Yaushe zaka girma ina maka kallon wanda ya girma shekaru aru-aru!" Labarin shekarun haihuwar Sarki Shago ne ya zo mata kanta. Ta ce mishi, "Son ka tuna shekarun haihuwarka?" "Eh Ummi 5/March" ya fada yana mai sauke ajiyar zuciya. "Shi kenan ka gaida tsigai!" "Zan gaya mata kuwa!" Kashe wayar tayi ta kalli agogon bangon parlourn, lokacin sallah ya saka ta ajiye ta nufi ban dakin da yake parlourn tayi alola sannan ta dawo tayi sallah a parlourn, Sailuba ta kawo mata abinci Kadan taci domin tana son bibiyar kundin inda ta fara jin wani abu a ranta ya fara mintsininta. Wanke hannunta tayi ta dauki kundin ta koma gefe a hankali ta zuba idanu tana kallon waje.
Kafin ta sauke ajiyar zuciya ta kuma cigaba da karanta labarin.
*Past connection*
Kamar yadda sarki shago ya faɗa, sun dauki hanyar naka, tare da Bargaga wanda yake takewa Sarki Shago baya. Duk da dare bai wani yi nisa ba domin suna ganin fatake da suka dawo daga tafiya ɗai-ɗaia hanya. Wani abu da Sarki shago yake da shi ne, yana da baiwar ji Allah ya mishi wani irin kunne matukar zai ji motsi zai fahimci ainihin daga inda yaƙe, a lokacin da suka dirfafi daji sai da suka yi tafiya mai nisa kafin ya fahimci wata tsuntsuwa tana biye da su, kallon Bargaga yayi ya ce mishi. "Tare muke da bako kasan da zuwan shi ne?" "Na zata kura ce take mana siddabaru don nan lura ba." Sake saka kunne yayi sai yaji tashin tsuntsuwar, kwari da baka ya dauka sai da suka sake kamar babu kome, kafin sarki shago ya juya tare da harbin tsuntsuwar, haka ta fado kasa matacciya, Bargaga ya sauka ya dauki tsuntsuwar ganin yadda take dauke da wani abu kamar maku yasa shi mikawa Sarki Shago, yayi mamaki da ya ga abin anan domin kyauta ce da ya kawo mishi daga a wata tafiyar da yayi, abin sai ya bashi mamaki bai kawo kome a ranshi ba ya mikawa Bargaga abun suka cigaba da tafiya.

Kafin dare ya kara rabawa sun isa garin kamar yadda aka musu kwatance da aka musu, kwana suka yi a garin domin idan zasu hau duwatsu da mutanen da suke, dole sai gari ya waye domin kuwa ana iya samun miyagun halittu a wurin, ko su basu tashi fitowa sai gari ya fara haske, haka yasa suka kwana washi gari tun kafin mutanen garin su fito suka fita, fitar da suka yi shi cikin asuban fari, wannan lokaci kuwa ba karamin ƙoƙari suka yi ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login