Showing 204001 words to 207000 words out of 304445 words

Chapter 69 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

93

da yake ihu, tare da wuyata yana saukowa boons dina ya shiga murzasu ta cikin kayan, yana kallon yadda na rintsa idanuna. A hankali yake ƙara abinda yake so ganin nayi luff, "Yaya ka daina don Allah!,"
Murmushi yayi sannan ya mike.
***
Can cikin dajin zaune suke gaban bokan, ya kalleta da kyau. "Uwar mijinsu tana tsaye akan Yaranta musamman ita yarinyar da tauraronsu ya zama kusan daya da juna. Duk yakin da zaki yi ba zaki tab'a nasara ba, sai dai idan kin haifi abin cikin nan, akwai wacce t fito farauta zata iya taya ki, zaki iya nasara yanzu amma ba zaki sake samun nasara ba matuƙar bata taya ki ba, ga wannan kin ganshi ki saka wannan wandonta ne ko? Kin tabbatar wandonta ne ko?" Gyad'a kai Ijlal tayi a wardrobe dinsa ta samu. Wnada ya tab'a tawowa da shi daga gidansu Ikhlas. Sakawa yayi a cikin wani danyen duma, sannan ya mika mata ya ce mata. "Ki tafi makabarta ki saka a cikin sabon kabari kamar yadda na kabarin nan ba zai tashi ba. Haka itama ba zata tab'a haihuwa ba. Har abada.....(Kuyi hakuri yau sai a hankali)
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 68

Cike da wani irin kallo Ijlal take bina da shi tana faɗin. "Ni kuwa zan ce shi ne, domin shi ne abin da ake jira a gidan Salmanu Faris!" A hankali na zagaya na zauna tare da daura hannuna a kuguna nace mata. "Ki yarda a ranki ita ce a jikinki, kuma muka jiranta zamu yi mata tanadi na musamman. Domin idanunki bai nuna min zaki iya gabza yaki akan shi ba." Na faɗa ina murmushi. "Me kike ci na baka ke zuwa? Yaushe gari ya waye da har rana zata fadi? A shirye nake nayi yaki da kowa akan shi!" Ta fada alamar yarda da kai. Yatsa na karkad'a mata nace mata. "Laa, ban ki idan kika yi haihuwa uku ko hudu kai biyar kafin ki haifi namiji amma haihuwar da namiji a cikin Zanzabira kamar farkawar wata babbar karni ne, wacce zata haifa kuwa Nadiyyah Jamil Chiroma ce, ki rubuta ki ajiye Nadiyyah Jamil Chiroma ita zata haifi magajin zanzabira." Ba ita ba hatta mai Babbar daki, abin sai ya bata dariya wato idan aka niman wawuya lamba daya aka samu Zainab an gama magana ita ba fa kanta takewa wannan rigimar ba, wa wasu take yiwa. "Ya isa haka. Da mace da namiji duk abin so ne. Ai ita ya mace tudu biyu take ciki. Ta samu soyayyar Uba sannan ta samu soyayyar Dangi ba ga Yarku Khairat tana wurin kakanninta ba, don haka mace da namiji matukar a gidan Salmanu za a haifa muna so muna kaunarshi." Da wannan Mai Babbar daki ta katse abinda Ijlal zata faɗa domin ta san mahaukaciya ce zata yi shirme Yanzu, haka yasa ta katse sa'in'san ai kuwa ta zauna tana jin ba dad'i, har lokacin da ya dawo Fada, an gama mishi abinci tunda ya nuna min anan zai na ci abincin rana, hankalina ya dawo jikina, Mai Babbar daki bata saka min idanu ba. Sannan abinda ma fahimta yana son tuwo, yana son tuwo sosai haka yasa na mai da hankali wurin mishi tuwon acca miyar ayoyo da normal stew na tsokar saniya sai nayi grill fish da ya sha kayan kamshi har da lemon tsami, na gasa kafin ya shigo na cab'a kwalliya, gashina na asalin buzaye ya sauka a kafadata, sai jan lalle da aka yi min yatsuna kuma aka bishi da bakin lalle, wani irin kyau nayi har ina daukar idanun, ga daurin da Yeemar tayi min itama Mijinta bai jima da yazo ya dauke ta ba, Madam ba azhar ba La'asar tana tule a parlourn Mai Babbar daki, na gama abincin na kai na zauna bayan na kara gyara fuskana, ina jin shi da ita a parlourn yana tambayarta lafiya ta zo wai ta zo ganina ne, tab'e baki yayi ba mamaki tana niman zaman lafiya ne ya ayyana a ranshi. Ni kuwa fitowa nayi a hankali cikin girmamawa na nufi inda yake na rungume shi ina faɗin. "Barka da dawowa Mai Martaba, ya aka ji da jama'a. Sannu Namiji Dan Mai Babbar daki, Uban Dan Ummu Maryama Uban Gimbiya Ummu Maryam, sannu da kokari takawarka lafiya zauna na rage maka nauyin kanka!" Ansar sandar nayi na ajiye a gefe sannan ka shiga warware rawanin kamar yadda yake yi kullum sannan na cire na ajiye, kafin na cire hular kanshi da alkyabbar na ajiye babban rigar na cire na ajiye a gefe ina kallon shi. "Na kawo maka waje ne ko na bar shi a dakin?!" Shafa fuskana yayi yana mai lallubo hannuna. "Nawa kika biya kudin Heena din?" Juya kai nayi ina murmushi na ce mishi. "Ummi Uwar Marayu ita ta biya min!" Bakin shi ya kai kunnena. "Gaskiya ya dace ki yiwa Ummin nan takwaran sabon miji gatar yayi yawa a toshe ta da sabon miji gal!" Bubuga kafa nayi a kasa ina faɗin. "Ooo nifa yarinya ce." Na tura baki, sumbtar bakin yayi na ture shi ya zauna ina faɗin. "Waje zan kawo maka?" Gyada kai yayi kamar maraya, bawan Allah nan ya manta da Matarshi a wurin, na shiga fitar da abincin na jera mishi, ina mai gyara zama akan pillow kujeran ina murmushi na shiga zuba mata, na ga hankalinsa yana wurinta yana mata yan tambayoyi tana bashi asma ranta a b'ace. "Kin je kin amshi sakon wurin Dr Munirah?" "Eh ta ce ta kuma tura maka ta email!" Ya gyada kai yana kallon abincin da na zuba mishi, "Maisha abincin nan ba zai min yawa ba?" Kallonshi nayi sai sunan ya zo min banbarakwai, haka na zuba mishi har ruwan wanke hannu, yana gama wanke hannu ya fara cin abincin a hankali yana, ina zuba mishi namar miyar. D'ago kai yayi yana murmushi. "Thank you Maisha!" Ya furta, murmushi nayi na cigaba da zuba mishi kafin na juya ga uwar Magaji fuskanta a sake na ce mata. "Maman Princess a zuba miki ne?" Cikin wani daukar zafi ta zuba min harara ta ce min. "Duk hassadarki akan Future King zai koma miki, ina tausaya miki domin gaba zaki zo kina son ya miki wani abu yana faɗin wa uwarsa zai yiwa ba Matar Ubansa ba." "Kuma aka gaya miki itama zata zauna bata rike na d'an bane? Ai daga kwana goma da suka wuce nasan nayi ajiya a nan ko?" Ya fada yana mai daukar wayarshi ya kara a kunne. "Giwar Salmanu Faris, ina nan gasu sai kin iso!" Murmushi nayi nace mishi. "Gara tazo ayi da ita don na dauke musu miji!!" "Zaki sani ai!" Ya fada yana murmushi. "Na saka miki ne ko a'a" "hmm zan ci!" Ga shegen kwadayi kamar wata mayya koda yake ance masu ciki suna da wannan kwadayin. Haka muka ci gaba da jefa wa juna bakar magana. Har Nady ta iso lokacin mai babbar daki ta fito parlourn itama na zuba mata abinci. Tana zuwa ta gaida ita ta wanke hannu ta fara cin abincinsa, tana faɗin. "Sir na gama kome." Ta mika mishi wani paper bag! "Thank you Giwar Sarki." "Ita ce giwar Sarki?" Ijlal ta kara tambaya a rud'e, "eh ai ta cancanci zama Giwar sarki." "Ni fa?" Ta nuna kanta cikin kuka ta ce mishi.."Danka fa nake dauke da shi! Amma duk ka raba musu girman da suka wuce ni!" "Fulani Babba, Ummi ce ta radawa Maisha, ita kuma Nady ni na ga dacewar na kirata giwar sarki, domin ta cancanci kyautar sunan da mai babbar daki bata rigani ba ita xan kira da Fulani Babba, ke za a kira ki da Fulani karama ba!" "A'a ni dai sai dai a bani Fulani Babba ita kuma ta rike karama, ko kuma ita Nady tunda babu al'amar zata haihu a rayuwarta ta rike Fulani karama, ni kuma a bani giwar sarki domin sunan dani ya dace." Wani shegen dariya muka saka mata ni da Nady muka cin abincinsa. A hankali na dauki kifin na saka mishi, "Da wacce ta haihu da wacce bata haihu ba duk dukkanku matana ne, amma dayanku ya gayawa daya magana ne ba zan lamunta ba." Yadda yayi maganar yasa na saci kallonta. Ta cika ta batse kamar zata fashe don takaici, abin da na lura a duk lokacin da aka cewa Nadiyyah ba zata haihu da shi ba sai naga kamar shi yafi ta shiga damuwa, cire hannunsa yayi a cikin abincin, abun ya bani haushi akan wata can ya ki cin abincin. Zobo ya sha. ita kuwa na gefe can tana jin dadin yadda ta kuntattawa Nady amma kuma sai gashi mijinta ne yake jin babu dad'i.
A gidan suka yi sallah, ya kwashe su zuwa gida. Ni kuwa na gyara ko ina domin ya ce ba zai kara cin abincin ba, fura zai sha, shima dai dare yayi saboda ya ci kifi. Haka na gyara mishi na kira shi na gaya mishi. Ya ce Faruq zai zo ya karb'a tunda na kira shi yake min wani abun kamar nayi kuka haka nayi ta share shi, Faruq ya so ya amsa ta hannun Sailuba. Ni kan na gaji barci ya dauke ni.
***
Duk yadda Alhaji Nafi'u ya so dawowa zanzabira abu ya ci tura. Domin kuwa mutuwar Uwais da wasu abubuwan da suke ta fitowa yasa aka fahimci shi ya tunzira Uwais. Uwar Uwais ta ce bata yafe mishi ba domin ya cutar da ita.
Ya san zuwa yanzu ba'a farautar rayuwarta shi, don haka yana can aka bashi rigar kariya domin kuwa an share duk wani tuhuma da ake mishi aka nuna ma baya kasan yana kasar waje jinya. Sannan ya ja bakinsa yayi shiru ya koma yana sakawa ana mishi aiki, koda yake Salmanu Faris ya dauke kai kamar bai da mu da shi na ko a ce bai da alaka da shi, haka da ya gani sai ya shiga fitinar Mutanen da suke jikin Salmanu Faris. Binsu ake da kashedi.
Ranar wata Alhamis da dare aka kaiwa Asibitin Salmanu Faris hari, yana cikin shirya kayanshi aka kira shi, haka ya fita a daren zuwa asibitin. Babban tashin hankalin Salamanun kada a tab'a mutanen da babu ruwansu, amma idan don asibitin ne ba zai kula ba. Lokacin da ya isa ya samu wutar tayi barna amma bata ci rai ba. Sannan anyi Nasarar kashe ta, yana tsaye ya dafe keyarshi Faruq ya zo cikin nutsuwa ya ce mishi. "Fetur ne aka saka!" "An sami wanda yayi haka?" "An gaya dai mutanen Alhaji Nafi'u wato Jagaba!" "Kasan inda za a same shi?" "An bi bayansu suna bayan gari!" "Muje!" Bayan sun shiga motar bude wani wuri yayi ya dauki wasu karafuna, team dinsa na security sun isa har sun zagaye hotel din. Lokacin da ya isa bakiɗaya suka shiga bayan wasu sun kewayenta gidan, yana tsakiyar mata aka shaye-shaye, rodin hannunsa ya nufe shi ya maka mishi, sai da sake kofin hannunsa. Ya sake mishi duka uku fuskarsa a rufe da mask. "Gaya min Uban waye ya turaka asibitin nan?" "Alhaji Nafi'u" ya fada yana me rike kanshi saboda bugun da ya sha. Sake shi yayi ya cewa Faruq. "Ka dauke shi!" Haka suka bar club ɗin.
Wayar Jagaba ya gani, ya dauka tare da bin bayansu. Goga suka samu yana tsaye. Ganin team na jami'an tsaro da bakaken kaya yasa shi cewa. "Oga ni dai ku taimaka ku bani shi,.idan ya mutu a hannunku nayi asarar da ba zan tab'a mai da irinsa ba." D'aga hular kanshi yayi yana kallon Goga wanda yake kallon Salmanu Faris da kyau. Zubewa yayi a ƙasa yana faɗin. "Umarni zaka bani na kashe wannan karen!" "Ya muka yi da kai?" Salmanu Faris ya tambaye shi, "Allah ya baka nasara na maka alƙawarin na daina daba da sara suka?" "Me yasa zaka zo nan?" Hawaye ne ya zubo mishi. "Ya kashe min duk wani Yaron da yake bina, yana ta bina saboda yana da goyan bayan siyasa! Mai Girma Gwamna yana tare da shi haka Alhaji Nafi'u, bani da kowa a duniyata duk wnada yake tare da ni sai ya bi ya kashe. Ka min adalci na rama, domin shi da mutanensa suka kai hari gidanka suka kashe Sarkin kofa, wato hukuma. A yanzu harin da zai kai gaba nake son dakatarwa. Don Allah ka bani shi." Ya fada yana kuka wiwi. Murmushi Salmanu Faris yayi ya ce.."kana kuka wiwi haka? Baka shirya fansa ba, sannan idan ka shirya zan baka shi."
"Ranka ya dade! Me kake so nayi?" Ya tambayi Salamanu Faris cikin tashin hankali. "Ka shigo tafiyarmu!" "Idan nayi haka zaka gani shi?" "I kai!" Ya fada yana cigaba da tafiya, "xan shiga!" Murmushi yayi suka bar wurin shima ya bi bayansu da mashinsa. Can gidan gonar Alhaji Nafi'u ya nufa, yadda ya shiga cikin gidan gonar zai baka mamaki domin kamar an san da zuwar, haka yasa bai wani sha wahalar shiga ba.
Fitowa suka yi a motar bakiɗaya, suka shiga taka mishi baya. A cikin gidan da yake dauke da hasken wutar lantarki ya shiga ya samu wuri ya zauna. Alhaji Nafi'u, Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari. Mai Girma Gwamna Musharraf. Sai wasu mutanen da bai san su ba. "Meye na tashin hankali samari!" Dariya yayi yana faɗin. "Babu kai!" "Mun barka kayi yadda kake so me yasa mu ba zaka bari mu yi yadda muke ba?" Kallon Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari yayi da ya fadi haka." Akan me ba zan barku ku yi yadda kuke so ba? Asibitin ba ita ba ce matsalar, ko raunina majinyarta cikin sune matsalata. Amma da sauki tunda Lab ne ya kone, ni kuma ku duba tv nasan yanzu labarin ya dauka bummmmm!" Ya furta a hankali, kunna tv suka yi babban kamfanin sarrafa maganin na Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari, ne yake ciki da wuta. Wani kyaf-kyafta idanun yayi tare da saka hannunsa a habbar shi. "Wayyo ni! Wa zai dakatar da wutar? Innalillahi wainnalihir rajoun, garin yaya haka ya faru?" Wayar Alhaji Nafi'u ce ya fara kara. "Dauka mana, zaka bani kyauta idan ka ji wannan labarin." "Mai gida, kamfanin ka na kasar waje mun ji labarin gobara ta kama!" Sake wayar yayi ya mike. "Koma ka zauna!" Ya fada da karfi. Zama bakiɗaya suka yi. "Kun kashe min mahaifi na yi hakuri, kun kashe Amininsa nayi hakuri, kun kashe min dan uwan nayi hakuri. Wancan asibitin daya dai-dai take da duk kamfanin da kuka zuba jari na bala'i xan yi tafiyar wata uku, idan kun so ku hana kowa zaman lafiya. Alhaji Mamman Abba yayari zai cigaba da rike gari. Na san kome zan tafi har inda matar da aka boye ta da Yaranta. Kuma abinda xan aikata ba mamaki ya tafi da yankaken makogaron Mata da yara biyu mace da namiji. Ko kuma na tawo da su, su ga dangin Ubansu!"

D'aga wayarshi yayi yana mai yin tare da fara video call. "Hello 👋🏿 Mrs Shaiba!" Wato Khalisah. "Hello Mr Faris ya kwana dayawa ina Baby take da fatan kuna lafiya?" "Muna lafiya, baby na barta a gida. Kina waya da Babanki kuwa?" "A'a mun jima ba mu yi ba!" "Me yasa darling ki daina mantawa da shi. " "Yayi wanka cikin kazanta ne bana son hatta Yarana su san mahaifina weak person ne please Mr Faris bar tunanin shi!" "Ok in sha Allah mun nan zuwa!" Ya kashe wayar yana mai kiran wani layin. "Asiya Rilwanu Abubakar Yayari!" "Yes My lord! Da na ganka cikin kayan sarauta sai na ji ina son zuwa Zanzabira. Please kace Maama ta bar ni na zo." "Zanzabira babu tsaro ki yi hakuri idan aka samu tsaro da kaina zan gayyato ki har nan. Kin ji My Love oya yi min kiss!" "Muaa!" Ta fada mishi. "Ina Boy?" "Gashi nan yaki karban wayar wai yana fushi baka zo ba!" "Nuna mishi Please!" Nuna mishi hoton yaron tayi tana dariya. "Boy Yayari na gaya maka dokinka na nan, zan zo na dauke ku idan lokacin yayi amma yanzu ba zaka zo ba, yi min dan murmushi mana." Ba musu ya sake murmushi yana faɗin thanks brother na ganka da kayan sarauta nima ka saya min irin naka ka ji!" "That's My boy na saya maka!" Sannan ya musu sallama ya ajiye wayar yana kallonsu. "Idan naso waya kawai zan bada umarnin a rufe tarihin Yaran nan, bakiɗaya. Amma rigima da ku ba akan Yaranka da babu ruwansu ba ne, a kanku ne kuka kara tab'a ni ku yi tunanin yadda za ayi slaughter and stabbed waɗannan yaran into pieces yadda ake butching namar dabba."
"Me kake so?" Alhaji Nafi'u ya tambaye. Murmushi yayi ya mike yana gyara zaman rigarshi. "Zaman lafiya a Zanzabira!" Daga haka ya yi gaba abinsa ya barsu ne su kintatta abinda ya dace da kansu idan ya ce zai biye musu zai iya kashe su, amma wannan ba shine tarbiyyar da aka mishi ba, ya barsu ne su girbi abinda suka aikata. Ya san rauninsu yasan abinda sukewa yaki, sannan basu kaunar wani abu ya tab'a wani nasu, amma su zasu iya cutar da duk wanda ya shiga harkansu.

***
Lokacin da ya isa gida karfe biyu na dare yayi, wanka yayi zuciyarsa a sake..dakin Nady ya nufa ya samu tana aiki itama. Rufe laptop din yayi yana kallon yadda take haɗe rai. "Sorry!" "Ban ce kome ba!" Ta fada tana murmushi. Kwanciya yayi ya rungume ta. "Kayi hakuri an b'ata maka rai ko?" Kwantar da kanta yayi yana faɗin.."karfe shida zamu bar garin nan." "Wai har da Faruq ne a tafiyar?" "Mamaki kike?" Gyara kwanciyarta tayi tana faɗin. "A'a!"
"Doctor Munirah ta gaya miki" "eh mun yi magana da ita, sai dai My King Matarka tana shiga rayuwata." Bude idanu yayi yana kallonta kafin ya ce mata. "Wacce cikinsu?" " Amaryanka, akan me zata na bibiyar abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login