Showing 300001 words to 303000 words out of 304445 words
"Yata ce take wasu abubuwan shine na kawo ta naji ko lafiya!" "Kamar ya?" Ya kuma tambayaarta nan ta gaya mishi, juyowa yayi gare ni. "Kina jin amai? Ko kasala ko kuma zazzaɓi?" "Ni" na nuna musu kaina, girgiza kai mai babbar daki tayi ita kan sakarcin Zainab kara gaba yake. "Ke babu wani abu da yake damunki?" "Eh tow baya da marana ke ciwo kaɗan kaɗan, sai wani lokaci na dinga jin kamar zuciyata tana bugawa da sauri da sauri." Iya bayanin da nayi kenan, "amai fa ko zubar da yawu yaushe rabonki da Al'adarki?" "A'a bana yi sai dai ina cin abinci bana koshi sam shi kuma kamar wata biyu ko? Dama ina skipping!" Gyada kai yayi ya ce min. "Sannu ko!" Yayi rubutu sannan ya kira wata a waya tazo ta dibi jinina da kuma fitsari. Ina zaune a wurin bayan kamar awa daya don har an fara sallah isha sai gata ta dawo, cikin ikon Allah ta mika mishi result din yadda Ummi ta kagu akan jin mai zai ce bai wani dame ni. Ta ce min.."Je ki waje ina zuwa!" Ta fada min a yanayin da kawai ni nasan akwai abu mai muhimmanci da zasu tattauna ne a kaina. Ina fita ta kalle shi ta ce mishi.."Meke faruwa?" "Tana da ciki ne, sannan zan so nayi mata scanner! Domin na san watannin cikin!" "Ba wata matsala?" Murmushi yayi ya ce mata. "Bata da matsalar kome sai mun ga scanner din!" Fitowa tayi ta kira ni na shiga na zauna a hankali ya nuna min gado, ya ce na kwanta na bude rigana Allah yaso ba doguwar riga ba ce riga da zani ce sai laffaya a kai. Kwanciya nayi na bude cikina kamar yadda suka umarce ni, ina kwanciya ya kunna wata yar computer din gabanshi, sannan ya zuba liquid din ya gama hada kome ya shiga duba a lokacin na ji marata tana dan zafi zafi. Murmushi yayi yana faɗin. "Hajiya ga jikokinsu!" A lokacin gabana yayi wani irin bugawa! Cikin sati goma sha daya da kwana biyar, yarki tana dauke da cikin wata biyu da kwana biyar. Saura kwana biyu ya cika wata uku!" "Alhamdulillahi Ubangiji ya inganta!" Wani irin abu nake ji, yana yawa a kaina bakiɗaya yaushe aka yi abin? Rasuwar mijin Yeemar ne har yana niman wata uku yanzu? Sai na tuna maganar da muka yi da Yeemar na cewa mijinta ya doshi wata uku, dafe kirjina nayi tare da kallon Ummi. Gyada min kai tayi tana faɗin. "Alhamdulillahi!" Kuka na saka mata tare da sauka na rungume ta, ina kuka. Tana buga bayana haka muka gama kome ya ce mata. "Zata fara zuwa awo nan da kwanaki biyu!" "Mun gode sosai likita."
"Tana shan ruwa sosai da kankana domin ruwan da yaran suke ciki bai da yawa!" "In sha Allah!" Sannan ta amso maganin da ya rubuta. Haka muka fito ina kuka tana rarrashina har muka isa wurin motar. Bude mana sadi yayi yana faɗin. "Allah ya inganta. Sannu kin ji Uwar Magaji!" Shiga motar nayi na zauna na cigaba da kuka, har muka bar asibitin gidan Ummin muka nufa muka yi sallah Magariba da isha, anan na ci tuwon kaishi miyar kubewa, har da guziri. Da kanshi ya zo ya dauke ni, wani murmushi nayi ina tuna Allah ya bani nawa,sai naji na kara godewa Allah. Wanka nayi na fito na kalli kaina a madubi, jakar da Baba ya bamu da ummi ta ce kada na rabu da shi a wurin kwanciyata, shi na saka a kasar pillow na kanta, yunwa ne ya dame ni, na shiga kitchen na dafa indomie ya ji kwai, sai tea da na juye na plast din na dawo parlourn na zauna ina kallon tv na cinye, in ban koshi ba. Kitchen din na shiga na dama kunu da guntun miyata nayi tuwon garin semo, na juye na kawo parlourn sai da naji cikina ya cika har wani kane-kane yayi min. Sannan na kwanta da yar jakata a saman kujerar parlourn. Tuni barci yayi gaba da ni. Ko ya ji a jikinshi wani abu ne ko ban rufe kofar ba, sai gashi a parlourn hango yadda na kwanta yayi daga ni sai wata yar karamar rigar barci da wandonsa dan karami. Haka ya dauke ni zuwa dakina, ya kwantar da ni sannan ya gyara min kwanciya da kyau ya min addu'a, fitowa yayi ya kashe wutan gidan da tv ya ga kayan abincin da naci, mamaki abin ya bashi. A hankali ya gama zamanshi ya kwanta a saman dogon kujerar parlourn domin dazun rigima suka sha shi da Ijlal akan abinda ya gaya mata zai bada yarta ga Zainab tayi tsalle ta dirka tana faɗin, bai isa ba fitina da rigima kamar zata mutu don bakin ciki. Bata gama jin yadda labarin yake ba fara bala'i, shi ba zai fasa kudirinsa ba. Babu wacce tafi karfinsa a cikinsu.
Haka fa gari ya waye ya wurin ya kwana, washi gari tun asuban fari yunwa ya gigita ni na farka wallhi ko brush ban yi ba nazo kitchen, daura wannan tafasa wannan har aka fita sallah asuba ina shan kunun garin dawa da tsamiya, ina sha ina jin wani irin gardi gardi, tas na shanye kofin na wanke na juya zan fita na hango shi jingine da kofar. Tura baki nayi ina faɗin "wannan abin ba kyau wallahi razana musulmi!" Na zo zan wuce ya fisgo ni da ƙarfi sai da na shi wani sharp pain, na rike marana da karfi ina zare idanu. Da sauri na ture shi yayi baya, na durkusa kasa ina karanto addu'ar da duk yazo bakina. Har na daina jin zafin na d'ago ina kallonshi shima a matuƙar tsorace yake kallon yadda na dauki wasu mintina a wurin idanuna a rufe. "Are you ok?" Ya tambaye ni da damuwa a kan fuskarsa da ta gaza boyewa. "Yaya mai nayi maka zaka cutar dani?" Zare idanun yai ya zauna a gabana bisa gwiwarshi. "Baki da lafiya ne?" Ya tambaye ni a rud'e. "Yaya meye amfanin zaman da babu kwanciyar hankali!" Hannunsa ya saka ya rufe min baki. "Sorry my Maisha!" "A'a Yaya!" Rungume ni yayi yana shafa bayana, ni kuwa na saka mishi kuka. "Allah ya isa min, Allah ya saka min cin amanata da kake yi, ke kuma in sha Allah sai dai ki kare da haka amma ke da haihuwa sai dai ki gani a bayan kaza" yadda ya mike tare da ruko hannunta yayi ta kifa mata mari, har sai da ya bani tsoro, nayi maza na rungume shi. "Ya isa haka! Ina jin tsoro!" Na fada ina kuka." Yadda na fadi haka yasa shi kyale ya ya janye ni daga jikinshi ya bar parlourn kafin wani lokaci fuskartar tayi simtum. Nadiyyah da yake bata da hankali ta nufe shi da rigima ya ce mata. "Idan kika min maganar banza itama Sadiyar zan hada na bawa Ikhlas na ga yadda zaku yi." Tuni ta kama hanyar waje, tana faɗin."cab ba zan yarda a bawa juya ita ba." "Kika ce me?" Da sauri ta fita har da gudunta. Gidan sai ya zama kamar na zaman makoki, ni da na tashi nawa halin sai na bar musu Mijin musamman da haka kawai nake jin yana min wari, bana kaunar ya ce zai rab'e ni wannan abin ya ƙara mishi takaicina, har yake ganin ai don baya shiri da sauran matan ne nake wulakanta shi. Ni kuwa bai san ba haka ba ne wallahi shi din ne bana son ya kula ni ta auratayya.
Ashe case ake ta bugawa shi da Ijlal, karshe sai da manya suka shiga maganar, ina zaman zamana yasa aka kai ni wurin mai babbar daki, anan ake case din. Nan aka shiga maganar na ce musu. "Ai na gaya masa ni ba zan rike yarinyar ba, a barwa Mahaifiyarta, nima Allah zai bani ko a ce ban da kowa a duniya nasan dai Allah ba zai wulakanta ni ba, balle ita Ijlal ɗin da a gaban kowa fada musu take ni juya ce. Ta rike yarta nima Allah ai baya barci kuma nasan yana sane da ni, ban ga abin tashin hankali har da wannan zaman ba." Kallonta Ubanta yayi ya ce mata. "Nakasashiyar kike gori akanta? Kin san yadda wahalar renonsu yake? Har kike fifika kada a rabaki da yarki? Allah ya baki kema naki Fulani ai duk mai rai bai fidda tsammani daga rahamar Allah " daga haka aka kashe case, ni kan a wurin Mai Babbar daki na zauna domin kamshin turaren wutarta ya min dad'i. Har dare ta ga bana da niyyar tafiya ta ce min. "Ya dai?" Kamshin turaren ne yasa sai gobe xan koma!" Don nasan zai koma wurin Matarshi ce. Ai kuwa ya ji haushi da ya kira na ce mishi. "Yaya sai da safe tunda kun shirya da matarka ni dai ina nan!" Na fada ina kashe wayar, na share duwawu nayi zamata a cikin gidan, ina jin muryanshi zan gudu daki. Sai da nayi kwana uku Mai Babbar daki take tambayata. "Zainab me yasa kike gudunsa?" Sosa kai nayi ina faɗin. "Ummi ni wallahi kawai nason zama da shi ne yana dan sani nake dan ja baya kuma yaya rikicinsa bata karewa, shi din kamar sarka yake yana faduwa yake rikicewa."
Murmushi ita ta fahimci yanayin cikin ne ya kawo haka bayan nan babu wani abu, shi kuwa ya damu ko na minti goma baya kaunar ya koma gidansa Babu Zainaba idan yace yana jin dadin ganin bata nan yayi karya. Haka yasa ya ke tausar zuciyarsa da take zuwa iya wuya. Gashi ko a fadar ma wani gyara aka tsiro yi, wanda bai san dalilin Faruq na sakawa ayi gyaran sai tsohuwar ganuwa da zai koma shima ana ta aikin fasalin gidan kamar irin ta gargajiya ce don haka Faruq ya dauko wasu kwararru mazana kuma magina, suka fara aikin gidan kamar yadda Mai Babbar daki ta zuba kuɗi, wanan aikin sai ya kawo wasu kananun magana a cikin fada da wajen Masarautar, akan me za a tab'a tsohuwar ganuwa Mallakar ahalin baki daya ce, don haka Mai Babbar daki ta ce musu tow ta ji a raba gado. A lokacin Hajiya Hadiza dai da tayi magana da nuna akan me Mai Babbar daki zata yi gaban kanta bata yarda da a raba a bawa kowa hakkinsa. Duk wannan rigimar Mai babbar daki cewa tayi a yi rabon gadon bayan nan basu samu lokacinta ba, abin dai ya koma ayi a bayan idanunta ba dai kan idanunta ba, domin taci dubu sai ceto. Wani mahaukacin kuɗin da sai da alkalin. Ya musu magana akan kayan magada bai da tsada don haka su rage, tunda filin na ahalin Yayari ne bakiɗaya.........
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 100
Kudin da aka fanshi filin ba kaɗan bane, haka yasa aka cigaba da aiki aka raba kudin har da yaran mai babbar daki, sai kuma biyan kudin ya janyo kome ya mutu ganin yadda kowa ya samu kudi kamar haka domin haka ya nuna cewa mutane zasu iya mutuwa akan kuɗi da kuma wani abu na rayuwa basu iya boye ciwonsu da bakin cikinsu, haka yasa shi kallon each any person da yake rayuwarsu, bayan sati biyu abubuwan kamar basu faru ba.
Da gaske ni a kaina ina jin dadin zaman gidan Ummi, shi yasa naki komawa haka ya kara tunzira shi. Ya kura min idanu cikin yanayin da yake kara tabbatar min da ya gaji da kin komawa dakina. "Mai kika mai da ni? Kin mai dani ban isa da gidana kenan? Kaf duniya ke daya ce nake bi kamar jela ina ta hauka around any corner, Zainab na gaji idan na isa dake ki koma dakinki na gaya miki!" Daukar pieces na pizza ba kai bakina dukka ina ci ina girgixa kai. Na d'ago kai na zuba mishi idanu na ce mishi. "My Namamajo?" A fusace ya daka min tsawa, sai da Mai Babbar daki da take parlour ta ce mishi. "Zo ka bar min gidana ta ce ba zata koma ba ka komawa wurin matan mana wacce irin rayuwa ce wannan? An tab'a yin auren nan dole ne! Idan na isa da kai kazo ka fita na gaya maka!" Magena Ismaha ta shigo dakin, sai da tayi wani dungure ta haura gadon, ta zo kan jikina ta kwanta, na yanko pizza na gutsira mata, ta fara ci tana nishi. "Na gaya miki bana son magen nan ko?" Kallonshi nayi kafin na ce mishi. "Ummi!!" Rufe min baki yayi yana kallon cikin idanuna, "me yasa baki jin magana? Ki dawo dakinki kin ji i promise zan yi wani abu akan lamarinku!" "Yaya ni ba zan koma ba!" Na fada mishi kai tsaye na cigaba da cin pizza ina gamawa na tashi na je na wanke bakina na gyarawa magena kwanciya, "wato magen nan sai naci Uwar!" Na kalle shi na ce mishi. "Na gode bata da uwar da tafi ni tunda Allah bai bani haihuwa ba ita ce nawa!" Na fada ina gyara mata kwanciya, na ja mata bargo ta kwanta da kyau Kasancewar an fara sanyi. "Ikhlasi!" "Yau kuma? Wani Ikhlasi ka samu? Kada ka lalata min suna my Baby! Idan ka fita ka ja min kofa ka kashe min wutar dakina!" Na gyara kwanciyar da kyau. Haka ya rasa yadda zai yi da ni ya ja min yatsa yayi kara a raina na ce sai dai kayi.
Amma yaji haushi, last haduwarsu ya ji wani sauyi a tattare da Zainab, sannana yanzu da yake ganinta ta kara cika tayi kyau tayi haske sai wani glowing take kamar daren goma sha hudu, dakyar ta isa gidan, Nadiyyah ta tare shi da mita ya tafi wurin yar iskar Matarshi, wayyo Allah kwad'a mata mari yayi z sai da ta ji kamar bata duniyar, faruq da yake kofar shi sai da ya sake murmushi, "gyara kintsi, Allah ya huci zuciyarka, Ubangiji ya saka maka sanyi da salama, an gaishe da takawa!" "Ni ka mara? Akan shegiyar da bata haihuwa an gaya maka bata yar iska har karuwa an gaya mata!" Murmushi yayi ya ce mata. "Duk da haka ita ba karuwa ba ce, ita kamila ce da ba a cika samun irinta ba, yarinyar da ni daya xan bada shaidarta ke fa?" Yadda yayi maganar yasa ta zuba mishi idanu kamar ranta zai fita don bakin ciki yadda yake gaya mata. "Mr robort da kika! Har yau yana threating dina da videonki, kin fahimci me nake nufi?" Daga haka ya barta a wurin ta fito kallonta Faruq yayi ya ce mata. "Da alamu ke jahila ce baki san kome ba idan har wacce take kare kanta da mutuncinta zaki tab'a!" Yadda yayi mata wani irin kallo yasa ta sake baki zata masa magana ya kalleta da stick din hannunsa wacce kullum tana tare da shi. Juyawa tayi ta bar wurin.
***
Lafiyar cikina Iyayena da Ummi suke tattalawa, ni kaina na rufawa kaina asiri na ajiye maganar shi da damuwarshi a gefe guda, haka Matanshi basu gabana sau tari suna zuwa har gidan wani bin bana shiga harkokinsu gaisuwa ya isa tsakanina da su, a hankali kuwa sai lamarina ya fara yawo a cikin masarautar wai na zo na zauna ba a san me haka yake nufi ba, wasa wasa magana suka yi ta fitowa Mai Babbar daki kuwa tayi kunnen Uwar shegu da su, karya mutum ya zo har gabanta ya mata iskanci.
Matar Mai Bauchi suka zo wani biki zanzabira. Ban san me na mata ba matar tayi ta yada min magana. Ban kulata ba domin bana jin ko waye zai min abu zan damu da shi, a daren Yarinyarta mai suna Nur ta shigo tana wasa da wuka, ni kuma ina ban daki ina mai don sai yanzu na fara irinsu Amai da zubar da yawu. Ihun yarinyar na ji na fito da sauri don nasan na bar wukar da na yanka mangoro, ina fitowa Nasiba uwar yarinyar da yar aikinta suka shigo a guje, lokacin da na kwace wukar na wurga can. Ina mai rike hannunta. Wani hankad'a ni Nasibah tayi na yi baya zan fadi mai babbar daki ta daka mata tsawa. "Ke!" Yadda ta daka mata tsawar ni kaina sai da na ji tsoro ya kama ni. Tana shigo ta fauce yar a hannun Nasibar. "Kul ba sa'arki ba ce, ina kallonki da take-takenki kada ki sake gwada haka kin yi na farko kin yi ma karshe kul, Sarauniya ce kada ki kara kai hannunki jikinta!" Sannan ta fita da yar waje. "Juyar banza kawai!" "Tunda ke kike badawa mai yasa baki bani ba, ko me yasa baki dawo da danginki da suka mutu ba, mtseew!" Na mike a hankali na wuce ban daki na wanke hannuna, na fito na samu an gyara dakin. Wajen na fito sanye da burmemen rigar da Mai Babbar daki ta dinka min da mayafinsa, a matuƙar dame na zo na zauna a gefenta. "Sorry Baby!" Na fada mata ina shafa kanta. "Bakya kusa ne ko?" "Ummi ina ban daki ne!" Yadda ta ga idanuna yayi zuru-zuru ta ce min. "Saura kwana goma a fara azumi anya zaki iya?" Murmushi nayi ina kallon yadda take kula da hannun yarinyar. "Ummi kin yi aikin asibiti ne?" D'ago kai tayi ta ce min. "Nayi school of nursing, a lokacin babu muslmai sosai sai mu yaran manya kasa!" Gyada kai tayi tana faɗin. "Kuma baki yi aiki ba?" Murmushi tayi ta ce min. "My duty na kula da mai martaba bayan na gama karatu, na kuma haifa mishi yara, a lokacin yana jami'a na kammala degree na na farko!" "Ummi!" Murmushi tayi tana faɗin. "Baki yarda ba ne?" "Subhanillah Ubangiji kada ya nuna min ranar da ba zan yarda da ke ba, yarda da takai yarda Ummi na yarda har a gaban Ubangiji na yarda da ke!" Murmushi