Showing 15001 words to 18000 words out of 304445 words

Chapter 6 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

31

ya sa baki mutane su zabe mu? Tow bari na gaya maka ka sake na zare hannuna kanka gabakidaya jahar nan babu wanda zai tab'a d'aga kai ya ce zai zabe ka." Sannan ya mike yana kallon tv. " A kodayaushe ka zama me hura wutar rikici ga mutanen da kasan zaman lafiya ba kaunarshi suke ba, haka zai saka rabuwar kai a tare da su, sannan ka zama ganga mai baki biyu,baka can baka nan ta haka za a rasa gane kan waye kai. Kada ka zama lusari mana."
"Allah ya huci zuciyarka." Murmushi yayi ya cigaba da cewa. "Labarin hatsarin da abinda ya biyo baya zai shafe mutuwar Yarinyar nan Joy, ka tura mutane na musamman ga Church din Catholic da kudi me yawan gaske, sannan a tashi Yaranmu da basu jin magana, su kai kansu ga hukumar tsaro da cewa sune suka kashe ta. Sauran bayanin zan samu shugabansu mu yi magana da iyayen yarinyar." "An gama ranka ya dade." Fita yayi daga cikin office din, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kira commissioner walwala da jin kai ya bashi sakon da ya dace.

Bayan nan ya kira Jagaba, wani dan daba ne da ya gagari garin Zanzabira. Ya ce mishi. "Ka same ni a guest house dina, zan maka bayani, karfe biyar na yamma." Karfe uku da wani abu Mai girma Gwamna ya bar office dinsa, kai tsaye gidanshi ya nufa yana isa abin da ya fara karo da shi Kanin Matarshi wato Khalifa, da ga Alhaji Nafi'u. A parlourn gidansa ya saka wata jami'ar tsaro mai kula da tsaron Amaryanshi a gaba yana mata rashin mutunci. "Khalifa wannan abinda kake bai dace ba? Ina Saimah ta kyale ka kake min haka a cikin gidana?" Murmushi yayi tare da mishi kukan bunsuru wato ya cika iska a bakinsa sannan ya furza yana dariya. "Na zo wurin yar uwata ne sai na ga wannan me manya abin zaman ta cika min idanu. Kasan halina matukar zan ga mace a dire take wandona ke buƙatar abokiyar hira." Ya fada yana wani mad'e. Ran Mai girma Gwamna ne ya b'aci. "Don Allah ka fita!" Ya nuna mishi hanya, "Yar uwata nake jira zata bani sako." Ya fada yana murmushi. Juyawa yayi ya cewa Matar. "Bimbo zaki iya tafiya ." Haka ta bar parlourn zuwa bangaren Amaryanshi. Juyawa yayi ya ga Saimah ta fito tare da wata matashiyar budurwa. "Na gode Ma in sha Allah zan isar da sakon." "Yallabai ka dawo ne?" Gyada kai yayi yana kallon yarinyar da suke tare da Saimah gaishe shi tayi. "Barka da yamma Yallabai." "Khalifa ka mai da ita lafiya kome yayi amma zuwa yammacin gobe ka dawo da ita domin bata gama ba aka kirata a waya. " "An gama first Lady" ya saka rigarshi a bakinsa yana faɗin. "Alƙawarina fa?" "Ka duba na tura maka." "Godiya nake First lady!" Kafin ya juya ga mai girma Gwamna. "Surukina ina godiya sai an jima." Ya fita yana dariya. Amsar jakar shi tayi ta wuce sama inda dakinsa yake ta tura tare da ajiye mishi. "Saimah kina nufin har yau baki bar wancan." "Ban gane me kake nufi ba?" Wani irin kallo yake mata, idanunsa ya cika da kwalla baƙin ciki. Kowani mutum yana ciwonsa inda ya gaza da inda yake da iko a kai. Shi tayi rayuwar daban ce da kowa. Ban daki ya shiga yayi wanka, sannan ta fito ya shirya tsaf ko abincin gidan bai ci ba, ya fita bayan ya leka dakin Yaranshi yan mata biyu. Kallonshi suka yi a dan razane. Murmushi yayi musu Nanny dinsu ta gaishe shi ya shafa kansu kafin ya fita. Wannan shine abinda Allah ya bashi tare da ita, amma yana tsoron kada haka ya saka suma a cutarsu.
Yana shiga harabar gidan, ya samu dan daban Jagaba. Lallai ya cika dan daba domin bakinshi tayi bakiririn kamar ya shafa shuni. Fitowa Mai girma Gwamna ya sauka suka shiga cikin gidan, a parlour suka zauna. "Allah ya taimaki uban marayu! Wani me gajeren kwanan ne za a aika garin da ba a dawowa!" Mikewa Musharraf yayi ya nufi wurin da aka ajiye kayan shaye-shaye ya dauki wani kwalbar whisky ya zuba a glass cup ya nufi inda Jagaba yake ya ce mishi. "Ka tab'a shan irin wannan ruwan?" "Allah ya baka sa'a wannan ruwan sai ku manya!" Mika mishi glass cup din yayi ya amsa yana kallon yadda fuskarshi ta bayyana da mamaki domin bai taba sha ba. "Akwai brand masu kyau ka sha Jagaba." Karba yayi yana sha yana dariya. "Me kake bukata?" "Ka tab'a kiwon Maciji? Bari na baka labarin nan, wani mutum ne yayi kiwon Maciji, har na tsawon shekaru uku yana kiwonshi macijin ya girma ya kai girman mesa, sai aka wayi gari macijin nan yaki ci ya ki sha, daga haka ya kwanta bai da lafiya har na tsawon kwanaki." Murmushi Jagaba yayi ya karasa mishi labarin. "Macijin ya hadiye me kiwonshi, banbancin Maciji da kare a bayyane take shi kare baya ciwon ubangidansa. Yunwar wa kake ji na ciyar da kai da jininsa da namarsa!?" Murmushi cikin jin dadi ya ce mishi. "Ka tura yara office din Yan sanda domin rufe case din Joy!"
"An gama haka ya maka?" Jagaba ya tambaye shi. "Yayi!" Min inji Musharraf,
"Ranka ya dade shi kuma yunwar fa?" "Da lokaci har yanzu ka cigaba da biyayya." Ya fada yana juya ruwan whisky din hannunsa.
**
Tsaye yake a gaban window ya harde hannunsa a kirjinshi. Tun safe da ya shiga wurin Mai Babbar daki, ta ce mishi. "Ba laifi ba ne idan bata san al'adarmu ba, amma kuskure ne tana biyewa wasu matan a gefen hanya tana haushi kamar kare, abin kunya ce na d'aga kai nayi magana akan wacece Surukata. Ba laifi zata iya daukar duk wani irin mataki, amma me yasa baka gaya mata tana cikin gidan da ba koda yaushe ake sake numfashi me karfi ba domin akwai daliban sanin halayyar dan adam, don haka na baka lokaci ka nimo y'a daga cikin gidajen Baffaninka ko kawunanka waɗanda zasu iya jure kowacce ihu."

"Allah ya huci zuciyarki," wannan shine abinda iya fada, amma tabbas Nadiyyah ta ballo mishi ruwa, bai san yadda zai yi da ita ba, amma da yana da wata hanya da ya dakatar dà haukarta. Yanzu babban damuwarshi zarginta da ake yi mata. "Sun isa gida lafiya?" Inji Faruq da ya shigo dakin. "Hmm!" Ya fada yana tsaye, bayan kamar minti goma ya juya yana kallon Faruq. "File din nan?" "Suna gida!" Gyada mishi kai yayi. Kallon window yana hango zirga-zirgan mutanen da suke wucewa. "Muje gidan ko?" Ya fada bayan ya juya. "Tow Yallabai!" Sai da ya fita Faruq ya haɗa kome ya bi bayansa. Har gida suka isa. Kalaman mai Babbar daki yana kara tab'a shi. "Haihuwa muke bukata, idan da ta haihu da zasu amma bata haihu ba kuma tana irin wannan shirmen bai dace da gidan nan ba." Taya zai gaya mata aurenshi da Nadiyyah babu wannan batun kara auren. Iskar bakinshi ya fesar sannan ya kwantar da kanshi jikin kujeran motar, idanunsa lumshe. Bude motar Faruq yayi ya shiga wurin tukin motar suka asibitin. Lokacin da suka isa gida Nadiyyah ta tafi gantali ita da kawayenta. Dakinsa ya shiga yayi wanka da alola sannan ya wuce masallaci tare da Faruq, ko kafin su dawo Mr Brandy ya gama mishi abincin, ci yayi kafin ya wuce dakinsa sannan ya janyo pillow, ya jefa a kasa ya kwanta cikin sanyin jiki. Tashi yayi zaune da ya tuna bai jima da cin abinci ba ya kwanta.
***
Pastor Mathew

Yana zaune tare da Alhaji Nafi'u da Malam Imran Bin Daddar. "Wato Pastor Mathew anyi kuskure." D'ago kai yayi ya kalli Malam Imran Bin Daddar. "Malam ba kuskuren ba ne abin dubawa, yadda zamu gyara alakarmu ne, yarinyar Joy ita ɗaya iyayenta suka haifa yanzu ya zamu yi da su?" "Pastor Mathew ka manta waye ni? Shi yasa na tawo maka da Imran don nasan shima abokin cin mushenka ne. Kada ka manta dukkanmu muna karkashin abu daya ne, idan ka so zaka iya hada karamin rigima. An kashe Joy saboda ta yi leken asiri ta san abinda bai dace kowa ya sani ba me zai hana a haifar da wata yar karamar hatsaniya a dan yi asarar dukiya da rayuka yadda zamu gyara alakarmu. Mu gwara kan addinai guda , idan ka amince ga wannan idan baka amince ba zamu samu iyayen Yarinyar baka san me zamu gaya musu ba " numfashi ya sauke tare sa jan jakar ya bude sabin takardan dollars ne cikin jakar. "A kashe kamar rayukan mutane ashirin a kona kananun shaguna talatin mu kuma anan zamu cusa musu kiyayyar juna. Matuƙar Ubangida yana raye ba zamu bashi kunya ba."

Dariya suka saka tare da mikewa suna faɗin. "Ga abu a fili, ka tsaya zaka yi gardama bayan nasan matuƙar da wannan tow ba mamaki kome zai zama me sauki ne a wurinmu." Inji Imran Bin Daddar.

Sun isa gidansu Joy Moses, abin tausayi Uwarta sai tashi take tana faduwa an kashe mata yarinya. Sun yi musu ta'aziyar rashinta, sannan suka bada hakuri da abinda ya faru. Alhaji Nafi'u ya ce . "Ni Nafi'u Shaiba nayi alƙawarin biyawa muku zuwa Jerusalem, domin aikin Ibada. Sannan zamu yi magana da gwamnatin jahar nan mai adalci akan ayi adalci akan duk wanda suke da hannu akan mutuwar yarinyar nan, ina me baku hakuri ." Yadda iyayen suke kuka yasa shima share kwalla yana girgiza kai kamar da gaske abinda ya faru kenan.
Bayan sun basu abinda suka zo da shi, sannan suka fito. Pastor Mathew ya mikawa Alhaji Nafi'u hannu. "Ka tabbatar yau an tsara kome ni kuma zan yi nawa aikin!" Ya fada yana kallon Imran Bin Daddar. "In sha Allah, nima zamu haɗu da mutanena mu bada goyan bayan da ya dace." Daga haka suka bar unguwar Morocco anan galibin christocin suke da zama da suka bar cikin hausawa suka dawo wannan unguwar sannan akwai daidaikun muslmai a cikin unguwar.
*
7:23pm

Saka links din rigarsa yake, Faruq ya tashi motar yana jiransui. Wata mota ta shigo da ita cikin gidan, fitowa tayi daga motar tana murmushi. "Na gode sosai, in sha Allah ku yi arrange din kome kafin na zo!" Ta fada tana d'agawa mai motar hannu. Bayan ya fita ta juya idanu hudu suka yi da Prince dinta. Gabanta ne ya fadi saboda irin kallon da yake bin ta da shi. "Prince!" Zuwa yayi ya shiga motar Faruq ta tashi motar. Bai ce mata cikanki ba koda ya dawo ma bai kulata ba, haka tayi ta niman hanyar da zai kulata. Wurin karfe goma na dare ta shiga dakinsa. Yana aiki a laptop. "Aslm Prince!" Bai amsa mata ba. Zuwa tayi gabanshi ta zube akan gwiwarta. "Sorry Babe ba zan kara ba!" Nan ma shiru yayi mata don bata ji tun kafin su iso Najeriya yake gaya mata gidansu ba irin kowani gida bane, baya son ta dauko mishi magana. Amma da yake bata jin magana. Haka ta gama magiyarta bai ce mata cikanki ba. Karshe ta fita ko kallon inda take bai yi ba.

File din nan da har yau ya kasa budewa ita ce, yayi kumdunbalar budewa tare da rintsa idanunsa, yana tsoron me zai gani
1990
*BLACK CAT*
CULT.
Abinda idanunsa ya fara gani kenan a pagen din farko, da sauri ya rufe files din gabanshi yana faduwa, da sauri da sauri sakamakon wani abu da ya shiga kanshi ya mishi Flashing din wani abu da ya tab'a faruwa a wani wurin....
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.



*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*



*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍

_Na gode sosai da addu'o'inku Allah ya bada lada, idan ta mu tazo Allah yasa mu cika da imani. Allah ya kyautata tamu bayansu Na gode sosai_

05
#Coincidence


"Kai Jigal ku tattara mana kayanmu." ya fada yana kallon Mutumin da yake rike da bindiga. Fadawa ne rike da sanduna, abin ya basu mamaki sai yan taurin cikin fada suma suka fito da bindigar toka, suka zagaye su. Ni dai yau na ga lukutar masifa, domin kuwa abin da yake shirin faruwa. Ina ga kamar rayuwata ce a garari. "Ka sake yarinyar nan ka wuce mu tafi kaga mun kama Yaranka." "Ba zan kyaleta ba, sai dai na kyale gawarta." Motsi nayi naji ya daka min tsawa. "Tsaya min ko na yanke makogaronki." Haka yasa na tsaya kamar ba na raye. D'ago kai mutumin da suke tare da mai bindigar fuskarshi sanye da face mask yayi ya ce mishi. "Tow ka kashe ta bar nan!" Ya fada yana me juyawa abinsa tare da mai bindigar. Wani irin tashin hankali na shiga na ce musu. "Yanzu haka zaku bar ni? Haka zaka kyale ni? Me yasa ? Me yasa rayuwar dan Adam bai daraja ne? Meye amfanin bindigar hannunku. Kashe ni zai yi fa, don Allah ku taimake ni, ku taimaka min kada ya kashe..!" Ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na ji wani abu me karfin gaske ya wuce da karfi tare da wani irin huci me zafi , ihun da yayi haɗe da faduwa yasani jin kome ya tsaya min domin nima suma nayi. Faduwar da yayi wnada yayi daidai da zuwan yan sanda yasa aka kwashe su daga shi har Yaransa zuwa state Headquarters na Yan sanda, ni kuma asibitin da yake kusa da Fada aka kai ni, shi kuma wanda suka sara aka wuce da shi babban asibiti da sanda.

------
Bayan an kawo ni asibiti karin ruwa suka min sannan Yeemar ta kira shugaban gidan Radio ta gaya mishi. Tana wayar wata Nurse ta zo, katse kiran tayi ta kalle ta. "Ki zo ana kiranki!" "Tow!" Daga haka ta bi bayan Nurse din, zuwa wurin kiran ganin ba likita ba ne ta kalle shi. "Kace Yeemar Omar ko?" Eh ta fada tana murmushi don ta gane shi, shine wanda ya fara harbin farko. Sai dai wani abu ne ya zo kanta. "Sir amma harbin da aka yi ba kai ne ka yi ba ko?" "Eh mai gida ne yayi, shine na zo a madadinsa na baku hakuri." "Ba kome ai ceton rayuwarta yayi." "Eh tow!" Ya fada yana kallonta. "Ina take?" "Tana cikin dakin!" Shiru yayi kafin ya sosa kanshi yana murmushi. "Ki gaishe ta!" Wayarshi ce tayi ƙara ya ciro a aljuhun gaban rigarshi, Sir ya gani da sauri ya juya yana d'aga mata hannu.

Sake baki tayi tana kallon yadda yake gudu, can ta tab'e baki ta shiga cikin dakin. "Ja'ira." Ta fada tana make ta.

***
Headquarters of police

Minti goma da kawo su, sai ga Kwamishinan yan sanda, hankalinsa a matuƙar tashe. "Wani dan iskan ne ya kamo su?" Shiru sauran officer din suka yi, yayi fada kamar zai dake su. Shigowar inspector Mu'azzam Adnan ya shigo office din, "Waye ya kamo Yaran nan?" "Sir ni ne?" Juyawa yayi ya kalle shi kafin ya ce mishi. "Waye ya baka izinin kama su?" "Sir daga kofar fada aka bada izinin kama su." Ya fada a hankali, "Wani dan iskan ne zai baka iznin kama su?" "Ni ne!" Ya furta daga bakin kofar shiga office din, inji Salmanu Faris da ya shiga office din, Faruq yana take mishi baya duk da haka babu wanda zai ce ya ga fuskar shi domin cikin face mask yake amma da alamu CP yasan kowaye shi. Kwarjinin da cika idanu da yayiwa CP yasa lokaci guda ya cire hularsa. "Mai martaba kai ne da kanka? Ai da ka gaya min da nayi maganin abu, ba sai ka zo ba. Yaran nan sun cancanci a kama su sannan zamu mika su ga kotu ta hukuntasu." Juya kai yayi kafin ya ce mishi. "Shi kenan idanuna yana kansu!" Daga haka ya juya suka bar office din.
Mikewa Goga yayi ya ce mishi. "CP kasan dole na bar office din nan domin mutumin Jagaba na tab'a idan na kara awa daya a wurin nan tabbas Uwata sai dai ta haifi wani. Don haka ka bude ni da Yarana mu tafi! Sannan ka ga jinin da nake zubarwa." Hararansa yayi yana me barin wurin. Bayan kamar minti goma, sai ga daya daga cikin jami'an gwamnati wanda kowa yasan shi shahararren dan bangan siyasa ne. "Bana kashe rigimarka da jagaba ba? Me yasa zaka dauki doka a hannu?" "Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa shi yasa na farmake shi!" Wucewa office din CP yayi, bayan kamar minti goma suka fito aka bude shi, da Yaransa suka bar Headquarters din.

---Karfe hudu na yamma na farka gidan muka wuce da Yeemar MD sai kiranmu yake yana son jin meke faruwa,tunda na amsa na ce mishi don Allah kada ya kara kira lafiya nake. Da muka isa gidan ma ba kwanciya nayi, Maluma take tambayar me ya faru Yeemar ta ce mata. "Jiri ne ya kwashe ta muna aiki!" "Hmm bata ji wasa take da cikinta ba dole ta fadi ba!" Ta wuce daga haka murmushi nayiwa Yeemar na ce mata. "Na gode sosai!" "Nima haka xan tafi office nayi report."


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login