Showing 60001 words to 63000 words out of 304445 words

Chapter 21 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

46

"Kayi hakuri!" "Daga yau na shiga tsakaninku." "In sha Allah!" Daga haka ya barsu maganar Ikhlas yana cizon ranshi.
- "Ke kuwa Ikhlas meye haka?" Inji Yeemar tana kallona. "Tow karya zan yi? Bana sonshi idan na boye kaina zan cuta gwara na gaya musu shi bai dace da irin mijin da nake mafarkin baza rayuwata akanshi. Sannan bai da abinda zan yi kwadayi akai, me aka yi aka yi shi?"
Yadda nake magana yasa suka yi shiru, don wallahi wani haushinsu nake ji, abincin da ban ci ba kenan, na juya musu baya na ji suna faɗin gaskiya an karrama su da kaji, tsaki nayi abinda bai dame ni ba.
--
Faris
A hankali ya isa gidansa, Faruq ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce mishi. "Sir akwai matsala ne?" Murmushi yayi ya ce mishi. "Me ka gani?" "Na ga yadda ka dawo kamar ranka ba dad'i." Murmushi yayi ya ce mishi. "Ko ɗaya!" Ya bude motar ya fita, cikin gidan ya nufa, koda ya shiga ya samu Nady tana sheshakar kuka, kallonta yayi kafin ya wuce ta shi ya gaji da fitina ga maganar wancan kwailar ga na Nady. Murmushi yayi ya d'agota tare da rungume ta.
"Shi kenan sai ka bar gidan daga mun yi magana!" Bubuga bayanta yayi har tayi shiru sannan ya nufi daki da ita, da farko ya zo gidan hauka ta fara mishi ya fita don an tura mata hoton yadda ya rungume Ikhlas bayan ya janyota daga jikin Babanta. Shine ta fara ihu da haukar yaci amanarta dama tasan haka zai faru.
***
Alhaji Nafi'u.
Fasa kayan kwalbar gayanshi yayi yana faɗin. "Uban waye ya ce ku sake Junaid?" "Daga sama aka bada umarnin sake shi, babu wanda ya san waye ya bada labarin kama shi." Cikin fushi ya ce. "Wani dan iskan ne yake warware min aikina?" Shiru suka yi domin ba zasu iya amsa mishi ba asalima tsoron yadda zai hukunta su ya sa suka yi shiru, don basu san yadda zai ɗauki lamarin ba.

Fita yayi daga gidan ya nufi Penthouse dinsa, kai tsaye can underworld din ya nufa, ya je ya zube a gaban magensu. "Na gaya maka yarinyar da muke nima ita ce Junaid ya bawa Dan gidan Attahiru." A wani haukace ya d'agi kai yana kallon magen cikin rawan murya ya ce. "Ba yar kanwata ba ce?" Gurnani Magen yayi yana faɗin. "Daga ranar da ka sake suka zama abu daya ba ni ba hatta Rilwanu ya rasa kujeransa,don haka ya rage naka ka raba tsakaninsu, yadda zamu same ta kai tsaye don matuƙar aka yi haka za a dace."
Shiru yayi yana nazarin yadda zai iya samun Ikhlas a ruwan sanyi ba tare da an samu matsala ba. Juyawa yayi ya bar duniar.
*
Washegari

An tashe mu, kun san wani ikon Allah ni fa ko lallen biki ba ayi min ba, abu daya nayi shine saloon, ina zaune sai ga Aunty Sajida da mai lalle, aka fara min kasancewar ina da haske amma ba sosai ba yasa aka min ja da baki yayi kyau, abin karyawa aka kawo mana wurin karfe sha biyu saura, saboda kawai an ga an kawo mana abinci daga gida, mu yan gidanmu haka muke karya muke da wuri shi yasa tun asuba na tura sakon a kawo min abinci sannan ina da wata irin hali ban cika yarda da inda nake ba. Mun karya aka kawo nasu, ko kallo bai ishe ni ba. Balle abincin.

Wurin karfe daya na rana aka kawo mana abinci daga gida, anan ne na ga ana ta shigowa ana kallon kular abincin kamar abin ya b'ata musu rai, su suka sani. Shigowarsa dakin lokacin ina nad'e abin sallah da nayi, su Aunty Sajidah suka shiga gaishe shi. Ni ko inda yake ban kalla ba. "Ke zo nan!" Yadda ya ce ke din nan haka nayi banza da shi na juya zan koma na zauna Aunty Sajidah ta ce min. "Baki ji ana kiranki ba ne?" Ya tambaye ni tana kallon inda yake. "Ni Zainab Junaid Gobir Ikhlas! Ake kira?" Na nuna mata kaina da kwarin gwiwa don ya ji sunana, gyaran murya yayi, wani ya leko yana faɗin. "Ko zaku iya fita hakimin Garin Farin ƙasa yana son magana da gimbiya Zainab!"
Mikewa suka yi zasu fita nima na bi sahunsu ji nayi ya rike damtsena da karfi sai da naji zafin har cikin raina, da sauri na fisge tare da ture shi. "Da izinin waye aka kawo abincin nan?" Hararan gefe da gefe nayi na haɗe rai naki magana, don Allah ya gani ina da taurin kai kamar na jinjirin jaki. "Tambayarki nake?" Juyawa nayi ban ga kowa a dakin ba ai nasan ya fita, tow amma don ma rena mishi hankali na fara juye-juye. "Look akan me za a kawo abincin?" Ai wallahi indai bai kira sunana ba, ba zan taba amsa mishi ba. Ganin da gaske naki magana ya sa shi kwafa ya fita daga cikin dakin, karamin tsaki na ja.
Nima da niman magana, bafa gida aka yi tunanin haka ba. Ni ce dai na turawa Abba sakon tun daren jiya a kawo min abincin karyawa. Ni ban yarda da yan gidan ba, hakan yasa aka kawo min abinci wani abu da zai baka mamaki yan gidan wasu irin kallo suke min domin dai ina hango kiyayyar da suke min shi yasa na gwammace na nime abinci daga gidanmu.

Shigowa su Aunty Sajidah suka yi, na lura kamar ransu a b'ace yaƙe. "Yeemar lafiya?" "Hmm an kai mu dakin mother in law dinki ne, ta gama mana cin mutuncin da ranta yake so. " Shiru nayi ina kallon yadda take fada. Gyada kai nayi ina me rausayawa. Murmushi nayi a raina na ce zan rama kuwa.

Karfe uku aka turo mai kwalliya sai da na gama hidimar gabana da sallah sannan na mata magana ta fara, a kayan da suka cire zan saka nayi tsalle nace ba zan saka ba. A mai da don daga ɓangaren Mamansa aka kawo gashi gidan an fara ciki, kannensa biyu mata suka taso akan lallai shi zan saka ina kallonsu bayan na daura daya akan daya na ce musu. "Ba zan saka ba, ni ban yi niyyar sakawa ba." Wasa wasa aka yi ta rigima da ni amma fir naki sakawa, ina zaune sai ga Mahaifiyarshi da kanta ta zo tare da jakade. Sai masu take mata baya. Tana shigowa ta same ni zaune ina kallon wayata. Yadda yan dakin suka mike sai da na gama ra'ayina na mike.
"Waye ya gaya miki muna maraba da mara d'a a cikin gidan nan?" Ta fada min, "Allah ya huci zuciyarki Mai Babbar daki,.tayi kuskure kuma za a ladbtar da ita." Ba a koya min raina na gaba ba, sannan na a gaya min idan babba yana magana na amsa mishi ba. Sai dai Matar ta zaqe dayawa da yawa na kasa daina kallon kwayar idanunta. "An gaya miki na amshi ki a matsayin Suruka ce? Waye Junaidu da zai haifa yarinyar da zata ja da umarnina?" "Mahaifina ne, dama shi ba kowa bane. Sai dai yana girmama aminta da aminci yana biyar bashin aminci da tsoka me daraja, Allah ya huci zuciyarki ba sakonki naki amsa ba. Na ga girma da darajar da nake da shi a gare ki yasa naki amsar sakonki ai ke Uwata ce ko ba don shi ba, ke me ce min je ki zauna da wancan bawan kuma na amsa da tow, Umma nima ina da tawa rayuwar na sadaukar sai na zama abu mara mutunci da daraja? Tun fil azal ban iya cin abincin ko ina ba, sai na iyayena Umma tsoro da damuwar kada a cutar da rayuwata ya sa naki abincin da an gaya min daga hannunki ya fito zan amsa koda kuwa ace kece kika ci bakinki da yawunki zan amsa amma ban san daga ina aka fara ba, na cusawa rayuwata abinda ban san daga inda yake ba, ki duba lamarin!" Kasa tafiyar tayi tana mamakin yadda nake magana..
"Mu bamu zargi Junaidu da kashe mana Mahaifi ba sai ke zaki zargi abinda za a baki ki ci?" Inji wata me kama da shi. "Da ina son rashin kunya da sunan mai Babbar daki zan kira da sunan Abba sarki amma sai ka yi dace ni zaurenmu an koya mana girmama na gaba da mu. Sannan kau kuma bani abuna tunda Umma Babba ta kawo min tabbacin na samu karɓuwa a matsayin surukar gidan kenan!" Na amshi kayan ina murmushin dole na wuce ban daki. Ita kanta Mai Babbar daki sai da na bata tsoro idan dan jarida bai iya tsara magana ba, gaya min wayar zai tsara mishi? Haka na shige ina yabon kayan a raina kuwa ina kwafa domin wallahi nasan a banza Maluma zata iya biyo har nan ta saka a min dakar sakwaran hege.

Bana ce nafi kowa ba amma kuma lokacin da na fito cikin shigar sai da aka yi ta min magana, sannan aka karawa kwalliyar.
-
"Daula baki da hankali ne? Akan me zaki kira sunan Ubanta. Kul na sake magana da ita ki saka baki." "Allah ya huci zuciyarki!" Inji daularh. "Gaskiya ya kamata ku ka girmanku, kada ku sake ta rena ku." Inji wata kanwar Mai Babbar daki. A can gefe akwai matar wan Mai Babbar daki Yarimar gabas, a hankali ta ce mata. "Amma nayi mamaki duk surukanki babu wacce ta samu ikon kallon kwayar idanunki sai wannan fitsarariyar. Tab!"
Ranta Mai Babbar daki kara b'aci yayi tayi kwafa tana jin kamar ta fasa ihu. "Ya maganar Ijlah?" Cikin farin ciki ta ce mata. "Tana tare da su Ilham!"
"Allah sarki!" Mai Babbar daki ta fada tana murmushi. "Ai na gaya mishi ina da matar da zai aura don haka Ijlah ce matar da zai aura in sha Allah." Hajiya Mardiya kawar mai babbar daki ce tun kuruciya...
*ina mata yan gayu ina mata yan yayi! Tow ku matso nesa ta zo kusa collaboration Tangaza_Perfume tare da Anum∆Luxury Perfume sun zo muku da kayan kamshi gida da na jiki kai ba iya nan ba hatta turaren kaya irinsu.*
Mamoul all colors are back in stock. Mamoul turaren turara kaya. Ga kamshi ga kama kaya da gida. Available in;
MAMAOUL MADINA,
MAMAOUL MARYAM,
MAMOUL BADAR &
MAMAOUL SABAYA. Each one 3500

*New Drop!*
*Nassem Oil – 100ml*
Rich, elegant & long-lasting.
This premium fragrance oil is everything your collection needs — and it’s only *₦8,000!*

*Luxury in a bottle.*
| Own Your Scent, Own the Room*

*Mosuf 50ml Body Spray*
Smooth. Fresh. Long-lasting.
Only *₦5000!*
✨💥
Smell amazing, every single day.
*DM to order!*

*Storm for Him & Her – ₦4,500* each
Fresh, fierce, and made to turn heads.
Whether it’s *Storm for Him* or *Storm for Her*, you’re getting bold confidence in a bottle — just *₦4,500!*

A perfect 50ml to carry your essence wherever you go. Subtle. Powerful. Unforgettable.
Now available: ₦2,300 per piece | ₦27,600 per dozen.
Available Just DM
08130269641

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.


*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*


*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Gyara zama Hajiya Mardiya tayi tana faɗin. "Har na turawa da mahaifinta abinda kike bukata ya ce shi ba zai mata dole ba, sai ya ji ta bakinta, shine na tsarata yadda zata gaya mishi kin san ba wayo ne da ita ba na dai gaya mata kome sannan yanzu haka na tsara mata yadda zata nunawa ita yar malamai iyakarta akwai wata bayan ita." Shiru Mai Babbar daki tayi domin suna yin maganar ne kasa kasa ne. "Kin san matar shi da yake tare da ita, saboda mahaifinta nake bayanta bayan nan ba wacce nake so kamar diyar Halima domin nasan wacece ita, yarinyar ta gaji Halima tabbas gidan sadauki zai cika da Yara maza. Ita wannan bana son ta cika wata guda a cikin gidan ba tare da tayi waje ba." Yadda Hajiya Mardiya take zugata haka take kara kunce mata cikinta.

Yarinyar da za a hada shi da ita bakiɗaya bata wuce sa'arsu Ikhlas ba, sai dai irin Yaran nan ne da za a ce uwa ba kwaba uba ba tsanani, don an yi mata wani irin goyon jeki nayi ki ne, yadda suke saka makircinsu Allah kaɗai zai iya warware kullin da suke, domin yadda Hajiya Mardiya ta jima tana son daya daga cikin Yaran Mai Babbar daki su shiga hannunta Allah kaɗai ya sani irin shirin da take akan su, sai gashi cikin ruwan sanyi Ta gama cin burin zata saka danta ya kara aure sai gashi Marigayi ya mata baya ba zani. Ta ji takaici lokacin da taji labarin auren domin kuwa taso su shiga jikin Mai Babbar daki ta basu damar auren Faris uwa uba, su san yadda zasu fitar da Nady koda yake sun lura da Nady ba mulkin Faris ba ne a gabanta ita rayuwar da take yafi mata. Haka yasa take jin zafin yadda Nady bata haukace musu ba, koda yake ta ji Mai Babbar daki tana faɗin ba son Nady take ba, babban burinta Mulkin garin zanzabira yadda koda Faris ya zama sarki babu macen da zata iya shan gabanta, sai ga Aurenshi da Ikhlas dukkansu kawayen nan sun ci burin ganin bayan auren Ikhlas da Faris a wannan kebewar da suka yi
Ma ji ma gani an binne tsohuwa da rai.

**
Karfe hudu ya dace a fita amma na ji labarin ance wai da Matarshi zasu fita don haka nima koda na yi sallah la'asar aka gyara min fuskana, karfe biyar daidai muka bar gidan, inda aka fitar har da kayanmu kome nawa da nayi amfani da shi sai da aka tattara domin single mistake zai iya zama tashin hankali a rayuwata, Hajja ce ta bada sautun kada abar koda chew gum ne idan na tauna to a dauko kada a barshi wurin, shi yasa kome sai da aka tattara hatta sharan da aka yi ana kwashewa Aunty Shukrah ta saka wani bakin leda ta kwashe tasaka a jakarta, ba wai rashin tawali'u ba ce a'a mutanen nan Allah ya basu duniya tow da ita zasu kashe ka har lahira. Haka yasa koda muka nufi wurin taron ni daya babu ango. Ran yan uwansa ya b'aci domin ba haka suka so ba, nima koda muka isa ban fita ba dole sai ya iso. Wurin karfe biyar da rabi sai gashi tare da da matarsa, duk da abin yi bakanta ran kowa amma ganinsa kuma sai yasa kowa ya manta abinda ya faru. Haka suka fito da ni, kaina a cikin net, ba zaka iya gane fuskana ba, haka muka jera a cikin wurin taron, kome na wurin yayi kyau ba laifi haka muka zauna aka yi ta hidima har da busa, wurin karfe biyar da arba'in aka tashi muka nufi Fada a mota yayin da shi da yan uwansa da Faruq suka hau dawakai domin yin kilisa, lokacin da muka isa gida su kuma suka fara, a kofar shiga Fada aka ce na tsaya, a can basu wani zuba kudi ba sai anan ne na san yan uwansa mahaukata ne, domin kudi suke zubawa.
Dangin Abba da na Maluma da na Umma suma suka ce basu iya ji ba, domin kudi suke zubawa har da CFA wanda yasa kowa a wurin sai da ya kalle su, ance sun zuba CFA dubu dari uku da hamsin. Aunty Shukrah da yake Ya Abid yana harkan trading na cryptor dollars tayi ta zuba, haka ya janyo kananun magnaa, Iram da bata zo ba sai a lokacin, don ni ban zaci zata zo ba, tana zuwa key mota ta saka min wnada ya janyo aka sake rangad'a gud'a me karfin gaske aka fara mata kirari. Gefena tazo ta tsaya tana magana kasa-kasa. "Am sorry! Ban san yadda xan gaya miki ba, amma ni na rigaki fara sonshi domin yayi min tun ganin farko, amma Abba ya min fin karfi ya baki, ina baki shawara ki rabu da shi bana son a cutar dake akan shi domin nima ina sonshi." Idan nace ban kadu ba ai nayi karya domin ji nayi kamar babu jini da numfashi a jiki, ji nayi kamar ina jan nunfashi da kyar na kalleta a hankali. "Kin san me kika faɗa?" Juya idanu tayi tana murmushi ta ce min. "Wancan basaraken nake so ki rabu da shi, duk da nasan ba son shi kike ba, ki rabu da shi ban miki alkawarin zan baki kyautar da baki zata ba?" Ta nuna mishi da yatsarta. "Duk da bana sonshi, sai dai ba zan iya rabuwa da shi ba, na shirya tsaf domin kyautatawa Abba, kuma zan yi mishi biyayya koda rayuwata zan bada."
Kallona tayi nima na kalle ta, cikin idanu. "Kina tsammanin zaki iya ja da ni?" Murmushi nayi nace mata. "Hala baki ana karfin muryan yan jarida ba ne, kuma a bayana baki san wanda ya tsaya min ba ne." Murmushi nayi cikin kwarin gwiwa na ce mata. "Ina ga ba iya ke ba, ga duk wanda ya tab'a ni, ina da Angel of the guardian da yake kare ni, wanda shima Allah yake kare shi. Kin yi kuskuren shiga gonar da bata ki ba, ina miki fatan ki isa gida lafiya!"

Daga haka na aro murmushi na daura a fuskata. Ban san lokacin da tsoron wancan Dracula din ya gudu a raina ba, amma ina ji a jikina duk motsina akan idanunsa yake, don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login