Showing 177001 words to 180000 words out of 304445 words
mishi. "Kasan password dina akayi login na account Dina kawai!" "In sha Allah gobe da safe za a kawo miki!"
Kashe wayar nayi na barshi ya amshi iko da account din, bayan na gama ci na fitar da plat din na dawo parlourn na cigaba da kallona, can na wuce naje nayi abinda zan yi, sannan na kwanta ina kwanciya barci yayi gaba da ni, shima haka ya shigo ya kwanta. Kwana biyu da yayi ya fita abinsa ban ji kome a kanshi ba, ranar ya koma hannun Ijlal, ina jin yadda aka hana mu sakat, karshe haka na watsar da su, ina kwance a parlourna sai ga shi ya shigo. "Kin san da zuwan kaninki?" "Eh!" Fitowa nayi sanye da doguwar riga sai hula a kaina juyowa yayi yana min wani irin kallo, juyawa nayi na koma dakin na dauko hijab n a saka na same shi a parlourn, "Gatan marayu, uwar marasa uwa baya goya marayu, mai uwa da uban ma kin goya kaf Zanzabira ke daya kike bani dubu ashirin domin na jadadda karamata ta kashe kudi ina godiya Yayata ta kai na, Mata a gidan Yaya Salmanu Faris, magajin zanzabira miji ga Sarauniyar zanzabira." Ya mika min jakar tare da cewa. "Gasu nan, jiya mun je da Chokuna ce ita ta taya ni saya itama taci daga arzikinki n aantaya mata dubu hamsin kin san mata ne sai da kashe musu kudi!" Ya fada yana sosa kai. "Allah ya dube mu ya shirya ka!" "Amin Ya Allah, don ma ban ce miki zan kawo miki ita ba!" Ya fada yana mijewa yana faɗin. " Nayi log out?" "Na gode ka saya min yoghurt din ko?" "Eh ki duba!" Ya fada yana mikewa. " Na gode sosai!" Har zai fita ya ce min. "Kina ta godiya ki turo min kudin hana ni barcin safe da kika yi, Dr na gode sai an jima!"
"Na gode sosai!" Har zai tafi ya dawo da baya ya durkusa a gabana. "Nasan ke ba me yawan surutu ba ne, amma ke din me yawan fara'a ce me ke damunki?" Hawayen da nake dannewa ne ya zubo min. "Gaya min me aka miki?" A hankali na fara sheshakar kuka ina faɗin. "Babu kome Ibrahim!" Rike hannuna yayi yana faɗin. "Ke ba mai yawan kuka ba ne, ke jaruma ce tun muna Yara gaya min me yake damunki? Ko abokan zamanki suna miki wani abu ne?" Girgiza mishi kai nayi, rayuwar aure yana bukatar sirri sannan idan na gaya mishi ya hana ni zuwa hidimar gobe zai fara tunanin Salmanu Faris yana azabtar da ni. " Ka gaida min Umma!" Na tashi nayi zan bar parlourn ya ce min. "Maluma fa?" "Maluma ta tsane ni, tayi sabon d'a madadaina!" Na barsu nan a tsaye, kallon Salmanu Faris yayi da kyau ya fa yadda yake wani kakkauda da kai. "Matarka ce, amma idan ta cigaba da kuka tana boye abinda aka mata zan ji na tsane ka, kayi hakuri yar uwata ce amma nasan bata ji tana da taurin kai, sai dai duk da haka ya dace a dinga duba girma da alkhairinta." Ba wannan maganar yaso fada ba, amma haka yayi shiru. Haka na kama aiki ina kuka, har wurin karfe daya ina abu daya ,nayi abincin a babbar kula sai kunun aya da nayi wanda yaji kwakwa da madarn condisen, na zuba a gora na saka a firji wurin karfe biyu faruq ya zo ta dauka masu, don matan gidan tun ƙarfe sha daya suka bar gidan.
***
Emirate council meeting
Karfe takwas na safe Mai Babbar daki ta samu marabtar baki daga cikin masarauta talatin da biyar na cikin jahar zanzibar, sarakunan yanka da suke ƙarƙashin Zanzabira, hakimai da dagatai, masu littafi da masu unguwanni. Sun hadu a wurin mai babbar daki duk da bata yi mamaki ba amma kuma tasan wannan aikin Alhaji Nuru Yayari, don haka ta ce a kai su babban parlourn Marigayin gata nan zuwa, haka ta shirya ta nufi parlourn dukkansu suna zaune a kasa tana shiga ganin haka sai ta dauki daya daga cikin matashin da suke parlourn ta zauna a gefenshi sannan ta kishimgid'a tana jin shi, aka shiga gaisawa, aka yi dan jajjen rasuwar marigayi kafin suka kawo mata zancen da ya kawo su, murmushi tayi kafin ta ce musu. "Maganar gaskiya shi Yarima baya son abin da ya shafi rayuwar gidan Yayari, ban san dalilinsa ba, amma ina martaba duk abinda ya ce baya so, kasancewar Allah ya karkato min da hankalinsa gare ni bana jin akwai dalili mai karfi da zai saka na cire shi a jikina baya son kome ya fi son zama lafiya akan wannan lamarin."
Gyara zama wani dagaci yayi wanda yafi sauran yawan shekaru ya ce mata. "Ki duba dai Mai Babbar daki, al'amarin nan sai kayi wanka cikin tabo kafin ka wanke kanka da tsaftacecciyar ruwa!" Girgiza kai tayi ta ce mishi. "Bana jin sai nai wanka da datti kafin na wanke shi da sabulu, abu ne na cusa rayuwa hatsari tunda ya ce baya so ina ga a bar shi kawai!" Duk yadda suka so tayi wani abu amma taki ba don kome ba, sai don Allah ya gani zuciyarta bata yarda da son wani mulki ba, idan har aka shigar da shi cikin masarautar rayuwarshi da iyalinsa na cikin hatsari, bata son fitina ko tashin hankali sannan bata son nutsuwar da yake da ita ya rasata, tunda tasan rauninsa mace ce a yadda yake da sanyin nan za a cutar da shi, gara ta hakura da duk wani abinda zai saka shi yin danasanin dawowa gida, wani lokaci kana son wani abu amma kake hakuri da shi, domin iya lokaci ne yake zab'a maka matsayarka.
"Ba zaki duba ba?" Suka kuma tambyarta dakatar dasu tayi cikin tsumewa wanda ya fitar da asalin yanayinta, na sarauniyar Zanzabira wacce babu wata bayan ita cikin wani irin zama da mulki wanda kana gani kasan abin a jininta da jikinta yake, mulki sarauta, dukiya ta gaje shi daga wurin Mahaifinta da mahaifiyarta, ita din daya ce daga cikin ahalin shehun Borno, don haka izza da kasaita a jininta ne, sukar da idanunta tayi kasa ta d'ago shi a hankali ta zuba musu a hankali cikin wata irin murya mai nuna alamar maganar da zata yi da gasken gaske take yinsa ta ce musu. "Ni nake da zabin da zai bi, amma bani da ikon halatta mishi abinda ba zai zama dolenshi ba, shi ɗa ne, ba bawa ba ya gaya min burinsa yayi aikin asibiti da kula da majinyata, ba mulki da matsalolinta ba, kowani mutum yana da zabi bana son na sare mishi gwiwa, yayi yadda yake so idan Allah ya nufa zai yi mulkin zanzibar ba makawa zai yi ko ana muzuru ana shawo, yanayinsa ne baya bukatar dole!"
Gyada kai suka yi yadda tayi maganar ko uban waye dole ya sarara mata balle ita ce Uwar duk wani a Zanzabira, jin haka yasa suka shiga bata hakuri domin sun gano kuskurensu na son lallai ta amince, daya daga cikinsu ya ce mata. "Zamu jira ki koda kuwa ace mutuwa zata aiko mana da sakon tana zuwa gare mu. Zamu jira har ranar da zaki kara kiranmu a karo na biyu mu dawo nan, Attahiru mutumin kirki ne, koda za a bi mu daya bayan daya a mana yankan rago zamu tabbatar da mun biya halaccinsa a gare mu, ki huta lafiya Allah ya huci zuciyarki amma muna nan muna jiran sakonki zamu yi dakon sakonki ba dare ba rana har zuwa lokacin da Allah ya diba mana."
A bayan nad'a Rilwanu Yayari bakiɗaya dagatai da hakimai basu mara masa baya ba, domin har yanzu akwai wannan traditional rules din a tare da su, sannan suna kallon abinda aka yi kamar son kai ne, sannan suna rike da wannan ritual na cikin tsohuwar masarautar da cewa, matukar amintaccen sarki bai bayyana ba tow su ba su marawa wanda aka zaba baya ba, saboda akwai babban al'amari da zai iya faruwa sun yarda da cewa matukar aka ki bawa Sarkin da yake da ikon zama sarki mulki tow akwai wani masifa da zai iya faruwa ko ya sauko musu domin salsala ba karya ba ce.
Koda Alhaji Nuru Yayari bai gayyato su ba, su dama zasu zo domin kansu sai gashi ya saka musu magana a bakinsu. Kowa yasan yadda zanzabira yake mutanenta basu san tsoro ko fargaba ba, ba tab'a cin su da yaki ba don ko zuwan Musulunci bai nakasasu ba, sai da aka samu wasu suka marawa dakarun Muslunci baya yadda ta haka ne kawai aka shiga har aka cisu da yaki amma suna da tarihin da baka isa ka ci su da yaki ba, jarumai ne kuma sadaukai ne, basu san me ake jira tsoro ko ja da baya domin babu shi a cikin alamarinsu. Strong bloodline yana yawo a jikinsu.
Bayan tafiyarsu bude idanu tayi ta ji kanta yana mata wani irin ciwo, a dan maganar da tayi sai take jin kamar kanta na damunta, ta jima sosai har sai da Sailuba ta biyo ta,.ta same ta a zaune a wurin tana nazarin abinda ya faru. Murmushi tayi ta mike. "Kin ji ni shiru ko?" "Eh ranki shi dade!" "Muje Sailuba!" Suka cigaba da tafiya har cikin gidan, a parlourn ta zauna tana kallon Yar wurin Aneesah da take zaune tana cin abinci. "Kun sabarwa Yaranku rashin karyawa da wuri!" Murmushi Aneesah tayi domin kwana tayi a gidan, idan da zaka tona zuciyar Mai Babbar daki, ka tambaye ta mene ne matsalar ta zata gaya maka Aneesah da bata iya zaman gidanta saboda fitar dangin mijinta, tun Mai Martaba yana raye kasancewar yan uwa ne wanda yake aurenta Mahaifiyarshi kanwa Attahiru Yayari ne, Uban mijin kuwa kusan abokai ne amma, idan ka cire yadda zaman yake an yi shari'a yakai sau goma amma kullum abu daya ne, gashi Allah ya bata haihuwa daya bata kara haihuwa ba, sai dai wannan zuwan da tayi zata yiwa Tufkar hanci domin ta gaji da case din Aneesah.
Wurin karfe sha biyu aka fara cika a gidan har da Yaran sauran matan, duk da suma wani suka zo amma wurin Mai Babbar daki suka tare ne,.anan aka yi ta hidimar Abinci, karfe daya. Faruq ya shigo musu da babban kular abincin, yana ajiyewa sai ga wasu dogarai da sauran kayan abincin Aneesah ta cewa Daularh. "Yarinyar nan tana da niman suna, ji yadda take hidima kamar an sakata.".......
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 59
"Ba saka ta aka yi ba, sai dai na fahimci har da mugun nufinki yasa yan uwan Mijinki basu sonki, kamar yadda suka tsane ki haka kema kika tsani Zainab, a lissafina idan aka gama hidimar sallah na shiga lamarinki amma yanzu na hakura ki zauna a inda kike idan kin san fitina zaki kawo min zaki iya komawa gidanki, ki cigaba da zaman ukubar da kike!" Shiru tayi bata ce kome, don tasan tunda mai babbar daki tayi magana tow wallhi zata iya koranta hatta su mai gado da Kubra sai suka kama kansu, wurin karfe biyu Nady ta shigo, tana me ajiye bokitin nama da wani katon tambulam da dambu ta gaida Mai Babbar daki da sallah sannan ta koma can gefe tana duba wayarta. Da yake sun san abinda suka yi basu sake jiki da ita ba, sannan itama Mai Babbar daki cikin kulawa take kallonta ta ce mata. "Ya jikin naki?" Dan yake tayi ta ce mata. " Da sauki na kusan komawa a duba ni!" "Tow Allah ya baki lafiya yasa zakkar jiki ce!" "Amin Ya Allah!" Tana zaune sai ga Ijlal, yadda ta shigo ta gaida kowa ta ajiye nata abin sallah, sannan ta nemi wuri ta zauna tana ta iyayi tana wani narkewa ita mai ciki, aka ta hira Sailuba sai raba idanun take tana kallon hnaya cewa take. "Ranki shi dade, hala Uwar dakinmu ba zata zo ba ko?" Ta fada ya kai sau uku, tana bawa mutane abincin. Sai da aka yi sallah wasu suka ji dadin cin abincin, gudar Iyaami ne ya karade gidan, kirari take tana karawa. (Sorry 😐😔 😔 i don't meant na zuga Zainab but tun farkon Labarina na gabatar muku da Zainab and ban yarda na wulakanta nady ba domin kowa yana da bad side dinsa idan nayiwa wani kuskure a labarin nan yayi hakuri maganar gaskiya Zainab ita ce Female lead ko Ijlal na barta ne saboda akwai mata Mahaukata irinta masu shigowa gidan miji don su fitar da ta ciki)
A hankali Faruq ya shigo hannunsa dauke da wata katon roba mai farin murfi, bayan shi wasu dogarai ne dauke da irin katon roban nan, abin gwanin ban sha'awa, yana tafe suna bin shi bayan Faruq da yake gabanshi, haka ya wuce kowani bangaren ya gaishe su da sallah, sannan ya wuce bangaren Mai Babbar daki, bai shiga ba sai da ya sallame Iyaami kafin ya shiga parlourn Mai Babbar daki, a nan ya same shi cike da mutane. Har gabanta ya isa ya gaishe ta, sannan ya zauna ta saka mishi albarka, kafin ya mike zai fita sauran yan dakin suna ta gaishe shi, yana amsa musu da kai. Sarkin Fada da ya shigo yana amsa musu, "Ina Zainaba?" Sunkuyar da kai yayi yana murmushi ya ce mata. "Bata jin dad'i ne." Ya furta a hankali, "Tow Ubangiji ya bata lafiya!" Duk da bata yarda da shi ba, amma sai bata ja al'amarin yayi nisa ba, ba dai girki ta iya ba zaman aurenta bata sai an gaya mata abinda ya dace ta cigaba da dafa musu abincin.
A yadda yake ganin sauran matan na walwala sai yake jin kamar bai kyauta ba, yasan da tana nan da tana can gefen Mai Babbar daki tana iyayi da shagwab'a kamar ita Mai Babbar daki ta haifa, shi ya rasa yadda aka yi ta shanye mishi uwa, bayan shima ya manta Maluma tana tare da shi abun sai ya koma kamar kishi ake da juna. Mikewa yayi ya bar gidan suka nufi massalaci, a can bayan sun yi sallah la'asar, kamar ance ya dawo gidan ya samu itama tayi baƙi. Sai yayi ta mamaki Aunty Shukrah da Yaranta biyu sai Yeemar da itama da Mijinta ya kawo ta. A hankali sai yayi ya samu nutsuwa, bai yarda ta ganshi ba ya juya abinsa ya bar gidan, dama ya zo takalarta da rigima ne ganin yadda aka zo mata sai ya ji babu amfanin d'aga mata hankali, waje ya fito ya samu Faruq suna hira da security din gidan, da Ya fito suka ce mishi. "Sir ayiwa Madam godiya ta bamu abincin sallah har da Nama thank you sir Allah ya kawo mata Yara uku every year, ta maka full da Yara a gidanka!" "Amin Bitrus!" Inji Faruq idan ya ce bai ji dadin addu'ar nan ba yayi karya, Allah ya gani yana son hada jini da ita ko don ya ga yadda zata yi da shi amma yasan kiyayya ba karya ba ne, hannu ya saka a cikin aljuhu ya zaro kudi ya mikawa Faruq ya basu, godiya suke ta yi don farin ciki kamar su kwanta su uku ne, ya basu dubu dari goran sallah. Bayan albashinsu, ana basu yan allowens domin su ji dadin Allah aikin, domin daga sama aka turo su,
Tunda suka fara aikin zuwa yanzu babu wanda zai ce bai samu a jikin Faris ba, domin irin mutanen nan ne masu kyauta kamar basu so. Bayan tafiyarshi haka kawai jikina ya bani yazo gidan koda na fito parlourn kamshi turarenshi yana nan a parlourn ban san me yasa nake son na tabbatar ba, amma ai ko fitarshi ba rabuwar arziki muka yi ba, haka yasa na share can dai kamar wacce aka mintsine ni na fito waje, na ga alamar ya zo gidan amma domin na tabbatar sai gani har kofar gidan. "Officer oga ya shigo ne?" Na tambaye su, "Yes ma ya zo yanzu ya fita I think wani abu ya dauka!" Yake nayi na ce. "Ok thanks!" Na juya. "Karya ce ba wani abu da ya zo dauka shi dai ya zo kara d'aga min hankali ne ya ga yadda xan yi tunda yana sane Nady tazo har kofana tana faɗin. "Zainab zan shiga wunin cikin gidan." Da bata yi niyyar zuwa ba, ina ga kwayar da ya sha a kaina ne bata sake shi ba, shine ya birkita musu lissafi. Har zata ta fi can ta kara min magana mika min wasu kula tayi tana faɗin. "Ga namar layya da muka soya, duk da na ga shi bai damu da namu ba naki ya ci har yau bai ci nawa ba!" Yadda ta iya fadar abinda yake ranta sai ban tanka mata ba na ce mata. "Na gode, nama da yake bi ai ba shi ya bani ba, nima mai babbar daki ta kawo min. Kin ga kenan dole na rike abina tunda ya iya yanka ya haramta min don nayi nawa na haramta mishi ba laifi ba ne!" "Na gaya mishi ai bai kyauta ba." Wani irin kallo na mata na ce mata.."ke da kike jira ta haɗa mu da shi ne zaki mishi magana idan wani ya gaya min zan ce karya ne, domin bakin da ya fada maka mutuwa zai yi matuƙar wahala.ya gaya maka rayuwa, haka bakin da ya gaya maka rayuwa tow yana kaf-kaf ya gaya maka mutuwa. Idan akwai abinda kike bukata ki gaya min don nasan ba kya kaunata tunda ni kishiya ce so mene ne?"
Rab'a gefena tayi ta shigo