Showing 297001 words to 300000 words out of 355604 words
ka kula mani da kanka sosai sannan kuma kada ka barni da kewarka sosai, idan ka jima baka kirani ba zan yi kuka, ni please ka bani real number ka ka ji?".
Nisawa ya yi cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa tare da jan hankali ya ce "Heartbeat kin gama yi mani komai a duniya, wannan addua'o'i da kika yi mani serious ba zan taɓa mancewa da su ba, a really love, ina fatan ki zama mallakina na har abada ni kaɗan, ba zan so na rasaki ba domin idan hakan ta faru zan shiga tashin hankali wadda wata kila ya zama sanadina, gaskiya ba zan mance da wannan rana ba, sannan na yi maki alkawarin ba zan taɓa barinki da kewana ba bugun zuciyata, tabbas zan kira ko kuma na tura maki saƙo, fata na dai ki kula mani da kan ki, kuma kada ki yi wa yaya Irfan wannan kayatatcen murmushi naki, idan ba haka ba kika yi mashi murmushi to ki rubuta ki ajiye tabbas zan yi kuka da hawayena, ni ba zan taɓa hanaki yin hira da shi ba for now, amma dai kada ayi mashi murmushi".
Jinjina mashi kan ta yi tare da faɗin "Shikenan tom zan yi kokari na kiyaye duk wani abin da kace bakaso ko kake so, amma tom ka turo mani hotonka mana in gani, na san cewa ni kam ka san ni tun da har ka kamu da sona, to tabbas ka sanni, please kai kuma ina son ganinka ka ji?".
"Heartbeaaaaat ba zan bari ki ganni ba har sai kin kamu da sona kamar yadda nake jin naki azababben soyayyar, sannan kuma ni ba hoto zan tura maki ba, kai na zan kawo maki har gida kin ji ko?".
Gyaɗa mashi kai ta yi kamar tana a gabansa, jin bata yi magana ba alamar bata ji daɗi bane yasa ya ce "Am so sorry my bugun zuciya zan tura maki hotona kin ji ko? Ton da hakan kike so zan tura maki da daddare yanzu dai please ki yi murmushi bana son idan kina magana dani face ɗin nan naki ya zauna babu murmushi, kuma kin ga ai ina son murmushi naki sosai ko?".
E ta amsa mashi da shi "To arinƙa yi mani murmushi zan ji daɗi sosai da sosai, yanzu dai zan tafi sai na dawo ko?".
To da amsa mashi da shi, shiru suka ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ce "I really love you more than your expectations". Ya yi maganar cikin wata iriyar shagwaɓa mai mugun janhanlin mai sauraro tare da kwantarwa da masoyi zuciyarsa.
"Heartbeat" ya ambaci sunan ta, "Na'am my heartbeat" ta amsa. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Heartbeat ina matukar san in ji kalmar soyayya ta fito daga bakinki zuwa gare ni kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi tare da cewa "I love my heartbeat". Wani irin numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya ce bye my heartbea. Bai katse kiran ba har sai da ta amsa mashi da bye ɗin ita ma, kiss ya yi wa jikin wayar tasa kafin ya katse kiran.
Shiru ta zauna a saman bed ɗin tana tunanin a ina tasan wannan voice ɗin, tabbas koba wannan muryar bane ta taɓa jin makamanciyarta a tare da wani na kusa da ita, to waye zai iya kasancewa? Ta mance ba zata iya tunawa ba.
Ta jima zaune a wajen tana jujjuya kalaman heartbeat nata a cikin ƙwaƙwalwarta kafin Irfan ya kirata a waya akan ga shi ya zo yana ƙofar gida.
Da sauri ta ɗauki wayarta ta fito, ta yi Sa'a palon kasa babu kowa, Ammie tana cikin ɗakinta, cikin sauri ta wuce waje dan ma kada wani abin ya dakatar da ita.
Zaune ta isko shi a cikin motarsa yana ɗan latsa wayarsa, ganinta yasa ya fito daga cikin motar da sauri tare da zagayawa ya buɗe mata ɗayar ɓangaren, sai kallonta yake yi ya kasa cire idanunsa daga kanta dan gaskiya babu karya ta yi kyau sosai yau ɗin nan.
Front seat ta zauna shima ya koma nashi ɓangaren ya zauna, cikin natsuwa ta ɗaga mashi gaisuwa, da faraa ya amsa tare da tambayar ya ta kwana daren jiya, kanta na kallon kasa ta amsa mashi da lafiya tare da ce mashi tana jin yunwa.
Ɗan leƙo furkarta ya yi cike da zolaya ya ce "Za'a bani abincin a baki idan muka je wajen cin abincin?" Hannu tasa ta rufe fuska tana ƴar dariya ta manta yadda suka yi da Heartbeat nata yanzu, ya ce mata ko murmushi kada ta yi bare kuma dariya, to ga shi dai ta mance ta yi dariya.
"Yaya Irfan Allah ka bari bana so" ta faɗa tana kara rufe fuska, hannayenta ya riƙo dukka biyu yana faɗin "Allah heartbeat wannan tsiyar taki ta isheni maza buɗe idanunki ki kalleni". Make kafaɗa ta yi tana kara runtse idanunta.
Hannun yasa cikin wasa yana ƙoƙarin buɗe mata idanun nata da gaske, faɗawa saman kirjinsa ta yi tana dariya tana faɗin "Allah yaya Irfan zan yi maka kuka idan baka kyaleni ba".
Mutuwar zaune ya yi har ga Allah babu wata macen da ta taɓa kwanciya a jikinsa sai Umaisha lokacin da take karama, lokacin da Ommu ta tafi ta barta, a lokacin ya sha goyanta sosai, bayan ita babu wata da ta taɓa zama a jikinsa, ko Aafia bata kwanciya a jikinsa sai dai ya riƙo hannunta, ita ma Umaisha da ta kai 10 years ta daina kwanciya a jikinsa sai dai ya riƙo hannunta, yau rana ɗaya Akila ta kwanta mashi ajikinsa, abin ya sanya shi sumar zaune, ya kasa motsawa saboda wani irin yanayi daya tsinci kansa a ciki.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ɗago kanta tare da shagwaɓe murya ta ce "Yaya Irfan zanyi maka kuka Allah idan ba mu tafi wajen cin abinci ba". Wannan shagwaɓa tata ba karamin sake haukata shi ta yi ba, haka kawai ya tsinci kansa da rungumeta sosai a jikinsa, bata wani damu ba saboda tana yi mashi kallon yayanta kamar yadda take kallon su Imran, kuma idan baku manta ba ta saba kwanciya a jikin Imran da Akil sosai da sosai shiyasa shima Irfan ta ɗauke shi kamar su Akil ɗin.
Itama rungume shi ta yi tana kara zuba mashi shagwaɓa, rankwafo da kansa ya yi a daidai sai tin tata kafin nan ya ambaci sunanta da wata iriyar murya wadda ta sanya ta jin faɗuwar gaba tare da ɗagowa da kanta cikin sauri, tana ɗagowa fuskarsu ta haɗu waje guda sakamakon ranƙwafo da kansa da ya yi daidai tata.
Kuskure ne dan kuna causing da mutun kuma kuna soyayya da shi kice zaki ruƙe mashi hannu ko ki kwanta a jikinsa, wannan babbar kuskure domin kamar yadda ya ji sha'awar yin soyayya dake a matsayin ku na causing haka zai ji sha'awar jikinki ya kuma ji felling akan ki, so wannan kuskure kwatanta abin da Akila ta aikata, yaya uwa ɗaya uba ɗaya daban, jinin dake guda a jikin ki da nashi iri ɗaya ne domin daga waje guda kuka sami jinin, sai dai wata hikima ta Ubangiji da yake banbance jinin dan samun maslaha, Allah mai ni'ima akan bayinsa, ya yi mana ni'imar banbantawa yaya da kuma kanwa jinin sune bayan kuma daga waje guda suka sami jinin, Allah ya banbanta mana ne saboda dalilin da dama, kaɗan daga ciki kuma akwai cutuka, kamuwa da cutuka, idan jininku ya kasance iri ɗaya sak to idan ɗaya ya kamu da cuta kuna gida ɗaya zaka iya ɗauka kai ma cikin sauki, amma idan jininku ba ɗaya ba, ba kallai ka kamu da wannan cuta cikin sauri ba, Ubangijin ya yi mana niimomi da dama me yasa mu ma ba zamu zage dantse wajen gode mashi ba?.
Zuba mata idanu ya yi yana ƙare mata kallo, ita kuma kirjinsa take kallo yayinda hannunta yake a saman butir na rigarsa tana wasa da shi.
Heartbeat ya sake ambatar sunan ta da murya can kasa kasa, na'am ta amsa mashi da shi ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba.
"Heartbeat ina sonki sosai, ban taɓa yin soyayya ba sai a kanki, ban taɓa zama da mace kamar haka ba sai a kanki, ban taɓa zama nayi hira da mace ba sai a kanki, ban taɓa ruke hannun wata mace ba bayan su Aafia sai a kanki, ina yi maki soyayyar da bana yi wa kaina ita, please ki ruƙe mani amana,! idan na narasaki zan shiga mawuyacin hali, ba zan ɓoye maki ba, na taɓa son wata wadda bata san ina yi ba, amma Allah bai kaddara ba, ta yi aurenta, akwai wannan tabon a zuciyata, dan Allah ki kula mani da kanki domin zuciyata ba zata iya sake ɗaukar wani taboba, komai kankantar wannan tabon kuwa zuciyata ba zata iya ɗauka ba, zan cutu matuƙa wata kila kuma sai dai in ce Allah ya bamu kyakkywar karshe" ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai kama da wadda zuciyarsa ta karaya da abu.
Ɗago kanta tayi hawaye na zuba daga kumatunta yayin da shi kuma idanunsa suka yi jawur kamar jini, amma da yake soyayya yana ganin hawayen idanunta ya sa ya ji hankalinsa ya tashi, gaba ɗaya ya rasa natsuwarsa, cikin sigar rarrashi ya ce "Haba my heartbeat menene kuma ya faru kike kuka? Me akayi maki?".
Duka ta kai mashi a kirjinsa tare da rungume shi sosai tana faɗin "Yaya Irfan meyasa zaka ce haka? Meyasa kake tunanin cewa ni zan barka? Me yasa zaka yi mani haka? Kana ganin hakan adalci kayi mani ne?".
Har ga Allah a cikin zuciyarsa yana jin tamkar wani abu zai faru shiyasa ma ya yi mata wannan maganar, amma da ya ga tana kuka sai ya ajiye zancen a gefe ya shiga rarrashinta babu kama hannun yaro.
Sun ɗan jima a haka kafin nan su dawo daidai, daga nan suka cigaba da soyayyarsu, gudun kada wani abin ya gifta a tsakaninsu na daga sharrin shaiɗan yasa ya ce mata ta tashi daga jikinsa bari ya kunna motar suje wajen cin abinci, to ta amsa mashi da shi, har ga Allah yana jin matukar daɗin kwanciya a jikinsa da ta yi amma gudun kada sheɗan ya yi galaba a kansu ne yasa ya ce ta tashi ba dan yana son su je wajen cin abincin yanzu ba, sai dan yana son ta bar jikinsa domin kula da addini da kuma al'adar mu.
Kunna motar ya yi suka bar wajen, kwata kwata ta manta da cewa bata gayawa Ammie ba, kawai ita dai ta bi yaya Irfan ɗinta abinta.
TSAKANIN YAYA IRFAN DA ƁOYAYYEN MASOYI WAYE KUKE TUNANIN ZAI YI NASARA? KO DAI DUKKANSU ZASU RASA NE? MU DAI JE ZUWA, ITA DAI AKILA GABA ƊAYA TANA SON SU KO MA DAI ACE BATA SAN ME TAKE SO BA TA KAIMAIMAI!!.
A ɓangaren su Jehan kuwa, bayan fitar Zinariya bai fi da minti ɗaya ba Jehan ta miƙe tana ruƙe da wayar Adiva ta shiga toilet, su kuma suna zazzaune a bakin bed ɗin suna jiranta.
Tana shiga ta ajiye wayar hannunta a saman gefen baff ɗin wanka, sannan ta cire kayanta ta yi fitsari, bayan ya gama abin da zata yi dukka sai ta ɗauki wayar tana ƙoƙarin gyara kayanta, a juge su Adiva suka faɗo cikin toilet tare da banko kofa A'isha ta sanya sakata.
Da mamaki Jehan take kallon su kafin ta ce "Lafiya Adiva, Maryam me ya faru kuka biyo ni cikin toilet haka?" Ta faɗa tana kare masu kallo.
Sai haki suke yi tare da jan numfashi sama sama, Aisha ce ta ce mata "Jehan wlh Zinariya ce suka dawo ita da ƴar gold hannunsu na ruƙe da wasu shegun bulalu shine muka gudu kuma...." Bata kai karshen maganar ba suka ji an murza key ɗin kofar ta baya alamar an rufe su a ciki kenan.
Zinariya ce ta rufe kofar tana faɗin "Dan ubanku yunwa ne zai halakaku acikin toilet ɗin nan, ba ku ba fita waje shegu marasa galihu". Sai surfa uban masifa take yi har suka fice daga ɗakin.
Zama a gefen baff ɗin wanka Jehan ta yi tare da kunna wayar Adiva ta fara dube dube akan shedun da ta tara na gidan nan, duk hirar da Aisha ta yi mata ranar akan abin da Hajiyar daɗi take yi na daga sayar da kodar mutane da saurasu, dukka Jehan ta yi recorded na komai a cikin wayar ta ajiye, ga kuma video wannan Alhajin shima babbar shaida ce a gare ta, bayan haka kuma ta yi video Zinariya in da take magana da Alhajin akan ba ya zaɓi yarinyar da yake so ba? Dan haka ya wuce ɗakinsa, shima wannan babbar shaida ce wadda in dai ana bin gaskiya da adalci iya waƴan nan sun isa a kashe Hajiyar daɗi tare da ruguje magoya bayanta, sannan kuma ba iya haka Jehan ta tsaya ba, har da office nasu ta ɗauka hoto da video da kuma wasu tsirarun mutanen dake a cikin gidan, ta tara shaidu da dama wadda zata ruguje Hajiyar daɗi da su, sai dai kashe wayar Adiva babu kati kuma babu data, tana son ta yi posting na wasu daga cikin shaidunta wa duniya kowa ya gani amma babu hanyar yin haka sannan kuma bugu da kari basu da network a cikin gidan, Network ɗin nasu ya zo ya ɗauke ya zo ya ɗauke haka yake, kuma Jehan bata wani damu sosai ba, domin tasan idan ta fara posting nasu a Media ma to tabbas Hajiyar daɗi zata fara bincikar waye mai yi masu hakan, idan suka kamata kuma da wuya su barta da ranta, hakan yasa bata damu ta nunawa duniya abin da yake faruwa ba har sai ta fita daga cikin gidan.
Zama suka yi a gefe gefen baff ɗin wanka dake a cikin toilet ɗin, tunanin makomarsu kawai suke yi, abin yana damunsu, ga shi waƴan nan shegu sun rufesu a cikin toilet ɗin ma baki ɗaya.
Miƙewa Jehan ta yi tare da hawa saman baff ɗin ta keƙa window toilet ɗin, bata iya ganin komai a wajen sakamakon kura da ya baibaye window ta waje, guntun tsaki ta ja tare da komawa ta zauna tana faɗin "A'isha dama sun taɓa yi maku irin haka ne su rufe ku a cikin toilet?".
Shiru Aisha ta ɗan yi kafin ta ce "E sun dai taɓa yi wa wata yarinya wadda ta zagesu lokacin Hajiya bata nan, shine sai suka rufe yarinyar a cikin toilet sai da ta yi sati ba ruwa babu abinci, ranar da suka ji Hajiya zata dawo shine suka yi maza suka zo suka buɗe yarinyar, wlh time da suka buɗe yarinyar nan ko miƙewa bata iya yi sai da aka ɗaga ta aka kaita cikin ɗaki, wannan ma fa tana shan ruwan cikin toilet ɗin kenan, da Hajiya ta dawo sai suka ce ai bata da lafiya ne, da haka maganar ta mutu, Hajiya ta kira wasu daga cikin likitocin ta aka duba yarinyar akayi jinyarta ta warke, wlh Jehan idan hajiya bata nan Allah waƴan nan tsinannun suna iya yin kisan kai su ce kwanan mutun ne ya kare na gaya maki".
Shiru Jehan ta yi tana ƙoƙarin saving na recorded da ta yi wa maganar Aisha na yanzu, duk wani tambaya da zata yi wa Aisha sai ta kunna recording dan ta naɗi komai domin samun hujjoji da sheidun yadda zata rushe wannan tsinanniyar gidan.
Bayan tayi saving ne sai ta ce "Tom mu dai dan ubansu dole su buɗe mu ko kuma mu karya kofar muga uban da za'ayi shegu tsinannu duk sai na ci ubansu, ba akwai hitter a cikin toilet nan ba?" Cikin sauri Aisha ta gyaɗa mata kai Alamar e akwai.
"Yauwa jona mana ruwan zafi ki gani, zamu bubbga kofar da iya karfin mu, idan suka zo suka buɗe mu suna nuna alamar zasu cutar da mu muyiwa shegu wanka da tafasasshen ruwan zafi fatar jikinsu ta saɓule mu kuma ci uban shegu sai muga uban da ya tsaya masu, shima wadda ya tsaya masu idan ya zo idan da dama sai mu haɗa da shi, yanzu dai abin da nake so da ku shine ku cire tsoro, kuna jin wannan shegen tsoron wlh ba abin da zamu cimma, baa zama gwani kuma baa cinma buri sai an cire tsoro, suma sai da suka cire tsoro suka iya kafa wannan tsinanniyar gidan, tsoron Allah kawai ya kamata bawa ya ji ba tsoron wani daga cikin halittun Allah ba, babu wani ɗan adam da ya isa ya kashe ko ya raya sannan kuma basu da wuta basu da aljanna to dan haka mai wuta da aljanna kowai zamu ji tsoro, dolene kawai sai kun cire tsoro mu tunkari matsalar mu, ko zamu mutu ko mu yi rai, idan kuka ruƙe Allah kuka fara faɗa akan gaskiya da ƙwatarwa kanku ƴanci to bai kamata ku ji tsoron wasu shegun banza ba, ƴan adams ne fa kamar ku, dan haka ku ajiye tsoro a gefe muyi faɗa domin mutuncin mu, addininmu, darajar mu, ƴaƴan gobe masu tasowa, da kuma ƴancin mu". Ta kai karshen maganar tana kare masu kallo, duk sunyi wani jugum jugum da su suna binta da ido
"Jehan zan baki shawara ina son ki sani Hajiyar daɗi fa ba kamar yadda kika ɗauketa bane, wlh faɗa gaba da gaba da ita ba abune mai yiwu ba, tun da kikaga wannan gida ya kafu tsawon lokaci kamar yadda Aisha ta faɗa to ina ga wlh akwai sa baki manya manya na wasu sassa daga kasarnan, to kinga ba lallaine bama ko mun fita da shaidar mu sami wata hukuma ta kula mu har ta dafa mana, kuma wlh idan kikace zaki yi fito na fito da ita zamu iya rasa rayuwarmu gaba ɗayanmu, ko da yaushe na sanki kina amfani da ƙwaƙwalwa why a nan kuma kike son ki yi amfani da karfin cin abinci bayan kuma kin fi kowa sanin cewa lallai anan ne ya dace da ki yi amfani da ƙwaƙwalwarki". Cewar Adiva kenan, kuma ta yi maganar murya ɗauke da damuwa fal ranta.
Ajiyar zuciya Jehan ta sauke kafin ta fara magana cikin harshen turanci dan ta san Maryam da A'isha basa ji, kuma