Showing 123001 words to 126000 words out of 355604 words
ɗan yi, na yan mintoci kafin ya ce "Yauwa to Asif ya yi maka?" Gyaɗa masa kai ya yi alamar E ya yi mashi.
Yau farinciki a wajen Musharraf ba'a magana, shi kuma Michael mamakin ganin Musharraf a hakan ya jefashi cikin tunani.
Suna zaune a wajen har lokacin sallar isha ya yi, a tare suka shiga toilet suka ɗauro alwala, Musharraf ya nuna masa yadda ake yi. Bayan sun fito, Musharraf ya yi kokarin nuna masa yadda zai yi sallah, nan fa ya ce aa ai yasan yadda ake yi, abin da dai ake karantawa ne bai sani ba, amma yana kallon friend ɗin James yana Sallah, bayan haka kuma a school nasu akwai musulmai da suke sallah yana gani.
Musharraf bai da mu ya ce to ya kwatanta masa ya gani, haka kuwa ya kwantanta, kaɗan ba yawa Musharraf ya ci gyaranshi sanann ya yi musu jagora ya tada Sallah in da ya ce duk yadda ya yi shima Michael ɗin haka zai yi, ba sai ya karanta komai ba tun da bai iya ba.
Sun yi Sa'a har suka idar da sallah ba wanda ya shigo cikin ɗakin, bayan sun idar da sallah ne, Musharraf ya zauna ya fara koya masa wasu abubuwa daya kamata ya fara iyawa
(To fa me kuke tunanin makomar Musharraf idan har zakunan gidan suka gane ya musuluntar da Michael wato Asif a yanzu? Hmmmm a kwai dai chakwakiya, ni dai na haɗa kaya na domin na je na gani ya Rimsha take, ta farfaɗo ne ko yaya)
💖💖NIGERIA 🛬💖💖
💖💖KATSINA STATE💖💖
Cike da tashin hankali maman Sadiq ta zuba mata ruwa, bakin ta ɗauke da kalmar shahada tare da salatin annabi ta farfaɗo. Baiwar Allah zuciyarta tamkar zai buga ya faso kirjinta ya fito waje.
Hakuri maman Sadiq ta yi ta bata, haka ta hakura ya zata yi, a halin da take ciki yanzu mutuwa shine abinda kawai ta fi buƙata, a cewarta ta ga ji da wannan bakar rayuwa mai cike da bakinciki.
After some hours👌
Bayan ta ɗan warware, har wanka ta yi, sannan ta nemi Yusuf da ya rakata wajen da ake wanke kai, gashinta ya yi datti sosai zata wanke. Nan Yusuf ya sanar da ita sai sun shiga cikin gari sannan za su samu shagon wankin kai. Buɗe trolleynta ta yi ta sanya wayarta a ciki sannan ta ɗauki hijabinta har kasa tare da face mask ɗin ta suka tafi bayan sun sallami maman Sadiq kenan.
Ahmad ya kira wayarta dan ya ji ko ta isa lafiya, amma ina shiru bata ɗauka ba, ya mata miss call ya kai goma, ta sanya wayar a silent bata ji ba, ya shiga damuwa sosai, sai tunani yake kadda ace wani abin ne ya sameta a hanya, ya yi kokarin kiran layin Ayla, amma a kashe, daga karshe dai ya hakura zuwa dare ya ce sai ya sake gwadawa.
Ita kuma Rimsha kuɗin mashi ta biya musu zuwa cikin gari.
Da suka je, a cikin kuɗin da Ahmad ya basu 20k ɗin nan, a ciki ta zari 2k ta biya aka wanke mata, dark black curly hair ta, ba karamin kyau ta yi ba, daga nan suka wuce wajen gyaran kafa, bata yi wani tunani ba kawai ta hau kashe kuɗin hannunta a wajen gyara, har da wani cewa a mata kunshi, ai kuwa kunshi mai kyau suka mata suka karɓi 3k, ta yi kyau kam iya kyau kamar ka saceta ka gudu da ita.
Rimsha tana bala'i son gyaran jiki da sauransu, tana da bala'i tsabta, ko nawane zata iya kashewa a kan gyaran jiki, haka ita ma Jehan akwai ta da bala'i tsabta, sai dai Rimsha ta fita.
Bayan an mata komai ta fito tsab, sai ta ce da Yusuf su tafi, shi kuma duk in da ta je yana biye da ita, haka kawai ta burge shi, saboda tafi jehan saukin kai da girmama mutane, domin kuwa ita tun farkoma yaya ta kira shi, saɓanin Jehan da take ce musu dirty boys.
Kamar yadda suka zo haka suka koma a kan mashin, sai dai kowa da na shi mashin ɗin, naira 7500 Rimsha ta kashe, wankin kai da gyaranshi 2k, wankin kafa da yanke kumba (farce) shi kuma 1500, kunshi 3k sai kuɗin mashin zuwa su biyu 500 komawa ma 500 saboda kowa da mashin nashi.
Suna komawa gida suka isko maman Sadiq a kitchen tana ta faman hura wuta, ɗaki Rimsha ta shiga ta cire hijabinta tare da yafa gyalen abayar jikinta ta fito ta kama wa maman Sadiq aiki, ta fara share tsakar gidan. Sai mamaki maman Sadiq take yi, sai tambayar kanta take yi ya akayi Rimsha ta iya aiki Jehan bata iya ba, kuma Jehan ce babba, sai dai babu mai bata wannan amsa, haka ta share zance ta ce da Rimsha ta koma ɗaki ta zauna, kada ta damu zata yi aiki, kin yarda Rimsha ta ya, ba yadda maman Sadiq ta iya haka ta kyaleta ta kama mata aikin.
(Nikuma na tattare kayana sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu a gidan Abba, wato wajen yaya Akil🙃 amma dai kawai cakwakiya, yanzu muka fara shiga cikin ainahin labarin, sai ku gyara zama Ma'assalam✍️🥱)
Kafin na tafi bari na yi muku tambaya, wace ce Hajiyar da ta ɗauki Jehan? Ina kuma ta kai ta? Me yasa ta ba su address na karya? Me hakan yake nufi? Ina su mum suka tafi? Ya makomar Rimsha? Ina jiran amsa.
💖💖TRIPLET'S💖💖
37-38
💖💖GIDAN ABBA💖💖
Aafia suna shiga ɗaki, Akila ta ce mata tana zuwa bari ta ɗebo ruwan zafi ta haɗa mata tea, ai kuwa Akila na fita Aafia ta tashi cikin sauri ta lallaɓo zuwa palon su Akil, kamar wata ɓarauniya haka take tafiya.
Tana shiga ta ɗauki wayarta dake saman sofa cikin sauri ta fice. Tana komawa ɗakin Akila ta fara neman layin Rufee.
Ai kuwa kamar jiran kiran Rufee take yi, bugu ɗaya ta ɗaga, murya kasa kasa A'afia ta ce "Kiyi hakuri Rufee, gobe zamu haɗu a school kin ji?" Daga ɗayan ɓangaren Rufee ta ce "Ba komai kada ki damu, yanzu dai abin da nake so da ke ki turomin hoton wannan da ya bugemun nan idan kina da shi" to A'afia ta amsa da shi, sannan suka yi sallama, cikin sauri A'afia ta shiga WhatsApp ta tura mata duka wasu hotonan Akil da take da su a wayar.
Bayan ta kammala ta ajiye wayar ta kwanta tana tunanin yadda za'ayi ta iya zama a wannan gida tare da Akil, dan ta san takura mata zai yi, saboda ya fi yaya Irfan tsanani, ya fi su Imran duka tsanani, gara Imran sau dubu a kanshi, shine karami amma idan ranshi ya ɓaci, Imran da yake babba ma lallaɓashi yake yi, yana da bala'i zuciya sosai.
A wannan yanayin Akila ta dawo ta sameta, saman bedside drawer ta ajiye cup ɗin kakkauran tea din da ta haɗa mata, sannan ta ce "Aunty Aafia ki ta shi ki sha kin ji ko?"
Tamkar da gunki Akila take yi, Aafia ta ki kula ta, ko sannu bata ce da ita ba. Allah sarki Akila baiwar Allah, ta yi tunanin ko dai A'afia bata ji me ta ce da kyau ba ne, sai ta sake maimaita maganar. Tsawa A'afia ta daka mata wadda ya sanyata wucewa ta fice daga ɗakin.
Kallon banza Aafia ta bita da shi, har ta kurewa ganinta, sannan ta ja dogon tsaki tare da runtse ido, a cikin zuciyarta tana jan wa Akil Allah ya isa na dukan da ya yi mata.
After some hours👌
Bayan sun ci Abinci dare sun kammala komai sun kwanta, Aafia tana tsaka da barci ta ji wani bala'i yunwa ya addabawa rayuwarta, cikinta sai kugi yake yi mata, har wani irin murɗa mata yake yi, ba shiri ta tashi zaune a tsakiyar gadon, wutar ɗakin a kashe ko ina duhu, hakan yasa ta laluɓi wayarta dake saman bedside drawer, ta kunna hasken. A hankali ta zuro kafafunta kasa tare da sauƙowa gaba ɗaya daga saman gadon, sannan ta nufi palo.
Ko da ta je palo ba kowa, kai tsaye wajen switch ta nufa ta kunna wutar, nan take haske ya gauraye palon baki ɗaya.
Saman table ta nufa, abin mamaki abinci ne a jere kala-kala a saman table ɗin, jolof rice, white rice and beans with steew, ga su indomie ne, gasassun kaji, ga soyayyu a gefe, abinci dai kala-kala, kuma dukka anyi serving nasu a cikin plate, sai ta shin kamshi suke zubawa kamar me,
Saboda tsabar yunwa dake cinta, cikin hanzari ta zauna tare da ɗaukar spoon, cikin natsuwa ta fara cin jolof rice, wani irin ɗanɗano na musamman ta ji a bakinta, lokacin da ta kai abincin, ɗanɗano ne wadda bata taɓa jin mai daɗi irin shi ba, har wani lumshe idanuwanta take yi, abincin ya yi daɗi over.
Cikin natsu take cin abinci, tana tsaka da ci ta kware ta fara tari, kamar daga sama wani kyakkyawar hannu ya ɗauko wani kyakkyawar glass cup mai ɗauke da ruwan sanyi dake wajen, ya miƙa mata, sai faman tari take yi, ganin an miƙo mata ruwa yasa ta karɓa cikin sauri ta kafa a bakinta ta fara sha.
Shi kanshi ruwan wani irin ɗanɗano ne mai zaki ga daɗi, tas ta shanye ba tare da ta sani ba. Bayan ta shanye, sai ta ci-gaba da cin abincinta cikin kwanciyar hankali.
Da zarar bakinta ya ɓaci za'a sanya tissue a goge mata, kwata-kwata bata yi tunanin waye mai mata hakan ba, bata ma san ana yi mata ba.
A ɓangaren su Ammie kuwa, tana tsaka da barci ta ji ana taɓa ta, cikin tsiwa ta ce "Kai Abba Akila ba zaka daina tashin mutun daga barci bako? Wlh kada ka sake yi mini haka, ni bana son jarabar tsiya..." Bata kai ga rufe bakinta ba a ka sake taɓata, hannunta ta kai ido a rufe ta bude hannun wanda yake taɓa tan, a tunaninta Abba ne.
Can kuma aka sake taɓa ta, dogon tsaki ta ja, ta miƙe zaune a tsakiyar gadon tare da fara surfa masifa tsakiyar dare, dan lokacin karfe 2 na dare zai yi.
Abba ne a tsaye a kanta ta gani, amma a nata ganin ne Abba a zahirin gaskiya kuma ba Abba bane, domin Abba baya ɗakin ma kwata-kwata sai Allah kaɗai yasan ina ya tafi.
"Abba Akila wai meyasa baka da imani ne wani lokacin? Yanzu ba zaka barni na kwanta na hutawa rai na ba?..." Bata kaiga rufe bakinta ba, ya ɗauketa da wani mahaukacin mari mai razanar da kwakwalwar duk wanda a ka yi wa shi.
Ji take yi dif komai ya tsaya mata cak, har wani bala'i duhu ta gani ya gilma mata ta cikin idanuwanta.
Ihu ta kurma tare da miƙewa ta damko kwalar rigar Abba da idanuwanta ke nuna mata.
"Har ni zaka mara? To wlh baka isa ba". Ta kai karshen maganar tare da ɗaga hannu zata wanke masa fuska da mari, abin mamaki ko da ta kai mashi marin, sai ta mari iska, bata ji komai ba, sake kai masa wani marin ta yi, shima sai ta ji iska ta mara.
Sau uku tana gwada marin, amma ina ko sau ɗaya bata sami damar taɓa fuskar ba, nan fa ta fara tsorata, jikinta ya fara kerma, cikin sauri ta saki wuyar rigar mutumin tana ja da baya-baya.
Ina bai bari ta yi nisa ba, ya damko wuyarta, nan fa ya fara yar carafke da ita a cikin ɗakin, kamar ba mutum ya riƙe ba, haka ya rinƙa wurgi da ita yana sake caf kota, sannan ga wasu siraran bulalu guda uku, wadda suke zane mata jikinta idan ya ɗaga ta sama, sai ihu take yi, amma babu wanda ya kawo mata agajin.
A ɓangaren ita kuma A'afia, sai cin abincinta take yi. Abin mamaki shine bayan ta koshi ta tashi zata ta fi, kamar daga sama taga wasu mutane su biyu masu kamanni irin na Abba sun bayya a kujerun gefe-gefen ta, ma'ana sun sanyata a tsakiya, tsabar tsorata yasa ta kurma ihu, tana kokarin guduwa, suka yi maza suka danneta suka fara bata abincin nan a baki.
Ji take yi cikinta na mata barazanar fashewa saboda ƙoshi, amma sun ki kyaleta sai da suka ɗura mata abinci na wuce misali, sai ihu take yi ba wanda ya iya kawo mata agaji dan ba mai iya jinta.
Sabo tsabar rashin mutunci irin na dodannin nan sai bayan sun kammala ɗura mata abincin nan son ransu, sannan suka fito mata da ainahin suffar abincin da taci dan ta gani.
Kai kai kai wai iya zubillah, wasu irin manya-manyan tsutsotsi ne sai yawo suke cikin plate ɗin, sauran plate ɗin kuma akwai mai ɗanyen nama, akwai nai hanjin mutun ba'a wanke ba, shi kan shi ruwan da ta sha kakkauran jinine mai kaurin gaske.
Ai daga wannan lokaci Aafia bata sake motsi ba, nan take numfashi ta ya ɗauke ta sume a wajen, tana suma suka ɓace abin su, kamar yadda suka ɓace kuma haka duk wani abu na su ya ɓace.
A ɓangaren Hajiya Umaiya kuwa, yau Abba ne ya mata duka ita kaɗai, sai ihu take yi tana tambayarsa shin me ta yi masa, amma ina bai yi magana ba, domin ba asalin Abba bane, sai Allah kaɗai yasan in da asalin Abba suka kai shi, lilis suka yi wa Ammie kafin su ɓace su barta da azaba. Sai bayan awa biyu da tafiyarsu sannan ta samu azaban ya sake ta, ta samu ta yi barci, amma fa Abba bai dawo ba har barci ya yi awon gaba da ita.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa.
Sun yi kaura lafiya, sun koma tsantsararren gidan su mai bala'in kyau da girma, hawa biyu ne, ya tsaru iya tsaruwa, Irfan ya kashe kuɗi wajen zuba musu tsan tsararrun furnitures masu bala'i kyau da tsada, kai kace gidan wani gwamna ne saboda haɗuwa.
Ansha walima da sadakar abinci, su Imran duk sun haɗu a part ɗin Irfan, sai murna ake yi.
Misalin karfe uku Aunty ta ce Ayla ta ɗauki abinci ta kai wa su yaya Irfan part ɗin su, domin yau cikin gidan a cike yake da yan Walima, kuma yaya Irfan ya ce yanzu ya kamata su dai na cin abinci a Palo gaba ɗayan su, su za su rinƙa ci a part nasu saboda yanzu Abbi baya zama da su, kada wata matsala ta sake faruwa, Aunty ta amince da hakan kuma ta ji daɗi.
Ayla ta yi wankanta fes, ta shirya cikin ɗaya daga cikin dogayen rigunanta, ta fito tas kamar ba ita ba, amma babu wani abin da ta fi yawan tunawa kamar Rimsha, ai na za su sake haɗuwa, shikenan sun rabu, idan ta tuna hakan sai ta yi kuka.
Jiki ta gaba ɗaya a mace ta ɗauko katon kular abincin, mai aikinsu kuma ta biyota da kular miya da kuma basket na su kayan latus da su plates and spoons.
Zaune daddyn Jelly yake a palon Irfan yana latse-latse a wayarsa, ya yin da shi kuma Irfan yake cikin toilet a bedroom nasa yana wanka, lokacin da ta shigo kuma, a lokacin Imran ya fito ya zo ya zauna a sofar kusa da daddy.
Gabansu ta zo ta ajiye abincin, ta yi musu sannu tare da gaisuwa, ta miƙe zata tafi abin mamaki daddyn Jelly da bai ɗago ya kalleta ba tun da ta shigo amma da ta miƙe zata tafi kamar daga sama ta ji yana cewa "Me ya sanya ki kuka kuma? Ba na ce kada ki sake yin kuka ba?" Cikin sauri ta juyo da kallonta kanshi, tabbas bai ɗago ya kalli fuskar ta ba, tun da ta shigo kanshi na kan wayarsa, to tayaya ya kalli fuskarta? Kuma tun da ta shigo kanta a kasa yake.
Ganin ta yi shiru yasa ya ajiye wayar tasa ya ɗago tare da yi wa yar aikin nasu umarnin a kan ta tafi, ita kuma Ayla ta zo nan, ya kai karshen maganar nasa yana nuna wa Ayla gefensa a kan tazo ta zauna.
Zuwa ta yi ta tsugunna a gaban shi tana faɗin gata nan, ita kuma mai Aiki ta wuce ta tafi abinta.
"Bappa ina kuka samo wannan yarinya kuma?" Imran ne ya tambaya yana kare mata kallo.
"Zan baka labari amma ba yanzu ba" to kawai ya amsa da shi.
Kallon tsab daddyn Jelly ya yi mata sannan ya ce "Me ya saki kuka? Na san dole ki kasance da damuwa a ranki, saboda iyaye ba wasa ba, amma ai nace kada ki sake kuka, kuma nace zan nemo miki iyayen naki, ko ba haka muka yi ba?" Cikin girmamawa ta gyaɗa masa kai alamar E haka suka ka yi.
Daddy Jelly ya kware wajen iya rarrashi, domin Jellyn sa duniya ce wajen iya kuka, sai ya ɗauki minti talatin yana lalllaɓa Jelly yana bata hakuri, har sai ta hakura, to yanzu kuma ya gama da Jelly ga Ayla. Hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon fuskar ta "Daga yau ki yi mini alkawari in dai zaki yi hawaye to sai dai ya kasance na farincikin haɗuwarki da iyayenki"
Kuka ta sa mashi domin ba zata iya dai'na yiwa Rimsha kuka ba, dole idan ta tuna Rimsha ta yi kuka.
Subhanallah daddy Jelly ya faɗa tare da miƙewa ya mikar da ita tsaye, bayan ta miƙe sai ya koma ya zauna tare da janyota ta zauna kusa da shi, shi dai Imran sai kallonsu yake yi yana mamakin yadda daddyn Jelly ya kware wajen kula da yara, ko da yake dama dole ya iya, kada ku mance shi kaɗan shi ya reni Jelly sa har ta girma.
Ɗan rungumota kaɗan ya yi a jikinsa sannan ya fara goge mata hawaye, kamar dai yadda yake yi wa Jellynsa haka ya yi mata, da kayar ta yi shiru, bayan ta yi shiru ne sai ta yi kokarin barin jikinsa, bai hana tana ba, domin shi matsayin jini ɗaya yake kallonta, ganin ta yake tamkar jelly barema da Jellyn nasa bata nan yanzu, bawan Allah yaso ya ja su Aafia a jiki dan su ɗebe masa kewa, amma sun ki yarda, shine yanzu yake jan Ayla a jiki ko kewa zai ragu masa.
"Kada ki damu, ki ɗauke yi tamkar yayanki ko daddyn ki, duk yadda kika ɗauka, yanzu dai kada ki sake yin kuka" Ayla ta