Showing 27001 words to 30000 words out of 355604 words
yasa baki ji ne?" Hajiya ta faɗa a raunane, dan jikin ta duk a mace, ta gaji sosai, kasan cewar tana da kiba da tayi tafiya kaɗan take gajiya.
Saman sofa tazo ta zauna tana faɗin "Tattara komai da kika fitar ki mai da shi" turo baki Jelly tayi tana faɗin "Ni Ummi ban iya ba" kwanciya Hajiya tayi tana faɗin "Wash Allah na gaji" ci-gaba da watsa kayan Jelly tayi abun ta, tana neman abubuwan ci kawai taci, shiru Hajiya tayi bata sake tanka mata ba, dan a gajiye take, ba zata iya rigimar jelly yanzu ba.
Tsab Jelly ta fitar da komai daga cikin kwalin sa, na ledoji ma ba'a bar su a baya ba, sai da ta yaje duk ledojin ta fito da abubuwan dake ciki, wayan da ake ci duk ta tara a gaban ta, irin su chocolate, sweet, popcorn, chips da sauran kayan kwaɗayi da maƙulashe da Hajiya ta sayo mata.
Yage ledar popcorn tayi, ta fara dumbuza tana kai wa bakin ta, Hajiya kuwa tana kwance idon ta a lumshe, saboda gajiya, bata san aikin da Jelly ke yi ba. Bayan ta gama da popcorn ta ɗauko wani leda mai ɗauke da chin-chin a cikin sa, yage shi shi ma tayi, ta fara cin chin-chin ɗin.
Kaɗan taci wannan chin-chin ɗin ta ajiye sauran tana faɗin "Ba daɗi kamar an wanke kan wancan matar, maman Afnan take kowa, kan ta a gwaguye ba gashi, sai masifa kamar sheɗaniya" Hajiya na jin ta, amma ba ta tanka ta ba.
Haka Jelly ta rinƙa cin abin da zata iya ci, wanda ta ji ba daɗi kuma haka zata bar shi, a watse a wajen, ta yage ledar.
Suna cikin wannan hali Nawid ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, waro ido Hajiya tayi tana kallon sa, hannun sa riƙe da yar karamar trolley ɗin sa mai kyau, ya dawo daga Katsina.
Saman kujerar kusa da Ummi ya.zo ya zauna yana ta faman washe baki, murmushi baki har kunne, Jelly kam kamar bata san da shigowar sa ba.
"Nawid lafiya kake wannan murmushi haka? Ko dai kakan ka ya maka wani kyautan ne?" Ummi ta tambaya tana tsare shi da ido, baki har kunne saboda murmushi yace "Ummi na samu mata ne wlh, shiyasa nake cikin farin ciki, shiyasa ma ki kaga na dawo da wuri dan na sanar dake, farinciki ya hana ni na cika satin da nace zan yi, dole na zo na sanar dake" zaro ido Ummi tayi kafin tace "Mata kuma? Ai na ka sami matar?" Kara faɗaɗa murmushin sa yayi tare da ɗan duƙar da kai ƙasa yace "Ummi a Katsina take, tana aiki a restaurant ɗin gwaggo Auta"
kara zaro ido Ummi ta yi kafin ta miƙe zaune tace "Lallai Nawid, ita kuma baby fa?" Zaro ido shi ma Nawid yayi yace "Ummi baby kuma?" "Kwarai da gaske baby fa" Ummi ta ba shi amsa with her full confidence
Tashin sense lokaci guda yaji duniya ta tsaya masa cak, har wani yanan duhu yake gani na gilmawa a idon sa, nan take yaji duniya na masa wani irin juyi, kan sa na sara masa, da karfi karfi, kamar zai rabe biyu, zancen zuci ya fara yi, "ko na rasa mata a duniya ba zan auri baby ba, yarinya bata da hankali, bata da kan gado ko kaɗan, kamar ni dr Nawid a ce wannan mahaucikayar ce matata, kai ina hakan ba zai yi wu ba, yarinyar da bata san kan ta ba, ita da kan ta, sannan ace ni in aure ta, muyi zaman mata da miji da mahaukaciya" wani irin zufar ne ya fara gan garo masa daga gefe da gefen kunnen sa, kasa ya duƙar da kan sa yana tunanin abun yi
"Nawid menene naga ka canza lokacin guda haka?" Cewar Ummi,
furzar da iska mai zafi yayi daga bakin sa, kafin yace "Ummi ni a kanwa na ɗauki baby, ko kaɗan babu son ta a rai na, dan Allah Ummi kiyi hakuri, kada ki sanya na auri ta, wlh idan na aure ta, na san zan cutar da ita ne, dan bana son ta" salati Ummi tasa tana tafa hannu, har ta kai karshen salatin "Nawid yanzu ni kake cewa baka son baby? To tun da baka son baby zaɓi na, ni ma bana son wanda ka kawo kake son aura, har zan ce maka ga zaɓi na kace baka so lallai ka girma"
zamowa ƙasa daga saman sofar Nawid yayi ya zube gwiwowin sa a kasa, cikin raunanniyar murya cike da tashin hankali yace "Ki yi hakuri Ummi, ba wai bana son baby ba ne, ina son baby amma a matsayin kanwa, dan Allah Ummi ki fahince Ni, ki so zaɓi na, ki bari na aure ta, wlh tana da kirki sosai"
Oho Allah ko yaushe Nawid ya zauna da Jehan har yasan tana da kirki, kai jama'a hmmm maza mutanen mu😹.
Ummi za tayi magana Jelly dake zaune tana faman cinye sauran naman ta na ɗazun tace "Yaya Nawid kar ka damu, ni ma bana son ka ai, tun da baka so na, Ni ma haka ne" guntun tsaki Ummi taje kafin tace "Ke baby ta shi ki kwashe kayan cimar ki, ki wuce ɗakin ki" ba musu ta tashi ta tattare kayan ciman ta, da wanda ta fara ci ta ajiye da kuma wanda ma bata samu daman ci ba, duk ta kwashe ta wuce ɗakin ta tana turo baki.
Dawo da kallon ta, kan Nawid Ummi tayi "Nawid idan dai har kana son auran wancan, tofa sai ka fara auran baby, zan sanar da Abbon ka, nan da 3 weeks masu zuwa a ɗaura muku aure a wuce wajen, idan yaso daga baya sai ka auri wan can, amma fa ka sani ba zaka kawo min wadda zata takurawa baby ba tom" kasa kasa yace "To shikenan Ummi Nagode" sannan ya miƙe ya ja trolley sa zuwa bedroom na sa murna ya koma ciki, yana tafiya yana tunanin hanyar da zai bi ya gujewa auren baby, "ko dai na ɗauke ta naje can wani gari na jefar da ita ne?" Ya tambayi kan sa, ɗayan ɓangaren na zuciyar sa ne yace masa "Da kuwa hakan zai fi, dan idan ba haka kayi ba Ummi ba zata fasa aura maka wannan mahaukaciyar kwailar yarinyar ba" tunani kala-kala yake cikin ransa har ya karisa cikin bedroom ɗin nasa.
A ɓangaren Abbo kuwa daga cikin bedroom nasa yana jiyo duk yadda Ummi tayi da Nawid, shi ma tunani yake ta yadda zai ɓullo wa lamarin, ji yake kamar yabi dare ya ɗauki baby ya kai ta gidan shi na Abuja ya ajiye ta a can, sai ya rinƙa biyan bukatar sa da ita, tun da daman a nan bai isa yayi hakan ba, saboda Hajiya, ga shi kuma yana bala'i son ya ga ya keɓe da baby, yana son kasan cewar tare da ita a ɗaki ɗaya. Shi ma tunani cike fal ransa yana tuna yadda zai sa mu mafita.
A ɓangaren Ummi kuwa tunanin bikin Nawid da baby kawai take, dan har ga Allah Ummi tana bala'i kaunar Jelly.
Wayar ta ta ɗauƙo daga cikin jakarta, ta danna kira, sannan ta kara wayar a kunnan ta.
Jim kaɗan a ka ɗa ga kiran "Hello Hajiya Batula ya kike?" Daga ɗayan ɓangaren Hajiya Batula tace "Lafiya lou Hajiya Turai ya su Nawid?" "Nawid yana nan lafiya yanzu ma kiran na shi ne ai" cikin sauri Hajiya Batula tace "Kiran nashi ne kuma? Kaddai ki ce min auren sa ne ya tashi" kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a kan fuskar Hajiya Turai, tana murmushi tana faɗin "Eh wlh auren sa ne ya tashi, ina Abla?" "Abla tana school, lallai abu namu maganin a kwaɓe mu, ki ce na kamo hanya kawai" kara faɗa ɗa murmushi ta Ummi tayi kafin tace "Sosai ma kuwa kamo hanya kam mai kyau ma, da wuri kai" "Yaushe ne bikin?" Shiru kaɗan Ummi tayi kafin tace "Eh nan da sati uku haka" "wow lallai dole nan da sati biyu nayiwa Kaduna diran mikiya"
ɗan tsagai ta murmushi ta Ummi ta yi sannan tace "Gaskiya kam abun da yasa ma kenan na kira ki, saboda matar tasa, ki taimaka tun ana sauran sati biyu biki kizo ki fara gyara min ita" shiru Hajiya Batula ta ɗan yi kafin tace "Gaskiya tun ana saura sati biyu kam ba zai yi wu ba, sai dai saura sati ɗayan dai, saboda saura sati biyu biki ina da manyan baki, kuma kinga Abla ma zata dawo hutu daga school, zan yi kokari dai ana sauran sati ɗaya biki nazo, ranan tun safe zan biyo jirgi, kuma ai tsakanin Maiduguri da Kaduna tafiyar ba yawa, jirgin safe zan biyo, ina dirowa mu fara aiki" ɗan canza fuska Ummi tayi alamar bata ji daɗin maganar Hajiya Batulan ba, amma ba yadda ta iya dole ta hakura ta bi yadda Hajiya Batulan tace, dan Hajiya Batula ta kware wajen gyara mata, kuma babban aminiyar tace tun na yaran ta. Ba dan taso ba, ta amsa wa Hajiya Batula da to Allah ya kai mu, sannan suka yi sallama, ta mai da wayar ta ajiye, ta koma ta kwanta, ta ci-gaba da tunanin tana kawata yadda bikin zai kasance a ran ta.
To masu karatu mu leƙo Rimsha mu gani me take aikatawa.
Tun karfe 6 na safe su ka farka su ka shirya, a tare suka je suka yi wa matar sarki sallama, sannan suka je wajen sarki a ɗakin sa shi ma, suka yi masa sallama, sarki da matar sa basu ji daɗin tafiyar da su Rimsha za su yi ba, dan har ga Allah tun da suka gan su, suka ji kaunar yaran har cikin ran su ya ka ma su, to amma ba yadda za su yi, tun da ba ƴaƴan su bane, dole su kyale su su koma wajen iyayen su, dubu biyu sarki ya basu, sai godiya suke zuba masa, baki har kunne saboda murmushi jin daɗin sun samu kuɗin mota, Rimsha ce ta kulle kuɗin a igiyar rigar ta kusa da in da ta ƙulle goran da duna ya bata
cike da murna suka fito tsakar gida, matar sarki ma ba'a barta a baya ba, ta basu kyautan 500, sosai suka ji daɗi sai murna suke, suka yi sallama, su Rimsha suka nufi waje matar sarki da sarki suka koma cikin ɗakunan su
Su Rimsh sun fito zasu tafi kenan suka ci karo da olohunwa yana ƙoƙarin shigowa cikin gidan, hannun sa riƙe da buta, alamar bayan gari yaje yayi.
Murya kamar na yan shaye-shaye yace "Wow beautiful girl" yayi maganar yana kallon Rimsha, shiru su dukan su suka yi, ba su yi masa magana ba, hannu olohunwa ya kai zai shafi fuskar Rimsha, cak hannun sa ta maƙale ya sanƙare kamar itace, ihu ya fara yi yana kokarin jaye hannun sa baya, amma ina ya kasa, su ma ihu suka yi suka bazama cikin gari da gudu, dan sun tsorata da ihun olohunwa
A guje sarki da matar sa suka fito, olohunwa yana tsaye a wajen ya kasa motsawa, ga hannun nasa sai kumbura yake ya sankare waje guda, su kuwa su Rimsha tsorata da ihun da olohunwa yayi ne yasa su bazama cikin gari suna gudu kamar marasa hankali, a tunanin su, wani abun mugunta zai musu.
Sosai suke gudu basu san in da suka nufa ba, sarki kuma sai faman kokarin janye olohunwa a wajen yake, amma abun yaci tira ko motsa olohunwa sun kasa yi, to kun san halin yarabawa da tsoro ire-iren wayan nan abubuwa, ihu matar sarki ta kurma tana neman a kawo mu su ɗauki. Kan kace me gidan sarki ya cika da jama'a maƙil, sai hayaniya ke tashi kamar gidan biki, sai kokarin ture olohunwa suke daga wajen amma sun kasa, kamar bishiyar da a ka dasa shekara da shekaru haka ya zama a wajen, gashi sai ihu yake ya ka sa magana saboda azaban zogi da hannun sa ke masa, hannun ya kumbura sosai har ya fara fitar da wani irin farin ruwa mai warin bala'i, alamar hannun ya ruɓe.
Su kuwa su Rimsha bayin Allah basu san meke faruwa ba, sai zunduma gudu suke wai kar olohunwa ya kama su, dan Ayla ta faɗa musu olohunwa fyaɗe yake yiwa mata shiyasa ma suka tsorata sosai da shi.
Sun yi gudu sosai, har sai da suka dai na ganin alamar wannan kauye gaba ɗaya, sannan suka tsaya wajen wani bishiyar lemon tsami suna mai da numfashi, suna haki.
Almost 10mins suna tsaye, sannan suka zauna, a kasan bishiyar, da yake akoi ganyen damuna sosai a jikin bishiyar, sai suka sa mu inuwa, wajen akoi sanyi sosai gwanin daɗin zama, haka suka baje
Ayla ta duɓi Rimsha tace "Allah ya cece mu, ba dan haka ba olohunwa fyaɗe zai mana, ɗan iska ne sosai, ga shi da bala'i shaye-shaye" da kyar Rimsha ta iya cewa "Gaskiya kam, amma kuma basu da mutunci in dai haka ne" ita dai Kausar ta kasa magana saboda ta fi su shan wahala, dan ta fi su ƙiba shiyasa ta fi su jin jiki.
Sun yi shiru su na zaune, bishiyar na kaɗa musu iska mai sanyin daɗi, har wani lumshe ido suke kamar ma su jin barci
Kaɗan-kaɗan daga can nesa suka fara jiyo hayaniyar mutane, suna nufo in da suke, kasa kunne suka yi suna sauraro su ji, wannan hayaniya ta mecece.
Basu fargaba sai ganin gungun jama'ar kauyen su ka yi sun nufo su, hannayen su riƙe da sanduna wasu kuma suna riƙe da wuƙaƙe, zuba musu ido su Ayla suka yi, sun kasa tashi ma bare su yi yunkurin guduwa, dan su a nasu tunanin ma basu yi laifin komai ba, sun ɗauka wasu can daban yan kauyen suka biyo.
Sun zuba ido suna ganin ikon Allah, har yan kauyen suka iso wajen da suke. Su na zawa ba su yi wata-wata ba suka fara sauƙe musu sandunan hannayen su a jikin su, sosai Ayla da Kausar ke ihu ita kam Rimsha tana zaune shiru, alamar bata san ma meke faruwa ba, ga shi kuma su yan ƙauyen a nasu ganin ido suna duka har da Rimsha, sai dai kuma abun da ba su sani ba sandunan nasu baya taɓa jikin Rimsha
Sosai yan ƙauyen ke dukan Kausar da Ayla, ita kuma Rimsha ga shi dai a zahiri suna sauƙe mata sandan a jikin ta, amma a ɓaɗini ba haka bane, domin ko kaɗan bata ji alamar saukan sanda a jikin ta ba, tana dai ganin jama'ar ƙauyen suna ɗaga sanduna kamar zasu buga mata, sai kuma taga sandar ya ɓace, ga shi sai magana take musu, amma basa jin komai da take faɗa, duka kawai suke kai mu su, a yaren yarabanci suna ce mu su mayu ne, su suka kashe olohunwa
Kausar da Ayla sun daku jikin su duk ya farfashe sai jini yake, bayin Allah, ita ma Rimsha a idon yan ƙauyen jikin ta ya fashe yana jini, amma kuma ba hakan bane.
Sai da yan ƙauyen nan suka ga kamar su Kausar sun mutu basa numfashin, sannan suka kyalesu suka wuce suka bar su a wajen kwance cikin jini.
Suna tafiya wani haske ya fita daga jikin Rimsha ya tashi sama, ya bi bayan yan ƙauyen, wannan hasken na fita Rimsha ta dawo cikin hayyacin ta, ta tsorata sosai lokacin da idon ta ya sauƙa kan su Kausar, cike da tashin hankali ta fara girgiza su, tana kiran sunaye su.
Sosai take kuka ta na kiran su, amma ina ko motsi ba sa yi, kamar sun mutu, juyawa gabas da yamma kudu da arewa Rimsha tayi babu kowa a wajen, kara sautin kukan nata tayi baiwar Allah, sai jan hanci take, hawaye bibbiyu a fuskar ta, banda sunan Allah ba abun da take kira.
"Sannun ki baiwar Allah" taji wani zazzakar murya irin nata sak ta bayan ta, a razane Rimsha ta juya, wata kyakkyawar yarinya ce, yar matashiyar budurwa, wadda ba zata wuce Rimsha ɗin a shekaru ba. Cikin sauri Rimsha ta miƙe tsaye ta kari sa wajen yarinyar tana kuka kamar ranta zai fita, da kyar ta iya cewa "Dan Allah ki taimake ni, yan uwana zasu mutu, suna zubar da jini" tayi maganar cikin ruɗu da kiɗi ma haɗi da tashin hankali mai tsanani.
Sanya fararen hannayen ta yarinyar tayi, ta goge wa Rimsha hawayen fuskar ta, a nitse tace "Ki yi shiru, abun da nazo yi kenan, taimakon ku" ta kai karshen maganar tare da wucewa wajen da su Ayla ke kwance.
A gaban su ta tsugunna tare da ciro wani magani daga jakar da take rataye da shi a jikin ta, cikin sauri Rimsha ta ƙariso wajen ita ma, tana hawaye ta tsugunna kusa da yarinyar tana kallon yadda yarinyar ke shafawa su Ayla maganin hannun ta.
"Ki yi shiru Rimsha, ki dai'na kuka kin ji?" Cewar yarinyar, zaro ido Rimsha tayi murya na kerman tsoro tace "Waye ya faɗa miki sunana" cool murmushi yarinyar ta saki, har sai da dimple nata irin na Rimsha ya lotsa, haka zalika murmushi nata yayi sanadiyar bayyanar kyawawan fararen hakwaran ta, har wani haske ke fitowa daga tsakanin hakwaran nata, yarinyar kyakkyawar yarinya ce ajin farko, jikin ta sumul babu ko alamar tabo a jikin, fara ce tas kamar farin turawa ko in ce yan Korea, hancin nan nata ɗan siriri kamar pencil, tana da manya-manyan ido kyawawa, sai dai abun mamaki idan nata sak na Rimsha babu abun da ya ra ba, ita ma sleeping eyes gare ta, haka zalika bakin ta sak na Rimsha babu abun da ya raba. Babu abun da ya fi jan hankalin Rimsha a fuskar yarinyar nan face gashin gerar ta da kuma yanayin shape na fuskar nata, babu abun da ya raba shi da na Rimsha ɗin, sosai Rimsha tayi mamaki ganin wannan halitta mai kama da ita, gashi kuma a tsawo ma ba zata wuci Rimsha ɗin ba, haka a shekaru, a takaice dai banbancin wannan yarinya da Rimsha hasken fata, ita Rimsha fatar ta chocolate color ne, yarinyar kuma fara ce tas, kuma jikin yarinyar bai yi yana yi da jikin ɗan Adam ba, dan baka iya ganin joint na jikin ta, sannan kuma babu tabo ko kaɗan