Showing 156001 words to 159000 words out of 355604 words

Chapter 53 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2802

ku a rufe hakan yasa na kara gasgata cewa E tafiya kuka yi, na shiga tashin hankali domin bansan in da zan je in kwana ba, ina zaune a wajen har yamma, da dai naga dare ya fara yi sai na tashi na koma bakin hanya na tari abin hawa dan na koma gida, ina komawa na tarrar an sanyawa gidan mu kwaɗo an rufe shi, nasha kuka sosai shine na zauna a bakin gate ɗin, tun da bani da in da zan je, a nan wata mata ta zo ta same ni, shine ta ce na zo muje gidanta ga gidan nata a can, ita makwanciyar mu ce, ba musu na bita domin ina jin yunwa kuma na gaji. Da muka je gidan matar ta riƙe ni da amana, sai dai kuma mijinta ɗan iska ne, sai cikin dare yake lallaɓawa ya shiga ɗaki na, yana mini baraza idan ban yarda da shi ba sai ya yanka ni...." Cikin sauri Jehan ta katse ta da cewa "Kuma kika yarda?".

Girgiza mata kai ta yi ta ci-gaba da cewa "A'a Allah yana tsareni Allah yana taimakona, ina tserewa duk wani tarko nashi, toilet nake gudu na shiga, ba halin ya buga kofar matar zata ji, sai dai ya hakura ya tafi, daga baya na dawo rufe kofana da key idan dare ya yi, amma dai nasha wahala ba kaɗan ba, lokacin da Hajiyar ta gane cewa mijinta yana nemana, sai ta bani laifi ta koreni daga gidanta, haka na bar gidan na fita kan hanya ba ni da mafaka, ranar na sha kuka, kuma duk in na kira layin daddy bata shiga haka ita ma mummy layinta baya shiga, na sha wuyar tafiya a ranar, ga uban trolley da nake ja, to a hanya na haɗu da wata Hajiya ta kawo ni gidan nan" ta Kai karshen maganar tana goge hawayen da yake zubo mata akan fuskarta.

"Yanzu ina wayar taki?" Cikin sauri ta miƙe ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko wayar tare da dawo ta zauna ta miƙawa Jehan ɗin. "Dama kin zo da kayan sawar ki ne ɗazun kika bani kaya marasa hankali?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce "An hana ni yin amfani da sune a gidan nan, iya kayan da Hajiya ta saya maki su kawai zaki sanya, shiyasa ban baki ba" guntun tsaki Jehan ta ja tare da miƙewa ta wuce izuwa wajen trolleyn, doguwar riga abaya pink color ta fitar tare da mayafinsa, ta ɗauka ta wuce toilet.

Jim kaɗan ta fito sanye da kayan a jikinta, da yake ta ɗan fi Adiva tsawo, sai rigar bata kai mata har kasa ba

Kallonta Aisha ta yi ta bushe da dariya tana faɗin "Amma Jenan kin kai yar duniya, wato tun da an hana amfani da su, ke kin yi kena, wato dai ayi uban da za'ayi, wlh ina jiye maki ni dai". Bata bi ta kansu ba ta koma ta zauna tare da ɗaukar wayar Adiva ta fara gwada layin daddyn Adiva wato uncle Shitu, layin akashe kamar kullun haka ma na mum ɗinta shima baya shiga, shiru ta ɗan yi kafin ta saka nata layin ta gwada shima shiru, mum ɗin su shiru, har na daddyn su shima shiru a kashe, a fili ta furta "Wannan wace irinyar bala'i ce, kowa layin a kashe sai ka ce abin haɗin baki" Ta kai karshen maganar tare da ajiye wayar ta kwanta tana jin cikinta yana mata bala'i kugin yunwa, kuma ta rantse wannan abincin dai da suka bata ba zata ci shi ba matukar ba tare da Adiva za su ci ba.

Suma kwanciya suka yi suka fara hira, ita dai bata saka masu baki ba, ita ma Adiva da ido kawai take binsu, Aisha da Maryam ke ta zuba kamar kanya

(To fah Jehan kina tsaka mai wuya ni dai na haɗa kayana zuwa wajen Rimsha dan muga ya suka je shopping)


Karfe 8 daidai na dare, bayan sun yi sallar isha, sun ci abincin da Rimsha da Akila suka girka, Imran ya ɗauke su zuwa shopping ita da Akila da Umaisha, da farko Akil ya ce Umaisha ba zata je ba, sai daga baya da Imran ya ɓata rai shine fa ya hakura ya ce ta sanya nikaf su tafi.

Sosai Akila da Umaisha suka ɗebi kaya son ransu, ita kuma Rimsha sai nuƙu-nuƙu take yi, domin kunyar ɗibar kayar take ji, da Akila ta lura da hakan ne sai ta fara ɗebar mata, har da su chocolate suka ɗeba, kayan sawa sosai, da suka zo layin breziya Akila da tsiya sai ta juya tana kallon Rimsha ta gani ko dai ta ɗaukar mata ne ko bata fara ba.

Ganin haka yasa Rimsha ta kama kanta ta bar wajen, Imran na zaune daga ɗan nesa da su, yana kallon su yana murmushi, abin gwanin ban sha'awa.

Ganin Rimsha ta gudu yasa Akila ta kwasan mata breziyar dozin biyu ƴan madaidaita, bayan ta ɗauka ne sai ta nufi wajen ta, nan ta same ta wajen kayan barci.

"Au a nan kika fi kauri kenan? Tom ni dai na fin son a rinƙa yi wa yaya Ahmad ciko" ko sannu Rimsha bata ce mata ba, dan bata ma gane me take nufi ba, sai dariya Umaisha take yi musu.

Daga nan suka wuce wajen always, kallon Rimsha Akila ta yi ta ce "Kin fara ne na ɗibar maki?". Duka Umaisha ta kai mata a baya tana faɗin "Me ta fara? Ke Akila kin lalace wlh, sai na gayawa yaya Akil ayi maza ayi maki aure kada ki wuce gona da iri". Turo baki Akila ta yi tana faɗin "Wai ke Aunty Umaisha na kasa da ke ne? Ni da kanwata nake magana, ba dole na tambayeta ta fara bane ko bata fara ba, ko so kike naje na kwaso mata abu kuma azo bata fara ba". Ita dai Rimsha ta rasa gane me ta fara, kwata-kwata ba ta fahinci akan me suke magana ba, domin hankalinta bai kai kan Always ɗin ba, yana kan lotion da shower gel dake kusa da wajen, so bata lura da always ɗin ba.

"Ke idan zaki ɗauka mata gara ma ki ɗauka mata, domin dai kin san dole zata fara, baki ga ma har kirjinta ya fara cika bane? To kirji ya cika kuma ai dole a fara".

Sake baki Imran ya yi yana kallonsu yana salati a cikin zuciyarsa, wai yaushe Akila da Umaisha suka iskance haka ne bai sani ba? Lokaci guda tunanin Jelly ya faɗo mashi a ransa, in dai Rimsha ta fara period to ba shakka Jellynsa ma ta fara, domin a irin ganin da yake yi wa Rimsha jelly zata fita shekaru, kuma haka ne Jelly ta girmi Rimsha, nan fa ya fara tunanin tare da addu'ar Allah yasa bata fara ba, Allah yasa a hannunsa zata fara, Allah ya bayyana mashi ita, lokaci guda mood nasa ta sauya, har ja idanuwansa suka yi, damuwa karara ya bayyana mashi a kan fuskarsa.

Su kuwa su Akila sai tsula tsiyarsu suke, basu yi tunanin yana ganin su kuma yana jinsu ba. Da suka gama da always sai suka wuce wajen pant, a nan ma sai da suka yi tsiya son ransu, har da wani cewa Rimsha ta fi su mazaunai dan haka ta juyo su gwadata karsu ɗauki pant karami wadda ba zai isheta ba, tun Rimsha na nokewa bata biye masu, har ta fara biye masu, suna yi suna dariya, abin gwanin ban sha'awa.

Sai da suka gama kwasan duk abin da za su buƙata, sannan sa ka wuce wajen biya, keken ya cika tab da kaya, dogayen riguna kam ba'a magana, sun kwashesu iya son ransu.

Haka aka yi wa Imran bill ya biya, ma'aikatan wajen suka shirya musu kayan a bayan mota, daga nan suka wuce gida.

Suna zuwa ya wuce bedroom nasa, su kuma a ɗakin Rimsha suka baje kayan saman gado, suka shiga rabawa kowa tana ɗaukar nata, suna yi suna hira. Ba su suka rabu ba sai da Akil ya kira Umaisha a waya, sannan ta yi masu sallama ta kwashi kayanta ta wuce, ita kuma Akila sai da ta taya Rimsha suka jere kayan a cikin wall-drof sannan ta yi mata sallama tare da kwasan nata kayan ta wuce zuwa cikin gida, bata so rabuwa da Rimsha ba, ta so su kwana tare amma ba dama, domin Ammie ba zata yarda ba, Ammie zata je ɗakin ta domin ta dubata, hakan yasa ta wuce ba dan ta so ba.

Ita kuma Rimsha Akila na tafiya ta miƙe ta shiga toilet, wanka ta yi ta fito, yau ga mayukanta da ta saba amfani da su lokacin da daddy yake nan, saman mirror chair ta zauna ta fara shafa Lotions ɗin, ga turaruka kala-kala, dama ba baya take ba wajen son kamshi, haka ta fashe jikinta sosai, sannan ta shirya cikin wasu riga da wando masu laushi na barci, ɗaya ne daga cikin kayan da suka sawo yanzu.

Bayan ta gama shiri, sai ta haye saman bed ta bi lafiyar gado, tare da jan lallausan bargo ta rufe jikinta, ta yi addu'ar barci ta lumshe idanu.

Ni kuma na haɗa kayana sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu a gidan daddy wato Washington DC bye

💖TRIPLET'S💖💖


E45_46


💖💖Washington DC💖💖

Zaune suke a palon kasa, Tga, John, Jay, da kuma daddy da Uncle Herry, Kamar dai kullum kowa da abin da yake yi, kowa hankalinsa na kan abin da yake yi, daddy da Uncle Herry suna shan black tea sun matso da glass table date tsakanin sofa set aky blue a gabansu, Jay da Tga suna aiki latsa waya da laptop, shi kuwa John yana kwance dan bai gama samun sauki daga horar da shi da Tga ya yi ba, yau ma kamar dai kullum ɗin sharholiyar su suke yi, kowannansu kananan kaya ne a jikinsa, bare ma Tga da shi rigar tasa ma ji yake tamkar ya cireta, saboda dama shi baya san harkar zafi ko ya take, har daddy da Uncle Herry dukka su three quarter ne a jikinsu zuwa gwiwarsu, yanzu daddy baya wani damuwa da rashin James domin kullun sai sun yi waya amma fa a na shi tunanin ne yana waya da James, a zahiriya kuma da Lion yake waya ba James ba.

(To fah🤔)

Lion ke shirya mashi wannan basajan domin basu son abin da zai ɗaga mashi hankali har ya yi sanadiyar taɓa lafiyarsa.

Wani daddaɗar kamshin perfume suka ji, wadda basu taɓa jin irin wannan kamshin a gidan ba, har suna rige-rigen ɗago kai su kalli bene dan suga waye ne mai wannan kamshi, domin ta bene kamshin ke fitowa.

Subhanallah miƙewa Tga, Jay, da kuma John suka yi lokacin guda suna kallon benen, daddy da Uncle Herry kuma ajiye cups ɗin hannunsu suka yi tare da zuba mashi idanu suna kallonsa.

A hankali yake sauƙowa daga benen Musharraf na gefensa sun jero, sai murmushi yake yi. Sanye yake da wandon jeans, cikakken wando ba crazy ba, ba kuma guntu ba, har kasa kuma asalin Jeans wanda babu wani alkus a jikinsa, daga ta sama kuma yana sanye da Round neck polo shirt sky blue, yau ya yanke brown hair nan nasa, duk da cewa dama bata da wani tsawo sosai bata kai na Lion da James ba, baya barinta tayi tsawo dan tana takura mashi a cewarsa, amma yau ya yanketa kusan gaba ɗaya, wadda ta rage a kansa bata wuci kamar na yara kanana wayan da ake yi wa kitson roba ba, dan ko kusan kamuwa wadda ta rage a kansa nasa ba zata kamu ba.

Kafarsa na sanye da Booth sky blue mai bala'in kyau, sai tashin kamshi yake yi, ya sanya glass baka a idanuwansa, fuskar nan tasa har wani kyalli take yi tana curly kamar wadda ya shafa baby oil, yau ya yi dressing na cikakken mutun mai hankali da ilimin tare da class.

Shi ma Musharraf shigarsa kusan iri ɗaya da Michael ɗin, sai dai shi rigar sa fara ce.

Basu taɓa ganin Michael a irin wannan yana yi ba, ga shi wani irin sihirtaccen gwarjini na jikin William jacop ne ya bayyana akan fuskarsa, kai da gani kasan jinin Lion ne, ya zama cikakken mutun, hannunsa na ruƙe da wayarsa, cikin natsuwa yake takawa har suka sauƙo kasa.

"Hi uncle T, daddy, Uncle Herry hope you are enjoying your afternoon?" Shine abin da Michael ya faɗa, ya yi maganar cikin wata irinyar natsuwa kai ka ce Lion ne ke magana a wajen, saboda tsabar natsuwar da ya yi, da kuma yadda ya fito da words ɗin, sai ka yi zaton James ne, dan shima James daga bayan nan ne ya fara magana ya ɗaga murya, shima yana yi ne dan basaja, amma ba don haka ba, shima kasa-kasa yake magana cikin natsuwa.

"Uncle T why are you stearing at me like this? Why are you people starding? Jay, John hope you are okey?". Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da mamaki, domin yadda suka tsare shi da ido, ga shi sun mimmiƙe suna kallon shi, abin ya ba shi mamaki.

Ganin sun kasa magana ya sa ya ce "Uncle ɗin James let's go" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi hanyar fita.

"Where are you going?" Tga ne ya tambaya cike da izza. Ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba ya ce "Uncle T am i a baby?" "Michael What do you mean by your statement?!" Cewar Tga.

Sai lokacin ya juyo a nutse ya ce " Yes Uncle am I a baby that you asked me where am I going". Tsabar haushi Tga ya ma rasa me zai ce mashi, wato shi ba yaro bane ya wuce a tambayi ina zai je, lallai Michael.

Wucewa ya yi ya barsu da mamaki, Musharraf ya rufa mashi baya, suna fitowa harabar gidan kamar kullun jibga jibgan sojoji ne ta ko'ina a cikin gidan, ko wannan su kuma riƙe da manya-manyan bugayen bindigu, wadda da ka gansu kasan sun wuce wane da wane su riƙe su, na manya ne domin kuma bawa manya tsaro.

Kai tsaye parking space ya nufa, yanzu Lion ya karawa gidan tsaro sosai saboda abubuwan da suka faru, kafin ka shiga parking space ɗin sai wata na'ura dake a wajen ta yi scanning naka sannan ka shiga, haka idan zaka fito da mota kamar dai a baya sai na'uran jikin gate ɗin ta faɗi kalar motar da aka fita da ita da kuma number motar kamar dai second gate, sannan idan ka je gate 2 ɗin ma sai ta sake maimaitawa dan tsaro.

Haka Michael ya fito da wata sabuwar motar suka fito suka hau titi zuwa gate 2, sai da nauran wajen ta gama scanning na motarsu tsab, sannan gate ɗin ya buɗe kansa, yana buɗe wa Michael ya danna hanchin motar zuwa babban gate, ba ɓata lokaci jibga-jibgan security dake a wajen suka wangale masu katafaren gate ɗin, da gudun gaske Michael ya danna hanchin motar waje.

"Michael ka ta fi a hankali mana". Cewar Musharraf ya yi maganar cikin yana yi na tsoro, dariya Michael ya yi yana faɗin "Uncle ɗin James kada ka damu, ko na yi gudu babu wani abin da zai faru, duk da cewa ma ban sanya alamar motar gidan mu bace, amma babu wani abu, bana son kuma na sanya ala'mar motar gidan mu ce saboda bana son magana ya koma gida akan an ganni a masallaci, idan haka ta faru nasan harbemu da gun za su yi mu dukkan mu biyu, shiyasa kaga na ɗauko sabuwar mota ba nawa da aka sanni da ita ba".

Mamaki ne ya kama Musharraf, godiya sosai ya yi wa Ubangiji da ya sanya ƙwaƙwalwar Michael ta buɗu haka har yake iya fitarwa da kansa dabarar da zai bi ya tsirar wa wani abin.

A haka suka isa masallaci suna ta hira cikin nishaɗi. Babbar masallaci ne sosai, da kusan ma shine babba a gaba ɗaya cikin Washington DC.

Kallon Musharraf ya yi kafin ya kashe motar a parking space na masallaci sannan ya ɗauki face mask ya sanya a face nasa, ya juyo yana faɗin "Uncle ɗin James idan na gaya maka nasan za ka yi mamaki, wannan mosque ɗin fa Lion ya gina shi, da kuɗinsa, da shi da wancan babban church da muka wuce a hanyar mu ta zuwa nan, dukka shi ya gina, shi kuma James nasa mosque ɗin da church suna ta wajen jam street, nine kawai a cikinsu ban taba gina wajen wani bauta ba, amma In Sha Allah zan gina, su da suke Kristen ma sun gina bare Ni, zan gina very soon sai dai ni ba zan gina church ba gaskiya". Ya kai karshen maganar tare da buɗe kofar motar ya fito waje.

*Masjidil Al Sultan* shine abin da yake rubuce a saman masallacin, "Asif who is Al Sultan?" Shiru Michael ya ɗan yi kafin ya ce "Like he is the one da yake control na mosque ɗin, domin lokacin da aka gama ginin Lion ya bani kuɗi na kawo mashi wai za su sayi wasu abubuwa na masallacin, alokacin shikuma ya tafi church dan ranar akwai church, sai ya ce in kawo wa Sultan, da na zo na tambayi waye Sultan sai suka nuna mani shi, gently man ne, yana da innocent face, baya da yawan magana, but is an old man sosai". Shiru Musharraf ya yi yana tunanin da alama Lion ba zai yi wuyar shiga addinin Musulunci ba, domin yadda yake taimakawa musulmai, duk da cewa ba iya musulmai kawai yake taimakawa ba, har da addininsa wato Kristen da kuma yan bautar gunki da sauransu, duk wasu gidan bauta yana kai musu taimako, baya ware ko ɗaya daga cikin su, amma Musharraf yana yi mashi kyakkyawar zato akan ba zai yi wuyar musulunta ba.

Yau dai a masallaci suka yi sallah cikin farinciki da annashuwa, cikin natsuwa.

Bayan sun idar da sallah suka fito waje, nan suka isko jama'a sosai a wajen harabar masallacin. Hannu Michael yasa a aljihunasa nan ya fito da kuɗi sosai, haka ya shiga rabawa musulman da suka fito Sallah a tare, ya zura ɗayar hannunsa cikin aljihun baya ya ciro wasu kuɗin ya bawa Musharraf dan shima ya raba sadaka. Allah sarki jinin William


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login