Showing 60001 words to 63000 words out of 355604 words

Chapter 21 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2777

nan suna cin karensu babu babbaka, su uncle Herry harda magana da bada umarnin, shi kuma daddy yana magana yana satar kallon Michael, still Michael bin su kawai yake da wayan nan shanyayun idon nasa, mai kama da mai jin barci, Bawan Allah bai ce komai ba, kamar ba Tiger'n daddy ba.

"This baby is for who?" John ne ya jefawa Jay tambaya. Kallon babyn da kyau Jay ya yi kafin ya ce "are we not looking alike? Is my son mana" kara zaro ido waje Michael ya yi duk da cewa su turawa yin hakan a wajen su ba wani abu bane, wani lokaci ma sai sun haifi ƴaƴa uku da mace sannan suke aure a tsakanin su, amma abin da ban mamaki ba su taɓa tunanin haka daga wajen Jay ba, domin su mutane marasa yarda da mutun kuma suna kula da lafiyar su sosai, shine yaushe ma Jay yake fita da har ya je ya aikata hakan bai gaya mu su ba, bayan kuma basa ɓoyewa juna komai, abin ba karamin mamaki ya ba su ba, Jay da baby, babyn ma ba karami ba zai kai 1 year tab.

Wani cool murmushi yarinyar ta saki lokacin da ta ji amsar da daddy da uncle Herry su ka bada na sun yi accepted na ta a matsayin surukuwa, ta riga Jay wucewa gaba tana ta murmushi ta nufi su dad.

"Don't come here!!" wani gigitatchiyar tsawa Micheal ya daka mata wadda ya sanya ta juyawa a guje ta koma ta rungumi Jay, su kansu su daddy sun tsorata ainun da jin tsawar da Michael ya daka mata, abin da ya bawa Michael haushi wato Jay ya daɗe tare da yarinyar har ma da baby a tsakaninsu.

Uncle Herry ne ya yi ta maza ya ce "Why my tiger? Why zaka ce karta zo nan?" "Shut up uncle!!" Tsawa ya dakawa uncle Herry, a fusace ya ce da yarinyar "get out!!" sanin cewa lion da James basa nan yasa Jay ya yi kokarin tirjewa Michael a kan yarinyar ba zata bar gidan ba ya yi duk abin da zai yi. Lallai yau a ke yin ta.

Da yar dugu Michael ya haura sama, harara Jay ya bi shi da shi yana shafa kan budurwar tasa, a zuciyarsa yana faɗin "Ba ka da abin da za ka yi, sai dai hakuri, ba ka da aiki sai bawa mutane umarni bayan shi ba wani abin da ka iya". A fili kuma kasa-kasa ya ce "Sorry Jennifer" ya kai karshen maganar tare da raba jikinsu ya riƙo hannunta su ka karisa wajensu daddy.

Daddy kam har jikinsa ya fara kerma, saboda baya son tashin hankali ko kaɗan dama daga jiya zuwa yau yana cikin rashin lafiya sosai, saboda rashin James da kuma lion.

Saman chairs Jay da budurwarsa suka zauna, suma su daddy komawa suka yi suka zauna, sai tunanin Michael dad yake yi.

Suna zama Michael ya fito da gudu hannunsa riƙe da pistol gun ɗin Romeo, sai ta su ya yi yana faɗin, Jennifer ta fita gidan nan ko ya harbeta ya harbe banza. A tunanin Jay Michael bai iya harbi ba dan haka sai ya ce ya harbeta ɗin su gani.

Ai kuwa Michael bai yi kasa a gwiwa ba ya ɗana kunamar bindigar ya harbi Jennifer a hannunta, Allah ma yasa Jay ya yi saurin janyota jikinsa ta kauce bullet ɗin ya same ta a hannu ba dan haka ba kanta Michael ya yi niyar harba.

A zafafe gaba ɗayansu suka miƙe ya yin da gaba ɗaya bodyguard dake wajen suka duka kasa gudun kar bullet ya taɓa su, ihu sosai Jennifer ta ke kamar makoshinta zai fashe saboda bala'i a zabar da take ji, ga jinin ta ya fara malala kamar famfo.

Kara sai ta Jay da bindigar Michael ya yi zai harbe shi, cikin sauri Jay ya zube kasa bullet ɗin ta fita ta samu bango, ji kake dam. Kamar wanda baya a cikin hayyacinsa haka Michael ya zama, duk ya ruɗa jama'ar dake palon kuma dukkansu sun san halin Michael sun san matsalar da yake da shi, komai daidai kwakwalwarsa ke faɗa masa.

Gudun cetan rayukansu suka fara, shi kuma yana binsu da gun a hannusa, yana kokarin harbinsu, sai ihu suke, Tga da yake soja ma ya gudu, dan yasan idan mutum irin Michael ya riƙe makami tofa zaman lafiyar ka shine ka gudu ka ceci ranka, idan ba haka ba, ka tsaya kace zaka nuna masa karfin dantse tofa zai maka illane kawai a banza saboda komai daidai kwakwalwarsa ke faɗa masa.

Kewaye palon suka fara yi Michael ya hana su haurawa sama. Ba su ankara ba sai suka ji karar wani harbin dum, Michael ya harbi uncle Herry. Ihu suka fara yi, John kam har da cire wando ya yi wurgi da shi gefe dan wandon tana hana shi gudu, irin wandon yan gayun nan ne wanda suke sakin sa yana faɗuwa rabin bayansu a waje, to idan yana gudu sai dai ya rike wandon idan ba haka ba faɗuwa za ta yi, shine ma kawai ya cire ya yi wurgi da ita gefe guda dan ya sami damar fecewa da kyau.

Gaba ɗaya palo ya hargitse Michael ya birkice mu su da gaske, ya koma mayinwacin Tiger, kokarin harbinsu kawai yake su kuma suna kokarin cetan rayukan nasu.

Kamar a mafarki suka ji wannan daddaɗar fitinannen kamshi perfume ɗin, cak suka tsaya da ga su har Michael ɗin, a razane suka ɗago kai suna yan waige-waige ta ina za su ga mai wannan kamshi, dan sun san mutun ɗaya ne mai wannan perfume ɗin, shiyasa ko barci suke idan suka ji kamshin sun san waye a wajen.

Tsaye yake saman bene can bakin kofar ɗakinsa ya goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa, harbin gun da Michael ya yi ne ya fito da shi, jikinsa na sanye da bathrobe milk color zuwa gwuiwar sa, zara-zaran dogayen kyawawan kafafunan nasa a wajen, ga wasu dark black gashi mai bala'i kyau da tsantsi kwance a kafafun nasa har izuwa idon sahu na kafar. Ya saki dark black curly hair sannan yau bai ɗaure ba da gani kasan wani aikin yake mai muhimmanci, fuskar nan tasa kamar kullun a ɗaure tamau kamar hadari, idon nan nasa yau sun sauya launi sun rikiɗe izuwa ja, ga shi sun rage girma alamar barci bai isshe shi ba, ko kuma wani abin ya taɓa shi.

Dukkan su sun yi mutuwar tsaye sun sha jinin jikinsu, duk wata halitta mai rai a palon sai da hantar cikin ta ya kaɗa. Tuni jikinsu Tga ya fara kerma dan ko a mafarki ba su taɓa zaton lion ya dawo yana cikin gidan ba, Michael ne kawai ya sani ko daddy bai sani ba saboda shigowar daren jiya ya yi kuma dawowar sirri ya yi dan wani aikin nasa da ya saka a gaba, yanzu ma da Michael ya je ɗakinsa ya ɗauko gun yana cikin dressing room nasa yana shiryawa bayan ya yi wanka kenan.

Fitsari a wando Jay ya saki dan ya san yau kashinsa ya bushe, ya kawo mace a gida lion na nan kuma macen ma har da babyn sa, bayan yasan cewa lion ya hana su yin hakan, dan tun basu kai haka ba tun ba su wuce 24 years ba lokacin ma lion bai wuce matakin general ba a wajen aiki, ton tsanar mum ɗin su bai yi mu su yawa haka ba, lion ya ce duk mai son yin aure ya nemi mata ya yi aurensa amma zai bar gidan nan za'a saya masa wani gida, duk rintse duk wuya kada su nemi mace ba tare da aure ba amma shi Jay ya yi hakan a tunaninsa da wawtarsa lion ba zai sani ba, shi a nashi lissafin idan ya kawota gida kowa ya ganta tunda lion baya nan, sai ya wuce da ita church a ɗaura mu su aure, dama ya jima yana dakon ranar da lion zai fita wata ƙasa sai ya gabatar da Jennifer ga su uncle, sai dai kash rana ta kwaɓe masa.

Tsuru-tsuru dukkan su suka yi, ya yin da Jennifer ta suma a wajen haka zalika shima uncle Herry ya sume. Duk da cewa Jay ya yi fitsari a tsaye bai daina matse cinyoyinsa ba kamar ba lafiya ba, jikinsa sai kerma yake tamkar wanda ya haɗu da zaki, ko da yake a cewarsu gara su haɗu da zakin a tsakiyar dokar dajin da ba komai sai mugayen namun dawa da su haɗu da Romeo sun yi laifi, domin zaki cinyewar lokaci guda zai yi mu su, shi kuma Romeo sai ya azabtar da su, ya basu wahalar da sai sun gwammaci mutuwa. Yau sun shiga tashin hankali ainun

Zama dad ya yi saman sofa dan ba zai iya ci-gaba da tsayuwar ba, zai iya faɗuwa kasa, jikinsa sai kerma ya ke yi. Allah sarki baya son tashin hankali ko kaɗan

Kuka Michael ya sa tare da sakin gun ɗin ta faɗi kasa, shi ma kuma zama ya yi a kasan yana kuka kamar ƙaramin yaro. Tga John duk zube gwiwowinsu a kasa suka yi jikin na ta ɓari, ga shi sun san lion baya son kalmar sorry ko kaɗan idan ma suka yi gigin ce masa sorry wlh tsab zai iya harbesu da gun su mutu, zaman lafiyar su shine su zube gwiwowinsu a kasa kawai su jira hukuncin da zai yanke mu su. Sannan kuma sun ɓata masa rai domin kuwa ga alama nan a kan fuskar sa.

Lalai yau kuna tsaka mai wuya, ni na yi nan, ba zan iya ganin kilishi da tsiren da za'a yi da ku ba yau🤣🤣🤣

💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 19-20🌹

Kuka Michael ya sa tare da sakin gun ɗin ta faɗi kasa, shi ma kuma zama ya yi a kasan yana kuka kamar ƙaramin yaro. Tga John duk zube gwiwowinsu a kasa suka yi jikin na ta ɓari, ga shi sun san lion baya son kalmar sorry ko kaɗan idan ma suka yi gigin ce masa sorry wlh tsab zai iya harbesu da gun su mutu, zaman lafiyar su shine su zube gwiwowinsu a kasa kawai su jira hukuncin da zai yanke mu su. Sannan kuma sun ɓata masa rai domin kuwa ga alama nan a kan fuskar sa.

Lalai yau kuna tsaka mai wuya,

Bodyguard dake palon gaba ɗaya miƙewa suma suka yi suka zube gwiwowinsu a kasa, ala'mar sun shiga tashin hankali da kuma bala'i yau. Tsit palon ya yi tamkar babu wata halitta mai rai a cikinta, numfashi ma a hankali suke saki

Shi kam Jay mutuwar tsaye ya yi ai, gaba ɗaya baya tare da mutane, da alama suman tsaye ya yi, Jennifer da uncle Herry da suka sha harbin bindiga a hannayensu suna sume hannayen nasu na malalar da jini.

Lion ya jima tsaye a wajen yana kallonsu ba tare da ya ce upan ko ya yi wani motsi ba, shi kuwa Michael yana aikin kuka da hawaye da yawu.

After some minutes, a hankali lion ya sako kafarsa ya fara taka benen ya sauƙo cikin palon.

Bayan ya sauƙo ne ya nufi hanyar fita daga palon, har ya kai bakin kofa sannan ya ce su biyo shi, ya kuma ce da Michael da ya ta shi ya ɗauko masa puffer Jacket a ɗakinsa saboda bala'i sanyi da a ke yi a waje, a cikin kam ba'a sanyi saboda na'urorin ɗumama ɗaki da suke amfani da su.

Jin haka yasa Michael ya miƙe cikin sauri ya haye sama dan ya ɗauko jacket ɗin, su kuma su Tga cikin zafin nama suka miƙe suka bi bayan lion. Har sun kai bakin kofa sai ku ma suka ga ba Jay, da sauri suka juya, Jay na tsaye ya kasa motsawa saboda bala'i tashin hankali da yake ciki, ji yake tamkar ya murɗe wuyarsa kawai ya kashe kansa ya huta da punishment da lion zai ba shi.

Cikin Sauri Tga ya dawo ya janyo shi suka nufi waje dan sun san lion baya jira sai dai a jira shi. Suna fita shi kuma daddy ya aiki bodyguard daya kawo masa first A box dan ya fara bawa Jennifer da uncle Herry taimakon gaggawa. Haka kuwa a kayi ɗaya daga cikin bodyguard ne ya kawo masa A box ɗin ya karɓa ya fara aiki. Sai godiya bodyguards ɗin suke na lion bai kula da su ba, ya kyalesu bai bi ta kansu ba

Shi kuma Michael cikin zafin nama ya ɗaukowa lion puffer Jacket ɗin ya kai masa wajen horarwan sa.

Waje ne da lion ya ware na azabtar da masu laifi a gidan, duk wani nau'i na kayan azabtar da ɗan adam akwai shi a wannan waje, kama daga ruwan kankara, sai wani ruwa mai kalar green color mai kauri kamar gantsa kuka, ruwan yana da kauri sosai ga wari, sannan akwai na'urori kala-kala irin na yankewa mutun yatsa, gabansa, hannu, kafa, da sauransu, ga wasu manya-manyan kunamu da wasu kwari da a ka tana da cikin wasu glasses mai kama da show glass, cikin kwarin nan har da wasu halittu da ke da cizon bala'i, idan suka cijeka sai kafi wata kana fama da jinya, wannan wajen duniya ne wajen kayan horar wa, akwai abubuwa da dama wadda ba za su kirgu lokaci guda ba.

A cikin wajen akwai zaratan sojoji masu lafiya da jini a jika, wadda da ka kallesu bakaga alamar imani a tattare da su ba, fuskokin nan nasu babu annuri ko kaɗan, ga su jibga-jibga da tsawo da ƙiba dukka, ga cikar halitta, sun samu horo mai kyau.

Gaban wannan green ɗin ruwan Romeo ya je ya tsaya, da sauri Michael ya ɗaura masa puffer Jacket ɗin nasa, a kafaɗar sa, zura hannayensa ya yi ya sanya jacket ɗin da kyau a jikinsa. Shiru suka tsaya suna kallon ruwan shi da Michael, ruwan yana da tsawo sosai, amma bai da wani faɗi sosai.

Tun kafin lion ya ce su shiga cikin ruwa suka yi sauri suka faɗa, Tga, Jay, da kuma John, shi kuwa Michel da shi ya haddasa komai yana tsaye kusa da Romeo har da wani kwanto da kai ya yi a saman bayan Romeo, yana turo baki irin na shagwaɓa.
Saboda son kai irin na Romeo sai bai yi yunkurin hukunta Michael ba, sai ma kara jan sa a jiki ya yi a cewar sa ai Michael bai da lafiya dan haka sai dai a lallaɓa shi ba dai a hukunta shi.

Kai Romeo wannan son kai ne, bawani bai da lafiya ya harbi uncle Herry da Jennifer da bindiga fa, ba shi da lafiya amma ya iya harbi ai😭

Su Tga kuwa suna shiga cikin ruwan, wasu zaratan sojoji guda biyu suka ɗauko wasu zabga-zabgan bulalu wanda ganin su da ido ma kawai ya isa ya saka mutun fitsari a wando, ga shi fuskokin sojojin nan babu alamar annuri ko kaɗan bare mutun ya sa ran zasu tausaya masa.

Cikin Ruwan da su tga suka shiga nan wayan nan sojojin suka shiga, amfanin su a nan shine, su Tga za su nitsa cikin ruwan tundaga farkon ta har kashe, za su yi tafiya a cikin kasan ruwan zuwa bakin gaba, idan suka ɗago kai wayan nan sojojin zasu zabge kan nasu da bulala, a dokar ruwan idan an shiga ba'a ɗago kai dan shakan numfashin sai an kai karshe.

Haka suka fara iyo cikin wanan kakkauran ruwan, wadda aka zuba masa abubuwa kala-kala, ga shi ba daman shan ruwan kuma ba daman numfashin.

Idan suka yi iyo kaɗan sai su ɗan ɗago dan su shaki numfashin, suna ɗagowa wayan nan jibga-jibgan sojojin masu kama da samudawa zasu zabga musu wayan nan zabga-zabgan bulalu dake hannunsu, sai dai ka ji shaw, ga shi ba halin yin kuka ga azaba, amma haka suke ɗan ɗagowa su shaki numfashi saboda kar su mutu, gara musu su ɗago su karɓi wannan bulala a kan rashin numfashi ya kashe su.

Lion na tsaye ta goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana kallon su, fusataccen fuskar nan tasa kamar hari tamau take, Michael kuma sai wani kara langwaɓe masa yake a baya.

Wahala iya wahala su Tga sun sha, ɗan gara ma Tga da yake ya ɗan saba dan ya yi training aikin soja, amma Jay da John ba'a maganar irin azaban da suka sha sun azabtu over.

(Hmmm Romeo ba baya ba wajen bada horo, idan ka bari ku ka yi arba kayi laifi ta bakin sojojin nasa gara ka kashe kanka da kanka a kan hukuncin sa, dan hukuncin sa ya fi haɗarin mota muni, musamman ma yanzu da yake cikin zafin kai yana aiki suka takura masa da hayaniya, ga kuma Jay ya kawo musu mace, macen ma har da yaro, tashin hankali lallai akwai show!)

Da kyar suka iya kai bakin gaɓar ruwan, duk sun ji ga ta, da kyar suke iya numfashi. Suna kai bakin kaɓa suka ɗago kai cikin sauri dan su samu damar yin numfashi. Sojojin dake zane sune suka fara fita daga cikin ruwan kafin su ma su miƙe zaune amma sun kasa fita saboda tsami da gwiwowinsu suka mu su dan rarrafe suka rinƙa yi.

Gyaran murya lion ya musu, cikin sauri suka tattara duk sauran karfin da ya rage musu su ka miƙe tsaye, sai tangal-tangal suke gwanin ban tausayi, ga shi kuma ba su isa su ce ba za su iya tafiya ba saboda sun san sauran.

Wucewa lion ya yi zuwa wajen ruwan kankara. Da kyar suke jan kafa suka fito daga cikin ruwan suka bi bayan shi. jay yana ji kamar ya murɗe wuyarsa kawai ya mutu, amma kuma idan ya tuna in ya mutu shikenan zai rabu da yaronsa sai ya fasa dan yana bala'i son yaron nasa.

Wajen ruwan kankaran nan Romeo ya tsaye tare da goya hannunsa a saman faffaɗar kirjinsa yana kara ɗaure fuska. Ba zaka taɓa cewa akwai kankara a wajen ba, saboda kamar swimming pool a kayi wajen sai dai wannan ya fi pool tsawo kuma bai kai pool faɗi ba, sannan an fure saman wajen da tiles ba zaka taɓa cewa akwai ruwa ko maka mancinsa a cikin wajen ba. An yi kofa biyu ma su design na cycle ɗaya a farkon wajen ɗaya a karshen wajen, ala'mar kofar shiga da fita ne, idan ka shiga ta nan sai ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login