Showing 327001 words to 330000 words out of 355604 words

Chapter 110 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2821

dan haka ba, kowani motsi zata yi akan idanunsa take yi, akwai wani mata ki da yake son ta kai ne dan ya yi amfani da ita, shiyasa ya rinƙa bibiyarta yana kula da ita.

Ya kuke ganin wannan abin zai kasance, daga karshe dai ga Aafia zata koma gidan Abbon baki ɗaya, to mu dai je zuwa, ni dai na yi gaba sai kun zo.

Yau murna a wajen ƴan gidan ba'a magana, sun yi wunin cikin farin ciki, while ita kuma Ommu tana cikin ɗaki tana zuba barcinta dan ita bata wani damu da fita waje ba, bata fitowa palo sosai sai dai idan wani abin zata ɗauka.

After some hours, bayan sallar la'asar rana ta yi sanyi, sun yi sallah sun ci abinci sun zauna suna hira, Ummi ta ce da Nawid su koma gida.

Miƙewa ya yi suka sallami su Abbi tare da yi masu godiya sosai da sosai zasu tafi, Abbi ya ce su wuce da Aafia, mamaki ne ya kama Ummi, a nata tunanin sai sun kawo lefe da sauran abubuwan biki, Abbi ya ce kada su damu abawa Nawid matarsa daga baya za'a kawo mata kayanta da abubuwan da ake buƙata, har kasa Ummi ta duƙa tana yi wa Abbi godiya tare da fatan alkhari, shima godiya ya yi masu na riƙe jelly da amana da suka yi, rungume Jelly Ummi ta yi tana mai kara jin kaunarta har cikin ranta, ita ma jelly sosai take kaunar Ummin duk da bata iya tuna rayuwar da ta yi a gidan nasu ba, amma dai ta na jin a jikinta tabbas ta taɓa rayuwa da su kamar yadda suka faɗa.

Har wajen mota gaba ɗaya family suka rakosu, sai kuka Aafia take yi, lokaci guda an rabata da ƴan uwanta, bata taɓa tunanin wannan zuwan da su yi zata rabu da ƴan uwanta ba, abin ya yi mugun taɓa mata zuciya, sai rarrashinta Ummi take yi tare da rungumarta suka zauna a gidan baya na mota, shi kuma Nawid gaisawa suka kara yi da su Imran sannan suka yi sallama bayan ya zubawa su Abbi godiya, ya shiga gidan gaba na motar, ayya Ummi ta ɗauka da Aafia da jellyn ɗaya ne, bata banbanta su ba ta rungumo Aafia kamar Jelly, a haka suka bar gidan, Nawid ya ja mota.

Duk wannan abin da ake yi Ommu tana sane amma bata leƙo ba, jirama take yi mutane su ragu ta jawo Umaisha ɗaki ta ɗaurata akan hanya dan su sami kuɗi, ita idan ba magana ta kuɗi ake yi ba, to ba zaka same ta a wajen ba.

Jama'a wai shin ina Ommu take kai kudi ne? Me take yi da sune?

Tana ji aka aurar da Aafia, amma bata wani damu ba, da ma taga ɗan ƴar uwarta ta aura sai ta ɗan ji haushi domin a nata ganin Nawid ba shi makudan arziki sosai.

Bayan tafiyar su Nawid ne su Abbi kuma suka juya za su koma cikin gida, cikin dabara Akil ya jawo Umaisha suka shige cikin motarsa dan shi fa baya iya zama 2 hours bai murjesu ba wato tula tula, idan bai taɓa su ba har zazzaɓi yake yi, Abbi yana ganinsu suka shiga cikin mota, amma sai ya yi kamar bai gansu ba, kuma tunani ma ya yi akan su zo su wuce gidansu kada su yi masu abin kunya a nan, yara kamar wasu chewing gum kullun suna manne.

Shi kuwa Imran ango na Jelly, yana son keɓewa da matarsa amma ba hali domin kuwa shi ba irin su Akil bane, yana da kunya sosai, daddyn Jelly da ya fahimci hakan sai ya ce da jelly'n ta je ɗakinsa ta ɗauko mashi agogonsa.

kamar ta san ɗakin nasa ganin Akila ta fita waje ɗazun da ya ce ta ɗauko mashi kuɗi, haka ta wani miƙe da sauri ta nufi wajen ita ma, kuma dama yasan bata san ɗakin nasa bane yasa ya aikata dan kawai ta fita Imran ya bi bayanta su je su ɗan tattauna, dan gaskiya Imran ya wahala akanta sosai, yana da kyau yanzu su sami lokaci sosai a tare.

Tana fita kuwa Imran ya zame cikin sanɗa ya bi bayanta, da yake part biyu ne a gidan, daga nasu Irfan ɗin sai na su Abbin, hakan yasa tana fita ta nufi ɗayan part ɗin, shima yana fita ya bi bayanta.

A palon ta tsaya da yake ɗakuna uku ne a cikin palon, ta tsaya tana tunanin wanene na daddy'nta, daga ta baya ya runhumeta tare da kwanto da kansa a saman kafaɗunta.

"Yaya Imran" ta ambata tana ƙoƙarin juyowa, "Waye ya gaya maki nine?" Ya yi maganar tare da juyo da ita suna fuskantar juna.

"Ba wanda ya gaya mani kawai a cikin zuciyata na ji cewa kai ɗin ne". Ranƙwafo da kansa ya yi a saman tata suka haɗa goshi, har cikin ido take kallon shi, yayin da shima yake kallon cikin idanunta.

"Jelly kin san yadda yaya Imran yake son ki kuwa?" Turo ɗan bakin nan nata ta yi har yana taɓa nashi, cikin shagwaɓa ta ce "E ai nima ina son ka ko?". Wani dogon numfashi ya ka lokacin da bakinta ya taɓa nasa.

A hankali ya ɗan fito da harshensa yana lasan saman lips nata, ƙoƙarin kwace kanta ta yi domin ta raba jikinta da nashi, riƙeta sosai ya yi tare da capko lips nata na kasa ya fara tsotsa, zaro idanunta ta yi tana kallonsa, cikin sauri ya sa hannunsa ya rufe mata idanun nata dan kunyar kallon cikin idonta yake yi a yayin da yake kissing nata.

Da karfi ta ture shi tana faɗin "Wlh sai na gaya wa daddy kai ɗan iska ne, wato abin da ake yi a film shine zaka yi mani ko? Wlh bana sonka tunda dai haka ka ke, kuma dole na gayawa daddy abin da ya ce kada na yarda wani namiji ya yi mani ka yi mani yau". Ta kai karshen maganar cikin kuka tare da juyawa da sauri dan ta koma cikin gida.

Da sauri ya riƙota yana mai bata hakuri akan dan Allah kada ta faɗa ya tuba ba zai sake ba, kin yarda ta yi har da rantsuwa sai ta faɗa.

Yana cikin bata hakuri ta kwace kanta da karfi, da gudu ta juya zuwa part ɗin su Abbi, dafe kansa ya yi yana tunanin jama'ar dake a cikin palon, dama dai iya daddy ne to da da ɗan sauki, amma har da su Akila a wajen fa, tuna hakan yasa ya juya da sauri ya je ya shiga motarsa tare da kiran Rimsha a waya akan ta fito da sauri su tafi domin a gaskiya ba zai iya haɗa idanu da jama'ar palon ba, kuma yasan ba makawa jelly sai ta faɗi wannan magana, me ma ya kai ni yi mata kiss a gidan nan? Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

A haka Rimsha ta fito ta same shi, cikin sauri ya ce ta shiga su je, ai kuwa ba ɓata lokaci ta shiga, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, kunya ta kore shi a gidan.

Yana shiga gidan Lion sai ya ga ba motar Lion ɗin, hakan ya tabbatar mashi da Lion baya gidan kenan, kallon gateman ya yi tare da tambayarsa Lion ya fita ne? E ya amsa mashi tare da ce mashi sun fita tare da Mark, jinjina kai ya yi kafin ya ce da Rimsha su je su duba jikin Areef sannan su wuce bedroom nasu.

Jerawa suka yi zuwa cikin gidan. Kwance su isko Areef, da kallo ɗaya Imran ya yi mashi ya san ba lafiya ba domin kuwa gaba ɗaya ya sauya kamar ba shi ba, abin da kuma yake faruwa shi ne, G.M.A sun gane Lion yana son cire Areef daga cikin su, ya sanya ta ko'ina ana yi wa Areef ɗin saukar Al Qur'ani mai girma, ga addua'o'i, shima Lion ɗin kwata kwata yanzu baya barcin dare, kwana kai wa Allah kukansa yake yi, yana gayawa Allah damuwarsa, azumi kuwa ba'a magana, yana yi wa Areef azumi sosai ga sadaka da karatun Al Qur'ani mai girma, duk fitar da yake yi kwanakin nan gidajen gajiyayyu da gidan marayu yake zuwa ya raba masu makudan kudaɗe, hakan yasa ya sakarwa Aseef ma kuɗi dan su yi ta sadaka ta ko'ina, saboda ya san duk girma bala'i da masifa da bawa yake a ciki, sadaka tana ruguje sharrin ta kawo Alkhari, wannan faɗar Allah ne, ƴan uwana mu lizimci yin sadaka ko yaya take, bata kaɗan ba ta yawa, abin da kake renawa wlh wani kuma ita ce abu mafi girma a rayuwarsa.

Lion ya fahimci kafin su fitar da Aseef daga cikin wannan bala'i sai sun tashi tsaye sosai, idan ba haka ba suna ji suna gani za su rasa ɗan uwansu lokaci guda, hakan yasa Lion yake cikin matsananciyar damuwa a kwanan nan, kwata kwata baya cikin kwanciyar hankali, kawai dai ba'a iya gane mashi ne shiyasa ba wanda ya san yana cikin damuwa.

G.M.A. sun gane ana ƙoƙarin cire Areef daga tarkon da suka sanya shi, shiyasa suke takura mashi kwanan nan, suna azabtar da bawan Allah nan fiye da tunanin mai tunani, kuma kada ku manta duk abin da Areef zai ji a jikinsa su ma TRIPLETS za su ji a jikinsu, yana ɗaya daga cikin abin da yasa Lion ya kara shiga tashin hankali, domin yasan Areef ya fi su shiga cikin wannan azaba da suke ji a jikin nasu.

A yau shugaban G.M.A gaba ɗaya ne da kansa ya zo jikin Areef yana azabtar da shi, shiyasa yau ya fi shiga bala'i fiye da kullun, kuma ogan nasu kun san ya fi sauran haɗari, abin da ya sa kuma ya shiga jikin Areef ɗin yau da kansa, dan saboda ya ga sauran idan suka shiga jikin na Areef da Lion ya zo kusa da Areef ɗin za su gudu saboda perfume nasa, to shine yau shi ogan ya zo da kansa dan ya samu ya azabtar da Areef yadda ya kamata.

Imran ya tsorata ji ya yi kamar kada su karisa cikin ɗakin, amma kuma sai ya daure suka karisa kusa da gadon.

Jin sallamarsu ya sanya Areef ɗago kansa tare da waro idanunsa da suka kara girma yanzu, dama ga su da halittar manya manyan idanu abin sai ya zama abin tsoro.

Yana ɗago idanu kai tsaye sai kan Rimsha, wani irin zirrrrr ya ji a jikinsa, cikin sauri ya miƙe zaune yana kare mata kallo, wani irin karfin bala'i ya ji ta zo mashi lokaci guda kamar wani doki.

A zafafe ya damki wuyarta da karfi ya shaƙeta, nan take kuma idanuwansa dukka suka sauya launi daga ask color izuwa jawur kamar jini, fuskar nan tasa har wani ja ta yi, kumatunsa har kerma yake yi, ba shi da wata burin da ta wuce ya ga ya zuƙe mata jini tas.

Da sauri Imran ya yi kansa yana ambato sunansa tare da fara yunkurin kwaceta daga hannunsa.

Yana daga zaunen da hannu ɗaya ya yi wurgi da Imran ɗin gefe guda, ita kuma tuni ta fara fita a hayyacinta, idanuwanta duk sun yi jawur sun firfito waje, ga shi gidan babu kowa, soja ɗaya ne kawai ya rage wadda yake a bakin gate, Lion ya fita tare da ɗayan sojan.

A yadda Areef yake yanzu ko sojoji goma basu isa su danne shi ba bare kuma soja ɗaya, mai kwatar Rimsha a hannunsa sai Allah sai kuma Lion.

Ba ƙaramin buguwa Imran ya yi ba, da karfi ya matse idanunsa saboda azabar da ya ji, amma da ya ga Rimsha tana ƙoƙarin mutuwa sai ya sake miƙewa ya nufi Areef ɗin, da iya karfinsa ya sanya hannunsa a kan na Areef dake a wuyarta yana ƙoƙarin ɓanɓaro hannun nasa.

Da karfi Areef ya shaƙo shi da hannunsa ɗaya ya sake wurgi da shi ta baki kofa, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion cikin ɗakin, domin karfe 5 ta cika ya dawo bawa Areef ɗin magani.

Sake miƙewa Imran ya yi bai lura da Lion ɗin ba ya sake nufar Areef ɗin, har kasa ya duƙa yana mashi magiya akan ya sake dan Allah kada ya kashe ta wlh bata da kowa, sake riƙo shi Areef ya yi ya haɗa kansu da Rimsha ya buga da karfi, wani irin azababben ihu Imran ya saki ita kuma Rimsha diff kake ji kamar babu rai a jikinta, kai daga ganin wanann karfi kasan ba iya Areef shi kaɗai bane.

Da karfi ya sake hankaɗe Imran ɗin, yana ƙoƙarin zubewa kasa da sauri Lion ya tare shi ya faɗa saman faffaɗar kirjinsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗauki Imran ɗin cak ya kwantar da shi a saman carpet dake a gaban bed ɗin na Areef.

Yau da yake ogan G.M.A da kansa ne sai bai gudu ba dan Lion ya zo, yana jin azaba saboda kamshin perfume ɗin na Lion ɗin, amma saboda taurin kai ya dage sai ya sha jinin Rimsha ya ki guduwa, Imran kuwa sai numfashin sama sama yake yi, amma dai ya ji mugun daɗi da Lion ya dawo, kuma ya sami kwarin gwiwa akan koma yaya Lion ba zai bari Areef ya kashe Rimsha ba, ko dan addinin Musulunci zai taimaketa.

Gently Lion ya tako zuwa gaban gadon, hannu ɗaya ya sanya da nufin ya ciri hannun Areef daga shakar da ya yi wa wuyarta, amma Areef ya ki sakinta, sai ma kara matse ta da ya yi, ɗan ciza laɓɓansa ya yi kafin ya murɗe hannun Areef ɗin da ɗan karfi, nan take ya saki wuyar tata, yana numfashin kamar nishi.

Tana ƙoƙarin zubewa kasa Lion ya riƙota da hannu ɗaya dan idan ta faɗi kasa akwai matsala, tana faɗuwa za su zuƙe mata jini kaf. Ɗaga ta ya yi da hannu ɗaya ya ɗaurata a saman kafaɗarsa, ya juya da niyar ya nufi waje da ita.

A zafafe Areef ya diro kasa daga saman gadon tamkar ba shi ne mara lafiyar da aka yi wa aiki ba, Allah sarki ba shi bane, kun san dama G.M.A a cike suke da bakin cikin dan Lion yana shiga masu hanci da kudundune, to yau suna ganin sun sami damar da za su ɗauki fansa akan Lion ɗin tun da ga shi ya zo, shiyasa gabaɗayansu suka zo suka taru a jikin Areef ɗin suka kara mashi karfi kamar kosasshen doki.

Ganin haka yasa Lion ba tare da ya yi magana ba ya yi wa Imran alama da hannu akan ya miƙe ya karɓe ta su fita, da sauri Imran ya miƙe ya zo ya karɓeta suka fita.

A zafafe Lion ya juyo suna fuskantar juna da Areef, daga kasa ya fara kallon Areef ɗin zuwa sama, G.M.A sun kara mashi girma kamar ba shi ba.

Lumshe dara daran blue eyes nasa ya yi kafin ya juya da nufin ya bar ɗakin domin tausayin ɗan uwan nasa yake yi, yana jin kamar ba zai iya dukan Areef ɗin ba saboda yau jikinsa a mace yake.

Yana juyawa Areef ya nufo yi gadan gadan, yana ƙoƙarin shaƙo shi ta baya, a sukwane Lion ya duƙa kasa tare da juyowa ya kai mashi wani irin duka a gefen kirjinsa wadda ta sanya shi yin baya.

Wani irin kukan damusa Areef ya yi alamar dukan ta yi mashi zafi. Da iya karfinsa ya nufi Lion, sai wani irin abu yake yi kamar horo.

Zuba mashi ido Lion ya yi sai da ya iso ya ɗaga hannu yana ƙoƙarin kaiwa Lion ɗin shaƙa a wuya, wani irin damƙa Lion ya yi mashi tare da ɗaga shi sama ya yi wurgi da shi a saman gadon, bai barshi ya miƙe ba ya sanya hannunsa ya shaƙesa da karfi tare da zaro mashi wayan nan dara daran blue ɗin nasa sannan ya daka mashi wata irin mahaukaciyar tsawa mai rikita ƙwaƙwalwa, nan take Areef ya natsu sit kamar babu shi a ɗakin.

A hankali Lion ya zame hannunsa daga riƙon da ya yi mashi a wuyar tasa, yana mai jin zafi a zuciyarsa, a zahirin gaskiya Lion ya fi Areef jin ciwo da kuma ɗacin halin da yake a ciki.

Juyawa Areef ɗin baya ya yi yana mai watsa dark black curly hair sa, shi kuma Areef wani irin numfashi yake fitarwa tamkar gurnanin zaki, daga ji kunsan ba lafiya ba, bawan Allah.......... Nima haka na ajiye alkalamina sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai mu.

💖💖TRIPLETS💖💖




E87-88💖


Juyawa Areef ɗin baya ya yi yana mai watsa dark black curly hair sa, shi kuma Areef wani irin numfashi yake fitarwa tamkar gurnanin zaki, daga ji kunsan ba lafiya ba, bawan Allah.

Lion ya ɗan jima a haka kafin ya juyo tare da zama a gefen ɗan uwan nasa ya fara tofa mashi addua'o'i yana shafa mashi,. Wannan abin da ya faru ba karamin ɓatawa Lion rai suka yi ba, yau da ido huɗu ya yi da su to wlh sai dai wasu ba dai su ba, yanzu idan ya ce zai dake su a jikin Areef ba za su taɓa tsayawa ba, sai dai ma ya daki Areef a banza, domin kuwa da zarar sun ga zai dake su to wlh gudu za su yi su barshe ya yi ta jibgan Areef ɗin a banza, shiyasa bai wani saki jiki wajen dukan Areef ɗin ba.

Ya jima yana yi mashi addu'a har barci ta ɗauke shi, sannan ne ya miƙe tare da gyara mashi kwanciya ya jawo bargo ya rufe shi zuwa kirjinsa tare da kara gudun Ac dake a ɗakin sannan ya nufi waje yana mai jin sauƙi a jikinsa, alamar sun rabu da Areef ɗin kenan.

Yana fita bedroom nasa ya wuce kai tsaya, toilet ya shiga, wanka ya yi tare da shiryawa cikin pajama launin white color, ya yi kyau sosai, sai dai kuma kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane tabbas bashi da lafiya saboda rama da ya yi, amma ba zaka taɓa gane cewa yana cikin damuwa ko yau ransa a ɓace ba, domin kullun a haka fuska take a ɗaure.

Saman bed nasa ya hau ya kwanta yayin da manyan malamai suke ta fama yi masu saukar Al Qur'ani mai girma, a daidai lokacin ne kuma Aseef ya kira shi a waya, kuma video call.

Bawan Allah har wani nauyayyar ajiyar zuciya ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login