Showing 78001 words to 81000 words out of 355604 words

Chapter 27 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2836

ya sa ya fara kishinta.

"Nawid na san ba iya wannan ne abin dake damunka ba, ka faɗa mini gaskiya me kake ɓoye min" Ummi ce ta sake jefo masa tambaya tana tsare shi da ido.

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, sannan ya fara magana "E Ummi ba shikaɗai ke damu na ba, akwai wani matsala dake cin min tuwo a kwarya, ke mahaifiya tace, bani da kamar ki, ba zan iya ɓoye miki komai ba"

Cikin sauri ta ce "Menene wannan kuma? ina jinka faɗa mini"

Juyowa ya yi suna fuskantar juna sosai, ya riƙo hannayenta cike da kaunar ta ya fara magana

"Ummi ki yi hakuri da abin da zan faɗa, amma ya zama dole na gaya miƙi, wata kila ke kina da hanyar iya maganin abin" tsare shi da ido kawai ta yi tana kallon sa, tana jiran ta ji me zai faɗa.

"Ummi ina zargin Abbo kamar yana da wata manufa a han baby" zaro ido sosai Ummi ta yi, har haɗe words ta ke wajen cewa "Wani irin manufa kuma Nawid?".

"Ummi yanzu idan a ka ce miki Abbo yana son baby ya za ki yi?" Dariya sosai Ummi ta yi, kafin ta ce "Nawid har yanzu kai yarone" "Yaro kuma Ummi?"

Gyaɗa masa kai ta yi, tana faɗin "E mana Nawid banda kai yaro ne tayaya Abbonka zai so baby? To ma idan ya sota ya yi yaya da ita? Kada fa ka manta Abbonka matansa huɗu, bayan gidan nan akwai nasu Zainab ka sani, ina hakan ma ba zai yiwu ba".

Shiru Nawid ya ɗan yi kafin ya ce "Amma Ummi ai abin da Abbo yake a kan babay ne abin ya yi wa sosai". Miƙewa tsaye ta yi tana faɗin "A'a ba wani yawa, kawai ɗoukin soyayyar yaya mata ne ke ɗibarsa, kada ka manta bamu da ƴa mace fa, kawai kaunar ta ya ke yi, dan haka ka dai na kawo tunani mara kyau a zuciyar ka, ka yi mana fatan alkhari kawai" ta kai karshen maganar tare da nufar ɗakinta tana faɗin ina babyn ma take, tazo na shiryata mai kunshi zata zo ta yi mata.

Shidai Nawid ya kasa magana tunani yake a zuciyar sa "Lallai Ummi kin yi nisa, yanzu in banda ke da abin ki, Abbo yana da mata huɗu, ƴaƴan sa mata sun kai shida dukka bai yi ɗouki a kansu ba sai kan baby tsintaciyar mage, anya Ummi ba amiki wani abin ba kuwa?". Sai zan cen zuci yake yi bawan Allah, abin ma yaso ya wuce tunaninsa.

(Nan na barosu na haɗa kaya na zuwa, wajen Jehan)


💗💗Super restaurant💗💗

Sai karfe 6 na yamma Jehan ta baro restaurant, sai sauri take ta nufi bakin titi dan tarar abin hawa zuwa asibiti, daga bayanta ta ji murya ana faɗin "Sannunki yan mata" kin juyawa ta yi, ta ci gaba da tafiyarta kawai, dan ba komai take kulawa ba.

Cikin sauri ya sha gaban ta, matashine wadda ba zai fi shekara 23 ba. Kallon sama da kasa ta masa, kafin a wulakance ta ce "Lafiya ka tare min hanya?"

Yar murmushi ya yi tare da fito da wayarsa kirar Tecno camon 11 yana faɗin "Wlh yan mata kin yi mini ne, idan ba damuwa ki zuba mini shaɗatar ki a nan" ya yi maganar yana miƙo mata wayarsa.

Tsabar bakin ciki ta ɗan jima kafin ta ce "Sai ka rasa uban waye yake koyawa yaran nan wasu abubuwan, zaka wuce ka je ka yi firsari ka je ka kwanta dare ya yi ne ko sai na ɗauki bulala na zane maka jiki? Yara kanana sai wani iya shege, yanzu ni ce zan baka number ta, lallai yaron nan" Da turanci ta yi maganar.

Kasan cewar yana jin turanci hakan yasa ya gane me take nufi, ya sha ruwan mamaki, cikin sauri ya fara bin jikinsa da kallo, ya tsurawa gaban sa ido yana son gane me Jehan ta gani ta ce masa yaro.

Wucewa ta yi abinta, ta bar shi a nan tsaye yana yan dube dube a jikinsa.

Mashin mai taya biyu ta tara ta hau zuwa asibiti, kamar kullun yauma ta sayowa su gwaggo abinci a restaurant nasu, dama kullun idan zata dawo zata sai takeaway guda uku, Sadiq ɗaya, gwaggo ɗaya, sai maman Sadiq ɗaya, ita bata wani damu da cin abincin dare sosai ba, Sadiq yana sayo mata maltina ta sha ta yi barci abinta.

Kamar kullun tana isa asibiti Sadiq yana isowa, a tare suka jera zuwa cikin asibitin, sai murna Jehan take, an ce gobe mum zata farfaɗo.

Allah sarki gwaggo ta rame sosai kamar ba ita ba, kusa da ita Jehan ta zauna, tana kallon fuskar mum ɗinta.

Mum kamar ba mai jinya ba ta yi ƙiba sosai, saboda karin ruwa da jini da aka mata.

Gaishe da gwaggo Jehan da Sadiq suka yi, sannan suka tambayi jikin mum, da fara'a gwaggo ta amsa, Jehan zata sake yin magana wata hamshakiyar Hajiya wadda da ka ganta kasan nera ta zauna mata, tasha kwalliya da sarkan gold, ta zuba abin hannu shima na gold, ga wani dankareren lace da ta sanya a jikinta abin ba'a cewa koma.

Kariso wajen na su ta yi, tana faɗin "Hajiya Aisha wayan nan kuma su waye ne?" Ta yi maganar tana nuna Jehan da Sadiq, Nan gwaggo ta gaya mata ƴaƴan ta ne. Murmushi Haniyar ta yi tana faɗin "Kai amma suna da kyau sosai wlh" shiru gwaggo ta yi bata sake magana ba, su Jehan da Sadiq ba wanda ta tanka matar a cikin su, shi Sadiq dama ɗan abi yarima ne a sha kiɗa, duk abin da Jehan ta yi, shi yake yi shima, to da ya ga Jehan bata kulla matar ba, shine shima ya ki kulata.

Cikin gwababɓen fulatanci Jehan ta tambayi gwaggo wace ce wannan Hajiya, nan gwaggo ta gaya mata, kanwar Hajiyar ce a ka kwantar a ɗakin kusa da su tana jinya, yau Hajiyar tazo daga Abuja duba jikin kanwar tata.

Shiru Jehan ta yi bata sake cewa komai ba, gaba ɗayan su shiru suka yi kowa da abin da yake tunani

Yau sun jima sosai a asibiti, sai wajen karfe 10:20 sannan suka sallami gwaggo Jehan ta bata abincin ta suka wuce zuwa gida, sun bar gwaggo tare da wannan Hajiya suna hira.

Yau kasan cewar sun yi dare ko da suka fita bakin titi basu sami abin hawa ba, hakan yasa suka fara ta fiya da kafa, suna yi suna hira, har suka ci karfin tafiyar ba tare da sun sani ba.

Basu ankaraba sai sukaga har sun kusa isowa anguwarsu, hakan yasa suka ce bari su karisa da kafa kawai.

Sun ci gaba da tafiya suna hira, sun zo daidai hanyar da zata shigo da su anguwarsu wasu jibga-jibgan mutane masu bakin kaya da kuma bakin marks a fuskar su, suka tare su.

Daga Jehan har Sadiq sai da suka kusa sakin fitsari a wandon su, nan take jikinsu ya fara kerma, ga shi wayan nan mutane za su kai su goma, ga shi baka iya gane ko ala'mar kamannin su, saboda dare ne sosai akwai duhu, kuma koda ma ba dare bane, sun rufe ko'ina a cikin su, ba zaka gane su wanene bane.

Ɗaya daga cikin su ne ya matso kusa da Jehan ya fara magana kasa kasa "Ke ina wayar da kika yi recorded na oga Farooq? Ki bamu wayar ko kuma mu kasheki a nan, kuma mun kashe banza" Wani wahalallen yawu ta haɗiye, nan take zufa ya fara karyo mata, ina amafanin karyar da ta yi, ta tambayi kanta.

Tana kokarin yin magana, suka ji jiniyar motar yan sanda sun zo wucewa, a guje wayan nan mutane suka bar wajen, ita kuma Jehan da sauri ta juya ta nufi hanyar komawa asibiti, tana sauri tana tunani a ranta ta ja wa kanta bala'i, a tunanin ta komai ya wuce, ta tseratar da Hanan, sai ga shi ita kuma ta jefa kanta cikin bala'i.

Da sauri Sadiq ya bi bayanta, har suna haɗawa da gudu, Sadiq ya ce "Jehan me kuma zai mai damu asibiti? Tun da sun tafi mu wuce gida mana" girgiza kai ta yi tana faɗin "A'a Sadiq ba zancen komawa gida, tun da ka ga sun tare mu a nan to tabbas sun san gidan mune, Farooq ya gaya musu in da gidan mu yake, shi ya sa suka zo suka tsaya a bakin unguwar mu, yanzu dole asibiti zamu koma, zan je in sanar da su gwaggo meke faruwa" tana magana tana kwaɓawa da turanci.

Haka suka sake takawa da kafa har zuwa asibiti, dan ba abin hawa, kasan cewar kauye ne da wuri suke shiga.

Yadda suka bar gwaggo da Hajiya haka suka dawo suka same su, cike da tashin hankali Jehan ta sanar da gwaggo abin da ta aikata, na karyar da ta yi wa Farooq na tayi recorded na muryan sa yana yiwa Hanan maganganun banza, ga kuma abin da karyan ta zamar mata.

Sosai gwaggo ta shiga tashin hankali ta kuma yi mata faɗa sosai, a kan ba yanzu ba ko gaba ta guji yi wa mutun karyar abin da ta san bata aikata ba, ga shi yanzu ta ja musu bala'i.

Sun shiga tashin hankali sun rasa mafita, idan suka ce Jehan ta koma gida, to tabbas wayan nan mutane za su iya bin dare su mata yankar rago, domin Farooq ba shi da mutunci ko kaɗan, zamanta a asabiti kuma ba zai yi wu ba, hakan ya sa suka fara neman mafita ta hanyar shawara.

A nan ne wanann Hajiya ta ce musu idan ba damuwa zata tafi da Jehan zuwa gidan ta, daga nan zata sama mata aiki a gidan masu kuɗi, ko wani wata za'a rinƙa biyan ta dubu ɗari, idan anyi mata salary Hajiyar zata rinƙa turowa su gwaggo.

Babu tunani babu komai gwaggo ta miƙawa Hajiyar nan Jehan domin ita burinta kawai Jehan ta tsira da ranta, bata son wani abin ya sameta, rubuta musu number wayarta Hajiyar ta yi tare da address ɗinta na Abuja da kuma gidan iyayenta dake nan Katsina. Gwaggo ce ta karɓa takardar sannan suka yi wa Haniyar godiya, gwaggo ta ce Sadiq ya koma gida da safe Hajiya zata wuce da Jehan Abuja, kwata-kwata sun manta da zancen aikin Jehan, sun kuma mance da Ibraheem na bin su bashin kuɗi.

(Toh fah, haka za ku yi wa Ibraheem, shi yana can yana kokarin yadda zai lallaɓa Jehan ta samu ta yi aiki ta biya shi hakkinsa, lallai akwai cakwakiya)

Haka Sadiq cike da tsoro ya koma gida yana ta tunanin Jehan, ya yi sa'a daya bi hanyar mutanen basa nan, sun gudu, saboda yan sanda dake zagaye a wajen dan maka yan shaye-shaye, ita kuma Jehan a asibiti ta kwana a kan gobe za su wuce Abuja da Hajiya ta kai ta gidan aiki. Sai dai bata ji daɗin rabuwa da su gwaggo ba, amma bata da mafita dole ta bi Hajiya.

To bari dai mu leƙo Washington DC mu dawo

💓💓Washington DC💓💓


Zaune suke gaba ɗayan su a palon kasa, ban da Lion da kuma James da baya nan, sai uncle herry dake asibiti shima baya nan, Jay ma yana wajen punishment nasa, dan yau tun safe ya dasa daga in da ya tsaya.

Dukkansu kowa za abin da yake yi, Tga da John sun kafa kai a kan wayoyinsu suna latsawa, shi kuma daddy yana kallon News a makeken Tv su, while shi kuma Michael yana buga game a system. Dukkan su kayan shan iska ne a jikin su, barim ma Tga shi ko riga ma bai saka ba, daga shi sai gajeren wando, ya bar wayan nan dama daman damtsen hannun nasa a wajen, ga sarkan kros daya sanya a wuyarsa, sai sharholiyar su suke banda Jay.

Cikin nitsuwa Musharraf ya sauƙo daga sama izuwa cikin palon. Sannu ya musu sannan ya wuce zai zauna saman sofa.

Dukkan su ba wanda ya amsa sannun na shi. Tsawa Tga ya daga masa wadda ya sanya gaba ɗayansu ɗagowa "What brought you here?!!"

Kallon Musharraf Michael ya yi sanna ya dawo da kallon sa kan Tga da yake ta wani cika yana batsewa, Allah Sarki Musharraf har jikin sa ya fara kerma, kasa zama ya yi saman sofar, ya tsaya yana kallon su.

A fusace Tga ya ce "Ba da kai nake magana bane?!" Shiru Musharraf ya yi dan ba shi da amsar da zai ba su, miƙewa Tga ya yi yana wani huci ya ɗaga hannu zai mare shi, cikin sauri Michael ya miƙe ya riƙe hannun nasa yana faɗin "No uncle me ya maka?" Kwace hannunsa Tga ya yi ya nuna Musharraf yana faɗin "Kada na sake ganin kafarka a palon nan, a word room zaka rinƙa zama".

Jikin sa har kerma yake yi ya wuce zai koma sama, Michael ya ce "Come back uncle" tsayawa Musharraf ya yi ba tare da ya juyo ya dawo ba.

Karisawa wajensa Michael ya yi yana faɗin "Uncle T wannan fa uncle ɗin James ne, kuma duk abin da James yake so nima ina son shi, dan haka ya zama dole uncle ɗin James ya rinƙa zama a duk in da yake so a gidan nan, duk in da James zai iya shiga a cikin gidan nan, nima zan shiga kuma shima uncle ɗin James zai shiga, ba kuma wanda ya isa ya hana shi, saboda James" Tga zai yi magana sai ya tuna Akwai camera a palon yanzu haka Lion na kallonsu, kuma sun san shi Lion idan ya fito bayan Triplets nasa yake bi, koda kuwa basu da gaskiya, sanin hakan yasa ya yi shiru bai ce da Michael komai ba, amma ya kudiri niyar azabtar da Musharraf ta kowani hanya, sai ya bashi wahalar da sai ya gwammaci mutuwa, dan shi baya son ganin wani a cikin gidansu, ga shi kuma Musharraf ya sanya hanun zama da su na tsawon shekaru huɗu, sanan babban abin haushi shine James da Michael suna son shi, idan kuma suna son shi tofa shima Lion zai so shi.

(Toh fa Tga a hakan ma bai san Musharraf Musulmi bane, idan ya sani kuma sai yaya?🤔)

Riƙo hannun Musharraf Michael ya yi suka koma saman sofar da yake zaune, suka zauna, cike da nuna kulawa ya ce "Uncle ɗin James ka san yadda ake buga game? Ka iya?" Gyaɗa masa kai Musharraf ya yi yana faɗin "E na iya sosai dan muna bugawa a gida"

A zahirin gaskiya Musharraf bai iya buga Game ba kawai saboda ya lura da cewa Michael yana son su buga tare ne yasa ya ce ya iya, dan ya sanya Michael farinciki.

Miƙa masa part ɗaya Michael ya yi yana faɗin "To karɓa mu buga, amma dama kuna da gida ne?" Nan ma gyaɗa masa kai Musharraf ya yi yana faɗin "E muna da shi" kara musu power game ɗin Michael ya yi sannan ya ce "Kuna da gida kuma kazo zaka zauna a nan? Ko da yake ra'ayin kane, yanzu dai nine mai mutane masu bakin kaya kai kuma blue za mu ga waye zai yi winning" to kawai Musharraf ya ce masa sannan suka fara buga game ɗin.

Tun daga farkon farawar su Michael ya fara tikar dariya, dan ba abin da Musharraf ya iya.

Zuba musu ido daddy ya yi yana kallonsu da mamaki, shi kuwa Tga ji yake kamar ya shake Musharraf ya kashe shi, John kuwa ɗan ba ruwana, ko a jikin sa, shi ko kashe kansu za su yi ma can ta matse musu.

LION

Zaune yake saman bed nasa, ya zubawa system dake gabansa ido yana bincike sosai a kan James, dan yanzu ya kara tsananta binciken nasa, dan ya samo wani information akan James ya bar kasar Spain last week ta jirgin ruwa ya nufi cikin London.

Makeken Tv dake manne a bango cikin bedroom ɗin nasa ne ta fara ɗauko masa hayaniyar su Tga a palo lokacin da Tga ke cewa Musharraf ya bar palon, shiru ya yi na ɗan lokacin kafin ya dakata da aikin da yake y, sannan ya kashe system ɗin dan ya samu abin da yake nema, juyowa ya yi ya zubawa Tv ido.

Wani sanyi ya ji har cikin ransa lokacin da yaga yadda Michael ke dariya saboda Musharraf, tun da suka taso suka girma suka yi wayo james ne kawai mai ɗan murmushi a cikin su, kwata-kwata Michael bai taɓa dariya ba, shi kam Lion dama ai ba'a magana kowa yasan magana ma ba wani yin ta yake yi ba bare wani abu wai murmushi.

Sosai ya ji daɗi, yau Musharraf ya saka Tiger dariya, zubawa Michael wayan nan dara-daran blue eyes ɗin nasa kawai ya yi yana kallon su, shi kuma Michael sai tikar dariya yake yi saboda yana winning na Musharraf.

Da zarar ya ci kwallo ɗaya sai ya kwashe da dariya yana faɗin "Uncle ɗin James na fika iya wa" Allah sarki Michael ɗan ba ruwa na, kowa nashi ne matikar Triplets nasa na son mutum, ba shi da wata matsala.

Ba Lion ne kaɗai ya yi farincikin ganin dariyar Michael ba, har da daddy da John, hakan yasa suka matso dan su karawa abin armashi saboda kada Michael ya dai na dariya, dan ya yi kyau sosai, shi kuma Tga bakin ciki ne yasa ya miƙe ya bar palon.

Da zarar Michael ya ci kwallo ɗaya sai John da daddy su tafa hannu suna faɗin "Tiger ya yi winning" hakan ba karamin daɗi yake sanya Michael ya ji ba, sai kara bada himma yake yi dan ya yi ta cinye Musharraf, shi kan shi Musharraf ya ji daɗin yadda Michael yake farinciki, ko dan saboda halakcin da James ya masa ya zama dole ya rinƙa sanya Michael farinciki.

Da wasa ta yi wasa Michael ya ga ya ci har kwallo 10 Musharraf bai ci ko ɗaya ba, har da juyowa ya yi ya mannawa Musharraf kiss a kumatu yana faɗin "Uncle ɗin James kullun da kai zan rinƙa buga game saboda in rinƙa yin winning ɗin ka" wani farinciki Musharraf ya ji, sai dariya suke gaba dayan su palon, shi kuma Lion ya zubawa Tv ido yana kallon Michael.

(Ni kuma haɗa kaya na nayi na bar gidan sai mun haɗe da ku gobe idan mai dukka ya kai mu)

💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 25-26🌹



Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login