Showing 240001 words to 243000 words out of 355604 words
saki tare da faɗa wa jikinsa tana faɗin "Ya Allah ka ɗauki raina na huta". Buge mata baki Imran ɗin ya yi tare da faɗin "Muje kada mu ɓatawa Saif lokacin, yanzu ma ba dan ya ga hawayena ya zuba ba, da ba zai yarda mu zo mu ɗauke ki ba, da kyar ya yarda, dan ma dai Akila ta kirani agabansa ne, kuma ya ji duk abin da ya faru, Allah ya rufa asiri kuma muna kusa, mun je sayawa James wasu magunguna, ba dan haka ba ai da kin ɓace Mani, yanzu dai muje, idan muka isa gida za mu yi magana, kada mu ja ya ce ba zaki zauna mashi a gida ba, da kyar da ma ya yarda, sai da na sha kuka ina gaya mashi baki da kowa, ke marainiya ce, idan na barki zaki iya faɗa wa mugun hannu har a lallata maki rayuwa, shi kuma baya son zina shiyasa ma ya yarda". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka nufi motar.
Tun basu kariso wajen motar ba Kamshin perfume nasa ya daki hancinta, har wani lumshe sleeping eyes nata ta yi tare da sake buɗe su a hankali.
Abin mamaki a maimakon Imran ya shigar da ita gidan baya dan tana tunanin Lion ɗin a gaba yake, sai ta ga ya buɗe mata gidan gaba, Lion yana baya, a cikin zuciyarta ta ce ashe ko a ina yake wannan sarauta dai tana nan, yanzu duk yadda suke da Imran ba zai iya zama a front seat kamar friend ba, sai dai ya zauna a baya Imran ya zama driver sa, tab lallai wannan akwai izza da isa wai, tunani cike fal ranta ta shiga gidan gaban Imran ya rufe kofar, ya zagayo ya shiga mazaunin driver ya tada motar.
Muryarta na kerma ta ce mashi "ina wuni GAR" dan sunan da ta san shi da shi kenan
Bayan Kamshin perfume nasa da zaka ji wadda zai tabbatar maka da ya cikin motar, to ba wani abin da zaka ji na daga motsi, kamar bai san da shigowarta ba bare kuma har ta sa ran zai amsa mata, shi da bai ma jin Hausa, yana zaune ya kwantar da kansa saman kujerar motar tare da lumshe idanuwansa kamar mai tunani. Black face mask ne a face nasa tare da puffer jacket ajikinsa, daga ta ciki kuma wata kyakkyawar tsadaddiyar Round neck t-shirt ne launin Ash color, wandon jeans para tas ce daga ta kasa.
Kasa kasa Imran ya ce mata ko da sunan wasa kada ta sake yin gigin yunkurin yi mashi magana, idan ba haka ba, zai iya sumar da ita ko kuma ya ce baya son ganinta dole ta bar gidan, to ta amsa da shi tana sauke ajiyar zuciya, da yake darene bata sami damar ganin koda kayan dake jikinsa ba bare fuskarsa. Ahaka suka nufi wani ƙaton pharmacy dake ɗan gaba da gidansu Imran ɗin, pharmacy ne mai girma sosai.
💖💖TRIPLETS💖💖
E 64
Kasa kasa Imran ya ce mata ko da sunan wasa kada ta sake yin gigin yunkurin yi mashi magana, idan ba haka ba, zai iya sumar da ita ko kuma ya ce baya son ganinta dole ta bar gidan, to ta amsa da shi tana sauke ajiyar zuciya, da yake darene bata sami damar ganin koda kayan dake jikinsa ba bare fuskarsa. Ahaka suka nufi wani ƙaton pharmacy dake ɗan gaba da gidansu Imran ɗin, pharmacy ne mai girma sosai.
A parking space nasu Imran ya yi parking, tun bai gama kashe motar ba Lion ya fice abinsa, domin sauri yake yi, zuba mashi ido Rimsha ta yi tana kallon yadda yake tafiya, da yake akwai haske sosai a wajen, daga ta cikin zuciyarta kuma, mamaki take tana faɗin, "Ashe dai haka tafiyarsa yake cike da izza da isa, wadda duk wanda ya ganshi dole ya matsa ya bashi hanya, dan bai ga irin takun yara ba, ashe dai ba a iya Tv yake irin wannan tafiya ba, haka tafiyar take".
Taɓa ta Imran ya yi yana faɗin "Rimsha ki natsu, duk yadda kike tunanin Saif ya wuci nan, dan haka ki kama kanki, ko da sunan wasa na gaya maki kada ki kuskura kiyi gigin yi mashi magana, kada ki bari hanya ta rinƙa haɗa ku, dan wlh tsab zai iya take ki, ya yi ball dake na dai gaya maki, yanzu dai bari na je na biya kuɗin maganin dan shi bashi da kuɗin Nigeria, shiyasa ya zuba mani kuɗi sosai a account na tun kafin ya zo, dan ba ya son wani abin haushi na canza kuɗi ko makamancin hakan, ki jiramu muna dawowa yanzu". To ta bishi da shi, cikin sauri ya fita daga cikin motar.
Yana fita wayar Lion dake a saman kujerar baya, in da ya zauna kenan, a nan ya barta, fara ringing wayar ta yi, juyowa Rimsha ta yi yana kallon wayar dan ya kawo hasken screen ɗin yana ta faman kirar number mai kira, haka kawai ta tsinci kanta da sanya hannu zata ɗauki wayar dan ta gani, ita da aka ce mata ko hanya kada ta bari ya haɗa su, amma tana neman kirawa kanta ruwa, domin kuwa koya ta taɓa wayar idan ya zo zai san ta taɓa shi.
(Ina iyeyen Rimsha? sai ku ja mata kunne, idan ba haka ba, da alama za'a mata bugu ɗaya ba tashi)
Bata kai ga ɗauka ba kiran ya katse, nan take hotonsu su uku ya bayyana a saman kyakkyawar fuskar wayar, dukkansu fuskar nan a ɗaure tamau, saboda tsabar rashin ji irin nata har da sako kanta dan ta kare masu kallo, kamar bata da hoton su su ukun a wayarta, da yake dai wannan na kan screen ɗin nasa, fuskokinsu ya fito sosai a cikin hoton, kansu a haɗe, hakan yasa yafi kyau, shiyasa ma ya sanya a gaban screen na wayarsa.
Hannu ta kai bari ta ɗauki wayar ta kare masu kallo, sai ji tayi aka ƙoƙarin buɗe kofar motar, har ga Allah bata ga alamar dawowarsa ba, a sukawane ta mayar da kanta tare da runtse ido tana karanto duk addu'ar da ta zo bakinta, dan neman tsari daga wajen Ubangiji, Allah yasa kada ya yi tunanin wani abin ya ce zai mata hukunci, da ta shiga uku da lalace kuwa, bugu ɗaya ba zata sake moruwa ba.
Zama ya shigo ya yi a in da ya tashi, dama abin da ya sanya ma ya fita, saboda Imran ba zai gane irin magungunan da yake so ba, kuma idan Imran ne ya je, zai ɓata mashi lokacin sosai, shiyasa kawai ya tafi da kansa, dan ko wace minti ɗaya a cikin rayuwarsa yana lissafa me zai yi da ita, baya asarar lokacinsa abanza, baya wasa da time, shiayasa idan ka ɓata mashi lokaci koda minti ɗaya ne sai ya maka hukunci ba kaɗan ba.
Kamar yadda ya zauna ɗazun haka yanzu ma ya zauna, tare da lumshe idanuwansa, ita kuwa sai shakar kamshin perfume nasa take yi tana lumshe idanu, tana kara jin wani balaƴaƴƴen azababben kaunarsa na kara ratsa dukkannin ilahirin jikinta. TO FA KINA DA AIKI GASKIYA
A haka Imran ya dawo ya same su hannunsa na ruƙe da wata babbar leda fara tas mai tambarin pharmacy ɗin a jiki, da alama magungunan ne a cikinsa.
A gefensa ya ajiye maganin tare da kunna motar suka bar wajen, suka nufi gida.
Suna isa gida, Imran ya yi parking a parking space na gidan, da gudu sojan dake bakin gate ɗin ya kariso wajen tare da buɗe masu kofofin motar gefen Imran da gefen Lion, ganin Rimsha yasa ita ma ya buɗe mata kofar, amma ya sha ruwan mamakin ganinta tare da su, abin da bai taɓa gani ba, Lion a kusa da mace, to wacece wannan? Ya tambayi kansa, har suka shige cikin gida ba tare da ya sani ba, ya yi mutuwar tsaye a wajen.
A palon kasa Rimsha ta tsaya, Imran ya nuna mata saman sofa ya ce ta zauna, shi kuma ya bi bayan Lion zuwa ɗaki James dan ya kai mashi maganinsa.
Bayan ya kai mashi ya dawo palo ya ce su je sama, ba musu ta bi bayansa, ɗaya daga cikin ɗaku nan dake a saman Imran ya wuce da ita, dan ba zai iya barinta a kasa ba, duk da akwai mai gadi, hankalinsa ba zai kwanta ba, gara ta kasance a sama kusa da shi.
Suna shiga ɗakin ta zaro ido tana bin ɗakin da kallo, komai na cikin ɗakin kusan irin na bedroom ɗin daddy'n ta a Abuja ne, ta sha mamaki sosai.
Saman bed Imran ya ce ta zauna, bayan ta zauna sai ya zauna a gefenta, a nutse ya fara magana. "Kamar yadda na gaya maki ɗazun, ki natsu wlh ina kara jaddada maki Saif zai iya yin ball da ke idan kika bi ta hanyar wucewarsa, ki kula sosai, ba sai kin gaida shi ba idan kun haɗu, baya son hakan, sannan kuma nasan da son da kike yi mashi, amma ki daure ki danne kada ki rinƙa yawan kallonsa, idan kika bari ya gane kina kallonsa wlh nan ma mun shiga uku, tun muna school nasan baya son kallo, ga shi da shegen bala'in kyau na fitar hankali, amma ya haramtawa kowa kallon face nasa, to kema ki kula da wannan, zaki iya shiga ko'ina a cikin gidan nan, amma banda ɗakin dake na farkon nan, shine nasa, kada ki yi gigin shiga tom, idan kina son leƙawa ki bari sai in ya fita, dan time to time yana fita, to ki bari sai baya nan, na san ba zaki iya cin irin abincinsu da suke girkawa a nan ba, saboda ba na kasar mu bane, dan haka kina da damar shiga Kitchen ki girka abinda kike so babu mai hana ki, amma dai ki kula, domin gases nasu na girki da sauran kayan aikinsu ba irin na Nigeria bane, na kasar su ne, a kasar tasu ma na musamman ne, to ki kula kada ki yi ɓaran ɓarama, na yi wa Akila massage akan ta haɗa maki kayanki dukka a cikin trolley ki, Akil zai je da sassafe ya ɗauko maki dan zaki tafi school gobe, yana da kyau ki kwanta ki yi barci, da safe zamu sake tattauna duk abubuwan da suka dace, ko kuma idan kin dawo daga school, yanzu dai ki kwanta bari naje wajen shi na duba Triplets nasa, Areef bashi da lafiya, idan Allah ya kai mu da safe kema sai ki je ki duba shi".
To ta amsa mashi da shi tare da yi mashi alkawarin zata kula
anya kuwa zaki kula? Keda wayarsa ma aka kira duk wannan bala'in tsoron sa dakike amma saboda gulma da fitina wai zaki duba ki gani ba? Baki san ko tsinke ya ajiye wani ya taɓa sai ya gane ba?🤔 Gara to ki shiga hankalin ki natsu.
Miƙa wa Imran ya yi yana sanya mata albarka ya fice daga ɗakin zuwa wajen su James.
Yana ƙoƙarin shiga ɗakin James ɗin ne wayarsa ta fara kara, dubawa da zai yi sai ya ga Dr Nawid ne, fasa shigar ɗakin ya yi ya koma saman sofa ya zauna tare da yin picking na call ɗin.
Daga ɗayan ɓangaren Nawid ya ce "Hello Prof ykk" nisawa ya yi kafin ya ce "Dr ina lafiya ya su Ummi?" "Su Ummi suna lafiya, please Prof gani a cikin gida, ka ɗan yi mani iso wajen Rimsha tun da kai baka ban".
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe wannan shine chakwakiya, ɗan satar kallon kofar ɗakin James ya yi kafin ya fara magana "Sorry Dr Rimsha bata nan".
Ɗan zaro ido Nawid ya yi yana faɗin "Bata nan kuma? To ina ta je?" Shiru Imran ya ɗan yi, dan har ga Allah baya son abotar su ta sami matsala, kuma ba zai iya yi wa Rimsha dole ba, abin da yasa ya bawa Nawid ɗin ma izinin zuwa wajenta, dan bai san akwai wadda take so bane alokacin, yanzu kuma da ya sani ba zai yi gigin yin hakan ba, sannan kuma A'A SALAHUDDEEN ya kira shi jiya ya sanar da shi, Rimsha ita ce yarinyar da yake so, kuma ranar Friday gobe kenan yana nan zuwa, dukkansu abokai ne tun na yarinta, ba zai so wani abin ya sami abotarsu ba.
"Prof da wata matsala ne? Ko dai iyayen Rimsha sun bayyana ne?". Cewar Nawid. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, kan sa ta kulle, har wani jiri yake ji.
"Dr iyayen Rimsha ba su bayyana ba, kuma tana nan, amma yanzu ta dawo gidan GAR ne da zama, saboda wata yar matsala, sai dai ka zo gidan ka ku gaisa, kuma ni zan so ka bari sai da safe ne kazo domin yanzu ta yi barci......." Bai bari Imran ya kai karshen maganar ba ta dakatar da shi da cewa "Gidan GAR fa kace?! Tab ina a'a wlh, angaya maka na shirya mutuwa yanzu ne? Ai ko masu gadin gidansa banson yin ido huɗu da su, bare kuma har na shiga har cikin gidan na zauna hira da Rimsha, dama dai a waje ne za mu haɗu, in ganshi da face mask da glass kamar yadda ya saba, to zan iya rokarka ka nema mani alfarma mu yi hoto da shi, amma gidan sa fa, kai a'a to me ma ya kai Rimsha gidan?".
Jin haka yasa Imran ya ji a ransa ya sami hanyar da zai rabu da abokansa lafiya kuma ya raba su da Rimsha lafiya, dan haka sai ya ce da Nawid "Dr GAR shi ya ce akawo mashi ita, na bashi labarinta ne, sai ya ce akawota, to da ta zo gaban shi kuma sai ya ce daga yau a gidan zata zauna".
Da yake ba wanda ya san da labarin Triplets sun tsani mace saboda mum ɗin su, basu fitar da sirrin gidansu waje, ba wanda ya san cewa ba su son mum ɗin tasu, sai Nawid ya yarda akan cewa Lion ne ya ce akawota,
A razane ya ce "Prof sai da safe, ko Rimsha ita ce autar mata ta duniya gaba ɗaya, to na hakura da ita, GAR fa tab ina wlh na hakura da Rimsha, ta yi zamanta a can bari na koma na karɓi zaɓin da Ummi tayi mani, dama yau saura kwana biyar a ɗaura aure, sannan kuma dan Allah Prof ka yi ƙoƙari ko ɗaurin aure ne ka zo ka ji?" Jinjina kai Imran ya yi yana faɗin "In Sha Allah zan zo ɗaurin aure kam, tun da ba zai wuci minti 20 ba".
To Nawid ya ce sannan suka yi sallama, Miƙewa Imran ya yi yana mai jin daɗi ya rabu da Nawid lafiya, sai dai kuma ya zuba karya da sunan Lion , idan ya gane kuma fa? Kun dai san halinsa, ta yi wu ma ya sanya camera a cikin Palon, idan ya zo yana dube dube zai iya gani, dan baka gane gabansa bare bayansa.
Da sallama ɗauke a bakinsa na shiga ɗakin, daidai lokacin Areef ya gama shan magungunan sa, ba laifi jiki yana ta yin kyau yana samun sauki, duk kumburin face ɗin nan nasa ya sauƙa, amma daga ta cikin jikinsa yana jin ciwo sosai, dan ba ƙaramin wahala suka bashi ba.
Hannu ya miƙawa Imran dan su yi musabaha, da murmushi Imran ya miƙa mashi hannu yana faɗin "My Areef bawan Allah sannu da jiki".
Fuska a ɗaure tamau kamar fuakar Saif Areef ya amsa da "Prof i really Missed you wlh". Imran bai damu dan ya ga face nasa a ɗaure ba, dama ya san James ba shi da wani sakin fuska shi ma, idan kaga yana murmushi to ya yi wani babban aikin alkhari ne, amma shi ma baya da sakin fuska ko kaɗan, a baya ma da yake yi, dan saboda basajar da yake yi ne, dan dole yake murnushin.
Yar hirar an jima ba'a haɗu ba Areef da Imran suka yi, shi kuma Lion ɗakinsa ya koma ya yi wanka ya yi shirin barci ya kwanta abinsa.
Sun ɗan jima suna hira kafin su yi sallama Imran ya wuce nasa ɗakin ya yi wanka tare da shirin barci shima ya kwanta.
Shima Areef gyara kwanciyarsa ya yi dan ba halin yin wanka saboda raunikan dake a jikinsa, ba zai yi wu a zuba masu ruwaba, sai dai zuwa gobe ko jibi haka, amma yana shan wahala ba kaɗan ba, ga azaban ciwo ka kuma rashin wanka, abin ya haɗe mashi, daɗin abin dai ɗaya Lion na kula da shi sosai da sosai, kuma ya ce gobe zai iya kai shi toilet ya yi wanka.
A ɓangaren Rimsha kuwa, Imran na fita, toilet ta shiga ta yi wanka, ta fito, haka ta maida kayan da ta tuɓe ta kwanta, yau wani mugun farinciki take ji na taga masoyinta, sai wani murmushi take yi tana shafa Tula-tulan ta saboda sunansa dake a wajen, cike da nishaɗi da murmushi akan face nata barcin mai daɗi da annashuwa ya ɗebeta.
To asuba ta gari My people, bari mu leƙa masoyan nan, wato babyn daddy da kuma daddynta.
💖💖GIDAN ABBI💖💖
Yau a tare suka yi sallar mangariba da isha, bayan sun idar ne suka zauna suka yi askar tare da kara koya mata karatun Alqur'ani mai girma daga in da ta tsaya, tun da ta kawo abinci bata koma ba, Aunty kuma bata ce a kirata ba, dan ta san halin daddy tsab zai ce ina ruwanta da matarsa ba zata dawo ɗin ba, ta dawo wurin mijinta kenan, hakan yasa ta zuba masu ido kawai tana jiran dawo wanta.
Bayan sun gama karatu ne ya ce "Baby mu je shopping yanzu ko sai anjima?" Kasa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta irin yadda Rimsha keyi, mafi yawancin abin da Ayla ke yi duk a wajen Rimsha ta koya, dan Rimsha ita ce malamarta ta farko, sai dai kullun Rimsha na gaya mata, ta koyi rufe sirrinta amma bata kulawa sosai.
Hannayen nata ya riƙo cikin nasa. "Baby menene kuma? Ko kina son wani abin ne?".
Faɗa wa tayi saman jikinsa tana murmushin, rungumeta ya yi yana faɗin "Babyn mijinta me ya faru ne? Me akayi kuma". "Ba komai daddy kawai dai har yanzu ina mamaki ne akan