Showing 9001 words to 12000 words out of 355604 words

Chapter 4 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2742

ɗin yin sauri yasha gaban ta, tare da yin patali da trey ɗin abincin dake hannun ta yana faɗin "Ke akoi sa'ar ki a nan ne, hattara yar talakawa, idan ba haka ba ki kare rayuwar ki a prison!!" Kallon trey abinci tayi, yadda ya faɗi kasa, abincin dukka ya tarwatse a kasa, plate ɗin ɗaya yayi gefen can ɗaya yayi gefen nan,

Dawo da kallon ta tayi kan bodyguard ɗin, sai wani ɗaure fuska yake, shi adole ya ɓata rai. Ta rasa me ma zata cewa wannan mummunar mutumi, yau bata jin yin magana, haka ta tashi cikin wani irin yanayi mara daɗi, saboda ɓatar Rimsha ya dawo mata sabo ne a yan kwana kin nan, yau sosai ta tashi da tunanin yar uwar ta, jikin ta duk a mace yake, bata son hayaniya

"Amma kai jahili ne ko" ta faɗa cikin harshen Hausa, a zahirin gaskiya bata san menene ma'anar jahili ba, a bakin amaryan baban Sadiq take ji word ɗin, amarya na yawan zagin baban Sadiq da wannan kalmar, tun daga nan Jehan ta riƙe, a cewar ta koma me kalma ce mara daɗi, shiyasa ta faɗa wa wannan bodyguard ɗin, dan tana son yaji babu daɗi, saboda ya bata haushi.

Aikuwa hakan ce ta faru, ya fusata iya fusata, ya ɗaga hannu zai mareta, cak aka riƙe hannun sa ta baya, cikin sauri ya juyo dan ganin wanene.

Ganin Nawid ne yasa ya ɗan ja da baya yana faɗin "sorry sir" kallon Jehan kawai Nawid yake, ita kuma kallo ɗaya ta masa, taja guntun tsaki tare da kawar da kan ta gefe guda.

Nawid na kokarin yin magana, muryan ta ta katse shi tana faɗin "Ka tsugunna ka kwashe abincin nan duka, sannan ka bani kuɗin abinci" rai a ɓace bodyguard ɗin yace "Ke baki da hankali ko? Waye yace miki idan yarima yazo nan waje, ana barin sa aje a bawa wasu talakawa abinci? To bari kiji, idan yarima yazo nan kowa dake nan fita waje yake har sai yarima ya gama abun da yake ya fita tukun nan"
_kallon tsab tayiwa bodyguard ɗin, sai wani huci yake shi a dole ran sa ya ɓaci.

"Au hakane tsarin ku? To idan ma haka ne, ni ba haka nawa tsarin yake ba, ni mutun ce mai adalci, banga wani ɗan adam da zai shigo cikin restaurant nan na tsallake wayan da suka riga shi, na kai mashi abinci ba, babu wannan mutumin aduniya, ni adilace bana zalunci, kuma ai bani kaɗai ce ma'aikaciya a wajen ba akoi wasu me yasa sai ni? Ku nemi wata ma'aikaciyar ta kai muku abincin ba dai ni Jehan ba"

Nawid na kokarin yin magana a karo na biyu muryan yarima ya katse shi cewa "Ku kawo min yarinyar nan gaba na" ko a jikin ta, ta juya ta nufi hanyar komawa in da suke girki, tana faɗin "Zanje na haɗa musu wani abincin kafin na dawo ka kwashe wanda ka zubar kuma ka ajiye min kuɗi na" tayi maganar with her full confidence, babu alamar tsoro ko ɗari,

Shi dai Nawid kallon ta kawai yake dan ba karamin burge shi tayi ba, yana son mace irin ta mai izza da dakiya, mara tsoro.

Tazo zata wuce su Yarima sauran bodyguard na shi dake wajen suka sha gaban ta, suna masu bata umarnin a kan ta wuce ta tafi gaban yarima ta zube gwiwowin ta a kasa da kan ta, idan ba haka ba su ɗauke ta da kan su, su kai ta gaban shi, ganin da gaske zasu iya ɗaga ta yasa ta wuce da kafar ta, ta karisa gaban yarima.

Yana hakimce saman kujera, sai wani shan kamshi yake, yana wani basarwa. Tsayuwa tayi a gaban sa, tare da kawar da kallon ta gefe, tsawa bodyguard ɗin suka daga kama, a kan ta tsugunna, dan ba'a yiwa yarima haka.

Shi kam Ibraheem yasha jinin jikin sa, dan yasan halin yarima Al ameen bashi da mutunci ko kaɗan, ɗane ga kanin sarkin yanzu, kasan cewar sarki bashi da ɗa namiji, hakan yasa ake cewa ɗan kanin sa yarima, wannan restaurant ɗin ma mallakin family sune, na kanwar sarki wato gwaggon yarima kenan, amma restaurant ɗin yana hannun babban ɗan tane. Duk lokacin da Nawid yazo Katsina a restaurant ɗin yake sauƙa, ya kwana a ɗaki ɗaya daga cikin ɗakunan Hotel ɗin, bai cika son kwana a gidan sarki ba.

Duk sauran ma'aikatan dake wajen sai da suka tsorata, dan sun san yarima bashi da imani, karamin aikin sa ne yanzu yasaka Jehan frog jump daga nan har gidan su da kafa.

Jehan na tsaye taki tsugunnawa yayin da shikuma yarima izzar sa ke ta daɗa motsawa. Karisowa wajen Nawid yayi yana faɗin "Al Ameen ka kyale ta ta tafi" ya kai karshen maganar tare da zama a ɗaya daga cikin gujerun wajen.

Sosai Jehan ta tsorata, ji take kamar fitsari zai zuba mata a wando, ga wayan nan bodyguard ɗin masu fuska abun tsoro, har kerman tsoro jikin ta ya fara yi.

"Kneel down!!" Yarima ya furta yana wani shan kamshi, shiru tayi tana tunanin, tayi kneel down ɗin ne ko kar tayi, idan tayi shikenan mutuncin ta ya zube a idon su Ibraheem, idan kuma taki yi, wannan mugun mutumi zai iya saka wayan nan munanan bodyguard ɗin su mata mugun duka, yanzu me mafita, ta tambayi kan ta, duk ta tsorata, yau duk wani izzan ta ya sauka, saboda bataga alaman wawanci a tattare dasu yarima ba, daman duk wayan da take wa tsiwa, dan tasan jahilai ne, babu ilimin boko, ba na islamiya, shiyasa take rai na musu hankali, su kuma su yarima, gogewa na duniya ne a tattare da su, wayayyun guy's ne, na bugawa a jarida, ga kuɗi ga mulki, ga ilimi da isa, ga izza da isgilanci.

Ibraheem da sauran ma'aikatan dake wajen sun yi shiru sun zuba musu ido, suna son suga, shin Jehan zatayi wannan kneel down ɗin kuwa? Koyaya.

Runtse ido Jehan tayi tana mai jin zafin rashin daddyn ta, yau da daddyn ta na nan, akoi wanda ya isa ya zo kusa da ita ne a cikin su, ji take kamar ta saka ihu ko zata samu sassauci a zuciyar ta.

Tsawa Yarima ya dakawa bodyguard ɗin, a kan su ladabtar da ita, su sakata kneel down ɗin dole, a sukwane ta waro idon ta waje, jin yarima yace bodyguard su ladabtar da ita,

bodyguard ɗin kuwa, cikin bin umarnin yarima suka fara kokarin riƙota, ban da sunan Allah babu abun da take kira a zuciyar ta, dan ta sawa ranta ba za tayi kneel down ba, dan kar mutuncin ta ya zube a idon su Ibraheem.

Bodyguards ɗin suna ƙoƙarin kamata Nawid ya daka musu tsawa "Kai kuna da hankali kuwa?!! Al Ameen meke damun kane? Mace ce fa, Ke jeki abun ki, koma bakin aikin ki, ki shiryo mana abinci da zamu ci yanzu" cak bodyguard ɗin suka tsaya suka fasa kamata, yarima na kokarin yin magana muryan Jehan ta katse su "Ni ba zan kawo muku abinci ba har sai na kaiwa wayan can da suka riga ku zuwa" tashin hankali.

Murmushi Nawid yayi yace "To jeki kai musu, idan kin dawo sai ki haɗa mana namu, ai kina da gaskiya, hakan shine adalci" Yarima zai yi magana Nawid ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Bana son na ji komai daga gareka, ke jeki abun ki" da sauri Jehan ta wuce ta bar wajen, shi kuma yarima rai a matukar ɓace ya miƙe ya bar wajen, yana cika yana batsewa, yau yayan sa Nawid ya tsinkashi a cikin jama'a, a kan yar talakawa kazama, a cewar sa.

Shi kuwa Nawid sai murmushi yake, bakin sa yaki rufuwa, yana ta bin Jehan da kallo, duk in da ta wuce sai ya bita da ido. Har ta gama serving wayan can da suka riga, sannan ta shirya nasu Nawid ɗin ta ɗauko, ta kawo musu,

Nan ta tarar Yarima ya tafi, ko a jikin ta, ta ajiyewa Nawid ta koma bakin aikin ta, shima Nawid ɗin bai wani damu da tafiyar da yarima yayi ba, dan ya san halin yarima fin haka ma zai aikata.

Cikin kwanciyar hankali yaci abincin sa tsab, sannan ya miƙe bayan ya gama, ya nufi wajen Ibraheem, yaje ya karɓi key ɗin ɗaki ɗaya, ya wuce ya nufi ɗakin, yana jin zuciyar sa na masa daɗi ganin Jehan da yayi, bai san taba, bai taɓa ganin taba sai yau, amma da kallo ɗaya, ya kamu da matsanancin son ta, niko nace tab kana da babban aiki in dai Jehan ce, dan bata san soyayya ba bashi kuma a gaban ta,

Tunanin Jehan cike fal ransa, ya karisa room number 14, ya buɗe ya shiga, yana mai sauke ajiyar zuciya.

A ɓangaren Jehan kuwa, ko a jikin ta, dan bata ma san yana yi ba, ita ko kallon fuskar su da kyau ma bata yi ba, zata iya sake haɗuwa da yarima a hanya ma ta kasa gane shi, dan bata kalli fuskar sa ba, ɗan gara Nawid da yake ya taimake ta, shi ta kalle shi sau ɗaya.

Lallai akoi aiki, to mu dai je zuwa, bari mu koma wajen su Rimsha muga wani hali suke ciki

Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .

💞💞TRIPLET'S💞💞






# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 4💔💔


💔RIMSHA💔


Lallai akoi aiki, to mu dai je zuwa, bari mu koma wajen su Rimsha muga wani hali da suke ciki.

Kwance suke bayin Allah kasan wannan itaciyar mangoron, duk da suna barci hannun su rike cikin na juna, sun kan kan me junan su sosai, kamar wani yace zai raba su.

Hasken rana daya ɗago ne ya haske musu idanuwan su, wadda hakan yayi sanadiyar farkawan su daga barcin wahala daya ɗauke su, a hankali suka waro jajayen idanuwan su waje lokaci guda, jikkunan su gaba ɗaya ciwo yake musu, tsananin yinwa da kishin ruwa ne ya tattaru ya musu yawa, plat tummyn su nan ya kara yin plat sosai saboda azaban yiwan, fuskokin su gaba ɗaya ya canza launi, sun zama abun tausayi, sunyi wiki wiki da su, gasu futu futu da datti, idan ka gansu ba zaka taɓa gane su ɗin bane.

A hankali Rimsha ta yunkura ta miƙe zaune tana faɗin "Good morning Kausar" miƙewa zaune ita ma Kausar tayi tana faɗin "Meesha yinwa nake ji, ba zan iya ci-gaba da tafiya ba muddin banci abinci ba" Rimsha na kokarin yin magana idon ta ya sauƙa a kan mangoririn (Mangos) da suka faffaɗu kasa daga saman bishiyan dasu wajen, kallon Kausar tayi a nitse tace "Kausar ga abinci nan Allah ya bamu, dama Allah ba azzalumin bawan sa bane sai dai bawa ya zalunci kan sa, yanzu mu ɗebi mangoririn nan muje mu wanko su, musha mu koshi, sai mu sha ruwa, mu ɗauro alwala muzo mu fara biyan bashin sallolin dake kan mu" shiru Kausar ta ɗan yi kafin tace "Meesha dame kike tunani zamu yi sallah? Bayan dukan mu babu mai ɗankwali bare hijabi" yunkurawa Rimsha tayi ta miƙe ta fara zaɓan mangoron da ya mata tana faɗin "Ba zani bane a jikin ki? Idan mu kayi alwala sai ki bani zanin ki na rufa nayi Sallah, idan na idar ni kuma sai na baki rigana ki saka, tun da ina da wando da best a ciki, idan kin saka rigana sai ki yafa zanin kiyi Sallah" murmushi ne ya bayyana a kan fuskar Kausar, dan jin sun samu hanyar da zasu yi Sallah su kaiwa Allah kukan su, daman tasan rashin Sallah da basa yi ne, yasa abun ya haɗu ya musu yawa, dan basu samun dama su kaiwa Ubangijin mu kukan su.

Tayi shiru tana tunani, bata san lokacin da Rismha taje ta wanko musu mangoron a wajen wani rami da ruwa ke taruwa a wajen ta dawo ba, sai ji tayi Rimsha ta ɗaura mata mangoro a saman hannun ta, tana faɗin "Kici da wuri muyi Sallah mu ci-gaba da tafiya dan mu samu mu bar dajin nan" godiya mai yawa Kausar tayiwa Rimsha tare da yi mata addu'ar fatan Alkhari da fatan nasara.

A takaice dai haka suka ci wannan mangaron sannan sukaje sukayi alwala sukazo sukayi kamar yadda Rimsha tace na musayan kayan su, sukayi Sallah, sannan suka ɗebi wasu mangoririn a hannun su, suka ci-gaba da tafiya, yanzu sun samu karfin jikin su, har hira suke suna tafiya.

Nan Kausar ke bawa Rimsha labarin yadda su Barbushi suka sato ta har suka kawota Daular mutuwa. "Ni dai sunana Kausar, bayarbiya ce ni yar jahar kwara state, munje kaduna wajen yan uwan mama ta ce, kasan cewar ita ba bayarbiya bace, ba haushiya ce, daga zuwa ziyara na fito ganin gari shikenan suka sace ni" sosai Rimsha ta jajan ta mata tare da yi mata fatan Allah yasa suna da rabon sake ganin yan uwan su, Amin Kausar ta amsa da shi sannan tace "Ke fa? Ya akayi suka kawo ki Daular mutuwa" Rimsha mace ce mai sirri duk da kananan shekarun da wuya ka samu tana yiwa wani ɗan adam hiran a kan rayuwar ta, dan haka sai tace da kausar "Ni yar Katsina ce, daga can suka sace ni na fito sayan ashana" Kausar ta nuna rashin jin daɗi ta, ta kuma yiwa Rimsha addu'a ita ma sosai, Amin Rimsha ta amsa da shi, suka ci-gaba da tafiya suna hiran gwanin ban tausayi da kuma burgewa.

Basu gane lokacin, kawai da sukaga rana ya ɗaga sosai, sai suka tsaya sukayi sallar azahar a kasan wata katuwar bishiya kanya, kasan cewar lokacin damuna ne, dajin akoi ruwa sosai ta ko'ina, ko baka ga rafi ba, zaka samu rami da ruwa, shiyasa basa wahalan wajen samu ruwa, haka zalika yanzu basa wahalar abinci, saboda lokacin damuna ne akoi ƴaƴan itace sosai, irin su gwaiva, mangoro, kashu, lemu, da sauran su, duk in suka ji yinwa, sai su tsaya ci tsinki ƴaƴan itace su ci sai sun koshi, Kausar itace ke hawa musu bishiya, Rimsha kam bata iya ba, kuma ita Rimsha akoi ta da tsoron bala'i, bazata iya hawa itacen ba, sai taga kamar zata faɗo kasa, itakuwa Kausar yar yarbawa, hayewa take kamar ɗan biri tayi ta tsinko musu ƴaƴan itace tana jefowa kasa Rimsha na ɗauka, sun zama kamar wasu ƴaƴan daji, har wani fresh suka fara yi ɗan wunin yau da suka samu ƴaƴan itace suna taci suna shan zuwa.

Idan sun koshi sai su ci-gaba da tafiya, har yanzu kuma basu fara jiyo kamshin wani garin a kusa ba, hakan kuma bai wani ɗaga musu hankali ba, dan sun ɗan samu sakewa da dajin, mafi yawancin lokaci Rimsha na yawan tunani a kan su gwaggo, haka zalika tana yawan tunani a kan GAR, mutumin da tafi so fiye da komai a duniya idan aka cire iyayen ta da Jehan da gwaggo, wani lokaci idan suka zauna a kasa wata bishiya, har zana fuskar sa da face mask take a kasa, dan ta kware wajen iya zane, idan kausar ta tambaye ta wanene wannan, sai tace wani ne wanda yake burge ta, kuma take kaunar sa, a hankali hankali har kausar ta fara iya zana fuskar GAR ita ma, saboda yadda Rimsha ke zana shi ko wani lokaci idan suka zauna.

Haka zalika idan suka zauna Rimsha bata da wani magana sai maganar GAR yana burgeta, tayi kewar ganin fuskar sa, bata damu da rayuwar ta kamar yadda ta damu da missed na fuskar GAR ba, tun Kausar na mamaki har ta dai na, ta dawo biye mata suna yi kawai, dan idan kana son kaga Rimsha na magana tana dariya to kayi mata maganar GAR yanzu zata amsaka da dariya a fuskar ta.

Allah sarki baiwar Allah, tana dakon soyayyan mutumin da bai san taba bai taɓa ganin taba, bai san hanyar African ba sai dai ya gani a Media, amma ita tun tana yar shekara 9 take kaunar ganin labarai a kan sa, a hankali har son sa ya shige ta, so ma mai bala'i tsanani, wadda bata damu da rayuwar ta kamar yadda ta damu da shi ba, wannan shine gaibu, ko ace soyayya da aljani ko soyayya da duhu dan duk ɗaya ne, soyayya da abun da baka ganin sa, akoi matsala, akoi cakwakiya. To mu leƙo wajen su Aafia mu gani me suke aikatawa ne.

💞💞KADUNA 💞💞

Sai karfe 6 na yamma Aafia ta farka daga barcin da ya ɗauke ta, cikin sauri ta miƙe zaune tare da dirowa kasa daga saman gadon. A sukawane tayo waje,

A palon kasa ta isko Akila, Abba, da Ammie, ba tare da ta gaishe da ko ɗaya daga cikin su ba, tace "Ina Umaisha?" Akila ce tace "Aunty Aafia barka da tashi" kallon sama da kasa tayiwa Akila kafin tace "Ina Umaisha nace?" Akila zata yi magana Ammie ta rigata da cewa "Ke mara kunya, ki kiyaye ni ko na tashi na miki ɗan banzan duka, zoki wuce ki bargidan nan ma kafin na tashi" Abba yana son yin magana amma ba hali, dan yana tsoron Hajiya Umaiya, bata da mutunci, haka yayi shiru yana bin Aafia da ido,
_Guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ni daman idan ba kaddara ba, me zai kawo ni gidan nan, ku faɗa min ina yar uwata, shine kawai a gaba na, banson wani abu kuma" miƙewa Ammie tayi da niyar ta dake ta, sai sukaji muryan Akil a bayan su yana faɗin "Ke baki da hankali ko? Idan baki shiga cikin hankalin ki ba, sai na karya ki kafin ki koma, wuce mu tafi na mai daki gida, motar naki ki bar shi a nan driver zai dawo miki da shi" tasan halin Akil sarai yanzu zai iya karya tan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login