Showing 51001 words to 54000 words out of 355604 words

Chapter 18 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2758

ke masa barazanar tarwatsewa ya yi, yana ganin yadda cikin office ɗin Dr ke juya masa kamar fanka.

Bawan Allah da ma ba ƙoshin lafiya gare shi ba Aafia ta tagayyara shi ta gama da rayuwarsa.

Dr na kokarin magana sai kawai ya ga Abbi ya zube kasa sumamme, a sukwane Dr ya yi kansa yana faɗin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ganin ya sume ya sa ya fito da sauri ya kira nurses suka zo suka ɗauki Abbi a saman bed na marasa lafiya, suka wuce da shi ɗakin da Aunty ke kwance.

Ba karamin tashin hankali Aafia ta shiga ba ganin Abbinta a sume, ta tsorata sosai tana son jin me ya sumar da shi. Cikin sauri ta ciro wayar ta ta fara kiran layin Irfan tana yi tana kuka hawaye bibbiyu.

Bugu ɗaya Irfan ya ɗauki kiran, a ruɗe ta ke magana "Hello yaya Irfan, Abbi ya suma Aunty ma haka ita kam kamar ta mutu ban san ya zan yi ba" daga ɗayan ɓangaren Irfan ya ce "Aafia ki nitsu ki faɗa min meke faruwa!" Muryarta sai kerma yake tana ta faman haɗe words ta kasa nitsuwa ta ce "Yaya Irfan jiya ne muna cin abinci da daddare sai Abbi da Bappa Maik su ka tashi zuwa bedroom nasu, palon ya rage daga ni sai Aunty, ita ma daga baya ta miƙe zata tafi sai ta faɗi kasa jini ya fara zuba mata, shine na gudu ne je zan faɗa wa Abbi sai naga yana toilet shi ne na ɗauko ta muka zo asibiti, sai yau shi kuma Abbi yazo dr ya kira shi dan su yi magana yana zuwa wajen Dr ya suma shima" dafe kai Irfan ya yi dan Aafia ta sake sa shi a duhu, ban da shine shine ba abin da take ta labka masa, ta ruɗe sosai.

"Ina bappa Maik ɗin?". Cikin sauri ta ce, "Abbi shi kaɗai ya zo banda Bappa Maik." Shiru Irfan ya ɗan yi kafin ya ce, "Tom ina zuwa." Bai jira amsarta ba ya katse kiran. Zarya ta fara yi a wajen tana kuka, duk wannan abin da ya faru bai sanya Aafia ta yi dana sanin zuba musu magani a abincin da ta yi ba, dan aikin ba nata bane na Rufee ce, sai dai ta ji babu daɗin ganin su a halin da suke ciki.

Sai safa da marwa take a wajen har Akil ya zo hospital ɗin ba tare da sanin taba, sai ji ta yi yana faɗin "Yaya Irfan ya kirani a waya a kan bappa yana hospital, ina yake? Me kuma yake damun shi?" A zabure ta ɗago kai dan ba ta san lokacin da ya zo ba, maganarsa kawai ta ji. Cikin ruɗu da tashin hankali shi ma ta fara ba shi labarin abin da ya faru, jikin ta har wani ɓari yake, da alama ta tsorata sosai.

Da yake shi Akil ɗan baiwa ne akwai kwakwalwa sai ya gane me take nufi, dan haka sai ya ce ina ne office ɗin dr, ba musu ta nuna mi shi, wucewa ya yi ya bar ta nan tsaye. Ya yin da ita kuma Umaisha ke can tana gwagwarmaya da Ammie, dan Akil na fita Ammie ta zo ta tasata a gaba suka wuce kitchen dan ta je ta karisa aikin da ta fara.

Tana aiki tana kuka hawaye sharɓa-sharɓa, ga shi tana aikin Ammie na aiko mata da zagi yar matsiyata da sauransu, abin ba ƙaramin ciwo ya ke mata a zuciyarta ba. Haka ta jure ta kammala aikin kitchen nan tas, amma fa tasha bakar wahala ba kaɗan ba, dan ita kanta har wani baki ta yi na wuya, sai haɗa bakin zufar kuran kitchen da ya hau jikin ta take, kasan cewar ba'a wani amfani da kitchen ɗin sai dai a ajiye ragowar abinci ko fruits, hakan yasa kitchen ɗin ya yi bala'i kura over. Baiwar Allah haka ta gyare ko ina tsab sannan ta fito.

A tunaninta ta gama zata wuce ɗakinsu, nan fa Ammie ta ce bata san wannan ba, tasata a gaba ta kuma yi zuwa bedroom na ta, sannan ta nuna mata bedroom ɗin Abba a kan idan ta gama nata ta haɗa dana Abba ta gyare tsab.

Kuka Umaisha ta kara saki mai ban tausayi lokacin da idon ta ya sauka a kan cikin bedroom ɗin, tamkar ba ɗan adam ke kwana a ciki ba, sai warin datti yake, ga saman mirror da sauran drawers ɗin duk kura ya baɗe su, shi mirror ma baka iya ganin komai saboda kura ya lulluɓe shi, mamaki da al'ajabi ya hana Umaisha motsawa, dan ita bata taɓa kallon bedroom na mutun mai rai da lafiya da datti haka ba.

Jikin ta har kerma yake saboda gajiya da kuma rashin lafiya da take ciki.

Tana jan kafa taje ta fara tikar aikin gyaran bedroom ɗin. Shi kuma Akil yana zuwa wajen dr. Dr ya masa bayanin abin da ke faruwa, shiru ya yi yana tunanin anya kuwa Aunty za ta iya abortion da kan ta, duk da cewa sau ɗaya ya taɓa kallon ta ya ga ala'mar kamala da mutunci a tattare da ita. Ganin tunanin ba wani mafita ne yasa ya miƙe ya nemi izinin ganin Abbi, ya yi sa a dr ya ba shi izini, wucewa ya yi zuwa ɗakin da Abbi ke kwance.

Har wani hasken wahala Abbi ya kara bawan Allah ya haɗu da jarabawa, yar cikinsa yau ta jefa shi cikin wahala da tashin hankali mai tsanani. Kusa da shi Akil ya zauna ya zuba masa ido yana mai jin kaunar bappan nasa kuma surukin sa har cikin ransa. Ita kuwa Aafia tana tsaye a waje, ta yi kuka har ta gode Allah.

Bayan wasu kwanaki.

A ɓangaren Abbi ya samu sauki sai dai ita Aunty Aafia ta ja mata bala'i domin kuwa har yanzu tana sume bata san in da kan ta yake ba, Allah ne kaɗai yasan wani irin magani Rufee ta baiwa Aafia ta zuba mu su a abinci, ta cuce su ta gama da su.

Abbi ya biya kuɗi ayiwa Aunty aiki sai dai kuma ya juya mata baya, domin sai ya fi kwana biyu bai zo asibitin ba, ya ce baya son ganin fuskarta tun da har zata iya zubar masa da cikinsa.

A ɓangaren Imran da Irfan kuma sun dawo dawowar da ba'a yi zato ba, dan dukkansu suna zargin gida babu lafiya, shiyasa suka dawo. Sun shiga tsananin tashin hankali jin abubuwan da suka rinƙa faruwa, musamman Imran kowa yasan yadda Imran ke bala'i kaunar Jelly tun tana da shekara biyu a duniya, ya shiga tashin hankali mara misaltuwa lokacin da ya ji zancen ɓatar ta, sosai ya dukufa neman ta a cikin garin Kano, dukkan su ba wanda ya kawo a ransa cewa Jelly na Kaduna a Kano suke yawon neman ta.

Ita kuwa Aafia bata samu damar haɗuwa da Alhajin da Rufee ke son haɗa su ba, domin kuwa ranar da za su gama Exam Irfan ne ya kai ta school kuma da kan shi ya je ya ɗauko ta bayan sun gama, tun daga ranar kuma bata kara fita ba, dan ko shopping take son zuwa shi ke kai ta, dan baya son fitar ta ita kaɗai, daman shi haka yake in dai yana gida to basa fita, hakan yasa ba su haɗu da alhajin ba, Rufee bata ji daɗin hakan ba, ba haka ta so ba, sai dai ta kudiri niyar sai ta haɗasu idan suka dawo hutu.

Tofa Rufee lallai a gaisheki, mu dai munyi gaba.

A ɓangaren Umaisha kuma ba ƙaramin azabtuwa take wajen Ammie ba, ga shi kuma yanzu Akil baya zama a gida sosai, yau suna Kano gobe suna Kaduna dan neman Jelly, har wani mugun rama Umaisha ta yi, wadda da kallo ɗaya zaka mata kasan ba lafiya ba, sai dai Akil baya cikin kwanciyar hankali da zai gane hakan, kuma kullun ya tambaye ta meke damunta sai ta ce masa bata da lafiya ne, tana ba shi wannan amsa ne saboda tsoron Ammie, dan Ammie ta ce idan ta kuskura ta faɗa wa Akil abin da take mata to sai ta kashe ta. Shi kuma baya kawo wani tunani a ransa, dan a tunaninsa Ammie na bala'i son ta yanzu, sai dai ya manta duk wanda ya ce bai sonka da safe da daddare ya dawo ya ce yana son ka to karya yake wani abin dai naka yake so.

A ɓangaren Rimsha kuwa yanzu ta zama yar Yarabawa, ta fara sabo da su, har yarensu ta fara ji, sai dai har yanzu mugun tsoron su boda Jami'u take, saboda dukkansu basu da burin da ya wuce su gan su kusa da ita, yanzu har Ayla ta fara gane abin dake faruwa. A ɓangaren Malika kuwa tun ranar da Rimsha ta mata ihu ta tsorata ta ɓace bata sake zuwa ba.

Idan muka koma Washington DC kuma.

An dawo da Michael gida dan ya samu sauƙi ba laifi, saboda aikin kwararun likitoci da ya samu, da kuma kyakkyawar kulawa, sai dai ciwukan nasa ba su gama bushewa ba, akwai ɗan saura, amma ba laifi. Shi ma Musharraf ya sa mi sauki sosai.

Yau ta kama Wednesday kwana biyu kenan da tafiyar lion gaba ɗaya William Jacop Family suna zaune a dining room suna cin abincin rana, banda James da kuma Lion dan su har yanzu shiru ba bu wani News a kansu dukkansu.

Wadannan jibga-jibgan bodyguard ɗin nasu ne ke tsaye a kansu suna zuba musu duk wani abin da za su buƙata.

Cike da murna Jay ya dubi uncle herry wato daddynsu ya ce "Dad I have a wonderful surprise for you" yar murmushi uncle Herry ya yi kafin ya ce, "Really? Which kind surprise is this? That make my son happy." Kara wash baki Jay ya yi kafin ya ce, "Close your eyes daddy." Ba musu uncle Herry ya rufe ido. Miƙewa Jay ya yi ya isa bakin kofar shigowa palon ya sanya hannu ya daddanna pin na jikin kofar, zuba masa ido suka yi gaba ɗayansu suna jiran su ga wai mene ne wannan surprise ɗin.

Michael da ke zaune kusa da dad ya langwaɓar da kai a kafarɗar daddy ya zubawa uncle Tga wayan nan shanyayun brown eyes ɗin nasa, yanzu sabon shagwaɓa Michael ya fito da shi, dama kuma Dr Tyrion ya ce sai sun kara hakuri da shi a yan kwanakin nan, abu kaɗan idan ka masa sai ya sa kuka, kuka kuma har da hawaye kamar ƙaramin yaro, bawan Allah.

Buɗe kofar palon Jay ya yi, wata kyakkyawar matashiyar baturiya ce tsaye a bakin kofar tana goye da baby ta gabanta a irin abin goyon babyn nan, Jay sai murmushi yake yi dan yasan lion da James basa nan shi kuma Michael bai da lafiya, dama sune matsalar gidan a cewar sa.

Iso ya yi wa yarinyar yana ta faman washe baki. Zubur Tga ya miƙe tsaye a zafafe, ba Tga kawai ba harta bodyguard dake tsaye a wajen sai da suka razana, dan yau sawon shekara 8 kenan suna aiki a gidan William jacop ba su taɓa kallon wata mace bayan mum ɗin su ba a gidan, yau rana tsaka rana ta farko mace a gidan William jacop bayan Josephine mum ɗin su kenan, a zahirin gaskiya har ta security dake bakin gate sun tsorata sosai da ganin mace a gidan, duk wani soja dake gidan sai da ya kallin yarinyar ya sake kallon ta domin kallon gawa suke mata, dan kuwa ko da sunan wasa basu taɓa gani mace a gidan ba, ba dan Jay shi da kan shi ya ɗauko ta a motarsa ba da ba za su bari ta shiga gidan ba.

"Jay me nake gani? Who is she?!!" Tga ya faɗa cikin tsawa wadda ya sa sai da yarinyar ta tsorata. Jin maganar da Tga ya yi ne ya sanya Michael da John ɗagowa a tare, shi kuma uncle Herry sai murna yake dan ba shi da burin da ya wuce daman ƴaƴansa su samu mata, ya tsufa yana son ganin jikokinsa, daddy ma ya ji daɗi sosai, dan shi ma yana son su yi aure amma dan ya san basa son ko maganar mace hakan yasa bai taɓa gigin kawo musu zancen ba ko da wasa.

Washe baki Jay ya yi yana faɗin "she's my girlfriend uncle ita nake son aura" da sauri Michael ya kai kallonsa kan babyn dake hannun ta yana son tantancewa shin ita ce uwar babyn ko kuma dai aro shi ta yi. "What girlfriend? are you mad jay? Are you heard what you said?" Tsuru tsuru da ido Jay ya yi dan bai taɓa tunanin su uncle Tga za su yi rejecting na budurwansa ba, a iya tunanin sa Triplets ne kawai basa son mata, suma saboda mum ɗin su ne yasa, kuma dan ya ga basa nan ya sa ya ce bari ya yi amfani da wannan dama ya gabatar da matar da yake son aura ga iyayensa, bai taɓa tunanin su ma basa son mata ba, shi kuma gaskiya yana son yin aure ya ga ji da zama haka. Tashin hankali.

"Jay are you out of your sense?" Cewar John, ya yi maganar yana satar kallon Michael da ya yi shiru kamar wani wawa yana bin su da ido kawai, ita kan ta yarinyar ta tsorata sosai, tazo da murnanta zata zama ɗaya daga cikin family William jacop, sai kuma ga shi suna kokarin yin rejecting nata, abin ya taɓa mata zuciya sosai, dan burinta kenan ta shigo gidan, ko zata samu damar ganin lion, dan a zahirin gaskiya ba Jay take so ba, saboda lion take soyayya da Jay.

Tirkashi wannan shine chakwakiya lallai yarinya kin ɗebo da zafi, kin ɗebo ruwan dafa kanki.

Tga na kokarin sake yin magana uncle Herry ya dakatar da shi ta hanyar cewa "is okay general bana son sake jin wani magana a nan, Jay come in with her, i really like her, i excepted her to be your wife". Cikin sauri daddy ya ce "Yes this is true, I'm with you herry, Jay come in, our new daughter you are welcome to William jacop family". Yau sun samu zakunan gidan ba su nan suna cin karensu babu babbaka, su uncle Herry harda magana da bada umarnin, shi kuma daddy yana magana yana satar kallon Michael, still Michael bin su kawai yake da wayan nan shanyayun idon nasa, mai kama da mai jin barci, Bawan Allah bai ce komai ba, kamar ba Tiger'n daddy ba.

"This baby is for who?" John ne ya jefawa Jay tambaya. Kallon babyn da kyau Jay ya yi kafin ya ce "are we not looking alike? Is my son mana" kara zaro ido waje Michael ya yi duk da cewa su turawa yin hakan a wajen su ba wani abu bane, wani lokaci ma sai sun haifi ƴaƴa uku da mace sannan suke aure a tsakanin su, amma abin da ban mamaki ba su taɓa tunanin haka daga wajen Jay ba, domin su mutane marasa yarda da mutun kuma suna kula da lafiyar su sosai, shine yaushe ma Jay yake fita da har ya je ya aikata hakan bai gaya mu su ba, bayan kuma basa ɓoyewa juna komai, abin ba karamin mamaki ya ba su ba, Jay da baby, babyn ma ba karami ba zai kai 1 year tab.

Wani cool murmushi yarinyar ta saki lokacin da ta ji amsar da daddy da uncle Herry su ka bada na sun yi accepted na ta a matsayin surukuwa, ta riga Jay wucewa gaba tana ta murmushi ta nufi su dad.

"Don't come here!!" wani gigitatchiyar tsawa Micheal ya daka mata wadda ya sanya ta juyawa a guje ta koma ta rungumi Jay, su kansu su daddy sun tsorata ainun da jin tsawar da Michael ya daka mata, abin da ya bawa Michael haushi wato Jay ya daɗe tare da yarinyar har ma da baby a tsakaninsu.

Uncle Herry ne ya yi ta maza ya ce "Why my tiger? Why zaka ce karta zo nan?" "Shut up uncle!!" Tsawa ya dakawa uncle Herry, a fusace ya ce da yarinyar "get out!!" sanin cewa lion da James basa nan yasa Jay ya yi kokarin tirjewa Michael a kan yarinyar ba zata bar gidan ba ya yi duk abin da zai yi. Lallai yau a ke yin ta.

Da yar dugu Michael ya haura sama, harara Jay ya bi shi da shi yana shafa kan budurwar tasa, a zuciyarsa yana faɗin "Ba ka da abin da za ka yi, sai dai hakuri, ba ka da aiki sai bawa mutane umarni bayan shi ba wani abin da ka iya". A fili kuma kasa-kasa ya ce "Sorry Jennifer" ya kai karshen maganar tare da raba jikinsu ya riƙo hannunta su ka karisa wajensu daddy.

Daddy kam har jikinsa ya fara kerma, saboda baya son tashin hankali ko kaɗan dama daga jiya zuwa yau yana cikin rashin lafiya sosai, saboda rashin James da kuma lion.

Saman chairs Jay da budurwarsa suka zauna, suma su daddy komawa suka yi suka zauna, sai tunanin Michael dad yake yi.

Suna zama Michael ya fito da gudu hannunsa riƙe da pistol gun ɗin Romeo, sai ta su ya yi yana faɗin, Jennifer ta fita gidan nan ko ya harbeta ya harbe banza. A tunanin Jay Michael bai iya harbi ba dan haka sai ya ce ya harbeta ɗin su gani.

Ai kuwa Michael bai yi kasa a gwiwa ba ya ɗana kunamar bindigar ya harbi Jennifer a hannunta, Allah ma yasa Jay ya yi saurin janyota jikinsa ta kauce bullet ɗin ya same ta a hannu ba dan haka ba kanta Michael ya yi niyar harba.

A zafafe gaba ɗayansu suka miƙe ya yin da gaba ɗaya bodyguard dake wajen suka duka kasa gudun kar bullet ya taɓa su, ihu sosai Jennifer ta ke kamar makoshinta zai fashe saboda bala'i a zabar da take ji, ga jinin ta ya fara malala kamar famfo.

Kara sai ta Jay da bindigar Michael ya yi zai harbe shi, cikin sauri Jay ya zube kasa bullet ɗin ta fita ta samu bango, ji kake dam. Kamar wanda baya a cikin hayyacinsa haka Michael ya zama, duk ya ruɗa jama'ar dake palon kuma dukkansu sun san


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login