Showing 321001 words to 324000 words out of 355604 words

Chapter 108 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2800

son yaga friend ɗin nasa a cikin damuwa, to ni dai na baka shawara idan ka ɗauka ka tsira akasin haka kuma ka san sauran". Shiru gate man ya yi yana nazarin maganganun Mark.

Ita kuwa saman ɗaya daga cikin kyawawan kujerun dake a wajen ta je ta zauna, wani irin daɗi ta ji lokacin da hancinta ya shaƙo mata kamshin perfume ɗin Lion, alama ya nuna yana yawan zama a wajen kenan, dan kuwa gaba ɗaya wajen kamshin perfume nasa ne yake tashi.

Cikin natsuwa ta fara yankawa kanta fruits ɗin tana sha, already a wanke suke daga fridge ta ɗebo su. Har wani lumshe idanunta take yi daɗin apple na ratsata ga kamshin perfume ɗin abin begenta dake karawa abin armashi.

A ɓangaren su Imran kuwa sai karfe 9 jelly ta farka daga nauyayyar barcin da take yi, Imran bai san ma tana period ba shiyasa ma ya yi kokarin tashinta da asuba ta yi sallah.

Tana buɗe waƴan nan dara daran idanun nata kai tsaye sai cikin idanunsa, yana zaune a tsakiyar gadon ya tsareta da ido tana kallonta. Sai tashin kamshi yake yi, ya yi wanka ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda milk color.

Wani kayatatcen murmushi ta sakar mashi tana faɗin "Yaya Imran baka tashe ni ba sai da na tashi da kai na". Shima murmushin ya sakar mata kafin ya ce "A'a na tashe ki mana, ke ce dai kin gaji sosai kika ki tashi". Turo ɗan bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran wajen daddyn fa?" "Tashi ki je kiyi wanka ki yi sallah ki shirya mu tafi".

Miƙewa ta yi tana faɗin To. Sai kuma me tana tashi suka kalli jini a wajen da ta kwanta, ihu ta kurma mashi tare da rungume shi dan tana mugun tsoron jini, kuma a tunaninta ciwo ta ji, idan ta ga jini har jiri take gani, shima dai rungumeta ya yi yana mamakin daga ina wannan jinin kuma.

Bai kai ga yin magana ba ya ga jinin gaba ɗaya ya ɓata mata kayan jikinta, a nan ne ya gane jinin menene sai dai kuma matsalar ta yaya zai yi mata bayani ta gane dan yasan halinta sarai. Can dai wata dabara ta faɗo mashi akan ya kira Akila ko kuma Rimsha ɗaya daga cikinsu ta yi mata bayani, dan yasan idan su ne suka yi mata magana zata ɗauki maganar da mahimmanci saɓanin shi da suke tare a baya ko da yaushe.

Haka kuwa aka yi, ya kira layin Akila bata ɗauka ba lokacin tana waya da ɓoyayyen masoyinta, kiran Rimsha ma ya yi a waya, a lokacin ita kuma ta gama shan fruits nata har ta dawo cikin gida tana kwance a bedroom nata, bugu ɗaya ta ɗauka ya ce ta zo ɗaki ta same shi, to ta amsa mashi da shi sannan ta fito ta zo.

Jelly na kwance a jikinsa tana kukan bata son ganin jinin nan, mamaki ne ya kama Rimsha akan wace ce jelly kuma.

Alama ya yi mata da hannu akan ta kariso saman gadon, da sauri ta kariso. Cke da jin kunya ya gaya mata abin da yake faruwa da kuma wace ce jelly sannan ya ɗaura da cewa ta yi wa jelly'n karin bayani akan jinin.

Abin da bai sani ba shi ne ita ma Rimshan bata taɓa yin period ba, shekarunta 14 ita kuma jelly 16, jelly ita ce sa'ar JEHAN 16 suke da shi, amma dai da yake ta yi karatun addini sosai, kuma ta samu karin haske wajen mummynta sai ta amsa mashi da to.

Da kyar Jelly ta yarda ya saketa ya fice daga ɗakin dan ya basu waje su ji daɗin yin magana, ya san halin Rimsha sarai da shegen kunya, idan yana nan ba zata yi wani magana ba.

Yana fita ta riƙo hannun Jelly ta fara yi mata bayayi ta yadda zata fahimta, a nan ne Rimsha ta fahimci e tabbas ita ma jelly ta karanta, sai dai rashin uwa ne yasa bata samu wanda zai iya fayyace mata komai ba, ita dai ta karanta mace tana jini kamar yadda suma su Rimshan suka karanta, Allah dai ya taimaka su mummy ta yi masu dalla dalla yadda za su fahimta ne shiyasa suka iya gane komai.

Sosai Jelly ta fahimta sannan Rimsha ta riƙe hannunta ta sauƙo kasan gadon ta nufi toilet dan yin wanka, ita kuma Rimsha sarkin son tsab ta gyaran bedroom ɗin ta fara yi tare da cire bed sheet ɗin ta sauya wata.

Kafin jelly ta fito ta gyare ko'ina tsab tare da feshe ko'ina da air freshener masu daɗin kamshi, ita kanta jelly da ta fito sai da ɗakin ya burgeta ina ga kuma Imran.

Zama ta yi a saman mirror chair tana kallon mayukan Imran dan bata ma iya shafawa ba, idan baku mance ba komai daddy ne yake yi mata, ba abin da ta iya sai karatun makaranta kawai, ko abinci a baki daddy yake bata.

A takaice dai daga karshe Imran shi ya zo ya shafa mata mai sannan ya ce Rimsha ta kawo mata kayanta kala ɗaya doguwar riga mai ɗan girma wadda zai yi wa Jellyn, domin kunga jelly ta girmi Rimsha.

To Rimsha ta amsa da shi sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har zata fita sai kuma ya ce mata ta shirya yanzu za su je gidan Abbi, da murna ta amsa mashi da to sannan ta fice.

Bayan ya gama shafa mata mai ɗin ya ɗago yana karewa surar jikinta kallo, daga ita sai towel a kirji wadda bai gama rufe mata cinyoyinta ba, wani irin yanayi ya shiga lokaci guda, ita kuma bata ma san yana kallonta ba, hankalinta na can wajen mirror tana kallon face nata, ita da kanta ta yi wa kanta kyau bare kuma shi, shi kuwa ji yake yi tamkar ya........Kayarsa, ya ƙosa su je wajen daddy a shafa fatiha ko kiss ne ya samu ya yi mata ko zai rage zafin da yake ji. TOH FAH TEAM ƊIN IMRAN, ANYI WALKIYA MUN GANKU, ASHE DAMA HAKA KUKE? DAMA WATO DAN RASHINTA A KUSA NE YASA KUKA KOMA SO SILENT KO? E LALLAI AKWAI AIKI

A haka Rimsha ta dawo ta same su, hannunta ɗauke da abaya pink color, ita ma ta sauya kayan jikinta zuwa abaya black color tare da yafa gyalen abayar a kanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba.

Jin sallamar ta ne yasa Imran ya dawo hayyacinsa tare da miƙewa ya fice daga cikin ɗakin da sauri yana faɗin su shirya su same shi a wajen motarsa, to suka amsa mashi da shi.

Kayan ma jelly bata iya sawa da kyau ba sai da Rimsha ta taya ta, godiya ta yi mata tana tambayarta sunan ta, "Sunana Rimsha". Ta bata amsa, sake maimai ta sunan jelly ta yi sunan ya yi mata mugun daɗi.

Bayan sun kammala suka fita zuwa parking space na gidan, zaune cikin mota suka isko shi yana jiransu, ya je ya yi sallama da Lion ya kuma duba jikin Areef sannan ya dawo cikin motar ya zauna.

Gidan baya Rimsha ta je zata shiga, cikin sauri ya ce mata A'a ta dawo gidan gaba su haɗu su biyun dukka, to ta amsa da shi tare da dawowa gidan gaban suka zauna a tare, jelly tana matukar kaunar Rimsha tun da ta fara ganinta shiyasa ta yarda suka zauna a tare.

Da gudu ya ja motar suka bar gidan, sai tambayarsa Jelly take yi nan gidan waye ne, ko dai shine gidansu, bakin abin magana ya ki yin shiru kwata kwata, haka ya rinƙa biye mata har suka isa gidan Abbi, ita kam Rimsha hanya kawai take gani abinta.

Yana kashe motarsa a parking space na gidan suka fito suka jera zuwa cikin gida, gaba ɗaya kayan da jelly ta sa sun sake ɓaci da jini saboda bata sanya always ba, amma ba su lura da jinin ba, da yake ta baya ne kuma jerawa suka yi zuwa cikin palo.

Bazata Imran yake son yi wa daddy shiyasa bai kira shi a waya ba. Da sallama ɗauke a bakinsu suka shiga palon, Aunty, Abbi, sune kawai a palon suna breakfast a saman table, da yake shima Abbi bai san jelly ba sai bai gane ta ba.

Da fara'a suka tarbe su tare da yi masu iso, saman sofa suka zauna, sai tambayar ina daddy yake Jelly take yi, har da wani cewa ko dai yana Kano ne?.

Abbi na ƙoƙarin yin magana aunty ta ce "Wannan yarinyar ta taɓa zuwa gidan nan ita da wata ƴar uwar Ommu, sun zo lokacin har ta ce mani mai idon mayu" kallon tsab jelly ta yi mata kafin ta ce "Ba dai Jalila ba sai dai wata" jelly bakin dai yana nan bai mutu ba, ba'a yi mata ya kyale.

Aunty zata sake yin magana Abbi ya katse ta da cewa "Imran wace ce wannan mai tsananin kama da Maik? Ko dai Jelly ce?". Gyaɗa mashi kai Imran ya yi alamar e, zubur Abbi ya miƙe yana mai kabbara ga ubangiji tare da ciro wayarsa da sauri dan ya kira daddy.

Lokacin da kiran ta shigo wayar daddy yana tsaye a gaban mirror yana gyara hular kansan ya yi waka ya shirya cikin manyan kaya zasu fita shida babynsa, ita ma ta yi wanka tana sanye da doguwar riga black color, dukkansu sun yi kyau sosai da sosai.

Ganin kiran Abbi ne yasa ya ɗauka da wuri. "Maik ka zo palo yanzun nan ka same ni". Shine abin da Abbi ya ce, wani irin faɗuwar gaba ya ji, da sauri ya nufi hanyar fita yana faɗin "Baby ta so muje Abbi na kiran mu, kuma yadda ya ce na yi saurin nan da alama akwai abin da yake faruwa". Miƙewa ta yi ta fara dingisa kafa dan har yanzu bata gama warwarewa sosai ba.

Ganin zata ɓata mashi lokaci ne yasa ya ɗauketa cak kamar yadda yake ɗaukar Jelly suka fita. Tun da ya doso palo gabansa ke faɗuwa, sunan Allah kawai yake ta kira a cikin zuciyarsa.

Suna shiga palo bai lura da su Imran ba ya nufi saman sofa ya ajiye Ayla, ɗagowa da zai yi idanunsa sai a kan fuskar Jelly dake zaune kusa da Imran tana ta kallon shi tun da ya shigo dan ta tabbatar da shi ɗin ne dan gaskiya ya sauya sosai.

Wani irin ɗagowa ya yi da sauri dan ya tabbatarwa da idanunsa abin da yake gani ne, ita ma miƙewa ta yi tsaye tare da nufo shi da gudu ta faɗa jikinsa tana ambatar sunan sa wato daddy.

Mutuwar tsaye ya yi kamar wadda aka zarewa laka a jiki, Abbi kam abu ya yi mashi daɗi har da ciro waya ya fara yi masu Video, a wannan hali Hajiya Hadizatu ta sauƙo kasa ta samesu, yau tana sanye ne da shadda yellow color, ta ci kwalliya da alama fita zata yi.

Kallon walaƙanci ta yi masu kafin ta ce "Matsiyata an taru kenan ba? Dan anga mijina yanzu ya wuce tsara shine duk aka tare mashi a gida".

Ɗago kai Jelly ta yi daga jikin daddynta ta kalleta sama da kasa kafin ta ce "Yaya Imran wace ce wannan kuma kamar wata busasshen kifi, fuska kamar na big da muke kallo a discovery". Jelly kenan bata barin ko ta kwana, ka yi mutunci da ita ma ya ka kare bare kuma rashin mutunci ta haɗa ku, ai gidan shi ka zo in dai jelly ce, tsab zata wankeka soso da sabulu, bata barin magana ta faɗi kasa ba tare da ta bada amsa ba

Guntse dariya Aunty ta yi shi kuma daddy sai lokacin ya ɗan samu karfi da ya sanya hannu ya ɗan bude mata baki, kuka ta sa mashi tana kara rungume shi, ita kuwa Hajiya Hadiza ran ta ya yi muguwar ɓaci, wato ita ce mai kamar an busar da kifi ga kuma fuska kamar alade ba, lallai idan ta kyale yarinyar nan ta cuceta, a zafafe ta yi kan daddy da nufin ya fisgo Jelly ta yi mata ɗan iskan duka duk da bata san wace ce bace kuma bata kalli face nata da kyau ba sakamakon tana manne da jikin daddynta.

Sai wani huci Ommu take yi jelly ta ɓata mata rai, gadan gadan ta mufe ta...........

Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu.

💖💖TRIPLETS💖💖




E85-86💖



Sai wani huci Ommu take yi jelly ta ɓata mata rai, gadan gadan ta mufe ta, da sauri Abbi ya tare ta yana faɗin "Amma dai Hadiza baki da hankali ko?, Me zaki daka a jikin yarinyar nan". Jelly kuwa tana daga kwance a jikin daddynta ta ce "Kai ni zaki daka ma kenan? Amma dai baki da hankali ko? To id...." Bata karisa ba daddy ya rufe mata baki tare da kara rungumeta sosai yana mamaki wai har yanzu dama jelly bata canza ba kenan?.

Shi kuwa Imran zuciyarsa har ta fara dukan uku uku dan Ommu zata bugi jelly, kuma dama ba bari shima zai yi a dake ta ɗin ba, shima daddynta fa bai yi kasa a gwiwa ba wajen sakinta ya juyo dan ya ga karshen rashin kunyar Ommu, idan ta yi gigin yunkurin taɓa ta wlh yau sai ya tsintsin ka mata mari sai dai duk abin da zai faru ya faru.

Ommu kuwa a kule ta ce "Matsiyata dama ba dole ayi haka ɗin ba, idan ba ku yi ba ai ba ku cika ƴaƴan talakawa ba". Shi kam daddyn Jelly mamaki ya hana shi yin magana, wai me Ommu ta gani a tattare da sune da take ce masu ƴaƴan talawa, ko dai wani sabon iskanci ne,? Domin kuwa Ommu ta yi masu farin sani tun iyayensu wato kakannin su Jelly suma raye kenan, tasan irin ruwan kuɗin da suke da shi kamar me, to kodai dan daddyn Jelly ɗin ya dawo gidan da zama ne?.

Shi kuwa Imran da abin ya ɓata mashi rai sai ya ce ya mata "Idan kina da account bani bari na baki koda 10 million ne ki rage zafi domin na ga kina da buƙa ta" ya kai karshen maganar tare da juyowa da kallon sa izuwa kan bappan nasa wato Abbi.

"Bappa ka yi hakuri amma ba zan iya juran wannan cin mutuncin ba, Irfan abokina ne kuma ɗan uwana, amma kuma ko da iyayen mu ne suka kauce hanya addini ya bamu dama mu yi masu gyara ta yadda za su fahimta, ina matukar kaunar Irfan kuma muna girmama juna, duk abin da ya faru shekaran jiya ina sane, to yana da kyau mu taka mata birki domin ba yara bane mu, ta zo ta same mu cikin kanne mu, ku kuma cikin ƴaƴanku ta haɗa mu ta ci mana mutunci saboda ita bata san mutunci ba, to wlh ya isa haka, dama saboda Irfan ne muke yi mata hakuri, wlh ba dan haka ba wannan da tana prison yanzu, duk abin da ya faru a gidan bayan tafiyar mu ranar Akila ta gaya mani a waya, wlh Allah zan iya cewa Ommu kin zama mace mai saa ta farko da Akil ya ɗagawa kafa, ina mai tabbatar maki badan Irfan ba da babu abin da zai hana Akil ya sharara maki maruka wadda za su sanya ki manta hanyar da ki ka nufa, su sanya ki gani taurari, su sanya kunnuwarki doɗewa, ni ki bani account number bari na cireki daga kangin tsiya da kuma talaucin nan ko zamu samu sake a gidan bappanmu idan muka zo!!". Ya kai karshen maganar rai a matukar ɓace, dama an ce mai hakuri bai iya fushi ba.

Sakin Jelly daddy ya yi yana faɗin "Rimsha ku je sama wajen Hanan ko, babyn daddy ta shi ku je ko?".

To suka amsa da shi, da kyar Ayla ta miƙe, da sauri Aunty ta zo ta dafa mata suka wuce sama, domin ita ma Aunty bata son tsayawa a wajen dan bata ma son jin hayaniyar tasu.

Dawo da kallonsa a kanta daddy ya yi tare da ɗaure fuska nan yau shima ransa ya yi mugun ɓaci, yau karo na biyu kenan da take cin mutuncin su a gaban ƴaƴansu to gaskiyar Imran ne yana da kyau su taka mata birki domin iskancin nata ya fara wuce misali.

"Hadiza ina ganin mutunci ki ne nima dan saboda Irfan, yaron kirki, Allah ya rufa mishi asiri ba ke kika raine shi ba, wlh nasan da ke kika ba su tarbiya ƴaran nan da sai sun zama kannen sheɗanu, yanzu ke ba abin kunya bane ma ki ɗauko kafar ki da sunan wai kin dawo gidan nan? Wlh ta bakin Imran kin yi babbar sa'ar Akil aure ta sauya shi, ba dan haka ba ko yaya suke da Irfan sai ya dalla maki mari, idan ma baki yi sa'a ba sai kin wuce gadon asibiti, yanzu tsabar rashin kunya ƴaƴan yaya babban ne talakawa? Ke kin sani a gaba ɗaya cikin mu a tsabar kuɗi dai daga Hosain sai Yaya babba wato Abban su Imran, ko dai dama baki san su Imran ƴaƴan yaya babba bane? To idan baki sani ba yanzu ki sani Akil kawai zai iya sayan Familynku baki ɗaya, sannan bugu da kari ƴaƴan Umaiya ce wadda ta ma fi yaya babba kuɗi, kuma ke kin sani ko ada baya da yaya ki ka kwaci kanki a hannun Umaiya? To ki sani barewa ba zata yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe ba, tun wuri ki fita har karmu idan ba haka ba zaki yi dana sani, yadda ki ka san Umaiya a da to yanzu Akil ne photo copyn ta, shiyasa ki ka ji munce maki kin ciri tuta tun da har Akil ya iya danne zuciya ya kyaleki!!!".

Cikin sauri Ommu ta ce "Yanzu kenan Umaisha ɗan gidan Yaya babban ta aura?".

Ba wanda ya tanka mata a cikinsu, cikin zumuɗi ta ce "Kai amma Alhadulillah da ya kasance ba ƴaƴan Matsiyata ƴar cikina ta aura ba, kai abin ya min daɗi". Tana gama magana ta juyawa ta nufi sama, sai daɗi take ji.

Girgiza kai daddy ya yi tare da komawa ya zauna a saman sofa, shima Abbi zama ya yi a saman sofa yana mamakin hali irin na Aunty, Baiwar Allah mace mai sanin Yakamata, bata son hayaniya, mafi yawancin mata suna son


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login