Showing 87001 words to 90000 words out of 355604 words

Chapter 30 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2792

sunan kasashen da suke da reshe a can ne, shine suka sanya a matsayin sunan kunguyar su".

Cikin sauri Tga ya ce "Wace kasa da wace kasa kenan?"

Ɗaukan wani ɗan karamin game Lion ya yi, irin wannan game ɗin da a ke haɗa shi da hannu, fara jujjuya game ɗin ya yi, yana kokarin haɗawa, zuba masa ido suka yi, sun ƙagu su ji amsar da zai bada, ga shi shi kuma idan ka masa magana sai ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya amsa ka.

Haka suka yi ta dakon jiran amsar shi, har sun fara fidda rai, sai can suka ji zazzakar muryarsa ya fara magana, ya kuma lumshe dara daran idanuwansa.

"*I .D. A. E. S. A* Yana nufin I. India D. Dubai S. Spain, sune kasashen da na yi bincike na gano su jiya zuwa yau, so sauran ban san ina bane" cikin sauri Tga ya ce "Amma Lion why not nu duba kasashen da suka fara da wayan nan harufan A.E.A".

Nan ma Lion ya jima kafin ya ce mu su "Ba iya sunan kasashe bane a wajen, har da sunan garuruwa, ina kyautata zaton saura ukun nan sunan garuruwa ne, ko kuma sunan wajajen da suke haɗuwa".

Shiru Tga ya yi yana tunani ko zai gano wani abin, amma sai dai ba abin da ya iya gane wa, dan bai isa ya haɗa kwakwalwarsa da ta Lion ba, a shirmen sa wai zai gwada tunano sunan garuruwa dake cikin Spain India da kuma Dubai, sai ya ga fa aikin ba ƙaramin aiki ba ne, ba zai yiwu ya iya gane ko gari goma ba, aikin na manya ne, ya jinjina wa Lion da ya iya gane wayan nan ukun ma daga daren jiya zuwa yau, kuma ba'a faɗa masa sunan kasashe bane, kawai saboda ya saba aikinne, sai ya lura da yadda a ka rubuta sunan, bai yi kama da sunan jimillan abu guda ɗaya ba, kuma basu yi kamanceceniya da abu biyu zuwa uku ba, aikin akwai rikita ƙwaƙwalwa, ya za'a yi Lion ya iya gane garuruwan da suka fara da A.E.A a cikin duniyar nan tab, ai garuran da suka fara da haka suna dayawa, taya zai iya ganewa, har ya zaƙulo garin da ya kasance eh shine suke nema, aiki ja.

Dukkan su sun ɗauki tsawon lokaci a haka suna kallon computer, ba wanda ya iya yiwa Lion wata magana.

Sai can Tga ya ce "Amma Lion ya a kayi ba su saka sunan dabar su na nan ba?"

Shiru ya yi na tsawon minti 10 kafin gently ya ce "Already manyan cikinsu mazauna nan ne, kuma nan shine maɓoyarsu, ba zasu taɓa saka sunan maɓoyarsu ba, ina da tabbacin akwai su sosai a nan, ina buƙatar kama James da kai na, ina son isa gare shi tun kafin CIA su rigani".

Kara zaro ido waje Tyrone. Tga suka yi a tare, cikin sauri har yana haɗe words Tga ya ce "Lion kana nufin CIA na neman James ne? To me ya musu?"

Shiru Lion ya yi bai sake yin magana ba, dan shi ba mai buɗe sirrinsa ga kowa bane, ko da Tga yake uncle ɗin sa kuma na hannun damar sa, baya yarda ya buɗe masa sirrinsa, sai dai idan ya gama bincike ya basu umarnin a kan su tafi aiki kawai.

Har zaman nasu ya kare kowa ya watse Lion bai sake cewa komai ba, ba haka Tga ya so ba, yaso jin da wani kungiya da wanne James ya ke yi wa aiki, sai dai ba hali, dan bai isa ya tambayi Lion ba, kuma ko bincike zai yi, ba wani abin da zai gane, dan binciken Lion na daban ne, kwakwalwar ba ɗaya ba.

Sai dai fa Tga ya shiga matsanancin tashin hankali fiye da misali, domin zuciyar sa ba zata iya jurar rashin James ba, kuma yasan a wannan hali tabbas Lion ya kama shi, to da kansa zai harbe shi.

(BABBAR MAGANA, TOH FA YAU A KE YIN TA)

Shima Lion ɗakin sa ya koma ya shige toilet dan ya zubawa kansa ruwan sanyi, ko zai samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar sa ke yi masa, har wani jiri yake gani, Bawan Allah tun jiya bai ci komai ba, ba abin da ya saka a cikinsa sai ruwa, ya dukufa bincike yana son gane in da James yake nan da lokacin kalilan.

Ni kuma tattara kayana na yi na tafi, sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu, much kauna my fans yan amana!!.🥰


💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 27-28🌹



Shima Lion ɗakin sa ya koma ya shige toilet dan ya zubawa kansa ruwan sanyi, ko zai samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar sa ke yi masa, har wani jiri yake gani, Bawan Allah tun jiya bai ci komai ba, ba abin da ya saka a cikinsa sai ruwa, ya dukufa bincike yana son gane in da James yake nan da lokacin kalilan.


Shi kuwa Michael yana can yana aikin shagwaɓa, ganin ba mai kula shi sosai a palon sai Musharraf ne, hanan yasa ya ce "John maltina nake son sha" a sukwane John ya ɗago ya kallesa, yau iskancin Michael ta kansa ya biyo, kuma idan Michael ya ce kai yake son ka kawo masa abu, tofa ba wani bodyguard da ta isa ya ɗauko masa, dan ba zai karɓa ba.

Haka ba yadda ya iya ya ajiye wayarsa tare da miƙewa tsaye ya nufi wajen tampatsa-tampatsan fridge dake cool room basu.

Jim kaɗan ya dawo hannunsa ɗauke da maltina mai sanyi tare da glass cup mai bala'i kyau.

Miƙa wa Michael ɗin yazo ya yi, kin karɓa Michael ya yi, ya wani make kafaɗa kamar yaro. Zuba masa ido John ya yi yana jiran ya ji wani iskanci kuma zai masa.

Ya jima a tsaye Michael ya ki yin magana, da dai ya ga da gaske Michael ba shi da niyar yin magana, sai ya ce "Please Michael take it now" girgiza kai Michael ya yi yana faɗin "No i can't" zaro ido John ya yi yana faɗin "Why?" "Saboda baka buɗe mini ba" John haushi kamar zai kashe shi, haka ya duƙa a wajen ya ajiye glass cup ɗin a kasa, sannan ya buɗe bakin robar maltinan ya zuba cikin cup ɗin, ya ɗago tare da miƙa masa yana faɗin "Okey ga shi nan to" sake make kafaɗa Michael ya yi, alamar baya so.

"Yanzu kuma me matsalar?" John ya tambaya yana kokarin ajiye cup ɗin a kasa, "Who ask you to put it for me inside the cup? Ni ba a cikin cup na ke buƙata ba" mamaki ya hana John magana, dan shi dai yasan gaba ɗaya yan gidan nan ba shan abu da bakin roba suke yi ba, ko ruwa sai bodyguard sun zuba musu a cup suke sha, wato yau da sabon iskanci Michael ya ke ji da shi.

John yana duƙe ya kasa miƙe wa, ganin haka yasa Michael ya saka musu kuka, daidai lokacin Tga da Tyrone suka sauƙo daga sama.

Har suna rige-rigen wajen haɗa baki, suna faɗin "Who touch our Heartbeat?" Cikin sauri John ya miƙe tare da tattare maltinan ya nufi cikin Kitchen, dan yasan Tga yanzu zai iya yi masa dukan mutuwa a kan Micheal.

Shi kuwa Michael ganin Tga yasa ya kara karfin kukan nasa, cikin sauri Tga ya kariso wajen yana tambayar me ya sa me shi.

Cikin kukan shagwaɓa ya ce "Uncle Please where is My James? Where is my blood? I missed him, i want to see his face, na ga ji".

Jin Michael ya yi zancen James ya sanya daddy juyowa yana faɗin "Michael James yana nan lafiya jiya munyi waya da shi ya cemin soon zai dawo" a sukwane Michael ya miƙe daga jikin Musharraf zuwa jikin daddy yana tambayar daddy a kan da wani number james ya kira shi. Nan daddy ya sanar masa a kan cewa da number wasu ma'aikatan da suka tafi tare ya kira shi.

Shi kuwa Tga ya san ba wani James da ya kira daddy Lion ne ya shirya wa daddy hakan, dan ya lura daddy na kokarin kashe kansa, a kan tunanin James shiyasa suka yi masa muryan James a waya, ko raɗaɗin zai ragu masa.

Haka daddy da Tga suka rinƙa bawa Michael baki a kan ya hakura James ya kusa dawowa, da kyar Michael ya yarda.

Yana yin da Michael ya shiga ya sanya Tga ya kara jin ba zai iya aminta da rashin James ba, ya zamar musu dole su dukufa wajen neman shi, idan ba haka ba, Michael zai kara birkice musu fiye da a baya.

After some hours 👌

Misalin karfe biyu na dare, duniya dukka sun yi shiru, Lion shi kaɗai zaune a palo saman table, ga kuma bodyguard suna tsaye a kansa dan zuba masa abinda zai buƙata, wayan nan bodyguard ɗin yadda kasan wayan da suke shan wani abin, kwata-kwata basa jin barci, da zarar lokacin cin abinci ya yi to fa suna wajen table tsaitsaye, suna zuba abinci, haka zali ko kwana za su yi a tsaya za su yi, matukar Lion bai zo ya ci abincin dare ba, ba su isa su je su kwanta ba, domin shine last ɗin cin abinci a gidan, haka suke hakuri su jirashi har sai ya zo ya ci, sannan suke shiga dakunan su, su kwanta, duk kuma ranar da ba zai ci abinci ba, to Michael ne zai zo ya sallame su, su wuce ɗakin su, su kwanta.

Suna nan tsaye sai karfe uku na dare sannan Lion ya miƙe ya nufi sama ba tare da ya ci komai ba, domin ya kasa cin abinci, tunanin James ya saka shi a gaba, ya sanya aikin a cikin ransa, kwakwalwar ban da tunani ba abin da yake yi, ya zafafa da yawa, domin yana son isa ga James tun kafin a riga shi, ga kuma tarin wasu aiyuka dake gabansa, ciki har da bincike a kan menene asalin damuwar Michael, me ya hassasa masa ciwon, sai dai ya fi kwallafa rai a kan binciken James.

Haka ya wuce part nasa, bakin sa har wani ɗaci yake yi mi shi, saboda wunin yau bai ci komai ba, sai uban yawan yin brush da yake yi tana kara mi shi yinwa.

Wanka ya sake yi ya shirya cikin kayan barci, riga da dogon wando, launin sky blue, sai kamshi yake zubawa ya haye saman lallausan katafaren bed nasa. Bawan Allah a maimakon ya yi barci ya huta wa ransa, sai ya jawo system da wayarsa ya fara bincike, duk idanuwansa sun yi jawur alamar barci da yinwa, amma ya hana kan shi saboda James, yana jin raɗaɗi a zuciyarsa wadda ba zai iya barci ba.

Yana kewar ɗan uwansa, sune duniyar sa, sune farincikin sa, ba shi da abin da yake gani ya ji daɗi sai su, bai san me yasa har ga Allah baya son daddyn sa ba, kuma yana kokarin sakawa zuciyar sa son daddyn nasu, amma abin yaci tira, dannewa kawai yake yi yake kula da daddy yadda ya kamata domin ya sauƙe nauyin da ya rataya masa a kansa, amma bashi da farincikin da ya fi Triplets, shiyasa baya iya hukunta su, dan da alama sune rauninsa.

A zahirin gaskiya Lion ya fi son Tga a kan daddy, yana iyaka bakin kokarinsa ya cusawa kanshi son daddy, amma ya kasa, bai san me dalili ba.

(Ni kuwa nace ai Lion shi son abu ba'a cusawa zuciya, ita ke zaɓar abin da zata so)

Rashin barcin da bai yi ba, yin hakan kuma ba karamin nasara ya samu ba, domin ya kara faɗaɗa bincikensa, a in da ya gano ba soke number James a kayi ba, sun yi amfani da kimiya ne wajen ɓoye number ta yadda duk wanda zai kira za'a sanar masa an soke number, sai dai ko da ya gane number tana nan, ba zai iya bin diddigin ta ba, saboda tana karkashin tsaro sosai, wadda dole sai ya nitsu ya musu kutse cikin tsaron su kafin ya iya samun damar laluɓo in da location na number take, kuma number bata kasance wa a kunne ko da yaushe.

Kamar yadda Bawan Allah nan ya ga rana haka ya ga dare, kun san barci idan baka samun yin shi, har wani rama yake saka ka, to shima haka ne, har wani rama yake yi, domin tun da James ya ɓace yake ta fafutuka, baya wani cin abinci sai ruwa, ga shi ba barci.

Misalin karfe 8 na safe, cikin hanzari Tga ya faɗo ɗakin Michael, sai sharara barci Michael yake abin sa, ya yi ɗai ɗai da kafafu ya baje sosai bisa lallausan bed nasa, ya wani rungumo pillow a kirjin sa, ga brown hair sannan duk ya bazu masa a fuskarsa, gwanin birgewa, yana sanye da kayan barci irin na jikin Lion wato riga da wando, sai dai kowa da kalar tasa.

Cikin zafin nama Tga ya haye gadon yana faɗin "Hey wake up, saura minti goma Lion ya fito" a razane Michael ya farka jin Lion ya kusa fitowa, zama ya yi tsakiyar gadon yana goge idanuwansa da suke cike da barci, ganin haka ya sanya Tga ɗaukan sa cak suka yi waje.

Abin da ya faru shine, tun da Michael ya fara samun sauki Lion yana ba shi horo na musamman, domin ya samu kwari, duk da cewa yana da shi a baya, amma a gaskiya na baya ba nasa bane, kwakwalwar tasa ke saka masa power a kan abu, ita ke sanya shi ya yi abu da karfin da zaka yi tunanin cewa karfin shine, amma ba nashi bane, yanzu da ciwon nasa ya fara warkewa, sauki na samuwa, sai duk wannan zafin nasa ya tafi, ya dawo real shagwaɓaɓɓe, ba shi da karfin komai, hakan yasa Lion ke bashi horo.

Saboda aiki da suka sha kan Lion, sai ya wakilta Tga a kan ya rinƙa saka Michael a gaba tun karfe 6 na safe zuwa takwas, ya rinƙa kula da shi yana yin training yadda ya kamata, har sai shi Lion ɗin ya fito, karfe takwas daidai zai rinƙa fitowa, sai ya duba me Michael ɗin ya yi.

Rana ta farko da Michael ya fara, kuka ya rinƙa yi ya ce shi ba zai iya ba, gara masa ɗaga wayan nan kananan karafuna da yake yi a baya shi da James, Lion ya ce ba zai yi wuba, ai wancan karon wasa ne, yanzu ne na gaske, dan haka dole ya yi, ya sha kuka ranar, har dare ya kasa tafiya da kafafunsa tsabar shagwaɓa wai ba zai iya takawa da kafafunsa ba, dan ya yi training na rana ɗaya, wunin ranar duk in da zai je Tga ke kai shi, haka da daddare ya zo ya baje lallausan bed ɗin Lion, yana masa kukan shagwaɓa wai kafarsa zafi.

Haka Lion ya ajiye aikin da yake yi, ya haɗa masa wani inji mai kama da robot ya rinƙa yi masa tausa.

Duk da haka washe gari Lion bai kyale shi ba, sai da ya yi training, sai kuka yake yi, to wannan kukan da yake yi ne ya sanya Tga ba zai iya jurewa ba, sai ya kyale shi yana ta barcin sa, har sai karfe takwas ta kusa, idan sun daidaici Lion ya kusa fitowa, sai Tga yazo ya tashe shi, su je wajen training ɗin, suna yin sa'a sau biyun da suka yi haka dukka Lion baya zuwa wajen yana fitane saboda aikin dake gaban sa, yau shine rana ta uku.

Tga na fita da Michael suka samu daddy a palon kasa, sai zarya yake yi, yana jiransu, da yake bakin su ɗaya dukkansu.

Kai tsaye wajen gym nasu suka wuce, a cikin gym ɗin akwai wata ɗaki, wadda yan koyo ke farawa daga can.

Kasan ɗakin wata iriyar katifar nan ne, wadda idan ka yi tsalle a kan ta zata kara wurgaka sama, kamar balo balo, kananan injuna ne a cikin ɗakin na yan koyon gym, amfanin wannan katifa shine, idan yan koyo sun faɗi kasa, zata tare musu jin ciwo, sai dai katifar tana karkashin wata na'ura wadda ana iya kunnata, idan kuma a ka kunna ta, zata rinƙa juyawa kamar fanka tana ɗaga mutun sama yana dawowa cikinta. Su kuma injunan dake wajen already a dashe suke, an dasa su ne daga kasa kafin a ɗaura wannan katifar, shiyasa ko katifar tana juyawa su ba za su motsa ba, sai dai ita ta yi ta juyowa, dan an musu kofa a jikinta yadda zata juya ba tare da sun hanata ba, kai daga ganin wajen nan kasan tsara shi a kayi, tsari ma na musamman.

Saman wani inji mai kama da keke Tga ya ɗaura Michael, saboda sabo da suka yi wajen canja saitin Injin, cikin kankanin lokaci Tga ya canza saitin zuwa tun awa biyu da suka wuce Michael ke amfani da mashin ɗin, shi kuma daddy dan ya karawa karyar tasu armashi har da wani ɗauko bottle water, ya hau sakawa Michael ruwa a faska, kamar zufar gaske.

Michael ma yanzu ya maye gurbin James a zama ɗan basaja, har da wani haki, da numfashi sama sama.

(Kai jama'a gidan daddy gidan comedy, ba kalar mutanen da ba bu)

A wannan hali John ya isko su.

"Ina ka tsaya John?" Tga ne ya jefo masa tambaya. Wucewa ya yi kamar abin haɗin baki, ya fara gyarawa Michael kafarsa yana faɗin "Naje word room duba jikin Jay ne, shine ya tsayar da ni, sai kuka yake yi uncle".

Guntun tsaki Tga ya ja, kafin ya ce "To angaya masa punishment ɗin Lion wasa ne, ya gode ma, da ya samu Lion yana tsaka da aiki, abubuwa sun sha masa kai, da ai ba a iya jinya zai tsaya ba, wata kila sai kabari, ɗan rainin wayo, lallai ma ya samu punishment mai sauki, tun da yau kwana uku da gama bashi horo har ya samu bakin kuka, ni lokacin da Lion ya bani punishment na wani laifi da na taba yi masa a baya a wajen aiki, hmmm sati biyu ban san in da kaina yake ba, duk tunanina na mutu ashe ina raye, shi ai Jay ya ma yi murna, tun da jinyar kwana uku kawai ya yi har ya samu bakin kuka".

Cikin sauri Michael ya ce "Yes Uncle T naga Lion ya mishi da sauki, kwata-kwata horo kala huɗu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login