Showing 117001 words to 120000 words out of 355604 words
na yadda yan unguwa ke faɗe, haka suka sake ji da kunnansu.
Jin haka yasa daddyn Jelly ya fara tunanin ko dai ita ma Jellyn sa abin da ya faru da ita kenan, tuna haka yasa ya ce "Zaki iya sanin inane hanyar Daular Mutuwa take?" Girgiza masa kai ta yi ala'mar a'a.
Kamar zai sake yin kuka haka ya tashi mota suka wuce zuwa gida tare da Ayla ɗin, sosai daddy'n Jelly bawan Allah ya shiga matsanancin tashin hankali, addu'a yake yi Allah yasa dai ba abin da ya faru da Jelly'n sa ba kenan, Allah yasa ba su kai ta can ba kenan.
Ko da suka koma gida, a babban palon gidan suka zauna, domin yau suke shirin kaura zuwa sabon gidan da Abbi ya saya, sai shirye-shirye maman Aunty take yi, dan ita Aunty har yanzu bata wani iya tafiya sosai.
Wayar da ya sake saya daddy'n jelly ya ciro daga aljihunsa tare da fito da hoton jelly wadda ya tura daga wayar Imran, ya nunawa Ayla hoton yana tambayar ta ko taga wannan a Daular Mutuwa, karɓar wayar ta yi tana kallon, kyakkyawar hoton Jelly, tana sanye da guntun wandon jeans iya gwiwarta, da kuma yar riga mai ƙaramin hannu launin pink color, ya rungume dollyn ta a kirjinta, sai murmushi take yi, ta saki gashin nan nata, ta yi kyau sosai.
Girgiza masa kai Ayla ta yi tana faɗin "A'a gaskiya ba'a kawo wannan Daular Mutuwa ba" wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Aunty dake ta faman kallonsu tana zaune.
"Halima ga kanwa nan mun kawo miki, ba sai na faɗa ba nasan zaki riƙe ta da amana, dan Allah ki ɗauke ta tamkar yar uwa, zamu yi bincike a kan ina iyayenta suke amma sai mun gama da case ɗin Jelly".
Da fara'a Aunty ta amsa da to, har cikin ranta kuma tana kaunar Ayla, da hannu ta mata nuni da ta zo, ba musu ta miƙe ta koma kusa da ita ta zauna, "Ya ya ne sunan ki?" Aunty ta tambaya tana kallon Irfan da yake ta fama da latsa waya.
"Sunana Ayla" maimaita sunan Aunty ta yi tare da faɗin suna mai daɗi.
"Irfan ina Aafia ne?" Sai lokacin ya ɗago ya kalli Aunty, dan baya shiga harkar ta ko kaɗan, idan kunga suna magana to wani abin ne take bukata, saboda yanzu Abbi kam sai addu'a ya dai na ko kallon in da take, ba kuma ita kaɗai ya juyawa baya ba, har da su Irfan ɗin, daddy'n Jelly da kowa da kowa, basu kawo cewa asiri aka yi masa ba, no sun bar abin ne a kan dan sun kafe masa a kan cewa Aunty ba zata aikata abin da yake tunanin nan ba, amma a zahirin gaskiya ba haka bane, asirin da Rufee ta yi masa ne ya sanya shi ya watsar da kowa da komai, sai tunanin Rufee kawai yake yi, ko ya fita company ma baya wani abu banda tunanin Rufee, ina take? Yaushe zai sake ganinta?, Aikin kenan kullun, shiyasa yanzu Irfan da daddy'n Jelly ke kula da Aunty, daddyn Jelly yana zama da ita yana bata hakuri ya yi ta tausanta, shi kuma Irfan da ta bukaci wani abin shi yake biya mata bukata, ya sawo ya kawo mata, iya shine kawai ke haɗa su, bacin haka baya shiga harkar ta, dan bai son reni, ya girmeta kusan da shekaru biyar zuwa shidda.
"A'afia tana gidan bappa babba, amma zata dawo" ya bata amsa tare da miƙewa, shima daddy'n jelly miƙewa ya yi suka nufi waje suna kara gayawa Aunty da ta shirya anjuma zasu wuce sabon gidan.
To ta bisu da shi, sannan ta kira mai aikinsu da Abbi ya kawo, a kan yazo ta shiga da Ayla ɗakin su Aafia ta je ta yi wanka ta huta, kafin a kawo mata abinci.
Cikin hanzari mai aikin ta zo ta mata jagora suka tafi zuwa bedroom na A'afia.
Sai da suka shiga Ayla ta ɗan zauna ta huta, sannan ta fara tunanin ina wayarta bari ta sake kiran yaya Ahmad dan ya taimaka ya tura mata layin Rimsha ta kirata ta gaya mata mamanta ta rasu, amma ina bata ga wayar ba.
Cikin sauri ta buɗe trolley ta fara dubawa, wasu tsadaddun kaya ne a cikin trolley, dukka kuma dogayen riguna ne masu kyau, sai hijabai da kuma mayuka da turaruka, sai wani haɗaɗen plat shoe guda ɗaya, sosai ta wargaza kayar amma bata ga wayar ba.
Kuka ta sa mara sauti mai tsuma zuciyar mai sauraro, hanya ɗaya da take da shi na yin magana da Rimsha, shikenan shima ya salwanta, idan ta tuna hakan sai ta ji zuciyarta tamkar zai fashe ya fito waje. Allah sarki wannan baiwar Allah akwai ciwo sosai a tattare da Rayuwar ta.
Mai aikin da ta mata jagora tana nuna mata ta fice daga ɗaki, dan haka bata samu damar ganin kukan da take yi ba, saman gadon su A'afia ta kwanta, tana hawaye har barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, ga kayanta a watse, ko wankar bata sami damar ta yi ba, haka ta yi barci.
A ɓangaren Rimsha kuwa.
Sai wuraren karfe 2:30 suka isa Katsina.
Suna isa ba ɓata lokaci ta tari abin hawa ta ce ya kaita unguwar farin yaro, domin kunnuwanta sun kasa mance mata da sunan unguwar, tun ranar da suka zo Katsina, ta kasa mance wa.
Ana kaita ta sallami mai mashin, sannan ta sanya wayarta a silent ta nufi cikin anguwarsu tana jan trolleyn ta, dan a bakin daidai wajen da aka tare Jehan ranar, a nan mai mashin ya sauƙeta, duk da cewa bata san anguwar sosai ba, amma tana iya kar bakin kokarin ta wajen tuna hanya.
Kasan cewar akwai face mask a fiskar ta hakan yasa jama'a wajen suke mata kallon wata ma'aikaciya, ga kuma kyakkyawar trolley a hannunta, abin ya kayatar, tana cikin hijabi har kasa.
Tun daga nesa ta hango gidan su, saboda tsabar murna ji tayi tamkar ta zura a kuje ta karisa gidan, wani farinciki na musamman ne ya dira mata a ranta, duk da tana cikin face mask amma bakinta yaki rufuwa saboda murmushi da take yi, tsantsar farincike ne a tattare da ita yau.
A hanzarce ta karisa wajen, turus ta tsaya ganin katon kwaɗo a jikin kofar, an rufe gidan, sakin trolley ɗin hannunta ta yi ta fara bubbuga kofar tana hawaye, tana surutai kamar haka ",Mummy, gwaggo, Jehan, ina kuka je? Ina kuka tafi kuka barni?". Abin gwanin ban tausayi
Yusuf ne ya hangota daga in da yake tsaye a kofar gidansu, a tunaninsa wata ce can daban, sai ya kariso wajen yana tambayar ta waye take nema.
A razane ta juya murya na rawa ta gaya masa, ga wayan da take nema, girgiza kai ya yi yana faɗin "Eyya ki yi hakuri ai sun barnan". Zaro dara-daran sleeping eyes nata ta yi har tana haɗe words wajen ce masa "Ina suka koma dan Allah, ka gaya mini, ni yarsuce".
Cikin sauri ya ce "Ke ce Rimsha wace ta ɓata?" A hanzarce ta gyaɗa masa kai alamar E ita ce.
"Allah sarki ai su mum sun sha wahala wajen neman ki, har suka godewa Allah, yanzu dai muje na kai ki wajen mamana ki zauna har yaya Sadiq ya dawo daga wajen aiki, wata kila shi yasan in da suka tafi, amma ni dai ban sani ba, domin shekaranjiya, yaya Sadiq da ya dawo da daddare yake ce mini ai su mummy sun bar nan, wlh bakina kuma ya mini nauyin na tambaye shi ina suka tafi".
Sosai Rimsha ke kuka tana tunanin ina su mummy suka tafi. Jiki a mace ta bi bayan Yusuf, ya ɗauka mata trolley ta suka wuce gidansu.
Sai kallonta yan unguwa suke yi.
Ko da suka shiga gidan, sai kallonta Amarya da su Hanan suke yi.
Kai tsaye ɗakin mamansa ya wuce da ita, kwance suka iskota saman yar katifarta.
Sallama Yusuf ya yi mata sannan suka shige ciki, da kallo ɗaya maman Sadiq ta yi wa Rimsha ta gane yar mummy ce, domin idan baku mance ba, ita Rimsha babu in da ta bar mum a kamanni, ita kuma Jehan daddy ta ɗauko.
Tarbar mutunci maman Sadiq ta yi mata sannan ta bata ruwa cikin sakin fuska.
Rimsha ta kasa shan komai, abu biyu take bukata, na farko ta ji ina su mum suke, na biyu kuma ta je a wanke mata kannan nata ya yi datti sosai, tun ranar da ta wanke a gidan su Kausar bata sake samun dama ta wanke ba.
Saboda tsabar ƙaguwa, ta kasa hakuri har sai da ta ce "Mama dan Allah ina su mummyna suke?" Cike da tausayinta ta ce "Kiyi hakuri yar nan su mummynki sun bar nan shekaranjiya, bayan an tafi da Jehan kenan".
Kara zaro idanuwanta waje ta yi, cike da matsanancin tashin hankali mara misaltuwa ta ce "Mama ina suka koma?" Ajiyar zuciya maman Sadiq ta sauke kafin ta fara magana "E gaskiya dalilai biyu ya sanya suka bar nan, na farko an tafi da Jehan mummynku tana a halin rashin lafiya, to a ranar da aka tafi da Jehan ɗin a ranar mymmyn ku ta farfaɗo, kuma anyi sa'a ta farfaɗo cikin koshin lafiyarta, jin cewa antafi da Jehan sai ta ce ba zata yarda ba, baki nan ga mahaifinku baya nan, sannan Jehan yar ɗaya ɗayan ma a ce an tafi da ita, gaskiya ba zai yiwu ba, ya zama dole Jehan ta dawo, shine suka nemi aron waya suka kira number da matar ta basu bata shiga, suka je ɗakin jinyar da matar take jinyar yar uwarta, a nan ake gaya musu cewa, ai ba yar uwarta bace, ashe wai kanwar kawarta ce ke jinya tazo duba ta, da suka tambayi kawar a ina za su ga matar, sai ta ce musu ita ma bata sani ba, domin a online suka haɗu, address ɗin da ta rubuta musu ma, ashe address ɗin gidan su wannan kawar tata ce, shine fa hankalin su mum ya yi muguwar tashi ko in ce miki hankalin mu ya tashi, muna tsaka da Wannan tashin hankali kuma bayan na dawo gida na baro su a asibiti dan ba'a sallamosu ba, da daddare wasu mutane suka shigo gidan nan, hannunsu riƙe da bindiga wai suna neman Jehan da iyayenta, ba su kira sunan Jehan ɗin kai tsaye ba, amma kwatancen da suka yi ya tabbatar da Jehan ɗin suke nema, da kyar muka sha a gidan nan, dan sunce sai mun gaya musu ko kuma su kashe mu, ga shi mu kuma ba zamu iya gaya musu cewa mummy na asibiti ba, hakan yasa Sadiq ya ce musu ai su mummy sun gudu ne sun tafi Kano, shine muka samu muka tsira, washegari da asuba Sadiq ya je asibiti ya sanar da su mummy abin da ya faru da mu, shine fa daga asibitin basu dawo nan ba, gari na yin haske ba su ma jira sallama ba, suka bar Katsina, mu dai sun ce mana neman Jehan za su je yi".
Tun da maman Sadiq ta fara magana Rimsha ke hawaye har ta kai karshen maganar, ta kasa yin shiru, tunani kawai take yi me Jehan ta yi suke nemanta, ko dai mutanen da suka kashe mata daddyn tane suka biyosu har nan.
Tana tsaka da wannan tunani bata kai karshen ba ta yanke jiki ta sulale kasa sumammiya.
(Nima kuma na tattare kayana zuwa Washington DC dan naje naga yaya baby Michael ya yi buɗa baki, sai mun dawo🛫🛬)
Misalin karfe 5 na yamma, gaba ɗayan su zaune suke a palon kasa, ban da Lion and James su ba su nan, sai Michael da Musharraf, suma suna part nasu, Uncle Herry yana zaune ga hannunsa duk bandeji, yau aka dawo da shi gida ba jima, daddy zai cigaba da ba shi kulawa, ita kuma Jennifer yan uwanta sun ɗauke ta, uncle T yana zaune yana fama da laptop, da alama wani aiki mai muhimmanci yake yi, John yana rike da wayarsa yana kallo, Jay kuma dama kunsan yana word room yana fama da jinya, daddy kuma yana kishingiɗe yana kallo.
Da kyar da kyar Michael ke sako kafarsa a benen yana saukowa palon kasa, dukkan su sun zuba masa ido, ban da John da ya kafe waya da ido, har daddy sai da ya miƙe zaune suna kallon yadda Michael ke wani irin layi kamar wadda yake cikin maye.
Bai bi da kan kowa ba, ya wuce saman sofa, ya yi bismillahi a bayyane zai zauna, daddy da Uncle T ne suka daka masa tsawa a tare suna tambayar me ya ce, ko kallon in da suke bai yi ba, bare ma su saka ran zai basu amsa, ya yi zaman sa kusa da John, yana jin cikin sa na mashi ƙugin yunwa.
"Michael na ji kamar kayi wani yare ne da zaka zauna yanzu" Tga ne ya tambaya, daddy kuma shiru ya yi yana maimaita kalmar bismillahi a zuciyarsa, domin shi ya ji abin da Michael ɗin ya ce.
"Uncle T please leave me, i don't want to talk now". Kallon daddy uncle T ya yi yaga alamar daddy fa ya lula duniyar tunani ne.
Michael kuwa yana kokarin kwanciya karaf idanuwansa suka sauka kan John, mamaki ne ya bayyana a kan fuskar sa, a zuciyarsa ya ce.
"Wai nikam me John yake yi da waya ne, kullun ba shi da aiki sai latsar waya, sai ya yi shiru a waje, ba zaka taɓa jin motsin sa ba, tamkar baya nan". Yana zancen zuci yana karewa John kallo, kara zaro idanuwansa waje ya yi ganin yadda John yake wani mammatse jikinsa. Cikin dabara ya kai hannunsa ya fusge wayar John ɗin, ya kawota sai tin fuskar sa dan ya ga me John ke kallo.
Shiru ya yi sumar zaune, gaba ɗaya palon kallon shi suke yi, suna so suji akan me ya kwace wayar John, amma ina ya kasa motsi, basu ankaraba kawai sai ganin wayar John ɗin suka yi ya faɗi kasa, alamar Michael ya sume musu awajen.
A sukwane Tga ya ajiye laptop ɗin sa, ya taso da sauri ya zo ya taɓa shi yana faɗin "Michael are you okey?" Yana taɓa shi Micheal na sake masa jiki ka faɗo jikinsa.
Jijjiga shi Tga ya fara yi sosai, tuni su daddy ma suka yo kansa, shi ma John ɗaukar wayar tasa ya yi ya yi kan Micheal ɗin, sai kiran sunan shi suke yi amma ina, sai da daddy ya ce a bashi ruwa domin Michael suma ya yi.
Kwantar da shi Tga ya yi ya damko wuyar John yana tambayar sa menene a wayar tasa da ta sanya Michael suma, John ya ji shaƙa da kyar ya iya miƙa masa wayar a kan ya duba ya gani, dan shima bai sani ba.
Tga na karɓar wayar John ya wuce da wuri ya je ya kawowa daddy ruwa dan a yayyafawa Michael.
Yana kawo ruwa daddy ya karɓa ya buɗe tare da tarfo ruwar a hannun sa, Tga na kokarin duba wayar John, bai san lokacin da daddy ya zubawa Michael ruwa ba, sai dai ganin Michael suka yi ya tashi da sauri ya diro kasa daga saman sofar, yana haki kamar wadda ya yi gudu.
Zuba masa ido suka yi har shi Tga ɗin, ya dakata da duba wayar ya koma kallon Michael, abin da ya basu mamaki shine, Michael na saukowa daga saman sofa sai ya fara ƙoƙarin cire wandon sa.
Abin da ya faru abin da ya gani a cikin wayar John ta sanya shi suma, film ɗin batsa John ke kallo wato bf, tun da yake a rayuwarsa bai san da wannan ba, shi kwata-kwata ma bai taba lura me a cikin wandonsa ba. Bawan Allah bai san komai ba saboda ciwon nan nasa, amma yau sai ga shi ya ga abu muraran ga mace ga namiji tsirara, shine ya diro kasa dan ya cire wandonsa ya duba shin shima abin da ya gani a video a tattare da namijin nan shine a wandonsa ne ko yaya.
Yau su daddy sun ga iko god, domin kuwa Michael dai ya ga abin da ya kwance masa lissafin ƙwaƙwalwarsa, cikin sauri Tga ya riƙe hannunsa yana faɗin "Michael what is wrong with you ne?". Kunsan Turawa basu da kunya ko kaɗan, a nan tsakar palo gaban kowa Michael ke son cire wandonsa dan ya duba.
"Uncle T I want check something inside my trouser". "What is This that you want to check".
Shiru ya ɗan yi kafin ya nunawa uncle T abin da ya gani da hannunsa, yana yi yana magana bawan Allah ya ce abin kato ne kamar hannusa.
Kallon daddy uncle T ya yi dan ya gane me Michael yake son dubawa, shima daddy ya gane. Allah sarki ciwon Michael bata yi masa adalci ba, domin ko abin da yake cikin wandonsa bata bari ya iya samun damar sanin menene ba, bare kuma har aje ga sauran abubuwa, ashe ba abanza shi Micheal ya fi kowa ganin mace a matsayin katon gardi ba, duk da cewa dukkan su gidan kusan haka ne, idan ban da Jay ba wani mai wani tunani a kan mace, barema Lion da James sun fi kowa yi wa mace kallon namiji, sai dai su da lafiyarsu suke yi mata kallon da ita da namiji duk ɗaya ne, kuma bata da wani amfani, tsaɓanin shi kuma Michael na shi ya haɗu da ciwo, su ko dan saboda aikin da suke yi ma ba za su so ganin mace a kusa da su ba, James yana ta'addancin ina yake da lokacin mace, shi kuma Lion a yanzu dai baya wani aiki a matsayinsa na babba, sai dai ya sanya yara su yi aiki, amma ba shi da wani feeling a kan mace, kuma hakan ya samo asaline saboda tun baya lokacin da yake aiki sosai irin horon da ya yi wa kansa kenan, a lokacin ya tsani mum ɗin su over, lokacin zuciyar yaranta, hakan yasa ya tsani mata gaba ɗaya, yanzu kuma daya girma sosai ya mallaki hankalin kansa, ya rage tsanar da ya yi wa mum ɗin, saboda a cewarsa bashi da lokacin ta yanzu, to amma saura mata kuma yariga ya faro gininsa babu su a tsarinsa, sai ginin nasa ta tafi a kan hakan kawai, har wa yau, bai