Showing 135001 words to 138000 words out of 355604 words
da ita, dama kin san Jehan akwai kyau iya kyau, wlh zaki samu kuɗi bana wasa ba" dakatawa ta yi dan jin me wacan ɗin zata ce.
Bayan ta gama ji sai ta ce "To shikenan kamar dai yadda aka saba, shabiyun dare na cika daidai zan kawo ta, amma fa kin san bata san komai ba kada ki bari su zinariya su taɓata har sai kin dawo, sai ki ɗaurata a kan hanya da kanki". Shirun minti biyu ta sake yi kafin ta kwanshe da dariya ta ce "Gaskiya na ji daɗi, amma da an kara mini wani abu a saman 1 million ɗin, kin ga fa budurwace". Dif ta ji an katse kiran ma'ana kenan ciniki ya faɗa Millon ɗaya aka sayi Jehan.
(Toh fa babbar magana🤔)
Bayan ta kammala wayar ta ajiye ta miƙe ta sauƙo Palo, yadda ta bar Jehan ɗin haka ta dawo ta sameta, shi kuma ɗan lele dama tun lokacin da ta fara waya ya fice abin shi.
Da kanta ta kawowa Jehan lafiyayyen abinci har da ruwan sha, har cikin zuciyarta Jehan tana tantama a kan wannan matar, amma da yake tana jin yunwa sai ta sauƙo ta ci abincin, bayan ta kammala Hajiyar ta nuna mata ɗaki akan ta shiga ta kwanta ta huta zuwa dare sai suje wajen aikin. Ba musu ta wuce zuwa ɗakin, ita ma Hajiya ta wuce ta koma sama abinta, ranta fes yau ta kawo mai tsoka an bata 1 million.
After some hours 👌
Karfe 12 na dare daidai motar wannan Hajiya ya fito daga gidan ta ya miƙi wani hanya, kai daga ganin irin wannan fita kasan babu gaskiya ko kaɗan a cikinta, ita kan ta Jehan sai mamaki take yi, anya ba wani abin a kasa kuwa? Kamar wasu munafukai, fita tsakiyar dare, kai ba'a kulla gaskiya a wannan lamarin ba kwata-kwata.
Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin su iso wani sihir tatcen gida cikin gidan.
(Tofa gida kuma cikin gida?🤔)
Da farko idan ka shigo gidan zaka yi tunanin normal gida ne kaman ko wani gida, sai dai ba hakan bane, ginin gaba anyi shine kamar normal gidan mutane, while daga baya kuma ta ciki aka yi wani irin tsantsarerren gida wadda kusan rabin shi a cikin kasa yake, hakan yasa ba zaka sami damar ganin wannan ginin daga ta waje ba, sannan ta bayan wannan ginin sirrin akwai wani gini shima mai kama da gidan mutane, a takaice dai gini a kayi kamar normal wadda ya kewaye wannan ginin sirrin dan kada a gane me yake ciki, idan har ba shigo da kai akayi ba, ba zaka taɓa tunanin cewa akwai wannan gini a wajen ba.
Horn ɗaya Hajiyar nan ta yi masu ganin wajen suka wangale mata tampatsetsen gate ɗin gidan.
Kutsa hancin motarta ta yi zuwa cikin gidan, a parking space nasu ta yi parking sannan ta fito tare da faɗin Jehan ta fito su tafi.
Ba musu Jehan ta fito suka kama wani ɗan hanya a wajen suka fara tafiya, ginin farko akwai wutar lantarki a wajen, haske ko ina, amma da suka ratsa cikin gidan zuwa gini na biyu sai taga wutar ginin na biyu daban dana farko, wuyar wajen green ne da kuma blue ba su da haske sosai, sannan ginin dake kewaye da wannan suna da tsawo sun kare wannan ta yadda ba wanda zai iya ganin wannan daga ta wajen.
🏬*A company of quality Prostitutes*🏬
Shine abin da Jehan tagani an rubuta a kofar shiga wajen, mamaki ne ya kara bayyana a kan fuskar ta, amma ta kasa yin magana domin bata ma san me zata ce ba.
Wani kafataren palo suka fara cin karo da shi, palon ya ji komai da ake buƙata, sai dai an yi wa palon tsari irin na office ne, idan ka ga palon zaka yi tunanin office ne, amma fa ya haɗu sosai da sosai, saman sofa suka zauna, daga gefe a cikin palon, wani kyakkyawar table ne mai ɗan girma sai kuma office chair a wajen, da alama dai wajen manager company ne.
Wani katon hoton ne ke manne a jikin bangon kusa da table ɗin ta sama, hoto ne wadda ko ba a faɗa maka ba kasan cewa wannan hoton mamallakin wajen ne, irin hamshaƙan matan nan ne, wadda Naira ta zauna musu, farace tas amma kana gani kasan farin bilicin ne, ga hancin nan nata kamar me a bage a kumatun nata, ga kofofin hancin nata a buɗe kana hango har canciki, amma a haka ta zo ta damɓara hujin hanci ta kuma saka wani katon yan kunne, abin ba kyan gani ita a dole ta yi kwalliya, a dake take saman wani haɗaɗɗen kujera irin na gidan sarautar nan, tana hakimce ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kai daga ganin wannan matar kasan ba sauƙi, dan ga shi a hoton ma fuskarta babu alamar annuri ko kaɗan, inaga kuma anzo zahiriyya? Ta ci uban make up a fuskarta, ga eyelashes da ta tabka a ido kamar bindin kaza, duk da wannan kwalliya da ta sha, hakan bai hana ka ganin muninta a filliba, mummuna ce sosai, daga gani wannan kabilace ba hausa fulani ba ce.
Ta shagala da kallon wannan hoton tana mamaki sai sinkayar Muryar hajiya ta yi tana faɗin "Jehan ta shi ku je ko" cikin sauri ta dawo da kallonta kan Hajiya, sai ta ga wata matace ke tsaye a kan su, ta shiga duniyar tunani kwata-kwata bata ga shigowar matar bama.
Matar irin Hamshaƙan tantiran yan duniyar nan ne, ta wani ci uban make up ga eyelashes ita ma a idonta kamar bindin zakara, ta ci matsu riga t-shirt da wando guntu zuwa gwiwarta, kayan sun matseta over, idanunta a buɗe garau suke, babu alamar kunya bare tsoron Allah, kai daga gani kasan bariki ya yi musu katutu, da alamama bariki ta kusa yayesu ma, amma kuma a shekaru ba zata wuci 35 years ba.
Ba musu Jehan ta miƙe ta bita, domin dama ta ƙagu ta shiga cikin gidan nan dan ta ga me suke aikatawa a cikin shi, sannan kuma aikin me zata yi. Suna shigewa cikin gida Hajiyar nan ta tashi ta fita zuwa wajen motarta, ta shiga ta bar gidan baki ɗaya ta koma gidanta.
Ita kuma wadda ta tafi da Jehan, bayan sun shiga cikin gidan, ɗakuna ne a gere a gere, a rufi ɗaya kamar hostel na student, ko wani ɗaki da number a jikin shi. Daidai tsakiyar wajen suka tsaya matar ta ce "Shekarun ki nawa?". "16 to 17 Jehan ta bata amsa.
Wucewa gaba matar ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, bin bayarta Jehan ta yi har suka je wajen wani ɗaki da aka sanya number 17 a kofar ɗakin, da hannun matar ta nuna mata ɗakin a kan ta shiga, ba musu ta buɗe kofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Ɗaki ne kamar ko wani ɗaki, sai dai kuma gadaje huɗu ne a cikin ɗakin, shiru ta yi tana kallon yan matan dake kwance a saman gadaje biyu daga ciki gadajen.
Shiru ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, kawai kallon ɗakin take yi. Kamar daga sama ta ji an taɓata ta bayan ta ana faɗin "Barka da zuwa gidan farinciki". Cikin sauri ta juyo da yake wutar ɗakin nasu green color ne baka iya ganin fuskar mutun da kyau, sai Jehan bata sami damar gane wace ce ta yi mata magana ba.
Hannunta yarinyar ta ja zuwa saman ɗaya daga cikin bed ɗin ɗakin, sannan ta miƙe ta canza musu wutar ɗakin zuwa blue light dan su samu damar ganin juna. Bayan ta kunna ta dawo ta zauna kusa da ita tana faɗin "Garama ki saki jikin ki domin ba bu wani abin da kamewa zata yi miki a nan". Ita dai ido kawai ta ke binsu da shi.
Hannu yarinyar ta sanya tana bubbuga yan mata biyu dake saman nasu gadon tana kiran sunayen su, da yake gadon nasu kusa da kusa yake da juna.
"Aisha Adiva ku ta shi ga bakuwa mun yi" miƙa Aisha ta yi kafin ta miƙe zaune tana faɗin "Sabuwar jini ce ko tsohuwa?" Duka yarinyar da ta tashe sun ta kai mata tana faɗin "Ke dai wlh Allah ya shiryeki" daidai lokacin wadda aka kira da Adiva ta farka daga barci tare da miƙewa zaune a tsakiyar gadon.
Duk da blue light da yake a cikin ɗakin bai hana Jehan gane furkar wadda ta miƙe yanzu ba, cikin sauri da ɗan karfi ta furta "Adiva me kike yi a nan? Ina daddy?" Ita ma Adiva ta gane Jehan, waro idanuwanta waje ta yi tana faɗin "Jehan ai ke zan tambaya me kike yi a nan? Ina kuma daddyna yake?".
Tofa zuba musu ido A'isha da Maryam suka yi.
Matsowa Adiva ta yi ta riƙe hannayen Jehan ɗin ta fara hawaye tana faɗin "Jehan dan Allah ki gaya mini ina daddy na yake? Tun da ya fita bai dawo ba" kankameta Jehan ta yi kafin ta ce "Adiva ki ajiye zancen su daddy yanzu, zamu yi shi daga baya, ni abin da nake son sani me wannan gida yake nufi? Ku yi mini bayani, ni a farkon shigowata naga ansanya A company of quality Prostitutes ina bukatar karin bayani a kan shi!".
Shekewa da dariya Aisha ta yi, zuba mata idanu suka yi suna kallonta, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce "Ni zan gaya miki gidan menene wannan" kasa kunne Jehan ta yi tare da tattara hankalinta izuwa ga A'isha'n dan ta ji gidan menene.
Nan fa Aisha ta fara basu bayani kamar haka.
"Company of quality Prostitutes gida ne da Hajiya kankana ke shigo da mata kala-kala kamar yadda aka shigo da ke, idan nace mata kala-kala ina nufin ko wace iriyar mace da wuya idan ba zaki sameta a nan ba, kama daga matan aure, zawara, yan mata, yara, manyan, tsofafi, ke harma da mahaukata" zaro idanu waje Jehan ta yi tana maimaika kalmar mahaukata kuma.
Dafata Aisha ta yi tana faɗin "Ki natsu zan warware maki komai a hankali, dan ni kaɗai ce a cikin ɗakin nan zan iya gaya maki asalin gidar hajiyar daɗi ko kuma hajiya kankama duk wanda kika kira dai dai ne, wayan nan da kike gani, Adiva da Maryam shekaran jiya aka kawo su, ni kuma na kai shekara ɗaya a nan, tun ina ɗakin yan 16 years, har aka dawo da ni nan wajen, so na san komai dan haka ku saurareni kawai. Hajiyar daɗi da kuke jin nan, hamshakiya ce, tana da kafa a wajaje da dama, sana'ar tane wannan harkar da kuke gani, bari na fara muku daga kan matan aure, akwai matar aure a harkar nan nata sosai, domin wasu alazawan sun fi son matan aure, saboda wani dalili nasu na kansu, mafiya yawancin matan auren da suke shiga wannan harka, yawancinsu mazansu ba mazauna bane, wasu kuma mazan su basu basu kuɗin kashe bukatun yadda ya kamata ne, wasu kuma mazansu basu biya musu bukatun su ne, shiyasa Hajiyar daɗi take janyosu a jiki ta rinƙa kashe musu kuɗi tana gyarasu sai ta rinƙa gaɗasu da manyan alazawan ana harka, amma fa kashe mu raba suke yi, ba karamin kuɗi hajiyar daɗi take samu a harkar ba...."
Jehan sarkin hanzari ta kasa tsayawa ayi mata bayani ta katse Aisha da cewa "Ya za'ayi matan aure su zauna a cikin wannan gida? To auren nasu fa ina suke kai shi? Ina suke kai mijin nasu da za su zo su zauna a nan?"
Hararar ta Aisha ta yi sannan ta ci-gaba da cewa "Ke na lura yar gaggawa ce, to yana da kyau ki koyi hakuri da juri dan zai taimaka miki, idan kika yi hakuri dukka wayan nan bayanai zan miki su, su matan aure da kike gani, Hajiya bata ajiye su a nan gidan, suna gidan mazajensu, idan mijinsu baya nan, ya yi tafiya suna kiran hajiya su gaya mata suna free, ita kuma hajiya da wani alhajin mai bukatar matar aure ya zo, zata tambaye shi irin macen da yake so, idan ya gaya mata sai ta kira irin wannan mace a waya, ke idan ma bata da irin wannan macen wlh kwana ɗaya ya yi yawa zata samo, idan ta fita taga matar aure mai irin wannan kalar haka zata bita ta fara yi mata ruwan kuɗi har ta jawo raayinta daga nan ta ɗaura ta akan hanya, sannan idan mijin mace ya kasance ba mai tafiye-tafiye bane, akwai dabarar da Hajiya take shiryawa mace idan wani alhajin na bukatarta, sai ta shirya mata karyar da zata yi wa mijinta ta fito, idan an gama komai sai ta koma gida, sannan misali yanzu idan mijin mace ya yi tafiya wani alhajin na bukatarta, tofa ba'a zuwa ɗaukarta sai cikin dare, ko kuma ita ta fito da kanta tazo wani wajen sai Hajiya ta tura a ɗaukota, yar sirri ake yin abin saboda yan kuɗaɗe kin gane ai? Kin gane na matan aure mu shiga ɓangaren yan lesbian ne ko dai kina da karin wasu tambayoyin?".
Shiru Jehan ta yi tana tunanin tabbas ta taɓa jin irin wannan case ɗin na matan aure suna zina, to amma a ina ne ta manta, yanzu ace dan mijinki baya baki kuɗi sai ki shiga saɓon Allah, sannan kuma ita Hajiyar daɗi ba zata taimaka wa mace ba sai in zata mureta ita ma?, Ai da kama ta ya yi tun da tana da kuɗi sai ta bawa matan jari ta ce su je su kama sana'a su fita har kar kuɗin mazajen nasu tun da basa basu, amma sai ta rinƙa ɗora mata a harkar banza wannan bala'i da me ya yi kama, ya zama dole na san abin yi dan gane da wannan gida, dole mu san yadda zamu rushe shi koma ta wace hanya ce.
Tayi nisa cikin tunanin da take yi Aisha ta katse mata tunani da cewa "Su kuma yan lesbian da kike gani, hajiya tana da mataimaka a online wayan da suke samo mata yara kanana, sai ta ja su a jiki tayi kamar karamar yarinya, ta ce ai tana son su da kawa ne, sai sun saki jiki, sai ta fara basu kuɗi a hankali-hankali har ta koya musu lesbian, kuma tana yin hakan ne saboda akwai manyan Hajiyoyin wayan da mazan su basa zama suna bukatar morewa ta lesbian, shine sai suce wa hajiya ta nemo musu yara yan shekara 15 zuwa 20 haka, shine aikin su Zinariya ta online suke nemo yara irin su facebook da sauransu, sai hajiya ta zubawa yaran kuɗi ta koya musu lesbian ta video a cikin wayarsu, idan suka iya sai ta haɗa su da wayan can Hajiyoyin, dukka kuma wannan abin ta waya ake yin shi, amma akwai yan lesbian da hajiya ke ɗaukowa na zahiri, ba na online ba, sannan akwai wayan da hajiya ke sayan su, kamar irin yaranda suka gudo daga gidan iyayen su idan za'a yi musu auren dole, ko kuma wayan da iyayen sun suka mutu suka gudo saboda wahalar matar baban su, ko kuma wayan da suke zuwa neman aikin yi, ko dai wayan da mahaifiyar su ta fita gida ta barsu da wahalar matan baba, idan sun gaji su gudo, kamar dai ni kin ganni gudowa na yi saboda za'a auramini ɗan kanin babana kuma bana son shi, ina shigowa Abuja wata mata ta ɗauke ni, na yi kwana uku a gidan ta sannan ta kawo ni nan ta sayarwa Hajiya, shine hajiya ta koya mini lesbian dan farkon zuwana wata hamshakiyar Hajiya ce ta ce tana son yin lesbian da ni, shiyasa hajiya ta koya mini, amma dai tana haɗa ni da mazan ma, sai dai ni bana son mazan nan nafi son mata, sunfi daɗi, kin ga Adiva tun da aka kawo su sun ki yarda da ni yarannan, har ita ma Maryam sun ki yarda, amma ban damu ba nasan dan Hajiya bata nan ne time da aka kawo su amma tana dawowa zata saita su a kan hanya, sai na cigaba da kwasan daɗi, ajiye zancen nan duk a gefe mu koma kan bayanin mu, dan ina son ki fahimci komai dan gane da gidan Company of quality Prostitutes".
Jehan ta ji abin da ya goge mata hadda yau, har wani bugawa ƙwaƙwalwar ta ya yi, wannan masifa da me ta yi kama innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kwata-kwata Aisha 17 years take da shi, amma Hajiya ta lalata mata rayuwa.
Ita kuwa ci-gaba da maganarta ta yi, ko a jikinta. "Akwai manyan masu kuɗi dake zuwa har cikin gidan nan, idan sun zo suna bukatar mace, kamar idan suna son mace yar shekara sha bakwai kamar mu, to hajiya zata zo ta tsara mana kwalliya dan su zaɓi wadda suke so, sannan Hajiya tana kai mata aikatau a kasashen ketare, wadda idan ta kai ki zata yanka miki kuɗin da zaki biya ta, kamar dai a nan ɗin ma, kin ga ni 500k ta saye ni, a lokacin ina yar kauye, idan ta saye ki 500k misali ke kuma sai kin kawo mata 5 million zuwa 10 haka idan ta kai ki aiki kasar ketare, zata biya miki jirgi da komai amma zata yanka miki makudan kuɗi shi zaki biya, idan ba haka ba ta kama iyayen ki ko kuma kanwarki idan kina da ita, wayan da take kaiwa aikatau kasar waje su sai ta san iyayensu kafin ta ɗaukesu, amma mu bata bukatar hakan, kuma jama'a da aikin kai mutane aikatau suka santa, basu san wannan harka tamun ba, da kuna shigowa ba kinga wani gida a farko ba? To shine gidan ta da kowa ya sani kuma sana'ar kai aikatau aka san tana yi a cikin gidan, ba'a san gidan nan da muke cikin ba, yauwa kada na mance akwai ma maza da suke neman maza suma akwai nasu part ɗin ɗan gaba da namu, dan kin san akwai manyan masu kuɗi dake bukatar maza yan uwansu yara dan holewa, shiyasa ma wasu zakiga basu kula matan su domin suna samun maza suna holewa, shiyasa sai kiga matan ma sun faɗa neman mazan da zasu ɗebe musu kewa, abin dai duka fifty by fifty ne....." Bata