Showing 6001 words to 9000 words out of 355604 words
motsin ɗan Adam, sai kukan wasu halittu wanda basu san menene ba ne, a daular mutuwa kuma ana basu abinci sau ɗaya a rana kuma suna ganin mutane saɓanin nan.
Suna zaune a wajen har barcin wahala da gajiya ya kama su, zaune manne da junan su sukayi barci bayin Allah, sun sha wahala, ga ba abinci, babu wajen kwana, ba wani motsin ɗan adam a wannan daji, abun ya haɗu ya cakuɗe musu.
To su Rimsha sai dai muce asuba ta gari, bari mu koma Washington DC mu gani ko zamu dace.
💞💞 WASHINGTON DC💞💞
Ya kasa motsawa daga wajen, sannan ya kasa cire fuskar sa daga kan fuskar Michael, dan ji yake kamar idan ya raba fuskar sa dana Michael zuciyar sa zata iya fasa kirjin sa ta fito waje, yaki bari ayiwa Michael sutura dan har zuchiyar sa bai yarda da cewa Michael ya mutu ba.
Duk dakiya da taurin zuciya irin na soja, sai da wayan nan jibga jibgan sojojin suka ji zuciyar su ta raunata, sai da sukaji mugun tausayin ogan su ya kama su, har wani fuskar tausayi sukayin yau.
A hankali hankali kunnen sa ta fara jiyo masa wani abun da ji yake tamkar gizone kawai kunnen sa ke masa, kara nitsuwa yayi dan ya tabbatar wa da kan sa shin abun da yake ji da gaske ne ko dai karya ne.
Tabbas gaskiyane sautin bugun zuciyar Michael ne ke fita a hankali hankali. A sukwane ya raba fuskar sa dana Michael ɗin, ya mai da kan sa sai tin kirjin Michael dan ya tabbatar da abun da yake ji, kasa kunnen sa yayi sai tin wajen bugun zuciyar Michael.
A sukwane ya ɗago yana faɗin "Call doctors for me!!" Yayi maganar da karfin gaske
Ji kake dap dap wayan nan jibga jibgan sojojin sun fita da gudun gaske dan suje su kira likita,
_shi kuma hannu yasa ya tallaɓo kan Micheal ya ɗan ɗago shi dan ya samu damar yin numfashi da kyau, dan kan sa yayi kasa sosai daman.
Kusan gaba ɗaya manya manyan likitocin dake cikin asibitin ne suka biyo bayan sojojin nan, da gudun gaske suka shigo cikin room ɗin.
Har likitoci nan suna rige rigen saka hannu, su karɓi Michael daka hannun Romeo, dan ko ba a faɗa musu ba sun san kiran da Romeo ya musu kenan.
Cikin kankanin lokaci suka dukufa aiki a kan Micheal babu kama hannun yaro, gefe guda Romeo ya koma ya tsaya yana shafa kyakkyawa dark black curly hair sa, yana cizan lallausan laɓɓan sa, tare da furzar da iska mai zafi daga bakin sa, a zuciyar sa yana yiwa ɗan uwan sa addu'ar Allah ya tashi kafaɗun sa.
Abun ka da kwararrun likitoci, ga kuma kayan aiki na zamani masu inganci, sannan ga kuɗi, dan in baka da kuɗi ko da kayan aiki ba mai kula ka.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka bawa Michael taimako sosai, ɗaya daga cikin taimakon da suka bashi shine sunyi kokarin wajen gyare wajen da yake bleeding, daman wajen kan sane ta baya kunnen sa ya fashe, sai kuma gefen cikin sa nan ma yaji ciwo sosai, wajen na bleeding.
Ba karamin daɗi sojojin nan suka ji ba, dan ko ba komai hankalin ogan su zai kwanta, idan hankalin ogan su ya kwanta, suma hankalin su zai kwanta su samu nitsuwa, sai dai abun da basu sani ba shine, ogan su fa hankalin sa ba zai kwanta ba, dan ko ya gama da case ɗin Michael akoi James a site.
Daddy kuma yana can gida yana fama da kokarin ceto rayuwar pastor, Tga John Jay duk suna gida hankalin su a matukar tashe, dan Tga ya sanar da su John abun da ya faru da Michael, sau biyu John yana suma, suna zuba masa ruwa yana farfaɗowa, kafin ya samu kan shi, saboda John yafi su Jay shakuwa da Michael, dan tare suke tsula tsiyar su a School, kuma mafi yawancin lokuta tare suke fita suje wajaje daban daban, irin su party da sauran su, shiyasa John yafi su Jay shiga tashin hankali, kuma duk wannan suma da yake yana farfaɗo dan bai yardan wa zuciyar sa Michael ya mutu bane, idan ya yardan wa zuciyar sa, kila mutuwa zai yi ma gaba ɗaya, dan son da yakewa Michael ba sone na wasa ba.
Good 3 hours doctors suka ɗauka a kan Micheal suna bashi kulawa yadda ya dace. Sai da suka tabbatar sun masa duk wani abun da ya dace, sun tabbata ya fita daga haɗari, sannan suka nemi iznin komawa office nasu daga wajen Romeo, Romeo ya basu izinin komawa kam sai dai yace likitoci uku su tsaya kusa da Michael su lura da shi sosai, kar su kuskura su fita daga room ɗin, hakan kuwa akayi, likitoci uku ne suka tsaya a kan Micheal sauran kuma suka koma bakin aikin su, kowannen su ya koma cikin office na sa.
Romeo bai bar hospital ɗin nan ba sai wajen 11 na dare, sannan ya wuce gida, amma kafin ta tafi sai da ya sanar da likitocin a kan gobe za'a mai da Michael gida wasu daga cikin likitocin su bisu gida suje suyi jinyar sa a can, dan su daman family William jacop basa zuwa asibiti, asibitin da kan ta take zuwa ta same su, ma'ana likitocin suke zuwa gida suyi jinyar su, yanzun ma Romeo bai san lokacin da aka kawo Michael hospital bane da ba zai yarda ba, sai dai ya ɗauko likitoci azo gida a kula da shi, yanzu kuma ba halin su ɗauki Michael a yau ne, saboda na'urori da aka dasa mashi, da sauran kayan aiki, dole dai su hakura sai gobe zasu samu daman ɗaukan nashi zuwa gida.
Jibga jibgan sojoji 30 Romeo ya sanya su tsaya a hospital ɗin, dan kula da Michael. Cikin ɗakin da Michael jibga jibgan sojoji 6 ne aciki dan bashi kyakkyawan tsaro, ga kuma kwararrun likitoci uku a zaune kusa da shi, abun ku da masu hannu da shuni, abun ba'a magana sai dai muce Masha Allah. Bakin kofar ɗakin kuma sojoji huɗu ne, sauran sojojin kuma suka kewaye asibiti gaba ɗaya.
Ko da Romeo ya koma gida, zaune su Tga suke gaba ɗayan su a palon kasa, bai bi ta kan kowa ba ya wuce da sauri ya nufi sama, saboda jinin Michael dake jikin rigan sa, baya son dad yaga jinin, za'a samu matsala idan ya gani.
Dad na tambayar sa ina Michael, amma bai kula dad ba, saboda bai son tsayawa har dad yaga jinin, yanzu sai ya birkice musu, shima dad ganin Romeo bai tsaya ya bashi amsa ba, sai yayi tunanin ba lafiya, dan haka sai ya miƙe da sauri ya bi bayan Romeo.
Koda ya shigo bedroom na Romeo, Romeo baya ciki, sai dai saukan ruwa dad yaji daga toilet, alamar wanka Romeo yake yi kenan, zama dad yayi a gefen gado yana jiran fitowar sa, dan yaga cikin kwayar idon sa ko zai ga wani abun.
Romeo na fitowa kallo ɗaya yayiwa dad, ya kawar da kan sa yana faɗin "My dad what are you doing here?" Tun da daddy yaji Romeo na tambayar sa me yakeyi a nan, sai yaji wani irin dan bai taɓa masa makamanciyar tambayar nan ba, daga nan yasan ba lafiya ba, a gefen shima Romeo duk sai yaji wani iri, bai san lokacin da yayiwa daddy wannan tambayar ba, ganin dad ya sa shi ya shiga ruɗune dan yasan halin dad sarai, zai tsare sane da tambayoyi, shiyasa tun bai fara yi masa tambayoyin ba shi yayi saurin tambayar me dad yake yi a nan.
Kamar wani mara gaskiya da sauri ya wuce dressing room nasa, yau ko shafa mai ɗin ma ba zai yi ba tun da dad na ɗakin, daddy kuwa ya zuba masa ido yana kallon sa yana mamakin me ya firgitar masa da lion nasa lokaci guda ne haka, duk yayi wani iri da shi, abun da dad bai taɓa ganin makamancin haka a tattare da lion ɗin ba sai yau.
Dad na zaune har lion ya gama shiri cikin kayan barci masu kyau da tsada, ya dawo cikin bedroom ɗin sai tashin fitinannen kamshi yake, sai wani ɓoye fuskar sa yake bai son suyi ido huɗu da dad, dan yasan dad akoi kaifin basira, duk da matsalar da yake da shi, yana da basirar gane abu da kallo ɗaya, suna haɗa ido zai gane lion na cikin damuwa.
"What is wrong with you my lion?" Dad ya jefo masa tambaya
Tamkar saukan aradu haka yaji tambayar dad
Juyowa yayi ya kalli dad kallo ɗaya, sannan ya kau da kan sa gefe, a nitse yace "Nothing My dad, have you noticed any change from me?"
_miƙewa dad yayi yazo kusa da shi yana faɗin "tell me the truth my lion, what is wrong with you? I knew there is something wrong with you, because I have seen some changes on your face" Ji yake kamar ya fasa ihu, saboda tsananin tashin hankali da yake ciki, tambayoyin dad suna sawa yaji tamkar ana caka masa mashi a zuciyar sa, abubuwa sun haɗe masa, bai san in da James yake ba, ga kuma Michael kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, tsananin ciwon da jikin sa ke masa ma kawai ya ishe shi, ba sai ya samu kari ba, ko ina na jikin sa ciwo yake masa, sakamakon ciwon da Michael ke ciki da kuma ɓatar James.
Jin yayi shiru ne yasa dad yace "why are you hiding something to me, I'm i not your Father?" Rungume daddy yayi yana ɓoye fuskar, dan saboda dara daran idon sa har sun canza launi, bai son daddy ya gani, "My lion please t... Bai bari dad ya kai karshen maganar ba yayi saurin rufe masa baki yana faɗin "Babu wani abun da na ɓoye maka My dad, just kawai I'm feeling headache ne" kokarin raba jikin su dad ya fara yi, dan ya samu damar ganin cikin kwayar idon lion, amma ina lion yaki yarda da hakan, dan ya rungume dad sosai, yau ga ikon Allah.
Da dai dad yaga lion bai da niyar sakin sa, sai yace "Sorry muje na baka drugs" "No dad ba sai ka bani ba, I I'll take it by myself" yayi maganar with full confidence, ta yadda dad zai yarda eh da gaske babu komai ɗin.
"Where is Michael and James, since morning banga James ba, Michael kuma tun ɗazun da yayiwa pastor wannan abun, ban sake jin motsin shi ba" har wani dum dum kirjin Romeo ya bada bugu, shi damuwan sa ɗaya, idan daddy ya san halin da James da Michael suke ciki, mawuyacin abune su ɗauke sa da rai a daren nan, zuciyar sa zata iya bugawa, dan Triplets na sa, sune duniyar sa, sune rayuwar sa, gashi ba isshesshen lafiya ke gare shi ba, ga tsufa, yana da saurin rikicewa a kan abu, abu kaɗan yake birkita shi.
"James baya nan, ya tafi Spain, Michael kuma yana white house" Romeo ya bawa dad amsa yana raba jikin su,
"Me James yaje yi Europe? Kuma why bai faɗa min ba?" Wucewa Romeo yayi, ya haye saman bed nasa yana faɗin "Ni na aiki James Spain akoi abun da zai karɓo min a can" shiru dad ya ɗan yi, kafin yace "Okey let me call his number" "No dad, no need ka kira shi, saboda yana tsaka da min aiki, idan ka kira shi za'a iya samun matsala" yayi maganar yana kokarin jawo wayar sa da system nasa, to dad yace masa tare da matsowa kusa da shi ya manna masa kiss a goshi, shima lion ɗin juyowa yayi, ya mannawa dad kiss a kumatu, daga nan sukayi sallama dad ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, zuba masa dara daran blue eyes nasa lion yayi yana kallon sa cike da so da kauna.
Har ya kai bakin kofa zai fita, sai kuma ya dakata tare da juyowa, a sukwane lion ya kawar da kallon sa gefe, dan kar dad ya zargi wani abu
"Ya kamata ka dai na cin abinci tsakiyar dare, yanzu ka sauko kaci abinci, dan naga yinwa a tattare da kai" cewar daddy, yayi maganar yana tsare lion da ido
"No dad, I'm not feeling hungry know, i can't eat food, amma kace Tga ya kawo min maltina" kamar dad zai sake yin magana, sai kuma ya fasa, dan ya lura lion ya fara ɗaure fuska sosai, saboda bai son yawan magana, surutu sa shi ciwon kai yake, wucewa kawai dad yayi, ya fice daga part ɗin ya koma palon kasa, ya sanar da Tga sakon lion, daman Tga kamar jira yake, ya matsu yaji halin da ake ciki game da mutuwar Michael, dan haka sai ya miƙe da sauri ya nufi sama, dan akoi drinks kala kala shaƙe da katuwar freezer a palon lion,
A ɓangaren lion kuwa, dad na fita ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tare da jawo system nasa ya fara bincike a kan ɓatar James, tunani yake, ko dai ya shirya ya tafi Spain ɗin yaje yayi bincike da kyau a can ne, dan gaba ɗaya binciken online ɗin nan bata masa yadda yake buƙata.
Baki ɗauke da excuse Tga ya shigo cikin bedroom ɗin, hannun sa ɗauke da plate mai ɗauke da maltina mai sanyi da kyakkyawan glass cup, mai kyau da tsada. Saman bedside drawer ya ɗaura plate ɗin, sanna ya zauna gefen lion yana faɗin "Good evening sir" shiru Romeo ya ɗan yi, kamar ba zai amsa ba, almost 3mins, sannan ya ɗago ya dubi Tga, kallo ɗaya ya kawar da kan sa gefe, gently in a cool voice yace "what is wrong with you uncle T?" Kamar jira Tga yake a masa magana, cike da damuwa yace "lion what about Michael?" Yayi maganar hawayen na kokarin zubowa daga idon sa, Allah sarki yana son jin ya su lion sukayi da gawar Michael, dan lion ya hana su zuwa asibitin, yace su zauna a gida, dan kar daddy yayi zargi wani abu.
"calm down micheal is not death he's alive" Duk rashin murmushi irin na Tga, yau bai san lokacin da ya saki cool murmushi ba, har hakwaran sa suka bayyana, ga kuma ido cike da kwalla, ga murmushi. Saboda daɗi bai san lokacin daya rungume Romeo yana ta murmushi kamar bakin sa ba zai rufuba.
Gyaran murya Romeo ya masa, wadda ya sanya shi raba jikin sa dana Romeo da sauri, da hannu Romeo ya masa nuni da hanyar fita daga ɗakin ba tare da yayi magana ba,Tga bai wani damu ba, dan ya lura aiki Romeo yake, ba dan aiki yake ba, ba zai ce ya fita masa a ɗaki ba, dan wani lokaci a ɗakin suke wuni, shi murnan Michael na raye ma ya wanke masa komai dake zuciyar sa, cikin sauri ya miƙe ya fice daga ɗakin, dan yaje ya sanar da su John Michael na raye, dama kuma shi John tun da yaji labarin mutuwar Micheal ɗin, bayan ya gama suman sa, sai ya dawo yana ta musu sambatu Michael bai mutu ba, Michael bai mutu ba.
Tga na fita Romeo ya ci-gaba da aikin dake gaban sa, dan neman mafita a kan case ɗin James. Sai ƙarfe huɗu na dare sannan ya kwanta, ya samu barcin wahala ta ɗauke sa, zuciyar sa cike da tunani kala kala a kan yan uwansa.
To kafin lion ya farka bari mu leƙo Jehan ɗin gwaggo mu gani me take ciki ne.
💞💞KATSINA STATE NIGERIA💞💞
Super restaurant
Tun karfe 7 Jehan taje wajen aiki, kamar kullun wajen serving abinci ta wuce abun ta, suna tsaƙa da aiki, sukaji diran motoncin a cikin restaurant ɗin, ko a jikin ta, ta ci-gaba da aikin da take dan daman ba ta shiga harkan kowa, kuma ko menene zai shigo cikin restaurant ɗin in dai ba ya biyo ta kan aikin taba, to bata kula shi.
Tana faman sakawa wasu costumers abinci, ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen tazo wajen ta tana faɗin "Jehan oga Ibraheem yace ki bar duk abun da kike, ki kaiwa su yarima abinci, yau har da dr Nawid suka zo" tana magana tana washe baki. Ko kallon in da take Jehan ba tayi ba, bare ta sa ran zata mata magana, dama kuma kowa ya san da wannan hali na Jehan, na rashin tanka magana idan aka mata, wucewa ma'aikaciyar tayi ta koma bakin nata aiki.
Shi kuma Ibraheem duk lokacin da manyan baki suka zo, yafi son ya aika Jehan, dan tafi kowa kyau a wajen, sai dai kuma tafi kowa miskilanci, da shariya, gashi idan tana wani aiki kasa ta wani tofa ba zata kula kaba bare kuma kasa ran zata maka wannan aikin da kace, haka take, yanzun ma haka ne, su yarima suna can suna jiran abinci Jehan na aikin gaban ta, taki ta kula su.
Tsab ta gama shiryawa costumers ɗin farko da suka riga zuwa abinci saman trey, sannan ta ɗauka ta fito wajen, daidai lokacin ɗaya daga cikin bodyguard na yarima yake yiwa Ibraheem faɗa a kan ya zai bar yarima zaune ba su kawo masa abinci ba, Jehan kam ko a jikin ta tazo zata wuce su, tsawa Ibraheem ya daka mata, "Ke Jehan ina abincin dana ce ki shiryawa yarima?" irin wannan abun da ake cewa burgagi shine Ibraheem yayi, dan yaga idon su yarima, ya daka mata tsawar amma zuciyar sa na dukan uku uku saboda tsoron amsar da Jehan zata bashi, dan yasan ba karamin aikin ta bane ta tsinka shi cikin jama'a. Sai dai kuma yayi sa'a ko kallon in da yake ba tayi ba tare yasa ran zata tanka mashi, tayi wucewar ta, ta nufi wasu ma'aurata biyu dake zaune saman table ɗin cin abincin suna jiran ta.
A fusace bodyguard da yake yiwa Ibraheem magana ya daka mata tsawa, "Ke ba da ke ake magana bane?!!" Kamar da ita ce sukayi magana ba Jehan ba, tayi wuce warta kamar kurma, daman ita Jehan maganar nata ma zuwa zuwa ne, idan ta ga dama in ka mata magana zata amsa, idan kuma bata ga dama ba, sai ka shekara kana magana bata san kana yi ba.
Ganin ta raina musu wayo ne yasa bodyguard