Showing 342001 words to 345000 words out of 355604 words

Chapter 115 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2834

ji daɗi da Lion ya ce Rimsha ta zama ƴar aikinsa daga yau, amma bai ji daɗin raba uba da ƴa da ya yi ba, bai kyauta ba suna tsaka da kewar juna na tsawon watanni, yau da suka haɗu kuma ya zo ya raba su, abin ya ɓatawa Areef rai.

Shi kuma Imran cikin sanyin murya ya ce "Saif it's my uncle, pls stop telling him that, please and please, evan for the sake of me" ya yi maganar tamkar zai yi kuka, domin abin ya taɓa mashi zuciya sosai, ganin daddyn Rimsha yake yi tamkar Abbansa, kuma ya ji zafin rabasu da Lion ɗin ya yi shi da Rimshan.

Shiru Lion ya yi har kamar ba zai sake magana ba. Sun kwashe tsawon good five minutes a tsaye a wajen, sai kuka Rimsha ta ke yi, shi kuma daddy yana kankame da ita a kirjinsa.

Har sun fidda ran zai sake yin magana, sai kuma suka ji sexy voice nasa can kasa-kasa ya ce "I dnt care even if it's your father not your uncle, am done talking". Tashin hankali, zaro ido waje Imran ya yi ya rasa bakin magana, shi kan shi daddy raba jikinsa da tata ya yi yana kallon fuskar ta, taci kuka har ta godewa Allah, duk idanun nata sun kunbura luhu-lugu, har wani ja kasar idanuwan nata suka yi, saboda kukan da ta sha, shi kuma Lion juyawa ya yi ya koma bedroom nasa.

Areef kuwa girgiza kai kawai yake yi domin dama yasan in dai Lion na waje ka gwada izza a wajen to ba makawa sai ya saka ka kuka, a tsarinsa koma a ina koma waye shi ne sarki, ba'a isa a nuna isa a kusa da shi ba Musharraf ya yi kuskure.

Mark kuwa cewa daddy ya yi ya wuce su koma airport kada Lion ya sake fitowa.

Juyawa daddy ya yi a yaune yake dana sanin sanin su Lion da ya yi a rayuwarsa, cikin kunan rai tare da raunin zuciya ya ce "Imran ga amanar Rimsha, sannan a yau saboda Rimsha zan gaya maka cewa ni ne Hosain, na san kasan labarin kanin Abbanka Hosain, to ni ne, na gaya maka hakan ne kuma domin ka kula da Rimsha kanwar ka ce, kada ka bari komai ya same ta, sannan kuma kada ka gayawa su Yaya babba cewa Rimsha ƴata ce, kada ma ka gaya masu ka ganni, akwai dalili yin haka, sai Allah ya kaddara saduwarmu ko idan kun zo in da nake zan gaya maka komai, yanzu dai gata nan ka kula mani da ita". Ya kai karshen maganar tare da juyawa wajen Areef, shima ya bashi amarnar Rimsha sannan ya wuce zuciyarsa cike da tunanin ya Rimsha zata rayu a cikin shegun kafuran sojojin nan, ga shi Lion ya ce Za'a karo wasu sojojin, ya san halinsu sarai basu da imani, da tsawa kawai za su sanya Rimsha mutuwa ba tare da ta shirya ba, ga shi basu ɗauki zina kamar wata laifi ba ce, amma kuma kasan cewar tana hannun Areef da Imran yasa ya ɗan sami kwanciyar hankali tare da kwarin gwiwa akan da izinin Allah babu abin da zai same ta, sai dai kuma yana jin bugun zuciya idan ya tuna cewa ƴar aiki Rimsha zata zama, yasan babu wanda ya isa ya canzata a wannan ƴar aiki da Lion ya kira ta da shi, sai shi Lion ɗin da kansa, kuma yasan aiki a karkashin waƴan nan masu taurin zuciya ba karamin abu bane, Allah nema kaɗai yasan irin aikin da zata yi wa su Mark kuma, Allah dai ya sa ba barinta da wankin kayan aikinsu masu hangen bala'in tauri da takalmarsu za'ayi ba. Sai tunani kala kala Musharraf yake yi har suka fita.

Ita ma Rimsha kuka take yi kamar ranta zai fita, rungumeta Areef ya yi yana rarrashinta, tana ji tana gani daddy ya wuce ya fita, da sauri Imran ya bi bayansa dan ya raka shi waje, sai dai fa duk jikin Imran ya mutu jin cewa Daddyn Rimsha shine Hosain kanin mahaifinsu, lokaci guda Imran ya ji cewa lallai yana son sanin ainahin tarinhin abin da ya raba kan wannan family har haka, me ya rabasu kenan, wannan gaba na tun ba'a san za su zo duniya ba, sun rarrabu kashi kashi ta yadda yanzu ƴaƴansu sun ta so amma basu san cewa iyayensu bane, kenan bayan daddy ma akwai wani ne ko kuma yaya, shin su nawa ne ma a wajen iyayen nasu, ina Hassan ɗin Hosain ɗin yake?. Wannan shine tambayoyi da Imran yake yi wa kansa da kansa, wadda kuma ba wanda zai iya ba shi wannan amsa sai Abbansa, domin shi ne yaya babba a cikin su Abbin gaba ɗaya, yasan komai kenan.

Allah sarki Areef sai fama da rartashin ta yake yi, yau Rimsha ta ci kuka kamar ba zata rayu ba, har wani sarkewa numfashinta yake yi, gata ga daddynta amma an sake rabasu, ita ba ƴar aikin Lion da zata zama bane ma ya dameta, duk da ta san cewa yi wa Lion aiki babbar bala'i ce domin sai mai dakiyar zuciya irin sojojin nasa za su iya, amma dai duk da haka abin bai taɓa ta sosai ba kamar yadda rabata da daddy ya taɓata. Allah sarki sai kokarin Areef yake yi da ita akan kada ta suma.

Daga karshe ma zazzaɓi ne mai zafi ya rufeta kwance a jikin Areef ɗin, kafin Imran ya dawo jikinta ya yi zafi jau kamar wuta, da yake tana kwance a jikin Areef ɗin sai bai ji zafin da jikin nata ya yi ba, har sai da Imran ya dawo yana ƙoƙarin ɗagata daga jikin Areef ɗin dan ciwon dake jikinsa kada ta fama mashi, a nan ne ya ji jikin nata ya yi zafi kamar wuta.

"Subhanallah Rimsha lafiya, zazzaɓi ne fa a jikinki". Shine abin da Imran ya faɗa bayan ya ɗago ta. Yunkurawa Areef ya yi wadda gaba ɗaya jikinsa ta yi la'asar saboda raba uba da ƴa da Lion ya yi, tsawon watanni ba su tare wannan wace iriyar bakar zuciya ce a kirjin Lion? Shine tambayar da Areef ya yi wa kansa, mutun yana ji yana gani ya raba uba da ƴa suna kuka dukkansu amma ko kaɗan Lion bai ji wani alamar tausayi ba bare ya tausaya masu, tamkar ma ba shi ya yi hakan ba.

Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.........

💖💖TRIPLETS💖💖




E91-92💖


Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.

Ɗagowa Areef ya yi ya kalli Imran ɗin kafin ya ce "Take her to hospital, ni ba zan iya dubata yanzu ba, because gaba ɗaya am very weak". Jinjina mashi kai Imran ya yi sannan ya saɓe ta a kafaɗarsa ya nufi waje da ita, shi kuma Areef ya koma ya zauna a saman sofa yana sauke numfashi a hankali.

Abin mamaki kuma abin al'ajabi shi ne da Imran ya zo fita gidan gateman ya hana shi fita, mamaki ne sosai ya kama shi tare da tambayar gateman ɗin akan me zai hana shi fita, cikin girmamawa ya ce "Am sorry sir oga ya ce kada na kara barin wani ya shiga ko kuma ya fita gidan nan ba tare da izinin sa ba, ko da kuwa kune". Imran ya gane matsalar wato yau ran Lion ya ɓaci, ba rashin lafiya ba ko mutuwa Rimsha zata yi sai dai ta mutu, dan mugunta da ganganma ya hana a fita da ita saboda yau babanta ya yi maga da izza kuma yana wajen, shine zai sauƙe akan ƴarsa kenan, Babbar magana.

Shiru Imran ya ɗan tsaya kafin ya juya kan motar ya dawo cikin gidan, haka ya sake ɗaukarta suka koma ciki domin yasan tun da Lion ya ce haka to fa ko Areef a wannan karon sai dai ya ce da Rimsha ta yi hakuri, amma babu wanda ya isa ya canza wannan magana daga ba za su fita daga gidan ba, lallai Lion ya shirya mugunta kenan.

A palon sama ya isko Areef a nan kuma ya gaya mashi abin da Lion ya ce, Areef bai yi mamaki ba domin kuwa ya san tun da suka yi haka da Musharraf tofa sai dai addu'a dan tabbas Musharraf ya ɗan ɓata mashi rai gaskiya ita kuma Rimsha sai dai suce Allah ya kwaceta daga hannunsa kawai, amma dai zata ci bakar wahala ba ɗan kaɗan ba.

Haka Areef ya daure ya ce da Imran ya ɗauko mashi A box a ɗaki bari ya duba ta, dama kunsan jami'ai irin haka ba su rasa iya wani sashe na aiki a ɓangaren lafiya domin kula da kansu idan bullet ya taɓa su ko makamancin hakan, to shima Areef hakan ne ya iya aikin likita duk da ba sosai bane.

Ɗakin Rimshan suka wuce, a nan Areef ya dubata tare da yi mata alluran zazzaɓi, amma fa sun sha dirama kafin ayi wannan aluran, sai da Imran yasa karfi ya danneta kafin nan Areef ya samu ya danna alluran ya yi mata, cikin alluran da ya yi matan kuma har da na barci domin ta ɗan samu ta huta wata kila idan ta tashi ƙwaƙwalwarta ta ɗan yi fresh.

A haka suka barota a cikin ɗakin tana barci suka koma palo suka zauna, sosai suka nutsa a duniyar hira a tsakaninsu, duk wannan abin da suke yi Lion yana jinsu domin ai a palon saman suke.

A ɓangaren gidan Abbi kuwa, bayan sun koma gida da suka yi sallar mangariba suka ci abinci ne suka wuce ɗakinsu while ita kuma Akila Akil ya zo ya ɗauketa ya mai da ita gida, yanzu ya rage daga Jelly sai Hanan, su biyu ne kawai a cikin ɗakin.

Yau wani irin wanka na musamman aunty ta ci, sai tariyo kalaman Akila a cikin ƙwaƙwalwarta take yi, wata magana da Akila ta sake gayawa Jelly safiyar yau ne ya tsaya mata a ranta, maganar kuma ba wata bace fa ce cewa da ta yi, ba sai kin tambayi mijinki wani irin dressing yake so ki rinƙa yi mashi ba, a cikin kayan da yake saya maki a nan zaki gane, idan ke amarya ce ki duba cikin kayan lefenki ki gani, abin da ya fi so shi zai saya maki dayawa, idan kuma kun jima da shi to zaki ga idan kun je sayan kaya zai yi ta cewa ki ɗauki kaza ki ɗauki kaza, to wani abin ba sai kin tambaye shi ba, da kansa zaki ga ya fi damuwa da saya maki irin shi dan yana so. Wannan magana ta tsayawa aunty a rai domin kuwa Abbi ya zu ba mata riga da wando masu shegen kyau sosai a cikin lefenta, a cikima ta ɗauki ɗaya daren jiya ta bawa Jelly, kenan Abbi yana son a rinƙa yi mashi dressing na riga da wando? Sannan ga uban wasu shegun kayan barci daya zuba mata wadda a kalla za su iya kai kala 20 saboda yawa, kenan shima Abbi yana so a rinƙa sanya mashi? Tabbas Akila ta faɗi gaskiya ko kala ne miji yake so zaki ga idan zaku sayi abu zai rinƙa ce maki ki ɗauki kalar can tafi kyau kuma zata yi maki kyau, bawai dan zata yi maki kyau ɗin bane, aa shi dai ya fi son ganinki da wannan kalar ne, amma sai kaga wasu mata dan ya ce ga kalar da zata yi maki kyau sai ta ce a'a ba zai yi mata kyau ba, aa ya yi haske sosai ko kuma ya yi duhu ko dai ya yi kalar fatar ta, complain dai kala kala idan bata son kalar abin da ya zaɓa mata ɗin, dama ba dan ya yi maki ke kyau ba yasa ya ce ki ɗauka, shi ne dai kalar da ya fi so, to dan haka sai mu lura.

Wasu shegun kayan barci Aunty ta ɗauko wadda kusan da su da babu duk ɗaya ne, haka ta sanya a jikinta kuma ta bi shawarar Akila bata sanya bra ba, ta sake su abinta, sai tashi wani fitinannen kamshi take yi, lokacin da ta shirya Abbi yana ɗakinsa baya nan, hakan yasa ta ɗauki wayarta tare da sanya hijabi ta fito zuwa ɗakin nasa, a lokacin ita kuma Ommu tana can tana saƙa ta yadda zata karɓi 10 million a hannun Akil ta hanyar Umaisha.

Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin Abbin, baya ɗakin yana toilet yana wanka, cire hijabin jikinta ta yi ta ajiye tare da nufar gaban mirror tana kara feshe jikinta da wasu kalar perfume ɗin nasa.

A haka ya fito ya sameta, bayan ta ya fara kallo, da farko ma ya zaci Ommu ce domin sirantar ko ace yanayin jikinsu kusan ɗaya, sai da ya ga tsawon da kuma tudun bayan ne ya fahimci ba Ommu bace, gabaɗaya kunya ta kama Aunty, bata saba ba, ta kasa juyowa su yi ido biyu da Abbin, har wani yarrrr jikinta yake yi saboda kunya.

Shi kuma Abbi ya tsare ta da ido sosai yana kare mata kallo daga sama har kasa, ta yi kyau iya kyau kuma ta tafi da imaninsa fiye da Ommu, domin dama babu haɗi ta fi Ommu komai, kawai rashin ɗaukar wankar shegun dressing da bata yi ne yasa ake mata kallon kamar ba komai ɗin.

Ta kasa juyowa shi kuma Abbi ya kasa cire idanunsa daga kanta, da dai taga ba zai daina kallonta ba kuma yaki karisowa cikin ɗakin yana tsaye a bakin kofar toilet, sai ta hakura ta juyo a hankali tare da fara kallon kasa ta ki haɗa ido da shi.

Ya ilahi ya lalliahi ai kuwa ashe bai ga komai ta baya ba sai da ta juyo ta gaba, cikin sauri ya kariso wajen da take tare da rungumarta a jikinsa, wani nauyayyar ajiyar zuciya suka sauƙe a tare, tunani ta fara yi kenan gaskiyar Akila? Lallai kam to ita ina zata iya irin waƴan nan dressing da Ommu ke yi, ai sai yara ita kunya ba zai barta ba.

Tana can tana tunani shi kuwa Abbi yana sabgar gabansa dama daga shi sai towel.... na haɗa kayana zuwa wajen daddyn Jelly dan na basu waje.

Sai lallaɓa Aylarsa yake yi suna kwance saman bed nasa tana kwance a saman kirjinsa, amma fa sai da aka yi wa Jelly dabara na cewa Ayla zata kwana da Ommu ne sannan ta yarda da rashin Ayla a ɗakinsu, ba dan haka ba, ba zata taɓa yarda Ayla ta kwana da daddynta ba, duk da an ce mata kanwar mummynta ne, amma ta yi mugun raina Ayla ɗin sosai, kuma da farko ma taki yarda ta kwana da Hanan, ta kafe sai da daddy zata kwana, sai da Abbi ya yi mata dabara tare da lallaɓata sannan ta yarda su kwana da Hanan ɗin.

"Babyn daddy daddynki yana cikin wani hali, zaki iya taimaka Mashi?" Ya tambaya yana shafa bayanta. Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "Daddy sosaima, zan taimaka maka".

Ajiyar zuciya ya sauke har ga Allah ba zai iya jure sati guda da Dr ta ce ba, yau kwana uku ma ji yake yi kamar zai mutu saboda azababben sha'awarta dake damunsa, to ina ga an cika sati, ai sai dai a kwashe shi sai asibiti kawai.

"Baby kanki nake so ki bani kin ji ko?" Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa. Da yake bata san me hakan yake nufi ba sai ta ce "To daddy na baka ai".

Kara matseta sosai ya yi a jikinsa, Baiwar Allah bata gama samun sauƙi ba amma yana ƙoƙarin sake tsunduma ta cikin wani yanayin kuma.

Juyawa da ita ya yi izuwa saman bed ɗin ya yi mata rumfa da kirjinsa, nan take ya fara murzanta son ranshi, a wannan karonma ta ci bakar wahala a hannunsa, ta yi kuka kamar mene ne, amma dai Allah ya takaita ba suma, bata suma ba, sai dai fa ta wahala zallar madarar wahala, sai nishi take yi tana kuka kasa kasa da kyar da kyar, kuka kuma mai taɓa zuciya, Daddynta yana neman kasheta shi da kansa.

Shi kuwa sai aikin rarrashi yake yi, duk ya birkice mata kamar ba shi ba, amma kuma ya kwashi daɗi iya son ransa, yau nema ya san ya kwanta da ita, ranar farko bakar wahala shima yasa saboda......

Da kansa ya yi mata wanka kamar dai yadda ya saba yi mata, magungunarta ya ɗebo ya bata ta sha sannan suka kwanta bayan shima ya yi wankar kenan, rungumota sosai ya yi a jikinsa kamar na ce zan kwace mashi ita, da haka barci ya yi awon gana da su sai sauke ajiyar zuciya irin na wadda yaci kuka ta ƙoshi take yi.

A ɓangaren Akila kuwa, yau ma dai masoyin ɓoye ya hanata yin waya da Irfan, idan Irfan ya kira sai ya ji wayar a kashe yayin da shi kuma masoyin ɓoyen sai misalin karfe 10 ya kirata a waya.

Gaba ɗaya ta mance da abin da ya faru jiya a gidan Abbi, ta mance ya ce mata shi ba mutun bane, hakan yasa ta ɗauki kiran tasa cikin zumuɗi.

Sallama ta yi mashi kamar ko da yaushe, cikin fara'a ya amsa mata sallamar tata tare da yi mata barka da dare, bakinta ya ki rufuwa saboda murmushi ta amsa mashi da lafiya Lou fatan shima haka ne?.

Ya ɗan yi shiru kafin ya amsa mata da lafiya Lou Alhamdulila ina su Akil da kuma ango Imran, ta sha mamakin jin wannan tambayar tasa, amma sai bata yi gigin tambayarsa a ina ya san cewa Imran ya yi aure ba, kawai sai ta ce mashi suna nan lafiya lou.

"Heartbeat ɗin heartbeat ɗinta me ya same ki? Yau na ji gabaɗaya kin sauya". Cikin shagwaɓa ta ce "Kai ne mana". Da sauri ya ce "Subhanallah ni kuma my heartbeat?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e shi ɗin dai.

"Heartbeat me na yi maki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login