Showing 18001 words to 21000 words out of 355604 words
jini yake.
Riƙe hannayen ta Rimsha tayi tana faɗin "Kiyi hakuri Kausar, ki dai na sosawa kinji? Kinga idan kika sosa wajen yana yin jini" rungume Rimsha tayi tana mutsu mutsu, saboda azaban zafin da yake mata "Meesha dan Allah ki barni na sosa kinji? Wlh zafi yake min, ga kuma bala'i kai-kayi" tayi maganar dakyar saboda kukan da take, rungume ta Rismha ma tayi tana ɗan shafa mata bayan nata a hankali tana faɗin "A'a Kausar kiyi hakuri ki daure kinji" kankame Rimsha tayi tana jin zogin har cikin ranta, yarinya abun tausayi, wayan nan mugayen abu duk sun kunbure mata baya.
Sun jima tsaye a wajen Rimsha na shafa mata bayan nata tana mata addu'a tana tofa mata, da kyar suka samu raɗaɗin ya lafa.
Sakin Kausar ɗin Rimsha tayi ta nufi riga da zanin Kausar da ta cire yake jefe, ta ɗauko ta karkaɗe mata su sosai, sannan ta dawo ta riƙo hannun ta tana faɗin "Kiyi hakuri kinji" shiru kausar tayi ta kasa magana saboda azaba, hannun juna suka riƙe suka ɗan matsa daga wajen bishiyar.
Can ɗan gefe suka tsaya, Rismha ta sanya mata rigan ta, sai dai bata ja mata zip ba, saboda bayan nata ya samu iska, haka ta ɗaura mata zanin ta, tana ta yi mata sannu, daman Kausar akoi ta da saurin kuka, kuma idan tayi kukan duk sai idon ta yayi luhu luhu kamar panke. Haka suka daure suka ci-gaba da tafiya suna hira,
In da sukayi kuskure wajen tafiyar nasu, tun da suka miƙi hanya ɗaya wato yamma basu ɗauki wani kwana ba, tafiya kawai suke a miƙe abun su, kuma suna sa ran ganin gari tab lallai, yau tsawon kwana uku suna wannan tafiya, amma ko alamar gari basu gani ba, sai ma kara nutsawa suke cikin daji mai girma da faɗin da basu iya ganin karshen sa, basu san ina suka nufa ba, shin ta gabas suke tafiya ne ko ta yamma, basu san ta ka mammen a wani kasa ma suke ba, su dai kawai tafiya suke suna burin fita cikin wannan bakin dajin, Allah ma ya tsare suna addu'a sosai, tun da suka fara tafiya basu haɗu da wani mugun abuba, haka idan sun tashi yin Sallah basu san gabas ba, kawai in da sukaga ya dace tanan suke kallo a matsayin gabas suyi Sallah.
Maraice ya fara shiga, irin bayan la'asar ɗin nan, rana yayi sanyi, tafiya suke suna hira da dariya, ita dai Kausar daurewa kawai take, tana biyewa Rimsha suna hira, amma harga Allah tana jin zafin jikin ta sosai, ga bayan nata sai kaya ɓaro ɓaro cizon cinnakun yake.
kasan wani katon bishiyar ɓaure mai cike da koren ganyen damuna, a nan suka zauna Kausar na tsokanan Rimsha wai har ta fara yin fresh, dajin nan ya karɓe su, ko dai suyi zaman sune kawai, sun zama yan daji, hararar wasa Rimsha tayi mata tare da ɗaukan wani ɗan karamin sanda, ta ɓare ɓawon jikin sa tas, sannan ta ta fara zanen fuskar GAR a jikin wannan bishiyar ɓauren, kasan cewar lokacin damuna ne, jikin bishiyar akoi taushi sosai, hakan ya bata daman zana katon fuskar GAR, zanen kuma ya fita sosai, kamar ka kira shi ya amsa, yayin da Rimsha ke zana shi ta wannan ɓangare ita kuma kausar tana zana shi ta ɗayan ɓangaren.
Sas suka zane jikin bishiyar nan da fuskar lion masoyin Rimsha, su dukkan su sai murmushi suke kamar wasu taɓɓaɓu, ita dai Kausar ba laifin ta bane, Rimsha ta koya mata, ance zama da maɗaukin kanwa shike kawo farin kai, ita kuma Rimsha laifin zuchiyar tane.
Har ta kai ta kawo, duk in da suka zauna karkashin wata bishiya, sai sun zana fuskar GAR a jikin wannan bishiyar kamar ba lafiya ba, wani lokaci ma ba zama zasu yi a kasan bishiyar ba, kawai zanen suke yi su wuce idan bishiyar ta musu kyau.
Sai da suka ga yamma na daɗa yi sosai sannan suka miƙe suna murmushi kamar ba lafiya ba, suka ci-gaba da tafiya suna hira.
Sunzo zasu wuce wata bishiyar kashu, Kausar ta tsaya tana tsinko kashu dake ta kasa kasan bishiyar, kasan cewar bishiyar tana da manyan rassa da sukayi kasa, ita kuwa Rimsha ta tsaya daga gefe tana bin dajin da kallo, dan bata jin yinwa, kuma ita bata cika cin abinci sosai ba, sai su wuni sau ɗaya zataci fruits, sai aukin shan ruwa.
Kamar a mafarki Rimsha ta hango wani yaro, wadda ba zai wuci shekara biyu ba, yana zaune kusa da wata bishiya, da sauri ta karisa wajen tana mamaki
Ɗaga kan ta tayi tana kallon yadda garin yayi, yamma yayi, to me ya kawo wannan yaron kuma nan? Ta tambayi kan ta, bata gama tunanin da take ba, taga wani zabgegen maciji mai kan faranti yana tunkaro yaron, a sukwane ta ɗauke yaron tana faɗin "Kausar ki bar ɗaukan kashu ɗin nan mu gudu maciji" Jin maciji yasa kausar tayi watsi da kashun dake hannun ta suka fara gudu.
Sanadiyar wannan maciji, da wanann yaro, yasa suka canza akalar hanyar da suke tafiya a kanta da suka juya suka gudu ta gefe, saboda tashin hankali da razana da suka shiga.
Sunyi gudu sosai, kamar ba zasu tsaya ba, sai sukaji daga can bayan su da karfi ana faɗin "Dare dare (kutsaya kutsaya)" ba musu suka tsaya, tare da juyowa suna haki kamar numfashi su zai ɗauƙe
Wasu mutane su biyu mace da namiji, suka kariso wajen su da gudu, suna haki suma suna jan numfashi.
Hannu matar tasa ta karɓi yaron ta dake hannun Rimsha tana faɗin "Nagode baiwar Allah" murmushi Rimsha tayi tace "Ba komai" Kausar sai faman haki take, saboda tafi Rimsha ƙiba sosai, da kyar ta iya buɗe baki tace "Ina macijin yake? Kun kashe shine?" mutumin da sukazo da matar ne yace "Eh na kashe shi" sai lokacin Rimsha ta samu damar sauke nauyayyar ajiyar zuciya saboda jin an kashe macijin, amma har lokacin kirjin ta na dukan uku uku, ta tsorata sosai da dajin, bata taɓa tunanin akoi irin wayan nan mugayen dabbobin a dajin ba.
Juyawa iyayen yaron sukayi zasu tafi, Kausar tayi saurin ce musu "Dan Allah ku taimake mu, ku faɗa mana hanyar da zamu bi mu fita daga wannan bakin dajin" mutumin ne yace "Me ya kawo ku dajin daman? Ni na ɗauka ai ku yan kauyen dake gaban nan ne" cikin sauri Rimsha tace "A'a muba yan can bane, mu yan Katsina ne" mata da mijin har suna haɗa baki wajen cewa Katsina kuma? Eh Kausar ta basu amsa, girgiza kai sukayi kafin suce "Katsina na can bayan ku, kun baro shi, nan kuna kusa da Ilorin ne, baku da nisa sosai da ilorin" zaro ido Rimsha tayi zatayi magana Kausar tayi saurin cewa "Ta ina zamu bi dan Allah mu je cikin Ilorin, dan shine garin mu" da hannu mutumin ya musu nuni da hanya, sannan suka wuce shida matar sa suka barsu tsaye sunyi cirko cirko.
Kallon Rimsha kausar tayi tace "Rimsha muje ko?" "Ina zamu je?" Rimsha ta tambaya kamar zatayi kuka "Gidan mu, bana faɗa miki ni yar ilorin bace" girgiza kai Rimsha ta farayi tana faɗin "A'a Kausar ni gida zan koma" riƙota Kausar tayi tana faɗin "ta ina zaki koma gidan? Ke da baki san hanya ba, kiyi hakuri idan mukaje gidan mu, sai asaki a mota ki koma gida" kwacewa daga riƙon da Kausar ta mata tayi, ta juya ta nufi hanyar da suka bi suka zo dan ta koma, tun da ance mata Katsina na baya sun baro shi.
Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰
Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .
💞💞TRIPLET'S💞💞
💔💔Episode 6💔💔
💔💔RIMSHA💔💔
Kallon Rimsha kausar tayi tace "Rimsha muje ko?" "Ina zamu je?" Rimsha ta tambaya kamar zatayi kuka "Gidan mu, bana faɗa miki ni yar ilorin bace" girgiza kai Rimsha ta farayi tana faɗin "A'a Kausar ni gida zan koma" riƙota Kausar tayi tana faɗin "ta ina zaki koma gidan? Ke da baki san hanya ba, kiyi hakuri idan mukaje gidan mu, sai asaki a mota ki koma gida" kwacewa daga riƙon da Kausar ta mata tayi, ta juya ta nufi hanyar da suka bi suka zo dan ta koma, tun da ance mata Katsina na baya sun baro shi.
Ganin Rimsha ta juya zata koma cikin wannan bakin wahala ne wato cikin dajin, hakan yasa Kausar tace "Meesha kin manta da wannan macijin da muka gani ko? To wlh akoi dubun sa a gaba, Allah ne ya tsare bamu haɗu da su a baya ba sai yanzu" a guje Rimsha ta juyo, tazo ta rungumi Kausar tana zare dara daran sleeping eyes nata, da suka shawuya sukayi ja.
Kankame ta Kausar tayi tace "Muje ko? Nasan mun kusa isa gida" shiru Rimsha tayi ba tayi magana ba, sai dai ta saki Kausar suka ci-gaba da tafiya tare.
Wannan hanyar da mutumin ya nuna musu, nan sukabi suka ci-gaba da tafiya, suna yar hirar su, amma dukkan su, zuciyar su sai dukan uku uku take saboda tsoron macijin da suka gani.
Gari ya fara duhun mangariba, basuyi wani tafiya mai nisa ba, suka hango wani kauye, da sauri suka karasa kauyen, kauye ne sosai, dan ko wuta basu da shi, irin kauyen yarbawan nan wadda suke ɗan yin sa a cikin daji, wanda bazaka wuce samun gida 10 zuwa 15 a wajen ba, mafiyawanci ma family ɗaya zaka samu a wajen.
Babu wanda ya kula su, kowa harkan gaban sa kawai yake, tsuru tsuru suka tsaya, ga mutane sun rasa waza su tunkara suyiwa magana, saboda fuskar kowa dake cikin wannan kauye a ɗaure basuga alamar wasa ba.
Suna tsaye har wani matashin bayarbe yazo wucewa, cikin sauri Kausar ta masa magana da yarbanci "Sannun ka bawan Allah" kallon tsab ya mata, kafin ya dawo da kallon sa kan Rimsha, itama ya kare mata kallo, wasu putu putu yan datti da su, kamar wayan da aka kwato su daga bakin kura saboda squeezing da kayan jikin su yayi, wucewa yayi zai bar wajen ba tare da yayi musu magana ba
Da sauri Kausar ta riƙo hannun sa tana faɗin "Please borda ka taimake mu" jin da gaske Kausar keyin yarbanci yasa ya dakata, dan da farko ganin Rimsha yasa ya gane ba yarbawa bane shiyasa ya wuce bai yi musu magana ba, amma yanzu da Kausar ta masa yaren yarbanci da kyau sai ya dakata yace "Me kuke so in muku?" Nauyayyar ajiyar zuciya Kausar ta sauke kafin tace "Mu baƙi ne, cikin Ilorin zamuje dare ya mana dan Allah wajen kwana muke nema" "Yarbawa ne ku?" Matashin ya tambaya, da sauri kausar tace masa eh ita bayarbiya ce, nuni ya musu da gidan sarkin kauyen nasu yace suje can, shine yake da alhakin bawa duk wani baƙo wajen kwana, godiya Kausar ta musu sannan suka wuce, shima saurayin ya wuce.
In da saurayin nan ya nuna musu, nan suka nufa. Gidane mai ɗan girman, bukkoki ne a cikin gidan, kamar kubbakar fulani, kun san dai yadda kauyen yarbawa yake ba sai na faɗa muku ba, ko da baku taɓa zuwa kasan yarbawa ba, to nasan kuna gani a Tv ko kunaji a labari.
Daidai zasu shiga cikin gidan sarkin kauyen wadda matashin ya nuna musu kenan, daga ɗan nesa suka hango wata yarinya tana zuwa, kallon juna sukayi kamar a mafarki har suna haɗa baki wajen cewa Ayla, da gudu suka tafi suka rungumeta, itama ganin su yasa ta taho da gudu, suka jungumi juna, tare da sakin kuka gaba ɗayan su, kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna kuka rungume da juna, kafin su raba jikin su, suna kallon juna, Allah sarki Ayla, duk ta rame, ta dawo kamar kashi da rai, duk fuskar ta ya rame sosai, sai ido zaka gani, kasusuwa wuyar tannan kamar mutun ya sanya sabulu ya ajiye a wajen saboda rama, tayi duhu sosai, alamar tasha wahala sosai.
Cikin kuka Rimsha tace "Ayla ina kika ɓace kika barmu? Mun juya bamu gan ki ba, mun koma baya nan ma bamu samu ganin kiba, ina kika bi?" Hannu Ayla tasa tana gogewa Rimsha hawaye tace "Zan faɗa muku, amma ba yanzu ba, sai mun nitsu" to kawai suka iya ce mata, sannan ta riƙo hannun Rimsha tana faɗin "muje gidan sarki" a tare suka jera zuwa cikin gidan.
Sunyi Sa'a kuwa sarkin kauyen yana da kirki, duk da cewa krista ne, amma yana da kirki, in da ya bawa Ayla masauki, nan ya bawa su Rimsha, wato ɗakin su ɗaya.
Sosai sukaji daɗi, ruwa suka fara ɗeba sukayi wanka, sannan sukayi alwala, yau sunyi wanka da sabulu, sau uku suna wanka, suyi su sake, sai daɗi suke ji, kamar wayan da suka koma cikin iyayen su, sai da sukaji jikin su ya ɗan sake musu sannan suka dakata da wanka suka fito, Ayla ta basu kayan da matar sarki ta bata, suka karɓa suka saka, suka tada Sallah.
Kafin su fara Sallah sai da suka tambayi Ayla inane gaɓar, bata sani ba ita ma tace musu, kawai nuna musu in da take kallo take sallah tayi, suma suka kalli wajen sukayi Sallah
Sai bayan sunyi Sallah har issha, sun zauna ne, matar sarkin mutuniyar kirki, ta kawo musu abinci, tuwon teɓa da miyar ganye.
Tana ajiye musu Abincin Kausar ta jawo kwanon, ta fara loma hannu baka hannu kwarya, yayin da Ayla ke taya ta, kamar wayan da basu taɓa ganin abinci ba.
Sosai Kausar da Ayla suka, take tuwun nan, ita kam Rimsha tun da ta ɗanɗana, sau ɗaya, ta cire hannu, tace bazata iya ciba, daman kuma Kausar tasan za'ayi hakan, dan ba kowa wani bahaushe ne zai iya cin abincin yarbawa tashi ɗaya ba.
Haka Rimsha ta hakura ta sha ruwa, ita kuwa Ayla yau kwanan ta biyu a gidan ta ɗan saba da cin abincin nasu, kuma ita daman can ba yar masu kuɗi bace, yar malam Shehu ne bata zaɓen abinci, duk wanda ta samu ci kawai take, ta godewa Allah. Yau su Rimsha suna cikin farinciki zasu kwana cikin mutane kuma ba'a daular mutuwa ba, yau zasu yi barci mai daɗi.
To muje mu leƙo su Aafia kafin nan mu dawo kila su Ayla sun gama take abinci tas.
Zaune suke gaba ɗayan su saman table ɗin cin abincin dare, daddyn Jelly, Abbi, Aunty, sai kuma Aafia dake ta faman wurgawa Aunty harara. Palon yayi shiru baka iya jiyo sautin komai, sai sautin karan chokula da suke cin abinci da shi.
"Abbi wan can Akil ɗin yazo ya ɗauki Umaisha a School" cewar Aafia, ba tare da Abbi ya kalleta taba yace "Ba yayan ki bane? Me yasa zaki kira shi Akil kai tsaye?" Shiru ta ɗan yi kafin tace "Sorry Abbi, yaya Akil yazo ta ɗauki Umaisha" jinjina kai Abbi yayi kafin yace "Eh ya sanar dani" da mamaki Aafia tace "Abbi ya sanar da kai fa kace? Gidan su fa ya kai ta, kuma ɗakin sa, wai matar sa ce" "Eh mana ai bai yi karya ba, matar sace" "Matar sa kuma Abbi? Yaushe ta zama matar sa?" Jinjina mata kai Abbi yayi yana faɗin "Daga lokacin dana aura masa ita mana"
Shiru tayi da kanta ya ƙulle, tana bukatar a mata karin baya ni. Ta buɗe baki zata sake magana, Abbi ya miƙe da sauri ya nufi bedroom na sa, yana dafe ciki, yana faɗin wash Allah, zaro ido Aafia tayi tana addu'ar Allah yasa ba wani mugun abu maganin nan da sukaci ya aikata wa Abbi ba, daman ita taki cin abinci, indomie ta girka ma kan ta.
Bata ankara ba sai taga daddyn Jelly ma ya miƙe da sauri ya fice daga palon yana dafe ciki, Aunty kuwa ta miƙe tana tana kokarin bin bayan Abbi, jiri ya ɗebeta ta zube kasa a wajen, tare da dafe cikin ta tana murkusoso tana juyi a wajen tare da zafafan hawaye, da karfi karfi take ambato sunan Allah tana kara riƙe cikin nata, kan kace me jini ya fara zuba, yana bin kafafun ta, ganin haka yasa Aafia ta tsorata sosai, kar aunty ta mutu fa, da gudu ta miƙe ta nufi bedroom na Abbi tana ta kwala masa kira.
Bawan Allah shi kuma yana can bayi yana fama da zawo, kamar zai mutu, saboda maganin ya kwance musu ciki, shida daddyn Jelly
shejiya Aafia ko loma ɗaya ita taƙi ɗan ɗana abincin, tabar su Abbi da wahala ga Aunty rai a hannun Allah
Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰
Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .
💞💞TRIPLET'S💞💞
💔💔Episode 7-8💔💔
Bawan Allah shi kuma yana can bayi yana fama da zawo, kamar zai mutu, saboda maganin ya kwance musu ciki, shida daddyn Jelly
shejiya Aafia ko loma ɗaya ita taƙi ɗan ɗana abincin, tabar su Abbi da wahala ga Aunty rai a hannun Allah.
Ko da ta shiga bedroom ɗin Abbi yana toilet, ta tsorata sosai kada Aunty ta mutu. Da gudu ta fito ta nufi part ɗin Irfan wajen daddyn Jelly, shi ma yana toilet, dawowa palon tayi ta zube kasa kan gwiwowin ta kusa da Aunty tana taɓa ta tare da kiran sunan ta, "Halima!!Halima!!" amma ina saboda azaba Aunty ta sume a wajen, kuka sosai Aafia ta farayi, tana jijjigata, ita har ga Allah batayi hakan dan ta kashe Aunty ba, kuma har cikin ranta take nadamar aikata hakan, sai dai kuma Rufee ba zata saka ta aiki ta kiyi bane, shine matsalar, ba zata iya cewa Rufee a'a ba, amma a kasan zuciyar tana son Aunty.
Ganin wannan kuka da take bashi da wani amfani yasa, ta miƙe tsaye, ta nufi