Showing 204001 words to 207000 words out of 355604 words

Chapter 69 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4774

ba riga sai dai zanina dana ɗaura a saman kirjinta, washegari da safe a na rinƙa tafiya da kafa, na ci bakar wahala, jama'a suna ta yi mani kallon mahaukaciya saboda babu riga a jikina, har na shiga cikin birni wuraren la'asar haka, ban ci komai ba, kuma ban wani damu ba, saboda mun saba da yunwa, a takaice dai na sha bakar wahala ka fin na samu wasu bayin Allah su ɗauke ni, har makaranta suka sanya Ni, suna bani kulawa sosai da sosai saboda basu taba haihuwa ba, ita kuma yaya Asma'u ban sake jin labarinta ba, shekarata ɗaya cikin na biyu na yi a wajen su, na canza na fara samun ilimi, satin da ya wuce ne suka zo mani da wata magana wai suna son na haifa masu yaro, dan basu taɓa haihuwa ba, matar ba zata iya aihuwa , shine suka ce zaa sanya kwan haihuwarsu a cikina, yaron zai girma na haifa masu, wannan dalilin yasa dama suka ɗauke ni suka sani makaranta dan na iya yadda zan kula masu da cikinsu.

Ban nuna masu a kan cewa ba zan yi ba, sai da na bari dare ya yi kowa ya yi barci, na kwashi kayana da yan kuɗin dake a gareni, na lalaɓa na buɗe gate ɗin gidan na gudo, ina fita na kwana a teburin mai shayin gaba da unguwar mu, da safe na wuce tasha na hau motar Abuja, ban san kowa a nan ba, kawai na hau mota, da muka shigo sai na rasa ina zan je, to ina tafiya a hanya ne muka haɗu da hajiyar da ta kawo ni nan, a takaice wannan shine kaɗan daga cikin abin da ya faru a rayuwata" ta kai karshen maganar tana kara sakin matsanancin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro.

Har wani tsuma Jehan ta ji jikinta yana yi, ji take idan ta tamki wannan uban nasu zata iya yi mashi yankar rago, bakin mugu azzalumi, ta kuduri niyar wlh ba zata barshi ba, matukar dai yana raye sai ta nemeshi ta ɗaukawa Maryam da Asma'u da mamansu fansa, dan ire-iren su take son zama yar sanda. Duk dakiya da dauriya irin tata sai da ta matsawa Maryam kwalla, abin akwai taɓa zuciya sosai, ace uban ka da ya haifeka, kai duniya ina zaki da mu?.

Rungumar Maryam ɗin ta yi tana mai bata hakuri tare da rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru. Jugum-jugum suka zauna kowa da abin da yake tunani na rayuwa.

After some minutes

A wannan hali Zinariya ta shigo ta same su, sai tashin wani azababben kamshin perfume take yi mai sanya mutun ciwon kai, bata wani da mu da halin da suke a ciki ba kawai cewa ta yi "Ke Aisha ke da Maryam da Adiva ku shirya kuna da bako a palon hajiya nan da minti talatin, zai zaɓa ɗaya ne daga cikin ku, ita kuma Jehan sai Hajiya ta dawo musan awani part take, namu jinsin ce ko dai mazan za'a barmawa!" Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta fice daga cikin ɗakin.

Ba musu suka tashi suka hau shiri, haka kawai Jehan ta tsinci kanta da kasa hanasu tafiya, tana ji tana gani suka gama shiri suka fice daga ɗakin. Abin dake faruwa shine akwai wani tunaren da Zinariya ke shafawa idan zata zo kirawa costumers mata su zaɓa, duk wanda ya shaki Kamshin turaren to fa ba zai iya yi mata kaddama ba, dole kawai su bi abin da take so.

Haka suka shirya suka fice daga cikin ɗakin har ma da yar zumuɗin su, bayin Allah sun shaki turaren Zinariya ta cuci rayuwarsu.

Kasancewar Alhajin da ya zo ɗin masoyin mata masu ɗan giba ne sai ya zaɓi Maryam, domin ta ɗan fisu kiba, Adiva kam kamar Jehan take, ba su da wani kiba ko kaɗan, ɗan gara ma A'isha ta fisu auki.

Bayan ya zaɓi Maryam ne A'isha da Adiva suka dawo cikin ɗakin, cikin zuciyarta Adiva kukan ɗaukar Maryam ɗin take yi, amma kuma a zahiri ta kasa nuna hakan, sai ma tsintar kanta da murmushi a kan fuskarta da ta yi, abin ya ɗaure masu kai, ga abu a cikin zuciyarsu suna ayyana wa amma yaki fitowa filli, haka ita ma Jehan ɗin ta kasance, sai kukan zuci take yi tana addu'ar Allah yasa kada ya lalatawa Maryam yaruwarta, yadda ta sha gwagwarmaya akan kare budurcin tan nan, Allah ya taya ta kare shi.

A ɓangaren ita ma Maryam ɗin a zuciyar ta tana jin ba zata iya barin shi ya aika abin da yake da niya ba, amma kuma a zahiri ta kasa hana shi, sai faman shafa ta yake yi tun ma a cikin palon Hajiyar kafin su shiga daga cikin ɗakin da ya kama, dan ya ce a nan zai yi amfani da ita, sai wani murza mata breast yake yi, ga bakin nan nasa bakin kirin kamar zunubi, da alama ɗan buguwa ne.

(To fa Maryam Allah ya kuɓutar da ku dukkanku na haɗa kaya na zuwa wajen mai Rimsha, sai na dawo dan ganin ya ake ciki)

🔥🔥GIDAN ABBA🔥🔥

Kamar yadda Dr Nawid ya faɗa kuwa bayan sallar isha sai ga shi nan ya zo, ya ci wanka ya sha dakakkiyar shadda blue color, ya yi kyau ba karya, amma fa ko kallo da ido bai samu daga wajen gimbiyar tasa ba, sai tashin kamshi yake yi yana ta zuba murmushi, ita kuma tana zaune saman sofa ta tsare gida ta haɗe rai, bai damu sosai ba, saboda yasan bata da lafiya...gaisuwa suka yi, daga nan suka zauna shiru, Rimsha ta yi kasa da kai shi kuma ya zuba mata idanu yana lallonta.

A haka Akila ta shigo ta same su, wani irin haushin Dr Nawid ne ya kamata, dan bata son abin da zai ɓatawa Rimsha rai kwata-kwata, kusa da ita ta zo ta zauna tana ɗagawa Dr gaisuwa, da fara'a ya amsa tare da tambayarta ya school, lfylou Alhadulillah ta amsa mashi da shi, daga nan ta dawo da kallonta kan Rimsha, ganin yadda ta yi kasa da kai kamar zata yi kuka ne yasa ta ce mata

"Meesha mu je ki nuna Mani in da kika ajiye kayan mun can" to ta amsa a tare suka miƙe Akila tana faɗin "Yaya Nawid ina nan dawo maka da ita" bai kawo komai a ransa ba, sai murmushi ma yake yi ya amsa mata da tayi sauri fa.

Suna shiga ɗaki Akila ta ja ta rungume ta, kasa-kasa ta fara magana "Rimsha ki dai'na ɓata rai kin ji? Ba ke kaɗai ce baki son shi ba har da ni, dan Allah ki saki ranki, idan kun ɗan yi hira na 30mins sai ki ce mashi kanki na ɗan maki ciwo zaki kwanta, kinga a haka za ku rabu lafiya, amma a duniyar yanzun nan baa fitowa mutun filli anuna ba'a son shi, wlh zaki ga uwa ɗaya uba ɗaya kuka fito da mutun ma a zamanin yanzu yana iya kashe ki akan abin duniya, dan haka ki sani ba'a shedan ɗan adam, ki san taya zaki zauna da kowa, kada ki damu In Sha Allah idan Lion ya fara son mu ba sai ma kin yi masu magana ba, ina da tabbacin sunan shi ma kawai idan suka ji daga ranar wlh ko millon nawa za'a basu, babu mai kara zuwa wajen ki ko ya kira ki a waya, so dan haka ki kwantar da hankalin ki, kuma yadda kike bala'in kaunar Lion mijin mu, dan ni na bashi ke, na san wlh ba zaki taɓa son kowa ba, bana son ki nuna musu tsanar da kika yi masu a fili, duk da yake abokin yaya Imran ba zamu yi shedar shi ba, ke bama su ba, mi sali ko yaya Akil ba zaki yi shadar abin da zai iya aikatawa akan abin da yake so ba, dan haka ki natsu komai cikin taku zaki bishi, yaya Imran ya ce zai zo wajen gyaran jiki ya same gobe da yamma idan yaya Akil ya kai mu, wai da na ce ba ya tafi Abuja ba? Sai ya ce mani wai ai daga Abuja ne zai zo ganin mu ya koma, wlh daga jin zancen yaya Imran tsara kayarsa ya yi, to ni dai nawa ido, yaya Akil kuma ya ce gobe zai yi maki komai na school, da da farko na ɓata rai, amma da na ji ke kike so, na hakura idan Allah ya yi muna da rabon fita Usa ɗin zamu fita In Sha Allah, yanzu dai ki je ku ɗan yi hira, kada ya zargi wani abin, ki saki ranki kin ji?".

Sosai ta ji shawaran Akila, kuma tana kara kaunar Akila sosai a ranta, saboda yadda take kara mata karfin gwiwa akan Lion, tana bata shawara mai kyau, tana nuna mata hanyar da ta dace, babu cuta ba cutarwa.

Rungumar juna sosai suka yi Rimsha tana faɗin "Aunty Akila nagode, Nagode sosai kin ji ko?" "Ba komai yar uwata, wlh ni kamar yadda su yaya Akil suke yan uwana haka kema na ɗauke ki, kuma daɗin daɗawa kema haka kika ɗauke ni, har kika iya gaya mani sirrin ki da ba zaki iya gayawa Jehan da kuke uwa ɗaya uba ɗaya ba, kai na ji daɗi kuma dole na riƙi ki amana saboda kema yar amana ce, yanzu dai ki je kada ya yi tunanin wani abin kin ji?" Gyaɗa mata kai ta yi alamar to daga nan Akila ta sumbaci lallausan kumatun, yar dariya ta yi har sai da dimple nata suka lotsa sosai, sannan ita ma ta sumbaci Akilar suka yi sallama, ta koma palon.

Shawaran Akila ya sanya ta samu natsuwa da farin ciki, ta ji gaba ɗaya ta saki ji, Akila yar baiwa, karama da hankalin manya, yar albarka, zama da kowa lafiya, kaunar kowa da kowa har wanda ma ya ce baya sonta, ita tana kaunar shi, ga A'afia nan bata sonta amma ita tana bala'in kaunar su dukkan su.

Hayewa ta yi saman bed ta kwanta tana tunanin yadda zata kaya, tana tunanin dole yau ta yi wa Rimsha tsawuyar dare dan Allah ya dafa masu, bata son ganin Rimsha cikin damuwa ko kaɗan.

Wayar Rimsha dake a gefen ta ne ya fara kara alamar shigowar kira, kobata ɗuba ba tasan mai kiran, Ahmad ne.

Ai kuwa tana dubawa shi ɗin ne, picking call ɗin ta yi suka gaisa tare da fara hira suna dariya, a nan ne yake tambayar address ɗin su kamar yadda ya yi wa Imran alkawari, ba musu ta gaya mashi, abin ya ɗaure mashi kai "Kaduna kumam?" Ya maimaita.

E ta amsa mashi tare da kara yi mashi baya nin in da unguwar su take.

Bata gama rufe baki ba, sai ji ta yi ya ce Heartbeat, ɗan zaro ido ta yi da mamaki ta ce "Yaya Ahmad ya aka yi kasan wannan sunan?" "Heartbeat kin san da waye kike magana kuwa? A'A ne fa" zubur ta miƙe zaune tana faɗin "Yaya Ahmad, yayan Anisa?" E ya amsa mata da shi, a tsorace ta ce "Dama kai ne mai son Rimsha?".

Babbar magana, Rimsha ta haɗa kuɗi da kuɗi kuma mulki da mulki faɗa, ta haɗa gwanki da Gwanki ita kuma tana can tana tunanin uban su a kuɗi da mulki, zuciyarta na a wajen Lion, wannan wace iriyar jarabawa ce? Lallai akwai rikici ba kaɗan ba, domin kuwa baban A'A SALAHUDDEEN idan ya samu labari to zai iya sanyawa a ɗaure Nawid ma da gaba ɗaya familyn sa, kuma su ɗauru ma har igiya ta saura, Ya Allah kasa Lion ya so Rimsha ya ɗauketa duk wannan rikici ta kauce, domin idan ba Lion ba babu wanda ya isa ya kwace ta daga family'n A'A SALAHUDDEEN, ga shi family'n sa basu da mutunci, sun raina talakawa, ganin talaka suke yi kamar takalmar sawarsu, yau ake yinta. Duk wayan nan zan tuka Akila ke yin sa a cikin zuciyarta, a yayin da shi kuma Ahmad sai hello yake ce mata. Soyayya mai saka Duk wani kuɗi da mutun yake ji da ita ya ajiye ta a gefe, banda haka me A'A SALAHUDDEEN zai yi da Rimsha? ga ruwa kuɗi abin da ake cewa kuɗi a tattare da shi, ga kuma uwa uba siyasa, kai anya ba mafarki nake yi ba kuwa. Akila kenan ta kasa wani kata ɓus sai tunane tunane take yi a ranta, abin ya kulle mata kai.

"Heartbeat ki yi mani magana mana, dama Rimsha kanwar Prof ce?" Da kyar Akila ta iya sai ta natsuwarta ta ce "E yaya Ahmad, kanwar mu ce" "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun rashin sani yafi dare duhu, yanzu kenan ita ce ɗazun ya ce zai bani na ce bana so, to Alhadulillah dai tun da abin ya zo da haka, ya zo mani da sauƙi, ranar Friday ina nan shigowa, nan da kwana huɗu kenan, dan Allah heartbeat ki kula mani da ita sosai kinji ko bugun zuciyar mu?" Gyaɗa mashi kai ta yi, ta ruɗe sosai tana al'ajabin abin, in dai mutun zai iya fitowa daga family'n A'A SALAHUDDEEN ya mutu akan Rimsha sosai haka, to da izinin Allah shima Lion zata iya yi wu ya so ta, kai A'A SALAHUDDEEN sune fa kasar nan gaba ɗaya a yanzu, kuma shine yaron *ABDULLAHI ABUBAKAR SALAHUDDEEN* na farko, yana da kanne mata huɗu da maza biyu, dukkansu basa a kasarnan suna England, ita kuma Anisa daddyn nasu ya rabu da maman nata ne yasa suka dawo Kaduna da zama, A'A yana bala'in kaunar Anisa sosai, saboda mamanta tana da kirki, da farko daddyn su ya so kwace Anisar, sai da Ahmad ɗin yasa baki sannan ya barta wajen maman nata, gaba ɗaya Family suna mutuwar kaunar Ahmad, shiyasa idan ya yi magana ba'a cewa aa, a yanzu haka duk cikin ƴaƴan *ABDULLAHI ABUBAKAR SALAHUDDEEN* Ahmad ne kawai yake a Nigeria sai Anisa da dama bata taɓa fita ba, suna da ruwan tsabar kuɗi abin da ake kira da asalin kuɗi ba kaɗan ba, abin ba'a magana, sannan duk cikin familyn SALAHUDDEEN Ahmad ne kawai ya ciri tuta yake iya zama da talakawa, yana da kirki sosai da sosai da kaunar mutane, yana da kyauta da saukin kai, ba shi da girman kai ko kaɗai, bai ɗauki rayuwa a komai ba, sai ita Anisa ta biyu, ita ma akwai izzar jinin baban nata a tattare da ita, sai dai itama zama da mamanta yasa take kaunar mutane, kun dai san tarbiyar uwa dole na daban yake, to wannan ma haka ne.

Kamar zautatciya haka Akila ta faɗa duniyar tunani, ta ruɗe sosai, dan bata taɓa zaton hakan ba.

Da Ahmad ya ga ji da magana, sai ya katse kiran, dan yanzu bai wani damu ba, tun da ya san har in da suke, idan suka mashi ba daidai ba suga diransa cikin Kaduna a daran nan, TO FA!!

(Akwai cakwakiya kenan, ni dai na haɗa kaya na zuwa wajen babyn daddy da kuma daddy, wato gidan Abbi.)

Su Aunty yau duniya ta samu, miji ya dawo sabo, sai tarairayar abin ta take yi, har wani liliya shi take, yau ansha soyayya an bar Ayla a Palo, almost 2 hours tana zaune a palon tana tunanin nata Babyn.

Sai can ya shigo palon bakinsa ɗauke da sallama, cikin sauri ta miƙe zaune tana faɗin "Sannu da shigowa daddy" hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce "To mummy" "Mummy kuma daddy?" Ta faɗa tana zaro ido.

Saman sofar kusa da ita ya zo ya zauna yana fiskantar ta ya ce "Me ya kwantar da ke a palon nan? Kuma me kike tunani?" Sunnar da kai kasa ta yi, tana wasa da yan yatsun ta, kasa-kasa ta fara magana "Babu komai dama muna hira da Aunty ne sai Abbi ya dawo suka wuce ciki, shine sai na kwanta nima a nan ina jiranta" "To tunanin me kuma kike yi?".

Yar murmushi ta yi kafin ta ce "Tunanin ka mana daddy". Bai san lokacin da ya saki cool murmushi ba, har cikin zuciyarsa ya ji wani sanyi ta ratsa shi (ko wani Namiji yana son ace ana yi da shi, ko da kuwa ba'a yi, matukar za'a ce ana yi da shi, to ba makawa zaka juya shi yadda kake so.)

"Baby dama kina tunani na ne haka?" Gyaɗa mashi kai ta yi tare da faɗin "E ina tunaninka sosai ma". Cike da zumuɗi ya ce "Okey gaya mani tunanin me kike yi akan mijin naki?".

Wayyo bata iya karya ba, kuma bata iya ɓoye abu ba, sai ta gaya mashi gaskiya tana ta tunanin ya za su yi idan suka yi aure. Ai kuwa bai san time da dariya ta kubce mashi ba, hannayenta ya riƙo yana faɗin "Babyna Allah wasa wasa kin iya soyayya fa, oya gaya mani waye ya koya maki? A tunani na sai na koya maki, ashe dai kin iya" ɗago da kai ta yi tana kallon kyakkyawar fuskarsa. "Daddyna Rimsha ce ta koya mani, ta iya abubuwan soyayya sosai, zama da na yi da ita ne na koya, kuma aunty ma tana daɗa koya mani wasu ai".

(Rimsha tamu sarkin soyayya ba🥰 ita ta koya mata)


Ɗan masowa kusa da ita ya yi yana faɗin "Da gaske?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.

"Wow ki ce na shirya kenan ba? Zan sha soyayya ko?" Yana magana yana kallon yadda take guntse dariya,

Zata yi magana muryan Abbi ya katse su yana faɗin "Kai kai kai kwarto a gidana da tsakar rana ban sani ba! Maik me nake ganin nan". Da yake sun saba wasa haka, sai ya fara murmushi yana ɗan shafa kansa.

Aunty kuma dake biye da Abbin a baya, sai murmushi take yi ta ce "A'a yayana ba kwarto bane, matarsa ya biyo kamar yadda kai ma ka biyo matarka" "Yauwa Sadiya gaya mashi gaskiya dai, ni mata ta na biyo" Ita kam Ayla kamar zata nitse kasa saboda kunya.

"Maik Sadiya kun saka mani kanwata jin kunya haka ba, gaskiya baku kyauta ba, Aliya ta so ki zo abin ki, kai kuma Maik kada na sake ganin ka a nan, kawai ka zo zaka tsara mani yar kanwata, to wuce ka tafi mun san halin ku maza". Gaba ɗayan su kayatatcen murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login