Showing 15001 words to 18000 words out of 355604 words
palo tanan saka yadda za tayi da Akil dan ya rabu da Umaisha, Akila kuwa tana fita ɗakin Akil nata ɗakin ta wuce dan taje ta kira daddyn Jelly dasu Abbi, yayan Imran, haka take, kafin tayi barci sai ta kira kowa daga cikin yan uwan ta, har da Abla sun sha hira sannan take barci.
Muleƙo Washington DC mu dawo
Yau ban haɗa muku page biyu bane, sakamakon bana jin daɗin jikina, shiyasa ban samu damar yi muku editing 2 page ba, amma In Sha Allah gobe zan biya
Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰
Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .
💞💞TRIPLET'S💞💞
# BOOK 2📚📙✍️
💔💔Episode 5-6💔💔
💔RIMSHA💔
💞💞Washington DC💞💞
09:30am
A hankali yake sako kafar sa a saman benen yana tafiya kafar baya son taka kasa, jikin sa gaba ɗaya a mace, sai wani cizan lallausan laɓɓan sa yake, jikin sa na sanye da Ripped Jeans black color, da white Round neck t-shirt, kayan sun masa kyau sosai da sosai, kamar dan shi akayi su, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal fari tas kalar rigan sa, ya ɗaure wannan kyakkyawan dark black curly hair nasa a bayan, ya bar wanna ɗan guntu a gaban goshin sa, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi yake, kamar anyi ɓarin turare.
Palon kasa shiru babu kowa kasan cewar already sun riga sun breakfast kowa ya kama harkan gaban sa, masu barci sun koma barci, masu fita sun fice yawon party da sauran su, dan basu da aiki da ya wuce wannan.
Jiki na kerman tsoro bodyguard dake cikin palon suka fara ɗaga masa gaisuwa ta hanyar ɗaga hannayen su, suna sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, ya sa kai ya fice daga palon.
Already an jera motocin da zasu fita, shi kawai suke jira. Yana fitowa jibga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, wucewa yayi kai tsaye ya nufi motar sa kirar Bugatti La voiture, da sauri wani jibgegen soja yazo ya buɗe masa motar, ya shiga ya zauna. A guje sauran sojojin suka haye saman bayan nasu motoncin.
A jere motocin suka tashi, suka fice daga gidan, tare da sakin jiniya, tamkar yaki zasu tafi. Kai tsaye white house suka nufa.
Kun dai san yadda white house yake ba sai na tsaya dogon bayani ba, ko ta ina sojoji ne kewaye a cikin gidan, hannayen su riƙe da manya manyan bindigu masu rai da lafiya, ga yan sanda ma ba'a barsu a baya ba, suna tsai tsaiye.
His excellency mr president yana cikin fadan shugaban kasa, kai tsaye wajen sa Romeo ya nufa yana taku irin na manyan jarumai sadaukan yaki, duk in da ya wuce sai sojojin wajen sun sara masa, jibga jibgan sojojin sa huɗu ne suka take masa baya har zuwa bakin kofar shiga cikin fadan, a daidai wajen suka dakata, shi kuma ya shige ciki.
Fadan shugaban ƙasa waje ne mai girman gaske, duniya ne guda, cikin fadan ɓangarori ne daban daban, sannan akoi ofisoshin da dama a ciki, kaɗan daga ciki, akoi office ɗin shi kan shi His excellency mr president, sai office na vice president, sai na secretary sa, da dai sauran su, sannan akoi manya manyan kujeru masu rai da lafiya, launin ja set nasu daban, haka zalika launin blue suma set nasu daban, akoi abubuwa da dama wadda faɗen su da baki ba zai yiwu ba, sai dai ku kawata su a ran ku, a takaice dai fadan shugaban ƙasa ya haɗu iya haɗu, domin tsayawa zayyana muku yadda cikin fadan yake zamu jima bamu gama ba, dan fadan dunaya ce guda.
Kusa da His excellency lion ya wuce yaje ya zauna, kallon sa cike da so da kauna His excellency yayi yace "My dear what is happening, naga kamar ranka a ɓace?" Ba sai na faɗa muku ba, kun dai san da turanci suke magana.
_Shiru lion yayi na yan sakanni kafin yace "kasan komai uncle ba sai na sake faɗa maka ba, Ina son a matsayin ka na president kayi magana da president na Spain, ina son a bincika min bayan James ya sauƙa daga jirgi ina ya nufa, shin ya hau wani jirgin ne ko kuma ya shiga cikin kasar ne, idan ya shiga cikin kasar wani gari yaje, uncle ina da ayyuka dayawa, ba zan iya zuwa Spain yanzu ba, kuma ina da tabbacin duk in da James yake yana cikin damuwa da tashin hankali, na kasa samun nitsuwa, ina jin har cikin zuciya ta, James na neman taimako na, a halin da nake ciki yanzu, ba zan iya fita daga Washington DC ba, saboda matsawa ta zai iya sanya mu rasa jigo na rayuwar mu, wato daddy, a situation ɗin da daddy yake yanzu, yin nisa da shi babban haɗari ne, da gara idan Michael yana da lafiya ma, zai iya ɗebe masa wasu matsaloli da kuma damuwa na rashin mu ni da James, amma ace babu ko ɗaya daga cikin mu, abune mai wuya a gare shi ya iya zama, jiya nayi tunanin zanje Spain da kai na, zuwa wayen gari na sake wani tunanin kuma, hakan ba mai yiwuwa bane, jiya ne kaɗai daddy bai ga James ba, ya damu sosai, yau da safe tun karfe 6 yazo bedroom na, wai sai na kira masa James a waya dan yayi mafarkin sa, da kyar na lallaɓa shi ya hakura, idan aka ci-gaba a haka, tofa akoi babban matsala, ka sani kuma ba sai na sake maimai ta maka ba" shiru His excellency ya ɗan yi kafin yace "Yes you are right, but kana ganin wani abune ya faru da James?" "No uncle i don't know, ban sani ba, kuma bani da amsa a kan hakan, sai dai ina ji a jikina hakan ne" shafa dark black curly hair sa His excellency yayi yana faɗin "I really like William family so much" ya kai karshen maganar tare da mannawa lion kiss a kumatu "Same here uncle we like you" ya faɗa shima yana mannawa kakan nasa kiss a goshi, murmushi His excellency yayi kafin yace "My lion zanyi yadda kake so, fata na dai James yana cikin koshin lafiya, sanna kuma ka kula da William da Michael sosai, yanzu nauyin su na kan ka, kada ka bari William ya san abun da ya samu Michael, idan hakan ya faru zamu iya rasa shi, ba tare da mun shirya ba" miƙewa Romeo yayi yana faɗin "Maybe in dawo yau maybe kuma sai gobe, duk yadda kayi da president ɗin Spain zan kira ka zuwa dare" ya kai karshen maganar tare da wucewa, ya nufi hanyar fita daga fadan, sai fatan Alkhari His excellency ke masa, a zuciyar sa yake amsa fatan alkharin da kakan nasa ke masa.
Yana fitowa sojojin da suka take masa baya zuwa bakin kofar fadan, suna tsaye a wajen, yana fita suka bi bayan sa zuwa wajen mota.
Kamar yadda suka zo, haka jerin gwanon motocin suka tashi, suka bar white house, suka nufi *Madstar Washington hospital center*.
Alhamdulila ba laifi jikin Michael ya fara kyau, saboda kwararun likitoci da suka tsaya, tsayin daka wajen ganin sun bashi kulawa, ga kuma kayan aiki masu kyau, inganci, da kargo. Sun cire masa kayan jikin sa, sun sanya masa kayan asibiti na majinyata.
Kusa da shi lion yazo ya tsaya yana kallon yadda fuskar sa ta sauya kamar ba Michael Triplets ɗin sa ba, ko motsi baya yi, da alama har yanzu bai san in da kan shi yake ba.
Romeo ya ɗauki tsawon lokaci yana kallon sa kafin ya juyo yana kokarin fita daga ɗakin idon sa ya sauka kan diamond watch nasu na Triplets na Michael, ɗaure saman wani kyakkyawan plate irin na ajiye zobe abun hanu na majinyata, da likitocin suka cire masa ne, sai suka ajiye a wajen, hannu Romeo ya kai ya ɗauki watch ɗin, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, yana yiwa Michael addu'ar samun lafiya.
Gida lion ya koma bayan ya bar hospital, dan baya son yin nisa da dad, kasan cewar ba Michael kuma ba James, idan shima yayi nisa da shi za'a iya samun matsala.
Babu kowa a palon kasa, sai daddaɗar kamshi air freshener da sanyin Ac dake tashi, ko'ina a palon a gyare yake tsab, kamar sabbin kaya aka zuba, wucewa yayi ya haura sama, kai tsaye bedroom ɗin dad ya nufa.
Daddy na kwance saman gado, yana kallon News a jikin makeken Tv plasma dake manne a bango a cikin ɗakin, kusa da shi Romeo yaje ya zauna yana faɗin "Good afternoon dad" murmushi dad yayi kafin yace "My lion how are you doing?" Shiru Romeo yayi bai amsa ba, dan shi ba hira yazo yi da dad ba, kawai yazo su zauna ne dan kar ya fara sa masa rigiman ya kira masa James ko Michael, dan dad idan ya fara rigiman shi kamar ƙaramin yaro haka yake zama saboda tsufa, sannan kuma ga ciwo dake damun sa.
Ganin Romeo yayi shiru ya zubawa Tv ido kamar mai kallo ne, amma kuma a zahirin gaskiya ba kallon yake ba, kawai dai yayi zubawa Tv dara daran idon sa ne, wani tunani daban yake yi "My lion wai up till now Michael bai dawo bane? Ko dai ya tare wajen His excellency ne" ba tare da ya kalli dad ba yace "in the evening zai dawo" "What about James?" Nan ma ba tare da ya kalli dad ba yace "Sai bayan two weeks ko three zai dawo" zaro ido dad yayi ya miƙe zaune yana faɗin "What? Wai me yaje yi a Spain ɗin ne daman?" Sai lokacin Romeo ya juyo da kallon sa kan dad "Ba wani aiki ne mai wuya ba" ya bawa dad amsa, dad na komarin sake yin magana yayi saurin cewa "No dad, please stop asking me these silly silly questions, don't worry they will come back soon" shiru dad yayi ba wai dan yaso hakan ba, sai dan kawai lion ya zauna tare da shi, yasan cewa idan ya cika yiwa lion tambayoyi da magana, yana sanya shi yin magana to zai tashi ta fice ne, kuma dad ba zai so hakan ba, dan Romeo baya zuwa ya zauna tare da shi haka, idan kaga Romeo yazo wajen dad to fa sai dai in drugs na shi zai bashi, haka kawai ba zaka taɓa ganin sa a wajen dad ba, yauma da dalilin zuwan nasa, bai son dad yazo yayi ta takura mashi a kan ina James ina Michael shiyasa yazo rufe wa dad baki.
Sun jima suna zaune shiru sun tsare Tv da ido, dad yana kallo da gaske, shi kuma Romeo yana duniyar tunani.
A gefe guda kuma, Musharraf ya kara samun lafiya sosai da sosai, sai dai ɗan kwana biyu da James baya nan, ya shiga damuwa sosai, saboda babu mai yi masa alwala, sai dai shi ya lallaɓa ya rarrafo yaje ya ɗauki ruwa yazo yayi alwalan da kan shi, haka zalika babu mai ɗaura shi saman kujera ya kai shi toilet, abun ya fara damun sa sosai, babu wanda zai iya tinkara ya sanar wa damuwan sa, dan shi gani yake duk yan gidan danja ne, babu mai saukin kai a cikin su.
To bari dai mu leƙo My Rimsha kuma muga wani wai na take toyawa.
💔💔RIMSHA💔💔
Makale Kausar take saman bishiyar gwaiva tana tsinko musu, ita kuwa Rimsha tana tsaye a kasa sai aukin cewa "Kausar ga wani nunanne ta can" bata san ya wuyar hawa bishiya yake ba, ci kawai ta sani, sai bakin iya magana, dan yanzu Rimsha ta kware wajen iya magana zaman ta da Ayla da Kausar, dan Ayla yarinyar akoi ta da surutu, amma mafiyawancin surutun nata mai amfani ne, ita kuwa Kausar akoi murya, kunsan dai yadda yarbawa suke, idan suna magana sai ka rantse da Allah faɗa suke, gata bata da jumiriyar yinwa, kundai san halin yarbawa da bala'i cin abinci basa wasa da ciki, shiyasa koda suka fito daular mutuwa ta kasa tafiya, sai da Rimsha ta goyata, saboda bata iya jurewa yinwa ko kaɗan, idan kuma taci ta koshi, tofa akoi iya magana, gata da karfi kamar doki, dan ko a gaɓɓai tafi su Rimsha, kuma tafi su ƙiba sosai, wahalar daular mutuwa ya mai da ta siriri ya, amma Kausar mace ce mai ƙiba, sak yarbawan haka take.
Tana makale saman bishiya tana ta faman gabzan gwaiva, daɗi da santi ya ɗebe ta sai surutu take hankalin kwance
"Meesha yau baki zana masoyin mu GAR ba" Kausar ta faɗa daga saman bishiya tana dariya, murmushi Rimsha tayi har sai da dimple nata ya lotsa, wani daɗi taji ya ziyarci cikin farfajiyar zuciyar ta, Kausar ta taɓo mata in da yake mata kai-kayi, ita ka ɗai sai murmushi take, tana cin gwaiva tace "Ke dai bari Kausar am, ina nan zuwa in zana shi, yanzu har jikin bishiya zan rinƙa bi ina zana shi, dan wannan daji tasan da zaman mu" dariya Kausar tayi kafin tace "Kai Meesha ina da shawara" cikin sauri Rimsha tace "Shawarar me? Faɗi ina jin ki" gefowa Rimsha gwaiva tayi kafin tace "Me zai hana mu tara kuɗi muje wajen wannan mutumi mu gan shi ido da ido" Rimsha bata san lokacin da dariya ya kubce mata ba, har da faɗuwa kasa, zuba mata ido Kausar tayi tana kallon ta da mamaki, bata taɓa kallon Rimsha na irin wannan dariya ba, sai dai murmushi kawai, amma yau Rimsha ce saboda dariya har da faɗuwa kasa
Da dai Kausar taga Rimsha fa bata da niyar dakatawa daga dariyar da take, sai tace "Haba Meesha menene kuma abun dariya?" Har wani dafe ciki Rimsha take saboda dariya, ga hawayen dariya nan wani na bin wani a kumatun ta, Kausar kuwa dataga Rimsha taki kulata sai ta saka kuka tana faɗin "Wlh idan baki dai na dariyar nan ba mun ɓata, haba dan Allah mahaukaciya kika mai danine?"
Sai da Rimsha taga Kausar ta ɓata rai da gaske tana kuka, sai ta dakata da dariyar nata, ta ɗago ta dubi kausar, murya ɗauke da dariya tace "Sorry Aunty yar lukuta, ai ke ɗin ce santin gwaiva ya ɗebeki sai faman sakin layi kike da zance, ke kwata kwata kin manta aina muke" A kule Kausar tace "sai dai sama da yar lukuta ba yar lukuta ba" guntse dariya Rimsha tayi dan tasan in tayi dariyar nan, bazasu wanye lafiya da Kausar ba, kuma tana sane da gangan ta kira ta da yar lukuta, tasan ba abun da Kausar ta tsana biyun wannan suna Aunty yar lukuta, baba da Mustapha suka sa mata sunan, suma dan ba yadda zatayi da sune yasa take amsa wannan suna idan sun gaya mata.
"Me ya baki dariya to?" Kausar ta tambaya tana kara haurawa saman bishiyar da kyau, dan ta hango wani gwaiva nunanne a can sama, sake kwashewa da dariya Rimsha tayi dan Kausar ta tuna mata da abun da ya saka ta dariya ɗazun
Saboda haushin dariyar da Rimsha take, tsinko gwaiva ɗanye Kausar tayi ta sai ta tsakiyar kan Rimsha ta kwala mata, ihu Rimsha tasa tayi baya tana faɗin "muguwa Aunty yar lukuta" sake tsinko ɗanyen gwaiva Kausar tayi ta jefo mata, a sukwane ta matsa a wajen tana faɗin "kin dai yi na farko kinci riba, amma ba zaki kara ki ci riba ba" harara Kausar ta wurga mata tana faɗin "Allah idan baki faɗa min abun da yasa kike min dariya ba, sai na sauko kasa na fasa ciro gwaivan, sai dai mu wuni da yinwa"
Fuska ɗauke da murmushi Rimsha ta fara magana "Ai kece da abun dariya Kausar, idan ban da ke, muda muke wannan kungurmin daji, wadda bamu san ina muka nufa ba, wai kike maganan mu tara kuɗi mu tafi America, mu zabiya uwar yawo, to amma uban waye zai bamu kuɗi a dajin nan? Kuma ma dakike wannan magana an faɗa miki GAR mutun ne kamar kowa? A'a GAR ba mutun ne kamar kowa ba, manyan shuwagabannin ma kafin su samu ganin sa sai sun shirya, shifa ba iya soja bane kawai, jikane ga shigaban kasa mai mulki yanzu, bayan haka, shi ba irin sojan da kike tunani bane, the general of the army fa aka ce miki, hmmm Kausar baki da lafiya, wai mu tara kuɗi mu tafi wajen sa, to ki bari muci mu koshi mu samu muga iyayen mu da yan uwan mu tukun nan, kafin muyi tunanin tsiyar da zamu zuba gaba, amma yanzu mu bamu da wani bakin magana, daga kikaji zaƙin gwaiva kawai ki fara sakin zance, kefa daman haka kike, da kinci kin koshi kin gane kanki shikenan kuma, sai ki saki layi kita zuba kamar kanya, zance mara kan gado.....bata karisa maganar ba Kausar ta faɗo kasa dim daga saman bishiyar nan, tana ihu kamar makoshin ta zai yage, a sukwane Rimsha tayi kan ta tana faɗin "Kausar lafiya? Me ya faru?" Ina Kausar bata saurare taba, ta hau cire kayan jikin ta, tana yasar wa a kasa, tana yi tana ihu
_Sosai Rimsha ta ruɗe tana faɗin "Kausar menene?" Ayya Rimsha akoi tausayi, har ta fara yi mata hawaye tun bata ji me ya faɗo da Kausar ɗin ba.
Tsab Kausar ta cire kayan jikin ta, ta zubar a kasa, sai sosa jiki take tana ihu, Allah sarki gaba ɗaya fatan bayan ta, yayi ruɗu ruɗu da cizon wayan nan mayun (ant) cinnakun ko ince kwarkwasa, ga cizon nasu da bala'i zafi, sai ya ɗauki sati wajen na maka zogi, gashi kuwa sun cijeta sosai da sosai, ruɗu ruɗu cizon nasu ya fito a bayan ta, sai kuka take tana sosa wajen, wani wajen ma idan ta sosa shi