Showing 348001 words to 351000 words out of 355604 words
ya sanyata ta shiga wata duniya.
Da kyar ta iya karisawa gaban lallausa kuma tsadadden Chinese carpet ɗin dake a ta gaban katafaren gadonsa ta ajiye tray ɗin, abin da ya sa ta kai wajen kuma ta ga su Imran a wajen suke cin abinci har shi ma Areef ɗin, a saman irin wannan carpet ɗin na ɗakinsu suke cin abincin.
Bayan ta ajiye ta tsaya a gefe tare da ɗaga mashi gaisuwa, tamkar babu shi a cikin ɗakin, latsa laptop nasa yake yi cikin matsuwa da kwanciyar hankali tare da aji.
Rimsha ta kwashi tsawon 40 mins tana tsaye a wajen nan ba tare da ta motsa ba, shi kuma aikin gabansa kawai yake yi, idan da saboda duk mai yi mashi aiki ya saba da hakan, idan baku manta ba haka bodyguards na gidansu suke fama da shi, wani lokacin ma ya gama zamansa suna tsaye ya ɗauki tsawon awa ko sama da haka, daga karshe kuma ya tashi ya bar wajen ba tare da ya ci abincin ba, shi dai halinsa sai shi.
Har hamman barci ta fara yi tsaye a wajen, shi kuwa saboda bakar mugunta sai da ya kara minti goma sannan ya miƙe a nutse ya shiga toilet, ta kasar ido ta bi shi da kallo zuciyarta yana mugun kara tsananta bugu da yake yi, tamkar zai fasa kirjinta ya fito, tana mutuwar tsoronsa fiye da tunanin mai tunani.
Brush ya yi sannan ya fito ya zauna a kusa da tray ɗin, ba tare da ya yi magana ba ya yi shiru, cikin sauri ta duƙa tana ƙoƙarin zuba mashi abincin. Wani irin razana ta yi jin sexy voice nasa ya ce ta miƙo mashi wayarsa dake a saman bedside drawer, da sauri ta miƙe ta ɗauko mashi wayar ta dawo ta miƙa mashi, ba tare da kalle ta ba ya karɓi wayar ya fara latsawa.
Ita kuma ta ɗauko wani cup mai shegen bala'in kyau wadda shi kaɗai ma kawai ya ishi mutun ya kwashi mintoci yana kallonsa, da alama kuma cup ne mai bala'i tsada, kuma da alama dai cup ne na musamman, sai kyalli yake yi fari tas da shi, zuba mashi hot green tea na kasarsu mai shegen kamshi ta yi, sai tiriri yake yi, a nutse ta tura mashi a gabansa, sannan ta fara zuba mashi abinci a plate mai shegen kyau, kuma plate ɗin irin cup ɗin ne, da alama set ne, ta san cewa shine abin da yake buƙata tun da shi aka shirya a saman tray ɗin.
Ɗaukar tea ɗin ya yi ya fara sha domin ya fi buƙatarsa da zafi sosai, a hankali yake kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa yana kurɓa.
Ita kuwa sai faman zuba mashi duk wani abin dake a saman tray ɗin take yi a cikin plates, bai wuce sha biyar ya yi wa tea ɗin ba ya dawo da kallonsa saman abincin da take zuba mashi domin ya gani kar ta cika mashi abinci sosai saboda ba wani ci sosai ke gare shi ba.
Lokacin da dara daran blue eyes nasa ya sauƙa a saman hannunta da take zuba mashi abincin, wani irin wurgi da cup ɗin hannunsa ya yi ya miƙe da sauri ya nufi toilet. A razane ita ma ta miƙe tare da dafe saitin zuciyarta dake yi mata barazanar tarwatsewa, Baiwar Allah faɗuwar gaba da bugun zuciyar ma kawai zai iya sanya ta ta mutu ba tare da ta shirya ba.
Shi kuwa amai ya rinƙa kwarawa kamar zai amayar da hanjin cikinsa, har wani ja idanunsa suka yi, tunani ta fara yi akan me ya sanya shi yin amai ne haka?.
Tana tsaye tana tunani har ya fito ya sameta. Kasa kasa ya motsa laɓɓansa ya ce ta zube gwiwowinta a kasa. Cikin sauri ta yi kasa jikinta na ta ɓari sosai, dama ga zazzaɓi. Rai a ɓace ya kara kallon hannun nata, a rayuwarsa ya tsani zanen lalle kamar me, kyamar abin yake yi fiye da tunanin mai tunani, wannan dalili ta sanya shi yin amai dan ya ci abin da ta taɓa da hannunta mai lalle.
Gaban mirrorsa ya nufa ya ɗauko wani chemical dake a cikin drawers na wajen, ya dawo wajen da take duƙe.
Gently ya ce mata ta bashi hannunta, jininta na karma ta haɗe hannunta dukka biyu ta miƙa mashi.
Babu tausayi ko kaɗan a face nasa haka ya zuba mata wannan chemical ɗin a hannayenta. Wani baƙin azaba ne ya dira mata lokaci guda wadda ya sanyata sakin wani irin kuka mai sauti tare da ratsa duk wata zuciya mai imani da tsautsayi, amma fa shi kokaɗan babu alamar tausayi a face nasa, ta yi mugun ɓata mashi rai ba kaɗan ba.
Nan take hannayen nata suka fara zubar da jini sakamakon chemical ɗin ya farfasa mata fatar jikinta.
A takaice ya ce ta yi mashi shiru ko kuma ya take wuyarta a nan, ba shiri ta ja bakinta ta yi shiru, tana jin azaba ta haɗiye kukan nata kamar an ɗauke wutar nepa.
Bayan ya gama zuba mata chemical ɗin ya rufe robar tare da maida shi mazauninsa yana faɗin ta goga hannun nata da kyau dan tsabar rashin imani da baƙin mugunta.
Hawaye wani na bin wani haka ta fara goga hannayen nata cikin na juna chemical ɗin yana kara ratsata.
Sai da ya tabbatar gaba ɗaya zanen lallen ya fita sannan ya ce ta miƙe ta je ta cinye abincin nan duka, kada ta rage ko kwara ɗaya, sannan ta kwashi kayan abincin ta je ta zubar da su a bola baya son ya sake ganinsu dan ta taɓa da hannunta kai lalle.
BABBAR MAGANA taya za'ayi ta cinye abinci kula guda, kula ma kuma ba ƙarami ba, sannan ga sauran kuloli na su ferfesu da sauransu, ga kuma su fruits, kun dai san halinsa idan ya yi magana whikenan babu wanda ya isa ya sanya shi ya sauya ko da kuwa me zai faru. (DA RABON CIKIN RIMSHA ZAI FASHE YAU)
Da kyar ta iya miƙewa ta nufi wajen abincin, tana mai danasanin zuwanta duniya ma baki ɗaya, ƴar tsawa ya daka mata akan ta fara wanke jinin hannayenta ta daina ɓata mashi ɗaki, kuma ta yi maza ta fara gyara mashi ɗaki wajen da chemical da kuma jininta ya ɓata kafin ta zo ta cinye abincin.
Ta rasa ya zata yi, ta rasa a ina zata wanke hannun nata da ya ce ta wanke, shin in je toilet nawa ne ko dai yaya? Ta tambayi kanta da kanta.
Ganin babu mai bata amsa yasa ta nufi waje tare da runtse ido tana mai jiran jin wani tsawar tasa, ai kuwa hakan ne ta faru domin kuwa sai lokacin idanunsa suka sauƙa akan kunshin kafarta, wannan dalili yasa ta sake jin voice nasa ya ce ta dawo ta ɗauki chemical ɗin da kanta ta zubawa kafarta ta goge kunshin nan, Allah sarki kunshin da aka yi mata jiya jiya.
Tana hawaye ta dawo da kanta ta ɗauki chemical ɗin daga wajen da taga ya ajiye, shi kuma komawa saman bed nasa ya yi ya zauna tare da cigaba da latsa laptop nasa kamar ɗazun.
Ita kuma da kanta ta zubawa kanta chemical tana kuka ta goge wannan kunshi na kafarta tas, sannan ta miƙe kafar tata sai jini yake yi ta nufi waje.
Tana fita bedroom nata ta nufa, tana shiga ta zube gwiwowinta a kasa tare da sakin wani marayar kuka, tana cikin yi sai ta tuna da abin da ya ce ne ta zo ta gyara mashi ɗaki, hakan yasa ta miƙe da sauri ta nufi toilet nata.
Wani irin bakin azaba ta ji lokacin da ta zuba ruwa a kafar tata da hannun nata, wani irin zogi da raɗaɗi suke yi mata, jikinta har lokacin kerma yake yi, ita tunanin yadda za'ayi ta cinye abincin da ya ce ɗin nan ne ma yake damunta.
Haka dai ta wanke kafar tata da hannun nata duk sun yi jawur da su, chemical ɗin duk ya tsastsage mata soft skin nata, duk wanda ya ganta a halin da take a ciki sai ya tausaya mata tare da matsa mata kwallah.
Da kyar ta iya jan kafarta ta koma ɗakin nasa, gyara wajen da ya baci da chemical da kuma jininta ta fara yi, sai da ta gyare shi tsab, sannan ta zauna ta fara cin abicnin kamar yadda ya saka ta.
Shi kuwa tamkar babu shi a ɗakin, ya fasa cin abicin ya hakura, dan already ta riga da ta tayar mashi da zuciya, komai ya ce zai ci yanzu amai zai sanya shi, idan baku mance ba dukka TRIPLETS shegen bala'in kyakkyanin ke gare su na fitar hankali, amma ɗan gara Areef da yake ya rayuwa a wurare daban daban wadda hakan ta sanya kyakkyanin tasa ta ragu, Lion da Aseef kam ba'a magana kyankyaninsu ya wuci tunanin mai tunani, ya wuci misali.
Wani irin wahalallen amai ne ya zo mata lokacin da ta fara cin abincin nasu, amma saboda bala'in tsoronsa yasa ta haɗiye amai ɗin, ta daure ta fara cin abincin, wani irin ɗanɗano ne abinci nasu yake da shi wadda ita dai bai yi mata ba kwata kwata, haka abincin nasu ya yi mata.
Tun tana ci da ɗan daɗin rai har ta fara kuka mai sauti, wlh tamkar babu Lion a cikin ɗakin nan, da kukan nata ma ya isshe shi tsawa ya daka mata akan ta dai'na damunsa ko kuma ya taketa a nan, ta gama cin abincin nan ta je ta gyarawa su Mark ɗaki.
Yau taga bala'i da tashin hankali, bata taɓa tunanin rashin imaninsa ya kai har haka ba. Tana tsaka da cin abincin tana kuka hannunta kuma yana jini har lokacin,
💖💖TRIPLETS💖💖
E93-94💖
Yau taga bala'i da tashin hankali, bata taɓa tunanin rashin imaninsa ya kai har haka ba. Tana tsaka da cin abincin tana kuka hannunta kuma yana jini kaɗan kaɗan har lokacin.
A haka Imran da Areef suka shigo suka same ta.
Wani irin bakin ciki Areef ya ji lokacin da ya ga me yake faruwa, Rimsha cikinta ya cika kamar zai fashe, ga shi kuma yanzu ne ma ta ci rabin abincin dake a cikin kular, ga kuma su ferfesu a gefe sannan ga fruits da su drinks, a ina zata zuba su kuma? Ga shi ya ce ko ɗiko na abin dake a kan tray ɗin kada ta tage mashi.
Imran kam kasa jurewa ya yi ya saki Areef ya juya da sauri ya fice daga cikin ɗakin dan gudun kada zuciyarsa ta buga, shi kuma Areef ya ma rasa me zai ce, ya rasa ta ina zai fara yi wa Lion bayani akan ya yi wa Allah ya rabu da yarinyar nan haka.
Sosai ya tsare Lion da ido yana kallonsa yayin da ita kuma take lodan abinci, tamkar Lion bai san ana ganinsa ba, kamar bai san da shigowarsu ɗakin ba, aikin gabansa kawai yake yi.
Wucewa Areef ya yi izuwa in da take zaune, a gefenta ya zauna tare da ɗaukar spoon suka fara cin abincin tare, ko sannu Lion bai ce masu ba, shi kuma Areef bai lura da hannun nata ba.
Da kyar da zufa suka kammala cin abincin nan, dukkansu sun kasa shan ruwa saboda bala'in ƙoshi, ita kam magana ma ta kasa yi sai nishi sama sama take yi.
Da hannu Areef ya yi mata alama akan ta kwashe kayan abincin ta fita da su waje, tana nishi da kyar da makyarkyata ta miƙe tare da ɗaukar kayan ta fice tana jan kafa.
Zuba mata ido Areef ya yi yana kallon yadda kafarta ya yi wani irin tsage tsage yana fitar da jini kaɗan kaɗan, tunawa ya yi da ɗazun kamar ya ganta da kunshi a kafarta, kenan chemical Lion ya zuba mata a jiki dan baya son ganin kunshin, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar bala'i ce, ya faɗa a ransa tare da miƙewa da kyar shima saboda ciwonsa ya haye saman bed ɗin na Lion yana tunanin ta yadda zai ɓullo wa Lion dan su warware wannan matsala a tsakaninsu.
Ita kuwa tana fita bedroom nata ta wuce da kayan abinci, saman carpet ta ɗaura tray ɗin tare da nufar toilet da gudu ta rinƙa sheƙa amai kamar wadda aka yi wa wahayin aman.
Amai take zubawa babu kama hannun yaro, baiwar Allah tun tana iya gani sosai har idanunta suka rufe, wani irin jirine ya kwasheta tana ƙoƙarin zubewa kasa a cikin toilet ɗin Imran da ya shigo tun ɗazun ya tsaya yana kare mata kallo, cikin zafin nama ya tarota ta faɗa jikinsa tana jan numfashi da kyar da kyar.
Zuba ruwa a cikin baff ɗin wanka ya yi tare da surka na zafi dana sanyi sannan ya ɗauketa kacokam ya sumdumata cikin ruwan.
Sai sauke wahalallen numfashi take yi, wani irin yanayi ta tsinci kanta mai wuyar fassarawa. Shi kuma juyawa ya yi ya fita daga cikin toilet ɗin dan ya bata dama ta yi wanka ko zata samu karfin jikinta.
Yana fita ya wuce bedroom na Lion, nan ya isko Areef kwance saman bed, daga baya ya tsaya yau iya ɓacin rai ya shiga ɓacin rai fiye da tunanin mai tunani, akan kanwarsa kam ba zai iya juran wannan walaƙanci ba, dole su bar gidan nan yau.
Cikin natsuwa ya ce "Saif zan ɗauki kanwata mu koma gida tun da Areef yana nan!" Shiru Lion bai tanka mashi ba, dama kuma yasan ba zai tanka a yanzu ba, sai time da ya ga dama.
Haka kuwa akayi sai da Imran ya ɗauki tsawon 20 mins a tsaye kafin nan gently ba tare da ya ɗago ba ya fara magana "Ba bu in da zaka je har sai na bar Nigeria, sannan kuma wannan yariya ƴar aikin muce, idan kuka matsa mani to wlh daga nan har Washington DC zata tabbata a ƴar aiki, so zaka iya komawa bedroom naka!!". Ya yi maganar with he's full confidence tare da nuna isa tamkar shine wanda ya haifi Imran ɗin, wannan isa da ya nuna ma ko Abban Imran baya nuna shi ba
Shiru Imran ya yi domin ba yadda zai yi, ba ta yadda zai fita gidan ba tare da izinin Lion ba, kuma ma ko da ya fita Lion yana zaune a cikin ɗaki zai sa a dawo da shi, wannan wace iriyar bakar kaddara ce? Ya tambayi kansa, shi kuwa Areef kashewa Imran ɗin ido ɗaya ya yi tare da yi mashi alama akan kada ya sake magana, domin idan ya sake magana za'a iya samun matsala, zai jawa Rimsha wata bala'in ce, gara kawai su kyale shi zuwa nan da kwana biyu idan ya sauƙa ya huce to sai su tunkare shi da zancen ta daina yi wa su Mark aiki, amma yanzu kam su kyale shi tukunnan tun da a yaune abin ya faru.
Jiki ba kwari Imran ya juya ya fice daga bedroom ɗin ya koma na Rimsha dan yaga wani hali take a ciki baiwar Allah.
Ta gama wanka sai faman dafa bango take yi dan ta fito daga toilet ɗin, wani azababben ciwo kanta yake yi mata, wani irin duhu duhu take gani a cikin idonta, lokaci guda gabaɗaya ta sauya tamkar ba ita ba.
Riƙota Imran ya yi suka kariso cikin ɗakin, saman bed nata ya zaunar da ita tare da ɗauko mata wani abaya daga cikin kayanta sannan ya zo ya sanya mata a jikinta kafin ya ce ta kwance towel ɗin bari ya je ya maida cikin toilet , ba musu ta ɗan miƙe ta kwance mashi, nan take ta fara rawan sanyi na zazzaɓi.
Bayan ya mai da towel ɗin cikin toilet ya dawo ya bata maganin da Areef ya bata ɗazun, sannan ya ce ta haura saman gado ta kwanta, haka ta haura ta kwanta ya ja bargo ya rufa mata tare da yi mata addu'ar barci ya fito ya barta kwance, zuciyarsa cike fal da tunaninta.
Bedroom nasa ya wuce a in da ya je ya yi wanka shima ya haye gadonsa tare da kashe wayarsa dan yau baya jin zai iya hira da jelly ɗin ma, yana cikin yanayi mara daɗi.
Shi kuma Areef yau a ɗakin Lion ya kwana, a tare suka kwana.
A ɓangaren Akil da Umaisha kuwa, kwance Umaisha take saman gado daga ita sai wata ƴar shegiyar riga mai ƙaramin hannu wadda ta tsaya mata a iya cinya, ba pant kuma babu bra a jikinta, haka zalika kwanciyar da ta yi yasa rigar ta yi sama, santala santalan cinyoyinta a waje, sai wani yauki take yi tana wani kara bin lafiyar gado, da alama cikin nata ɗan son jikine.
Ɗaure da towel a kugunsa ya fito daga toilet, yayin da yake riƙe da wani karami kuma yana goge kansa da jikinsa da shi.
Wani irin yawu ya haɗiye ganinta da ya yi a haka, wurgi da towel ɗin hannunsa ya yi ya haye saman gadon yana faɗin "Wife kina haukata yaya Akil sosai".
Juyowa ta yi suna fuskantar juna, turo bakin nan ta yi cikin yauki da shagwaɓa ta ce "Yaya Akil dan Allah ka matsa mani jikina ciwo yake yi mani".
Bakinsa ya kawo saitin kunnenta yana faɗin "Yanzu zan baki abin da ya fi matsa jiki, gwaggo batula ta wani ce mani wai na barki sai babynmu ya yi kwari idan ba haka ba zan iya zubar da cikin, ina ba zan iya ba, Allah zai tsare mana babynmu dan haka ajiye zancen gwaggo Batula a gefe, bari na kara mani wani babyn dan mu sami twins tun da wanan ɗin bai yi girma ba, 2 weeks ne kawai, bari yau na karo guda biyu, idan kin kasa haihuwa sai na taya ki".
Ita ma da yake yar nema ce sai ta mirgino ta shige jikinsa, riƙeta sosai ya yi tare da kawo bakinsa daf da kunnenta kasa kasa kamar wani na yi masu laɓe ya ce "Wife kin san fa aka ce mace tafi daɗi idan tana da ƙaramin ciki, dan haka bari na shanye daɗin dukka na more kafin ki haife cikin na kara maki wasu, dan Allah ƴaƴa dozen nake so".
Ita dai bata yi magana ba sai wani nanukar jikinsa take yi ɗan cikin nasu ma da gulma wai ɗumin jikin babansa yake son ji kullun, shiyasa take ta wani kara shige mashi jikinsa, shi kuwa ganin haka yasa ya fara bata