Showing 138001 words to 141000 words out of 355604 words

Chapter 47 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2786

kai karshen maganar ba aka buɗo kofar ɗakin.

Zinariya ce ta shigo tana faɗin "Surutun me nake jiyowa daga wannan ɗakin?" Shiru suka yi, ba wadda ta yi magana. "To koma me kada na sake jin bakin wata a ɗakin nan, ku kwanta ku yi bar ci" tana kai karshen maganar ta fice tare da rufo musu kofar.

Kasa kasa Aisha ta ce "Mu kwanta zuwa gobe zan karisa gaya maki me da me ake yi a cikin wannan gidan, amma fa akwai abubuwa fiye da tunanin ki" ta kai karshen maganar tare da kwanciya ta ja blanket ta rufe jikinta.

Adiva da Jehan kam sun yi sumar zaune domin abin ya wuci tunaninsu. Da kyar Adiva ta iya jan Jehan suka haye gadon Adiva suka kwanta, ita dai Jehan ta kasa barci sai tunanin take yi a kan yadda maza basa iya kula da matan su har su faɗa irin wanann abin, sannan suma maza da suke bin maza yan uwansu basa biyawa matan su buƙata har matan su faɗa irin hannun hajiyar daɗi, wannan bala'i da me ya yi kama, Hajiyar daɗi ta koyawa yara kanana lesbian a online sannan idan ta gama ta barsu ba kullun take basu abin biyar buƙata ba, dole suma su fita domin neman wasu na kusa da sun dan biyar bukatarsu, shiyasa wannan ta koyawa wannan wannan ta koyawa wannan har abin ya yi yawa, ya yaɗu sosai, wannan bala'i dayawa take Allah ka tsinewa mutane irin Hajiyar daɗi. Sai kusan asuba Jehan ta samu barci ya yi awon gaba da ita

(*Ni kuma na kwashe kayana zuwa gidan Abbi, wata kila kafin na dawo Jehan ta farka, amma me kuke tunani zai faru a gidan hajiyar daɗi? Jehan zata yarda ta zauna kuwa? Duk da ance Hajiyar daɗin ta wata irin siga take jan ra'ayin mutane, kuna ganin ra'ayin Jehan zai jawu kuwa? Tofa a wani part za'a sanya mana Jehan ɗin mu?🤔 Nayi nan sai kun zo*)


💖💖GIDAN ABBI💖💖

Aunty and Ayla, zaune suke a katafaren palon kasan na sabon gidan da suka koma, sai hira suke yi abinsu, Ayla na bata labarin abubuwan da suka rinƙa yi ita da Rimsha, sai murmushi Aunty take yi, idan ta ji wani labarin kuma sai idanuwanta sun kawo ruwa.

Sun nutsa cikin hirarsu, suna yi ne cike da girmama juna da kuma kaunar juna. Kamar daga sama su ka ga faɗowar mutun cikin palon, ba karamin tsorata suka yi ba, babu ko sallama ta shigo musu cikin palon, wani irin taku take irin na kasaitattun matan nan, babbar mace ce, jikinta na sanye da wani dankareren lace mai bala'i kyau da tsada launin pink color, hannunta da wuyarta dukka shake suke da kayan ado na gold, wato sarka da abin hannu, sai ta shin wani fitinannen kamshi turaren humra take yi, ɗinkin doguwar riga aka yi mata, irin ɗinkin manyan Hajiyoyin nan, ta yafo wani ɗan iskan karamin mayafi a kafaɗarta, ɗayar hannunta na riƙe da jaka irin suwaga bag ɗin nan mai bala'i kyau, while ɗayar hannun nata na riƙe da wayarta kirar Iphone 14, sai wani taunar chewing gum take yi, kafar ta na sanye cikin plat shoe dukka Pink color, ta sha make up kamar kamar yarinya, alhalin babbar mace ce ba karama ba, tana da matsakaicin jiki haka zalika tana da matsakaicin tsawo, farace amma ba tas sosai ba, da ka ganta kaga jinin kanuri wato barebari, tana da kyau daidai gwargwado.

A tsakiyar palon tazo ta tsaya tana karewa ko'ina na cikin palon kallo, mamakin irin dukiyar da aka narka wa palon nan take yi, tamkar bata san da su Aunty a palon ba, sai wani ɗage hanci sama take yi.

"Malama lafiya kika shigo mini gida babu ko sallama?" Cewar Aunty. Yadda kasan kurma haka wannan Hajiyar ta kasance, ba wadda ta kalla a cikinsu, bare ma har su saka ran zata amsa musu.

Ganin haka yasa Aunty ta ɗan tsorata saboda duniyar yanzu ba abin yarda bace, jikinta har ya fara kerma, da sauri ta ɗauki wayarta ta fara kiran layin Irfan, bai ɗauki wayar ba, hakan yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya domin ta samu natsuwa, saboda ta san su Irfan ɗin suna nan kenan, domin dama haka yake yi mata, in dai ta kira shi yana gida to baya ɗaukar kiran, sai dai ya baro part nasa ya zo ya ji da kunnansa kiran me take yi mashi.

Ai kuwa hakan ne ta faru, ba'a fi minti biyu da kiran da ta yi mashi ba, sai ga shi nan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

Cak ya tsaya ya kasa karisowa cikin palon, zubawa Hajiyar nan ido kawai ya yi yana kallon ta, ganin abin yake yi tamkar mafarki yake yi, ita kuwa Hajiyar har lokacin bata ɗago ido ta kalli mutun ɗaya daga cikin su ba, palon kawai take bi da kallo.

Sun jima a haka ba wanda ya yi wa ɗan uwa magana har sai da daddyn Jelly ya shigo cikin palon bakinsa ɗauke da sallama, ya zo duba Ayla ce dan tun safe yau ban sake ganin taba.

"Lafiya Irfan ka tsaya a nan baka shiga ciki ba?" Yar firgita ya yi kafin ya buɗe baki yana kokarin yin magana kenan wannan Hajiyar ta riga shi da cewa "Ba dole ya tsaya a wajen ya kasa magana ba Maik, ai kasan ya ga dodanniya ne a cikin palon shiya sanya".

Sai lokacin daddy Jelly ya kai kallonsa kanta, haka zalika sai lokacin ya san da ita a cikin palon, ɗaure fuska sosai ya yi rai a matukar ɓace ya ce "E ba shakka dole mana, ashe dodanniyar ya gani da gaske, a'a Irfan banga laifinka ba dole ka kasa shiga daga ciki, ke Hadizatu wlh idan akwai abin da ya fi dodanniya annoba to kece!!". Ya yi maganar yana kare mata kallon.

Jin abin da ya faɗa yasa ta bushe da wani irin dariyar shakiyanci, zuba mata ido kawai suka yi suna kallonta, sai da ta yi kai isarta sannan ta tsagaita tana kare musu kallo, "Wato kai AbdulMalik har yanzu baka chanza ba, to point of correction ba Hadizatu sunana ba Khadijat, ka rinƙa kara T a gaba saboda sunan ya fita sosai".

Saboda tsabar bakin ciki, daddyn jelly ji ya yi kamar ya je ya shaƙeta ta mutu kowa ya huta bala'i kawai.

"Yaya Maik wace ce wannan ɗin?" Aunty ce ta tambaya tana kare mata kallon. Satar kallon Irfan ya yi kafin ya ce "Hajizatu kenan mahaifiyar su Aafia tsohuwar matar yaya Deen..." Bata bari ya karisa ba ta ce "Kai kai kai haba Maik ya za ka ce mini tsohuwar matar Deen? To idan ma haka kake tunani tun wuri ka canza domin ni na wuci tsohuwa, ko ka mance bai sake ni bane? To idan ka mance na tuna maka, kuma nan da sati mai zuwa zan dawo ɗakin mijina, domin wannan gida gidan Khadijat ne, da ni ya dace"

(Babbar magana,😯 ɗan sanda yaga gawar soja!!)

Wani dukan uku uku Aunty ta ji gabanta ya yi, da kyar ta iya haɗiyar wani wahalallen yawu mai wuyar wucewa, nan take zufa ya fara tsastsafo mata daga gefe da gefen kunnen ta, wani irin jiri ta fara gani tare da wasu taurari masu haske suna gilma mata ta gaban idanun ta, ta kasa sake yin magana, ta yi mutuwar zaune.

Daddyn Jelly, Irfan, Ayla duk sun lura da halin da ta shiga lokacin guda, dama kuma sun san za'a yi hakan, domin ko da da Aafia kawai ka zauna ta ishela bala'i ta wannan duniya, ballantana uwarta gaba ɗaya, Hadizatu bala'i, Hadizatu gobara daga kogi kasheki sai dai lillahi, da Irfan da Umaisha duk basu son halinta ko kaɗan, duk da cewa ita Umaisha tana karama ummun tasu ta bar gidan, amma duk da haka ta san bala'i Ommun tasu, lokacin da ta bar gidan ba karamin daɗi su ka ji ba, bawai dan ba su son taba, sai dan abubuwan da take yi wa Abbi, a lokacin ba shi da kuɗi, idan ya zo fita bai bata kuɗin cefeneba ko kuma ya bata kaɗan, wuyar rigarsa take kamawa ta cima shi mutunci fes, kuma haka zata yi girki ta hana shi, wani lokaci Umaisha ke ba shi abincinta, sai dai ko ta bashi baya ci, hakan yasa ya dai'na tunanin cin abinci a gida, daddyn Jelly yasan komai da yake faruwa a lokacin, dan lokacin shima yana Kaduna bai koma Kano ba, daga baya ya koma Kanon. Wani lokaci ma har kusan faɗa suke yi da Hadizatu, bata da mutunci ko kaɗan.

Jugum-jugum suka yi dukkansu suna kallon ta, daddyn Jelly ya ce "Irfan zaka iya tafiya" ba musu Irfan ya wuce part nasa dan dama kamar a kan kaya yake tsaye, yana jin zafin ya ga ana ciwa mahaifiyarsu mutunci, amma koma me ita ta ja ma kanta.

Irfan na tafi daddy ya ce "Wlh Hajizatu, ki zo ki wuce ki fita daga gidan nan ko kuma in taka wuyarki, kuma bari kiji ko mafarki kika yi kin dawo gidan nan a matsayin matar yaya Deen, to idan kin farka kiyi sadaka, wlh baki isa ina raye ki dawo ki sake kuntatawa rayuwar ɗan uwana ba, Allah ya rufa mashi asiri ya huta da bala'in ki shine yanzu zaki ɗebo jiki ko? Dan kinga yanzu ya yi arziki, to wlh baki isa ba, dama tun farko akasi aka samu wajen haɗa jini dake, da kuma mukaddari daga Allah, to yanzu tun da Allah ya yi mun raba gari ki yi maza ki kama kanki, ko yaya Deen bai sake ki ba ni na sake ki saki uku a madadin shi" ya kai karshen maganar yana yiwa Ayla alama da hannu a kan ta tashi ta shiga ɗaki. Ba musu ta miƙe ta haye sama.

Takowa Ommu ta yi, irin takun nan na nuna isa, har gaban shi ta zo ta tsaya, from head to toe ta kare masa kallo sannan ta ce.......✍️

Sai mun haɗu ranar Monday idan mai dukka ya kai mu dan mu ji me Ommu za ta ce wa daddy...

💖💖TRIPLET'S💖💖


E41-42


Takowa Ommu ta yi, irin takun nan na nuna isa, har gaban shi ta zo ta tsaya, from head to toe ta kare masa kallo sannan ta ce "Kayi kaɗan Maik, kuma ka kwana da shiri kamar yadda na gaya maka, next week ina nan dawowa, domin wannan gidan gidan Khadijat ce" ta kai karshen maganar tare da fice daga cikin palon fuuu kamar kumfa.

Dawo da kallonsa kan Aunty da ta yi mutuwar zaune ya yi "Ki yi hakuri Sadiya, kuma kada ki ɗauki zancen nan nata kin ji?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi alamar ta ji, amma cikin zuciyarta ita kaɗai ta san me take ji. Karisowa cikin palon ya yi, ya zauna saman sofa yana faɗin "A kira mini babyn daddy mu ɗan yi hira".

Murmushi Aunty ta yi tana faɗin "Yaya Maik ko dai za mu aura maka ita ne? Dan ka fita daga cikin wannan gwabrancin na shekara da shekarun, Wlh tana da hankali sosai". Dariya ma abin ya bashi, abu kamar wasan yara, cikin raha da wasa ya ce "To ai dama aurentan zan yi, kinga idan Allah ya yi muka gane Jelly sai na haɗa su na riƙe su sanya mini hawan jini da ciwon zuciya na mutu da wuri ku huta". Yar dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Kai yaya Maik yanzu me jalila take yi maka da za ta iya sanya maka hawan jini? Sannan ita ma Ayla banga wata matsalar a tattare da ita ba" "Ke dama ta ina zaki ga matsalarsu, ai ina rokar Allah ya sanya a gane Jelly, zan baki ita na kwana biyu, ina ga ko kwana ɗaya ma ba zata yi ba, zaki dawo mini da aba ta" kara faɗa murmushinta tayi tana kwalawa mai aikinta kira.

Da sauri yarinyar ta zo tana faɗin gata nan, umarni ta bata a kan ta kira mata Ayla, to ta amsa da shi, sannan ta tashi ta haye sama.

"Yaya Maik ni fa ba zan taɓa gajiya da Jelly ba, ni ban ma san me ta ke aikatawa da kake cewa babu mai iya ta ba sai kai ba, ban taɓa zama da ita ba, amma ina ji a jikina tana da kirki da hankali sosai" jinjina kai ya yi irin alamar abarkaza cikin gashin ta, sannan ya ce "Ai ni yanzu ma ina tausayawa duk wayanda Jelly ke hannunsu, addu'a nake yi Allah ya dawo mini da abata lafiya" Amin ta amsa da shi, sannan ita ma ta kara mashi da nata addu'ar.

Tun daga Ayla ta sako kafarta a sama benen daddyn Jelly ya tsareta da wayannan dara-daran idanun nasa irin na Jellynsa, sai kallonsu Aunty take yi tana murmushi.

Kusa da shi ta zo ta zauna dan yanzu sun saba, gaishe shi ta fara yi sannan ta tambaye shi batun school, dan ya ce Irfan ya sanya ta makaranta, tana son yin karatu sosai.

Sai kallonta yake yi ya ce "Sarkin son karatu ba, to yaya Irfan ɗin naki ya gama komai, saura mu jira narar Monday kawai ta yi" kayatatcen murmushi ne ya bayyana a kan fuskarta, sannan ta sanya hannu ta rufe fuskarta. "To jeki ki shirya mu je shopping a sayi wasu abubuwan buƙata na school dana gida". Da sauri ta miƙe tana faɗin "to daddy".

Binta da ido ya yi har ta kurewa ganinsa, sannan ya dawo da kallonsa kan Aunty dake ta kallonsu tana murmushi.

"Kina bukatar wani abin ne idan muka je shopping ɗin Sadiya?" Ya tambaya yana ƙoƙarin miƙewa. Cikin sauri ta ce "Yaya Maik zauna mu yi magana", ba musu ya koma ya zauna yana kallon Tv dake magana kasa kasa, dan shi dama idan ba dole bama baya son shigowa part ɗin Abbi, sai dan ya zamar mashi dole, haka idan ya shigo ko ɗaga ido baya yi ya kalli Aunty har sai idan bisa kuskure, ko zai kalli wani abin, kallonsa ya faɗa kanta.

"Yaya Maik wlh Allah kana son Ayla, me yasa kake ɓoye mana?" Wani irin murmushi ya yi wadda take fita da ɗan sauti kamar dariya. "Yanzu Sadiya ni na ce maki ina son Ayla? Me yasa kike haɗa ni da yar cikina ne? Kawai wlh tausayin ta nake da kuma kaunarta kamar yadda nake son Jelly, sannan kuma tana da hankali sosai, ga son karatu shiyasa nake jin ta a rai na, kuma nake son ganin ta kusa da ni tana farinciki, daɗin daɗawa kuma, ita marainiya ce a halin yanzu".

Ita ma Aunty kara faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce "Yaya Maik wlh ba iya kaunar uba da ƴa kake yi wa Ayla ba, wlh kana son ta, so na soyayyar miji da mata, kai ne dai ba zaka yarda ba, amma tun jiya na fahimci hakan".

"Sadiya baki son zaman lafiya na lura" ya kai karshen maganar yana miƙewa, "Yaya Maik cewa fa na yi ka zauna muyi magana, to ai bamu kammala maganar ba, ina kuma zaka je?". Ba musu ya koma ya zauna yana faɗin "To maganar taki ce na lura kwata-kwata bana tsayawa a saurara bane, saboda zancen naki bai ɗauki hanyar da hankali zai kama ba".

Aunty zata yi magana Ayla ta sauƙo kasa, jikinta na sanye da hijabinta har kasa, wadda Ahmad ya saya mata, zuba mashi ido Aunty ta yi tana kallon yadda yake kallon Ayla, a cikin zuciyarta tana faɗin "Wlh yaya Maik ko kana so ko baka so ka kamu da son yarinyar nan, garama ka yi sauri ka auri abarka tun kafin arigaka, gamu da matasa a gida, suma kuma suna zuwa da abokan su, kana yin sake wani zanyi wuff da wannan santaleliyar yarinyar, ka dawo kana gwara kai da bango kana dana sani".

Kusa da shi Ayla ta sake dawowa ta zauna tana faɗin "Daddy na gama shi" ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya ce "Waye ya ce maki ki sanya perfume a jikin ki?" Kasa ta yi da kanta, cikin girmamawa ta ce "Kayi hakuri daddy".

Kara ɗaure fuska ya yi ya ce "A'a ba zan hakura ɗin ba, koma ki canza kayan kisa wasu wadda ba perfume sai ki zo mu tafi". To ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe ta koma sama, Aunty dai tana ganin ikon Allah kishi karara daddyn Jelly yake nunawa a fili amma sai ya ce ba son Ayla yake yi ba tausayinta yake yi, ina aka taɓa yin hakan?.

Shiru suka zauna har Ayla ta canza kaya ta dawo. Miƙewa ya yi, ya yi gaba ta bi bayansa tana yi wa Aunty sallama. Fatan alkhari aunty ta yi musu a bayyane, daga ta ciki kuma ta yi musu fatan Allah yasa kafin su dawo sun kullu soyayya, dan tana bala'in son daddyn Jelly ya auri Ayla, ta san idan ya aureta zata samu farinciki fiye da tunanin mai tunani, mutumin kirkine sosai daddy, ga son mutane, sannan ya iya aikin komai na gida, yana da kula da yan uwansa ma bare kuma matansa, ga riƙo da addini, ya san darajar mace, ta ko'ina ya haɗa, idan Ayla ta same shi zata fita daga wannan kukan maraicin nata da take yi.

Haka Aunty ta zauna tana ta tunane tunane. Su Ayla kuma sun wuce shopping. Ni kuma na tattara kayana na wuce izuwa Washington DC dan jin wace waina ake toyawa.


💖💖Washington DC💖💖

Misalin karfe 8 na dare, Musharraf na kwance saman bed nasa, shi kaɗai a ɗakin, shi kuma Michael ya fita palon kasa. Kamar a mafarki ya rinƙa jiyo motsi kamar na mutun, idan ya tashi ya duba kuma, sai ya ga wayam ba bu komai, wani lokaci ma inuwar abu yake gani kamar mutun kamar wata halittar da ban, ta bakin kofa, amma idan ya tashi zai duba sai inuwar ta ɓace, abin har ya fara bashi ɗan tsoro-tsoro, tunani ya fara yi a kan mafarke mafarken Michael da ya rinƙa yi daren jiya, abin ya fara ɗaure mashi kai, shin meke faruwa acikin wannan gidan ne? Ya faɗa a cikin zuciyarsa.

Kamar a mafarki ya ji an kara masa karfin gudun Ac ɗakin, cikin sauri ya miƙe yana kallon yadda Ac ke gudu, ɗaukar remote ya yi ya rage gudun.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login